KALBIM BOOK 1 BY MAMUHGEE

KALBIM BOOK 1 PAGE 6

6
*ZUZEAMVENTURES*
08144015291
Aslm barkanmu da wannan lokaci
Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi
Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin mata
Maganin sa ni’ima da dandano
Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291
Idan maganin mata kikeso akwai
Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah
Bononza Bononza Tsimin mangoro 1k Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500
Garin bata gaban kishiya 500
Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500
Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500
Za a bakisu akan 3800
Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k
️️️️️️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 Infection ruwan tsarki 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki

 

************
Malam AYOUB LIMBA ma’aikacin wata maaikatar qera robobi ne dayakeda gaskia da amana tareda kwarjini da farin jini sosai ga duk wanda yayi hulda dashi sbd gaskiyansa da hakurinsa tareda sanyin halinsa.

Ayoub baida uwa a cikin matan babansa ya taso sbd tasa uwar ta rasu tin yana qarami,

Cikin azabar yan ubanci data matar mahaifinsa ya taso babu sauki ko sassauci a halinda ya taso cikinsa a gidan mahaifinsa gashi mahaifin nasu bame zama bane yawon nema yake zuwa,

Azaba da ukubar gidan ya sakasa zamowa me zafin nema da kokarin aiki wanda ya saka ya fara banbanta da yaran gidan sbd yanada ‘da’a kokarin bin na gaba,

A cikin masu aikin me gari ya samu ya shiga suna zuwa kauyuka cin kasuwa suna siyar masa da hatsi da albarkatun gona sukan yi kwana biyu basu dawo ba.

Tin ana ganinsa yaro shekarunsa basu kai ba har kokarinsa ya kwacesa ya zama sharp yana iya huldodi sosai wanda ya saka ya samu matsayi me tsafta a zuciyar me gari daga nan ya hadasa da wasu mutanensa dake wani kauye masu zuwa birni suka fara zuwa dashi,
Cikin kankanin lokaci acan ma ya samu mutane masu kaunarsa ya bar kauyen kwata kwata sedai yazo ganin gida Allah ya fara rufa masa asiri.

A wannan lokacin da Megari yake tamkar mahaifinsa sbd kauna da kuma juya masa dukiyar dayake yi a can birin sbd shekarunsa sunja sosai ya zama matashi me gaskia da amana kwatsam Allah ya karbi ran maigari wanda hakan ya saka kaf yan kauyen masu hassadarsa suka taso suka zuga iyalan megarin suka kwace komai nasu tas basu bar masa komai ba.

A cikin gidansu kaf daga yan uwansa har matan babansa harma maqota hassadarsa sukeyi dama matasan kauyen kaf sbd babu wanda ya taba fita birni nema a tarihin kauyen sai shi ya shiga cikin masu arziki harma da dan karatunsa ya koyo dan haka tsanarsa suke ji sosai da baqin cikinsa sbd babu me abinyi a cikinsu
Gashi ko gona babansu baida bare suyi noma daga me saida rake sai me saida itace da dadai sauran irinsu da baa wani samun komai.

Rasuwar me gari da wata hudu nasu mahaifin ya rasu dan abinda ya bari wanda duka idan aka hada bazaa samu dubu dari ba aka tattara aka raba aka bawa kowa ya tattara yabar kauyen.

Watansa biyar da tafiya ya samu aiki a wani kamfanin qera roba wanda gurin qerawan yake wajen birni sosai harya zo kusa da kauyensu sosai dan haka sai hakan yai masa dadi dan babu jimawa ya fara gini a kauyen da dan qaramin filin daya siya.

Aikinsa yana rufa masa asiri sosai dan abinda yake samu din yanayi ba laifi hakama shi kadaine dan kauyen a cikin kaf ma’aikatan gurin dan haka shine kusa yakeda sani sosai a bangaren dan haka kowa ya tashi neman abu shi ake nema.

Hakurinsa da kwantar da kansa tareda rashin rawar kai ya saka yayi farin jini sosai da suna a gurin,

Sabuwar hassada ce da baqin ciki ta sako yan kauyen da yan uwansa gaba daya suka fara kokarin ganin sun masa baqin ciki amma bai taba damuwa kuma yana taimaka musu sosai.

A maaikatar yake kwana amma yana gama gininsa na qasa ya dawo gidansa daga nan yake zuwa aikinsa kullum akan kekensa sabuwa dal daya siya.

Gama gidansa da wata uku ya hadu da Fatima da sakina qawayen da suka taso tare tin yarinta baa kauyensu suke ba kauyen kusa dasu,

Fatima a hannun kawunta take sbd itama marainiya ce dan haka kawun na ganin Ayoub nada abin lasawa tini ya basa aurenta ba bata lokaci akai auren bayan tabarma da buta sai setin kayan cin abinci na silver babu abinda ya siya mata ya tattara aka kaita sedai daga baya ayoub ya siya musu katuwar katifa da abubuwan buqatarsu suka gyara gidansu.

Zuwan sakina gurin fatima kauyen Allah ya hadata da baba ila shima ya aurota suka dawo zama kauye daya.

Baba ila kwata kwata baya kaunar Ayoub dan yana cikin yan hassadarsa dan haka ya fara shiga tsakanin Amintar Sakina da fatima duk da sam sakina bata yadda da hakan ba saida fatima taga hakan zai fara kawo matsala a auren sakinar se ta dan ringa janyewa sbd a zauna lafiya.

Shekara daya da auren cif Fatima ta haifi Namiji wanda Ayoub ya sakawa sunan Maigari wato ABDULAZIZ AYOUB LIMBA.

Abdul ya taso mahaifinsa da ummansa suna tsananin sonsa da kaunarsa cikeda gata da kulawa musamman da mahaifinsa ya kasance masu dan karfi a kauyen,

Ayoub baya barin Abdul fita waje wasa ko yawo kaman yanda yaran kauye sukeyi hakama sitiran sakawansa da cimarsu ma daban take me tsafta da wadata,
Ayoub ya killace iyalinsa sam baya barinsu shiga mutane sosai sbd yasan baa kaunarsu a kauyen dan haka zaa iya cutatar dasu dan haka ko fatima bada kowa take hulda ba bayan danginsa wainda itama suka tsaneta da ‘danta amma duk da hakan tana dan mu’amalantarsu.

Abdul yana kaiwa shekarun fara karatu Ayoub ya sakasa primary school dake can local government kullum yana kaisa da keke ya daukosa idan antashi.

Fara karatun Abdul ya sake banbantasa da yaran kauyen gashi ya taso baa wani shiga mutane dashi sai ya kasance baida iya muaamala da mutane,
Gurin aikin babansa ne kadai yake sakewa yayi wasa sbd acan suna sonsa kasancewansa fari sosai Kyakkyawa sbd daga babansa har ummansa farare ne tas.

Abdul ya dauko farin jinin babansa da kwarjini tin yana yaro duk inda akaje dashi idan ba kauyensu ba da bazasu taba sonsu ba sansa akeyi sosai.

Abdul nada shekara goma sha uku ya zama wani irin nitsatsen yaro mai daukan ido da nutsuwan data kere ta masu shekarunsa wanda asalin miskilanci ne daya taso a cikinsa na tasowa kai daya ba abokin wasa sai iyayensa yai masa yawa gashi lokacin ilimin boko da addini duk babansa ya tsaya akai yana basa.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected