KALBIM BOOK 1 BY MAMUHGEE

KALBIM BOOK 1 PAGE 7

Mama sakina ma bata cikin walwalan kwata kwata sbd ganin halinda suke ciki dan haka bayan yan garinsu sun koma itama ta koma gida sedai duk bayan kwana daya sai tazo ta dubasu.

Kawun fatiman da zai tafi ganinsu da abinci sosai baiji tausayi ko kunya ba ya diba abincin sosai ta tafiyarsa.

Yan uwan ayoub din ma da sukaga hakan suma suka taho suka debi abincin me yawa sosai da cewa ai suma sunada gadon Ayoub dan haka tinda baibai komaiba a basu abincin.

Abdul ne rayuwarsa tafara sauyawa sbd karatunsa daya fara rawa sbd kulawa da mahifiyarsa wadda ta kasa dangana da rashin baban dan haka lafiya kwata kwata tafara kaurace mata,

Ta rame ta koma kamar wadda bata taba lafiyaba rayuwarta,
Bata wani ci bata wani sha bata cewa komai sai dole ga cikinta yanata girma dan haka komai a gidan shine yakeyi masu,

Shine yake musu wanki,ya dafa musu abinci,ya kai mata ruwan wanka yayi shara ya nemo,ya kuma tafi makaranta,sannan ya zauna yasha kuka a duk lokacinda ta kasa riqe abinda takeji tafara kuka haka yake yi a tareda ita,idan ciwo ya taso mata ma shine me zaunawa ya kula da ita ba magana haka zatai ta warke sbd basuda komai.

Ahankali baba ila ya gaji ya hana sakina zuwa gidan kaman yanda ta saba dan haka duk abinda suke buqata sedai Abdul din yake ya karbo musu dan abincin da zasu ci da wasu abubuwan kaman sabulun wanka ko omon wanki.

Hakan ma baba ila ganin yayi kaman zaa karya tattalin arzikin gidansa duk da na sakinar ne take basu dan haka ya haukace musu yace ya hana,

Ahankali rayuwa tafara yi musu tsananin gaske sbd komai basuda shi basuda me basu basuda hanyar samu,

Umma ta koma masa kamar me tabin hankali yau lafiya gobe ciwo kwata kwata batada sauran lafiyar ma da zata san tawakkali da dangana bare tasan itace ya kamata ta dauki juriya ta kula da Abdul ta tsaya masa sedai shine ya koma ya tsaya akanta.

Tsana me tsananin gaske Baba ila da yan gidansu Ayoub sukai masa sbd yanda tin yan yaro ya tsayu kan uwarsa gashi yai neman taimakon a gurinsu amma sun bayyanar masa da tsanar da sukaiwa mahaifinsa a fili dan haka sai yaji yafisu jin tsanarsu me tsananin gaske dan haka bai sake ko bi ta hanyar kofar gidansu ba Dan yafison mutuwa ta daukesa kaman yanda ta dauko babansa daya sake zuwa gurinsu.

Baba ila kuwa sbd tsananin kaunar datake tsakaninsu da mama sakina dayake jinta kaman ummansa data haifesa yasa yake danne ciwo da radadin tsanar da yayi musu sbd mama sakina ta tabbatar masa har abada kada yace zai rabu da ita sbd itama uwarsa ce ko fatima na raye ko bata raye.

Rayuwa tafara yiwa mama sakina tsanani itama sbd baba ila daya dena bata komai sbd kada ta taimaka musu daman matansa da yayansa kwata kwata basa kaunarta,
Abincin da zata ci kansa ankoma a gidan a qaramar roba ake bata shi wanda ita kanta baya isarta amma a hakan wata ran take juyewa a leda ta bawa Abdul din ya kaiwa fatima wadda da kansa yake bata itama bata wani ci kadan take ci sbd yanayinta.

A haka ya dage yana karatunsa duk da wata rana yaje ne wata ran baya zuwa amma a hakan yana kokari sosai
Suma malamansa da suka gaji da dukansa aka fahimci tsananin rayuwar dayake ciki sai aka dena dukansa aka barsa a hakan idan yazo shikenan idan baizo ba shikenan.

Mama sakina ta koma sabulun da zatai wankan ita kanta batada shi batada ko man shafawa masifar rayuwa tafara sakota gaba dan haka Abdul din daya fahimci hakan saiya rage zuwa kwata kwata gurinta yafara aikin wahala da wanda zai iya da wanda bazai iyaba haryafara sabawa idan ya samo yana dan siya musu harma da ita mama sakinan yana bata omo ko wani abin idan ya siya musu.

Sun wayo gari sitirar sakawa tai musu wuya daga shi har ummansa sbd sata da aka ringa sakasu gaba da ita saida suka rasa komai a gidan bayan tabarma data mutu sai karamar katifar da itama ta mutu sai kuwa buta daya da bokitin wanka da tukunya shi kadai suka rage musu.

Cikin ummansa ya tsufa harya wuce lokacin haihuwa a lokacin ne katangar gidan ruwa ya zubar musu da ita aka sace duk kwanon langa langar gidan da sauran abubuwan dan haka suke a rabe a gefe cikin gidan wanda har dakin da suke ruwa yake daga saman sbd har saman anhau an sace langalanga kadan aka bar musu dan haka idan ana ruwa suna gefe dan ruwan yana dan shigowa kadan kadan ta sama.
#MAMUH
#BESTLOVE
#BESTROMANCE
#HOT
#STRUGGLE
#BILLIONAIRES WAR
#AY LIMBA

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899*_Arewabooks@Mamuhgee_*

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected