Tantiriya a Gidan Yari Book 2 Page 26-30
A nan dai ranar suna yaro yaci Suna Sajid na yanka raguna har biyu,duk wani kayan barka na jariri nayi,muna zaune abinmu da Asiya,lokacin na samu iyayenta suka yafe mata sannan suka amince zasu aurawa Zubairu ita,bayan ta yaye jariri aka daura mata aure da Danyayin ta,ya gina musu gida me kyau aka Kai Masa Amarya Kuma a dalilinta wallahi ya daina shaye shaye ya shiryu suna zaman su lafiya da yaransu uku Yasmin,Mufeed da Aryan sai kai Sajid babba,Na sha kaika Kuma kana zuwa da kanka amma tunaninka Zubairu ba mahaifinka bane kawai na auri Asiya na saketa Zubairu ya aura, to kaji daga yau Zubairu shine mahaifinka,Kuma Ina so ka sani kaddara ce babu ta Inda bata zuwarwa mutum,Dan Adam bashi da wayo ko dabara,Iyayenka sunyi kuskure na biyewa son zuciya,Asiya kuruciya da giyar so ce ta kwashe ta,Zubairu Kuma yayi ganganci ya biyewa zuciya,wannan ba wani Abu bane akwai ciwo dole amma ai baza ka kashe kanka ba,ka fawwalawa Allah.
Daga Kai sai Sajid ana yayeka sai Nabeel,watarana akan harkar sufuri na naje Jigawa birnin kudu,Ina mota Ina tafiya wata yarinya budurwa tana ta gudu a titi da sassafe fara ce tas Yar Fulani jikinta furu furu,tana ihu tana a taimaketa da sauri na tsaya tazo ta fada motata tana haki lokacin ban tambayeta komai ba sai da ta huta sannan nayi parking nace wacece ke? tace sunanta Sa’ade ita Yar asalin jigawa ce Birnin kudu,marainiya ce iyayenta sun rasu a hannun kanin Ubanta take,tace wani ne yake sonta sunansa Suffiyan akan bata sonsa ya saceta ya boyeta a wani gida a jigawa dutse kwananta ashirin kullum sai yayi amfani da ita har Allah yasa yau ya manta kofa a bude ta fito ta gudo shine tace na taimaka mata,har gidansu na mayar da ita,amma a lokacin Dake Suffiyan me kudi ne Wanda ke rike Sa’ade kanin Ubanta sai yace karya take yi ya zaneta yace karuwanci ta tafi dama,ai shi dama Suffiyan ya fada Masa tana zuwa gidansa,bayan na tafi da wata biyu ciki ya bayyana a Jikin Sa’ade,Kanin Ubanta yace karya take Suffiyan bazai lalata ta ba,shi da matarsa suka dinga gana mata azaba har watarana lokacin cikin ya gima ta kusa haihuwa naje garin na nemi gidan su Sa’ade,Ina zuwa naga ana dukanta ga tsohon ciki tana ta kuka na karasa nace cikina nane ni nayi cikin Ina son abina,ita kanta tayi mamaki amma na dage nace cikina nane,a garin sai da aka cika ana kallona ana tsine min,Kanin Ubanta yace to wallahi sai an daura min aure da ita,akace haramun ne aure da ciki nace ba komai a daura
Na bada sadaki aka daura na taho da ita gida,tun a mota na saketa nace ba aure tsakaninmu,itama taji dadi.
Haka na kawota itama suka zauna tare da Habiba ta kula da ita har ta haifo Danta santalele kyakyawa gashi nan ranar suna na yanka Masa rago, na rada Masa Nabeel,kayi hakuri Nabeela kai rago daya na yanka Maka.
Haka na dinga sintiri da Sa’ade muna neman Suffiyan Wanda ya mata ciki Allah ya taimake mu muka same shi kuma Nabeel sak mahaifinka kayi a kamanni kyakyawa ne amma sai ka dakko Dan hasken mamanka ka sirka da duhun ubanka sai ka zama ruwa biyu ga ka nan rass da Kai,Kuma Alhmdllh da muka je ya karba domin lokacin yayi nadamar Halayensa ya nemi yafiyar Sa’ade ta yafe Masa,haka kanin Ubanta suka daidaita ya gane gaskiya na maidata gida,cikin ikon Allah ta samu miji na gari me kudi ya aureta a ta biyu a Nan Jigawa kaima ka Santa Nabeel kana zuwa kaji asalinka,tana da yara shida yanzu da Mijinta,Kuma itama ni na mata kayan daki da komai,babanka yanzu ban San me yake ciki ba amma dai nasan ita mahaifiyarka ta sani tunda ta fada min.
Sai ke Laila Mahaifiyarki Zahrau,yaren Edo state ce,ba musulma bace a lokacin tayi aure a Lagos Bata taba haihuwa ba,kasuwanci ya kawo mijinta Arewa Kano,ya Dade a Kano katsam sai ta musulunta wannan yasa ya mata duka ya saketa,ya fadawa iyayenta suma suka ce basu ba ita kar ta dawo wajen su,akwai wani malami babba Malam Yusuf a unguwar da suke shine ya musuluntar da ita,bayan abinda mijinta yayi mata sai ta koma ta fadawa Malamin,ya lallasheta yace ta dawo gidansa ta zauna,haka ta koma can da zama sun Saba da matansa,tana sha’awar namiji amma kowa a musulmanmu sunki aurenta da ta samu saurayi sai iyayen saurayin su hanashi aurenta suce ai Tubabbiya ce sabon musulunta ce,kowa ai ta cewa Tubabbiya ce ana kyararta ana ganin ma kamar ba wani addini take ba,to yare sun Saba da saka kaya damammu,tana yin shigar da taga dama Malamin ya koma sha’awarta sabo da rashin Imani ya fara nemanta har ya dirka mata ciki,Kuma bayan zance ya fito yace karya take,naje unguwar lokacin wani uzuri ya kaini na harkar siyar da mota naji matasa suna labarin ance Malamin ma yace korarta zaiyi,Ni Kuma sai ta bani tausayi
Naje nan ma nayi
shishishigi nace cikina nane,dama Malam Yusuf mufita yake nema sai ya kebe dani gefe yace na aureta,yasan fa haramun ne amma ya aikata nace bazan aureta ba ya nace, to ni ba wani jajirtacce ba kawai nace a daura Allah ya yafe min,aka daura aure na tafi da ita gidana,Satin latifa biyu na saketa Kuma ban taba ma shiga dakinta ba,bayan ta haihu ta zabi suna da kanta aka sa miki Laila,bayan ta yaye ta barni ke ta Samu miji Isa na aurar da ita na mata komai,Laila kina zuwa Kuma ke sai da na miki aure muka je da Latifa wajen Malam lokacin cuta ta kamashi yaga mutuwa da wuri ya amsa cewar ke yarsa ce Kuma ya Sanarwa danginsa kaf suka yafi juna da kyar,amma iya mamanki kika sani kawai.
Sai Kai Haidar tunda still ka girmi Annoor daga Laila sai Kai tsiranku ba yawa,Annoor yace nine karami ma kenan,yace kwarai kuwa,Abba yace mu aci gaba sauri muke ka tsaya surutu,Dan Allah Jauro mene haka haba komai sai kayi kunbiya kunbiya.
Mummy kuwa ta Kai sati guda Baseeru kullum sai dai yazo ya kwashi harka ya fece,Hakan ba karamin Kona mata Rai yake ba kullum da karyar da yake shirgawa ko ruwanta baya sha,yau Mummy ta gama girki tace yau dole sai Baseeru yaci abincinta,tana kitchen ta bude abincin tana zuba Masa magani a ciki,me aikinta ashe tana labe tana kallo tana dauka a wayarta,Mummy Bata sani ba Baseeru ya hada baki da Yar aiki tuni ya biyata wasu kudi,ficewa tayi da sauri bayan ta gama dauka ta kira Baseeru a waya yace Mero ya akayi? Mero tana kasa da Murya tace shegiyar ta zuba Baseeru,dama kace yau zaka zo? Baseeru yace Mero Ina hanya ma tasan zanzo,Mero tace to wlh Yana nan flas ruwan hoda Alqur’an karka ci,billahillazi zata kaika kiyama Baseeru,aradu na Gani da idona,kwarankatsa dubu ta dakko he zubawa take he zubawa take yi a ciki,ai kuwa na dauka a waya hine nace bari na fada Maka,Baseeru yace Na’am Mero to he aka yi Yaya? shima yayi mata irin hausarta ya tsokaneta shi a dole wayayye,Mero tace hine hine nace uhmmm….Dama….ta rankwashi kanta tana sosawa taci gaba da magana Hine nace dama uhmmm…abin nan…abin Nan…………………..
Ina son Dan Hajiya Spark mijin wannan me kyau din, Ina gani suna zuwa tare wajen Mummy wallahi ni hi nake so,na fasa karbar kudin kayi min hanya ya Soni ya aureni wallahi Baseeru Ina sonsa tunda kaga Kai mijin uwarsa ne ko? Baseeru ya sheke da dariya yace Mero Ina laifin kice kina so na ai nine daidai ke,Mero tace cabdi jam hummm uhmm wallahi ni Spark nake so jikinsa me kyau so nake nima na dinga rungume hi,rannan matarsa haka ta dinga rungume hi suna ta wani umhmaahchacha da Baki yana tsotse mata kumatu na gani a Jikin mota suna ta yi,Nima ina son irinsa gahi Yana ta kamhi kullum wallahi Allah ni hi nake so,ko Kuma idan bazai so ni ba ai akwai kaninsa wannan yaron Arham ko Rafeeq Ina sonsu a bani Daya.

