Tantiriya a Gidan Yari Book 2 Page 26-30
Haidar yace Innalillahi shike nan Annoor da Iman sun ja mana abin kunya a family,dama ni wlh naga rashin dacewa kusancinsu yayi yawa,Annoor yace da nayi me? ubanka nayi mata,Nabeel yace Uhmm Dan Allah ayi mana bayani Annoor ya jawo mana,Rahma tace an barmu a duhu,Iman kuka take Wiwi ta cika palon shi yasa aka yi zargin Annoor ne ya mata wani Abu shima gashi ransa a bace,tace cikin kuka wlh indai har uwata karuwanci tayi nima sai nayi….yiiiiihihihiiii ….Annoor ne ya gwada yanda Iman tayi yace nima hakaaaaakakakaaaaa……ke dalla rufe mana baki tun yaushe kika yi karuwancin kin dame mu,ki barmu Muji da abinda ya damemu,Kai Haidar ba Kawu ne Baban mu ba dukka mu Tara yaran Shegu ne ba Yan sunna ba,ma’ana Yan gaba da fatiha,Rahma tace na’am?????…..Iman da kuka tace Eiiiiiiiiii……Kuma ma an saki Aunty Na’ima…..sabo da itace ta fadaaaahhhhhhh….taci gaba da kuka.
Nabeela tace Innalillahi wayyoooo ubana ya cuceni ya saka Aliyarsa ba a muhallinta ba aka sameni,Nabeel akwai rago bashi da juriya kamar mace ya dinga hawaye,Haidar yace kaji dadi ma Kai kayi kukan ni da zanyi kukan ma da naji sauki,Sajid yace Allah ya rufa min asiri nayi aure ba a sani ba lokacin,da dangin matar sun sani bazan auru ba, Karima da Laila suka ce wlh Allah ya tsallakar damu har da yaran mu mun Haifa.
Jauro yace hmm kowa ya nutsu na baku tarihinku tunda duk nasan cikinku Kun San Iyayenku mata amma Baku San mazan ba Kuma Alhmdllh dukkanku nasan Iyayenku Maza nasan Inda suke Baban Annoor ne kadai sai dai Mamanka ta fada Maka tasan Inda yake ita yanzu.
Abba yace Dan Allah ku nutsu ke Iman zan karyaki idan baki daina mana kuka ba,Annoor ya jawo Iman Jikinsa zo ..Abba ya daka Masa tsawa saketa dan ubanka ba muharramarka bace,ke ma Habiba kina da laifi wlh baki iya tarbiyya ba ace a gabanki yara suna haka kina gani sabo da ba naki bane.
Jauro ne ya dakatar da Abba yace karka yiwa Habiba haka bani da kamarta suma basu da kamarta itace duk taci Kashi da fitsarinsu har suka kawo haka,Habiba tana da Sanyi bata da zafi bata iya fada ba shi yasa take kyale su in tace su bari sai dai tace Allah ya shirya haka take Kuma Allah ya shirya tunda aka tsaya a iya haka.
Abba yace madalla ayi a Fadi gaskiya ni Ina sauraro,Jauro yace ah ko Kaine dai aka sameka ta haka ai iya damuwar da zaka yi kenan, Hashimu ka isheni fa,wai sanda na samo su kana nan ne,Abba yace yanzu mun hadu Ina nan kayi bayani sauri muke,nazo gidan Nan a sa’a yau Inama ma sunana Sa’adu sabo da Sa’a ta.
Jauro yace Kun riga Kun san sunana Kun San asalina da iyayena,muna zuwa kauye da ku,amma zaku ga tunda kuka fara wayo ban sake kaiku kauye ba,nayi hakane sabo da gudun kar Yan uwana ko wasu a gari su fada muku ko ayi muku gori,shi yasa tun Kuna yara rabon da ace kunje kauye ku mazan kenan matan ma basu taba zuwa ba dan ban bari sunje ba,kunyi kunyi har kuka hakura,sannan ko mazan ma bana yarda su kwana tare muke zuwa mu dawo tare,haka a kauyen ma bana bari su fita ko kafar gida daga gida sai mota duk ba komai bane sai wannan dalilin.
Sannan zaku ga bama zama a gari daya, Kun sani farko a Katsina muka zauna,muka koma Jibgawa,na dawo da ku Minna yanzu muka dawo Kano,bana so a San wani Abu a gari bare ma Yan unguwa suyi muku gori shi yasa ban bari mun ta zama a wajen Daya ba tunda Kun sani Allah ya azurtani Kuma Kuma kowa na bashi Ilimi boko Dana addini sannan Kuna da aikin yi ai Alhmdllh.
Farko gata Ummin ku Habiba ita na fara aure Kun sani tunda na aureta ban taba haihuwa ba gashi Allah ya sa min masifar son yara,Ina so ace yau ga wannan a karkashi na suke amma Allah bai bani ba,dangina kaf sun tsani Habiba akan cewar itace juya Bata haihuwa,ba zagi da wulakancin da basu yiwa Habiba ba tun Ina kauye lokacin bani da kudi har Allah ya azurtani na dawo da ita birni.
Iyayena sun tsani Habiba har cewa suke lallai sai na saketa ko na Kara aure,Hakan yasa tace na rufa mata asiri na Kara auren kawai ko ta huta da gori,ana haka na auri matata ta biyu,itama shuru shuru bata haihu ba tace baza ta zauna ba haka na sallameta, tana tafiya ta auri wani ta samu ciki ta haihu yanzu yaranta shida Kunga ya tabbata daga ni ne rashin Haihuwa,haka na sake auren wata itama ta dinga yi min wulakanci iri iri ko Shekara bata yi ba na saketa taje ta auri wani itama tana nan da yaranta yanzu ta haihu.
Na sake auren wata wannan kuwa kullum a zagina take juya marar haihuwa,taimakonka nayi Dana aureka,babu masifa kamar ace mace ta dinga ganin dan ta auri mijinta ma taimakonsa tayi ya shiga uku,ta zageni babu irin cin mutuncin da bata min ba,rabuwar mu da ita shine zagin Habiba da tayi,babu wacce ta isa na aureta ta zagi Habiba na kyaleta,sabo da Habiba nayi nayi akan ta amince na saketa taje ta auri wani ta haihu taki yarda,tace tsakani da Allah take so na, rashin Haihuwa bazai sa ta juya min baya ba,Habiba matar rufin asiri ce,ta karbeni a duk yanayin da nake ciki,talauci,arziki ga rashin Haihuwa duk tana zaune dani,sannan na Tara mata yara ta rike min Kuma bata taba musu kallon banza ba bare gori,ta rike kowa kamar ita ta haife shi.
Abba yace Dan Allah tsaya Jauro bakina Yana kaikayi,Jauro yace Ina ji sarkin shishigi,Abba yace Kuma duk Habiba adalcin da ta Maka baka hakura da yi mata kishiya ba ka Kara auren Na’ima? Allah ya rubuta min ya zanyi,Kuma idan namiji ya Saba da mata biyu baya iya hakura,idan Allah yayi zan Kara idan Allah baiyi ba Habiba for ever Habiba for life inji bature,Habiba harda Jin dadi ta gyara zamanta.
Jauro yace lokacin da na bar kauye na koma katsina muna zaune akwai wata yarinya me suna Asiya a makwaftanmu,tana yawan zuwa gidana jininsu ya hadu da Habiba,kullum in ta dawo daga tallan gyada to tana gidana,Iyayen Asiya wasu masu mugun son Abin duniya ne duk da basu da kudi amma wai Asiya da tallan gyada zata ciyar da su,gyadar da gaba daya bata fita dubu daya ba a lokacin wai da gyada zasu ci su Sha,Kuskuren iyaye kenan wasu,Babar Asiya a lokacin tace indai Asiya Bata yi tallan gyada ba to baza ta samu kayan daki ba idan aurenta yazo,sannan bata kauna Asiya ta dawo mata da gyada ba tare da ta siyar da ita ba.
Asiya suka takurawa da uban tallan gyada ba dare ba rana,daga nan Kuma suka koma yi mata funkaso da Miya tana kaiwa tasha,to Kun San dai Tasha tana da shugaban ko,to shugaban tasha a katsina wani me Suna Zubairu Dan yayi shi yaga Asiya yace yana sonta,Asiya yarinyar kirki ce wlh me addini da hankali,ta fada son Sarkin Tasha Zubairu Danyayi,shima da gaske aurenta zaiyi suna soyayyar su me tsafta,to gaskiya Zubairu Dan shaye shaye ne shi sosai, sai iyayen Asiya suka ce Sam baza su bashi yarsu ba,har yayi alkawarin in ta aure shi zai daina shaye shaye sabo da son da yakewa Asiya,amma suka ki yarda,Asiya tayi kuka sosai,Baban Asiya sai ya samo mata wani Dattijon mutum tsoho zai mata auren dole,Zubairu Dan yayi sai ya sace Asiya suka gudu,sai bayan watanni biyar Asiya ta dawo gida da ciki kato.
Babanta suka mata dukan tsiya suna tambaya waye ya yi mata ? tace gida ,zubairu ya kama musu a Zaria suka zauna abinsu,tace wallahi Kuma akasi aka samu sau uku kacal ya taba amfani da ita duk wannan watanni da suka kwashe,Kuma duk da tana da cikin itace ta gudo amma Zubairu Yana son abarsa.
Ya dawo Yace ai Yana sani suka yi haka so suke dole sai an bashi Asiya,Asiya tace nice nan nace yayi min ciki idan aka ganni da ciki dole a daura mana aure, shi kuwa Zubairu ya Shole abinsa,ni kuwa lokacin naji labarin Asiya,iyayenta sun koreta,ni da Habiba muka fita neman Asiya muka sameta a kasuwa take kwana tana tashi ga ciki,ta bani tausayi ace ga ciki mace ta dinga kwana a rumfar kasuwa kamar mahaukaciya sai na dakko Asiya na dawo da ita gidana,tayi zamanta muna kula da ita,Bata da matsalar ci da Sha da sutura har tazo haihuwa na kaita asibiti ta haifo Danta namiji santalele.
Na Nemo Zubairu yazo ya dauki dansa yayi Masa Addua Yana ta kuka sosai,a wajen nace Dan Allah ni idan ta yaye Dan Ina so,Asiya da sauri tace mun bar Maka sabo da suna gudun abin kunya.


