Tantiriya a Gidan Yari Book 2 Page 21-25
Baseeru ne ya shugo gidan shima anci gayu fes da shi,yana zuwa Mummy harda yin tsalle ta fada Jikin Baseeru,Baseeru ya rungumeta fuskarsa tana kallon bayanta Yana ta zuba gwalo ko uban wa yake wa oho,Mummy sai faman goga Masa kirji take,Baseeru yace yawwa nanika min su,manna su,tace Dear abinci fa? Baseeru yace an samu matsala wlh daga gidan abokina nake matarsa ta nace sai naci abinci na cika cikina ko bangaren ruwa a cike yake taf ba waje,Mummy taji wani ba dadi tace ba komai next time,a ranta tace ai sa guba kauyenci ne yanzu ai na canja salo zaka ci ubanka sai duniya ta San a gidana kake tukun zan gama da Kai,baza ma ka mutu a gidana ba,bare a tuhumeni nasan ta Inda zan kaika lahira.
Shi kuwa Baseeru Mummy ya fara sarrafawa gata itama an kwana biyu kadan ake jira ta zurma ya kwashi gara yau ma sosai tun yamma sai magriba ya hakura,tace dole sai ya kwana,Baseeru yace to bari naje Sallah na dawo Yana fita ya fece gidan Daddy Inda yake gadi ya bar Mummy bau tana jiransa.
Tunda taga bai dawo ba ranta yayi mugun baci tace wato ya maidani sex machine yazo ya kwasa ya tafi.
Wayarta ta dauka ta kirashi,bugu daya ya daga yace Me gidana nane ya kira ni ki rufe gidanki bazan dawo ba,Mummy takaici yasa cikin bala’i tace zaka ci uban babanka Baseeru,wlh dani kake zance,Baseeru yace zaki ci uban Babarki surayya kike ko Yusra wlh zan tsine miki ki San tsinuwar miji Kuma,Yar iska marar mutunci,Mummy tace kaiii wato idan na zageka sai ka rama kana me gadi? Tsaki ya ja yace baki da hankali zanzo gidan sai na ci mutuncinki ya kashe wayarsa,Mummy ta Kalli wayar tana girgiza Kai tace eyyaaaaaa Basiru baza kayi karko ba,baza ka Dade a duniya ba,baza kayi tsawon rai ba,mutum ya lallabani da Yaya ya kare ma.
Spark kuwa sabo da haushin Mummy da yaji ta hanashi bincike gashi me gadi ne ya aureta wannan yasa yace nima wallahi ta Abba suruki na bazan boye gaskiya ba, Hakan yasa duk Wanda ya tambaye shi a dangin su ya Mummy Dinka? yace tana gidanta lafiya Lau ai sun rabu da Abban nawa na biyu, yanzu gidanta ya dawo da zama,me gadi ne ashe,da ance a garin ya? Yace kuje wajenta kwaji zancen ba a gulma dani.
Yau ma yaje gaida Mima tace Ina Mummyn taka kuwa? Yace hmmm ai ni yanzu na koma Kuma abin tausayi,ya kamata ki tausaya min ni da Naila mun koma yaran talaka, to uban namu na biyu me gadi ne,yanzu ma uwar tamu tana gidanta ya koma zuwa gidanta,Ashe gadi yake yi ba gidansa bane,Auren dauki sanda muka koma mu ai,Mima tace ban gane ba? Yace kije kyaji tushen zancen.
Ayi min afwa tunda kuka ga shuru akwai uzuri ne.
Masu Sharhi Ina godiya wlh Allah ya bar kauna
Mrs chief My love har naga kira
Kar ku ce AsmaBaffa wai ko nima na zama Abba Dolo ne yau.
AsmaBaffa


