Tantiriya a Gidan Yari Book 2 Page 21-25
Sai wurin magriba ya dawo ya samu Iman ta hade cikin sabon ankon Leshinta na dinner brown zata tafi make up daga can ya wuce,tana ta sauri ta fito da handbag dinta,Annoor yace ke Ina zuwa? tace biki mana,ki jirani na kaiki,ni sauri nake time yayi wurin make up zanje kafin ayi min make up din kazo ka sameni a can ban iya jira ta wuce da sauri ta fice tana cewa na fadawa Kawu da Ummi ta shiga napep,sai da ya gama shirinsa sannan ya fita a mota wata baka,a waya ya kirata ta fada Masa Inda take yaje har can ya samu an mata make up dinta kawai tafiya zasu yi,tayi kyau matuka mota ta shiga sannan ta dakko turare zata shafa yace turare so kike wani yaji kamshi ya biyo ki,Iman tace to mene ai na Isa aure ko Dan wani yazo zance wajena mene,yace wlh duk Wanda yazo zance wajenki sai na hada gobara a gashin hammatar babarsa,sai na hura hayakin bala’i a gashin Hammatar uwarsa,ki kiyaye ni Iman,Iman dariya ta dinga yi tace wannan zagin fa? tsaki ya ja har ya kaita bai kulata ba,Yana mota Yana jiranta har ta gama Shan dinner dinta Yana jiranta ta fito su tafi gida,ko da ta gama tazo kawai kallonta yake kamar maye har sai da tsargu.
Washe gari Abba,Mohsin,Hidaya suka zo gidan Jauro suma a motar Mohsin,Jauro sai washe baki akeyi yace ga abokina yazo Hashimu ku shugo,ai Gyatumar kakarsa ita ce ta Sha nono ta saki kakar gyatumi na ta kama itama,Annoor Yana zaune Iman tana gefensa a makale,Abba ya Kalli yaran Jauro ya Kalli Iman,Jauro ya kalla Yana so yayi magana akan ba muharramai bane amma kullum Iman tana Jikin Annoor,Jauro ne ya gallawa Abba Harara ya Masa fulatanci yace wlh idan ka fada sai mun Bata ka kyale ni,Abba shima da fulatancin yace sai a bar yara suna tattaba Jikin juna idan wani Abu ya faru fa ni na gaji da gani zan fada,dama baka fada musu gaskiya ba gaskiya ka dauki hakkinsu,Jauro yace wai yaranka ne ko sanda na samo abina kana wajen? Abba haushi ya kama shi an Hana shi ya tona asiri,sai kallon Annoor yake da Iman,hannunsa yake ta faman yarfewa a haka ya zauna tare da sa yatsa a Baki ya ciza da karfi sabo da haushi,goshinsa ya shiga tsatsafo da gumi.
Yana can Yana tunanin yanda zai Fadi gaskiya kowa ya huta suna ta gaida shi bai ji ba,sai da Jauro yace ana gaishe ka munafuki,dariya Abba yayi ya amsa,yace Ina Habibalo me gashi kamar Shekar ungulu kaf riga babu marar gashi irin Habiba,Jauro yace ai ta hada iri da Fulanin kasar Kenya wannan bakaken wuluk shi yasa ita baka ce,Kai in banda kaddara da rashin wayo a haka Kuma kake son Habibalo? Abba ya furta,Jauro yace ai gwara ni gani nayi nace Ina so ko banza kowa yasan ni namiji ne Kai fa sai samo Maka aka yi kana ta dolanci a gari, zance ma kasawa kayi,Abba yace amma dai kaga tawa matar manya ce Kubra.
Habiba ce ta fito da fara’a tace Hashimu Kaine? Abba yace Habiba duk daular nan da kike ciki amma baki washe ba? Ke kuwa ko kanti ai Kya shiga ki samo Mai me kyau ki Dan haska,ayi duniya Habiba goshinki kamar ana daka gawayi a kai kullum, Jauro yace ana magana zata isheka da tsufa ne,tsofai tsofai Dani,Abba yace shi yasa duk ka zama tsohon dole,Jauro yace ba dole ba na hadu da Yar gargajiya,Habiba tace kwayi Kwa gama wallahi Mai dai da girmana bazan shafa ba,Jauro yace aikuwa ma kalli na bati a wajen,su Mohsin dariya duk sukeyi ba a magana,Habiba ta mike ta kawo musu kayan ci da Sha,Nabeela kuwa Hidaya ta ja dakinta,Iman tana makale wajen Annoor,Abba shi a dole abokin Baban su Iman yace ke Iman tashi daga Nan,Baki da aiki sai zama a wajen namiji,idan gaskiya ne kaunar yan uwan juna ne ki dinga zama kusa da Nabeel ko Haidara mana sai ki tafi wajen Annoor shi kadai,tashi daga nan ko ki tafi dakinki ko ki San Inda dare ya miki,Iman tashi tayi ta tafi dakinta Rahma tana ta dariya tace oh kai jama’a abokin Kawu irinsa,Abba ne ya Kalli Rahma yace ke dai da alama da wuri zaki tsufa,Rahma shuru tayi ta tashi tare shigewa dakin Iman tana kyalkyalawa Iman dariya an korota.
Abba so yake ya fada su ba Jauro ne ubansu ba,ya rasa yanda zaiyi, sai ya bullo da nasiha,yace Kunga duk Kun Isa aure ku samu ku fitar da mata ayi muku aure,shi aure Rahma ne,Yana hana barna da zinace zinace,wlh idan da aure wani ko Zinar gado ce bazai yi ba sabo da yana da matarsa.
Haka yaran da basu da Uba a hausance amma ko wanne Da Yana da Uba sai dai ace kafin a shafa fatiha aka same shi Kuma bashi da laifi ko kadan iyayensa ne masu laifi,Haidar yace ni misali ma Abba ace Dan shege ne Ina ruwana,zanji dai haushi amma ya zanyi zan kashe kaina ne zanyi kokari na nemi lahira ta,tunda dai ai ba a ce Dan shege bazai shiga Aljanna ba,Abba yace Kai amma Allah Maka albarka wlh,Abba yace Kai fa Nabeel? Nabeel yace ta ya zan zama ma Dan shege Allah ya kiyaye ma Dan Allah ku daina hadani da shege ba dadin ji,Abba yaji tausayinsu yace Annoor fa? Annoor yace ni idan Iman tana raye ace Dan shege ne ni mana me ya dameni tunda Ina da Yar uwata a kusa,Jauro yace kamar gaske Mutumin da kullum sai ya sata kuka da gori da bakar magana.
Mohsin Yana jinsu amma chat yake da matarsa Beauty bama ya Jin me suke fada sai yamma likis suka fito zasu tafi Haidar ya kalli Hidaya yace Tana za a tafi,dariya Hidaya tayi tace wlh ni ba Tana bace,Jauro yace rabu da shi budurwar da zai aura Bata kaiki ba wata Kunkuma ce,Abba yace Kunkuma? Kai Haidar ka kiyayi kanka da Kunkuma gwara ka more kuruciyarka ka zaba ka darje,dariya suka yi Annoor Yana ciki bai fito ba shi,dakinsa ya wuce.
Washe gari da safe Chika kayanta ta hada kaf zata tafi gida,Malama tace nima tafiya zanyi ai,Chika tace ya fiye miki dai yanzu Ina zaki je? tace gidan Yan uwana zan tafi duk da basu kaunata haka zan je, Chika tace zo mu tafi gidan mu kawai,tace a’a zan koma gida haka karki damu ta goge hawayen da ya gangaro mata kadan,Chika tace ke Ikhram wlh kiyi aure ki huta da gararin nan, ni dai na tafi,Chika ta fito kida Islam ya kunna Dan ya dawo da safe,Chika Misam ta gani Yana jiranta da key din mota a hannunsa,wankan da yayi ne ya tafi da Imaninta,ya Sha swagg,Chika tace dole yaron nan yayi iskanci ya hadu,sai Kuma tace uhm yabon Kai jahilci Dan zan aure shi sai na yabe shi,gabansa ta karaso ya karbi Jakarta,rawa ta fara tana girgiza mazaunai,Islam ya kalleta dariya ta bashi duk Inda Chika taji kida Inshaallah zai wahala Bata yi rawa ba ko a gaban uban waye,Misam murmushi ya saki ya juya tabi bayansa tana cewa Islam bye bye,yace to sai mun zo daurin aure,Rafeeq yana zaune yace dan iska ya samo dai dai shi,Misam yace uwarka Rafeeq ya fice, mota suka shiga,Chika tayi adduar shiga abin hawa, Misam ya ja suka tafi,Yana tafiya Chika ta tsokane shi tace Baby Fuck me,da sauri ya juyo yace na’am to me kika ce?,dariya ta dinga yi tace just kidding you,tsaki yaja yace yau kwana nawa banyi komai ba,gaskiya nayi saurin tuba ya kamata ace idan na tuba sai na koma na Dan sake yi ko sau biyu ne sai nayi Istingifari,Chika tace tuban muzuru kenan ba kyau,kana yin tuban muzuru wlh karka kawo kudin aure kaje ka auri Karuwarka,wai me kake ji a wajen Karuwa,? shaddar kasuwa kowa hawa yake,yace Haram tafi dadi ne,Chika fushi tayi ta bata rai tace kaini gidan Naila zanyi magana da ita,Murmushi ya saki yace okay amma mene na fushin? Ai dole nayi fushin tunda Haram tafi dadi sai kaje wajen Haram dinka.



