KALBIM BOOK 1 PAGE 40
40
*KALPANAH COLLECTION*
08105064494
Shin ke daliba ce ko kuma uwa wadda har yanzu bata daina rokon urgent 2k a wurin yan uwa da kawaye ba,tou nesa tazo kusa domin kuwa na kawo miki maganin matsalarki,domin kuwa *Kalphanah Collection* ta shirya tsaf domin taimaka wa duk wani dan kasuwa ko kuma wanda yake son fara kasuwanci.A *Kalphanah Collection* muna saida kaya kama daga Jaka,Takalmi,Atamfa,Laces,Kayan yara da kuma kayan kitchen.Wani abun mamakin ma muna saida kayan mu ga masu siyen daya ko kuma sari,ga waenda basuda jari ma mun tanadar masu hanyoyi daban daban da zasu fara neman na kansu.Hajiya kina gida kwace zaki dinga jin saukar kudi a asusun bankin ki.Ga musu fuskantar qalubale a kasuwancin su kuma an kawo muku sauqi domin kuwa an bude muku group dinku da zaku dinga tattauna matsalolin ku.
https://chat.whatsapp.com/IyDlSVdw1rDIlCNNQMel68
Kedai idan kin shirya ki dannan link din nan na kasa domin shiga group dinmu ki ganewa idonki kunsan ance gani ya kore JI
Karki yadda ki wuce bakiyi joining group din nan ba domin kuwa yanzu sallah tana qaratowa ko bakiyi kasuwanci ba zaki siya domin amfanin ki na yau da kullun kuma ko baku buqata yanzu nan gaba zaku iya neman ta.
Siyen na gari maida kudi gida.
08105064494
**************
“Thank you” AZIZ yace yana kashe wayarsa ya ajiye gefensa ya dago ya kalli fahad dayake jiran umarninsa bude baki yace
“Dukkanin Abinda ka sani na bayanin daya buqata ka hadosa cikin gaggawa inason sanin koma menene daya shafi wannan maganar”
Cikin tabbatarwa Fahad yace
“Angama Sir”
Harya juya zai fice AZIZ din ya kirasa ahankali
yana juyowa yace masa yanason Ipad din Sayd a hannunsa yanzu.
Ficewa fahad yayi ya koma dakin Sayd wanda yake toilet yana sakarwa kansa ruwan dumi sbd sake samun karfi.
Baima tsaya komaiba daukanta kawai yayi ya fice ya kaiwa AZIZ wanda yana karba mai tsaye history na browsers dinsa ya ringa shiga.
Shiru yayi yana bin duka histories din wainda duka bincike ne kawai yake akan Masu ciki da yanda ake cire zuciyar dan adam sai kuma bincike akan scar din da aikin zuciya yake bari wanda kusan shine yafi yawa.
Shiru yayi yana ajiye ipad din gefensa tareda dan rufe idanuwansa yana hana kansa tinanin komai dan baisan me sayd zaiyi da wannan binciken ba seda kuma binciken da zaayi akan zaadens ne yake buqatan sanin dalili ga kuma dr Abraham da shima yake nacin neman bayanin komai akansa wanda duka idan aka hada link daya ne asibiti tinda shima Sayd idan har yasan Abraham a asibitin ne wanda duka kuma dai haihuwan Ummitah ce takaisu asibitin da har akai haduwar.
Nunfashi mara sauti ya sauke yan bude idanuwansa ya dauki wayarsa ya miqe yabar office din zuwa cikin gida.
Kai tsaye dakin Sayd din ya sake zuwa ya dubasa ya tararda ya kwanta bacci ma ya daukesa dan haka ya wuce nasa bangaren bayan ya sanarwa mama ta kwantar da hankalinta b damuwar komai bane may be ma stress ne na aiki da zaman da basu cika yiba.
Yadda mama tayi ta dan kwantar da hankalinta sbd Sayd shima ‘da ne gareta tana kaunarsa sosai da sosai.
Falaq bata gida tana school shiyasa gidan yake tsit sai data dawo hayaniyar gidan ta dawo.
Abincin rana gabaki dayansu gidan sukaci a dining kaman yanda suka saba
Sayd ma ya fito dashi akaci abincin sbd bayason yabar kofar da AZIZ zaisan akwai abinda bayason ya sani dan haka ya sake.
AZIZ din kuwa ganin ya sake batareda ya sanar dashi komaiba ya sakasa tabbatarda abinda yake binciken ba alkhairi bane tinda yake kokarin boye masa.
Da daddare da kansa ya raka Falaq dakinta sai datai bacci ya fito ya wuce bedroom dinsa yana kashe wayoyinsa,
Wanka kawai yai yayi shirin bacci ya kwanta yana rufe idanuwansa batareda bacci yazo masa ba sbd abubuwa da yawa ne a zuciyarsa da kansa wanda duk dare kafin ya kwanta kewar yar uwarsa ce take zuwar masa wadda yakewa fata da adduar tana cikin rahamar ubangiji.
**Washe gari ma basu fita aiki ba a gida suka wuni Sayd din ya sake warwarewa shima kuma hutu da kadaici yake so dan haka ko fitowa baiyiba abincinsa ma sedai aka kai masa palonsa aka jera masa acan yaci.
Sayd kuwa Fita yayi sbd tsananta bincikensa da ayanzu shine abinda yake tsananin buqata.
Wayar Latif Sayd ya kira wanda yake cikin yan Amanar maaikatan AZIZ kuma duk da basa kasar haryanzu LIMBA na biyansa Albashi hakama shine drivern da duk yawon asibitin da sukai harma da ranar haihuwa shine yake yawo dasu har suka baro Nigeria shine drivernsu.
Latif dayake Shagonsa daya bude yana business dinsa yana ganin kiran ya daga cikeda girmamawa yana cewa
“Oga Sayd”
Gaisawa sukai Sayd din ya gyara zamansa yana sauke numfashi me sanyi kafin ya bude baki cikin bayyanarda Buqatan abinda zai tambaya batareda delay ba
Shima Latif din Nutsuwa yayi yana aje abinda yake tareda wucewa kurya inda baa shiga saishi kadai ya zauna dan jin abinda Sayd din zai fada.
“Latif ka tina a ranar da Ummitah ta rasu akwai Dr da shine yayi mana bayani kuma shine ya kula damu a wannan lokacin???
Cikin nazari Latif ya dan shiga tinani yana kokarin tinawa da lokacin sbd dashi suke tare a asibitin.
Cikin rashin tabbatarwa yace
“Eh wani black haka naji suna kiransa da kaman Dr samail ne ko yaya ma suna…..katsesa Sayd yayi da sauri da cewa
“Yes,yes yes Dr Ismail,yes thats the name”
Jin yayi wani abu daya danne zuciyarsa ya dan fada ya sauke numfashi yana miqewa tsaye yana jin sassauci a ransa yace
“Latif inason kaje asibitin ka bincikamun Dr Ismail din,
Inason sanin bayanai akansa,
Waye shi,
Familynsa,
Aikinsa,
Yana ina yanzu?
Da address dinsa, No i want to know every single abu akan rayuwarsa cikin gaggawa”
Shiru Latif yayi kafin ya sauke numfashi yace
“Angama Oga Sayd sbd babu abinda bazan iya yiwa Familyn Sir AZIZ ba,
Ayau zan ziyarci asibitin na fara sanin Full name nasa da idan yana nan kafin sauran binciken zuwa gobe da kwana biyu zan hado maka komai”
“Thanks” sayd yace yana kashe wayarsa ya wurgar a kujera yana dafe kansa tareda lumshe idanuwansa.
Falaq data kasa gane kan daddynta kwana biyu damuwa ta shiga tafara dagawasu mama hankali wadda itama tane kasa gane kan AZIZ din da kuma sayd da shima duk ya kasa zama kwana biyu
Magana tai musu wanda ya saka Falaq dawo da Daddynta daidai shima sayd ganin AZIZ baice masa komaiba kuma yasan yanda AZIZ din yake da karantar abu da ilimin gane abu atake ya sakasa dawowa daidai sbd tsaro.
********cikin kwana biyu Fahad da Latif suka duqufa da mugun bincike da bin duk wata hanyar samo bayanan da suke nema baji ba gani,
Shi kuma Sayd jin yake kaman zai zare sbd jiransu Amma ya boye yana ayyukansa hankali kwance sbd AZIZ daya fara fita office dan haka ya dan zama busy da ayyuka da kuma handling abubuwa.
Latif ne yafara hada bincikensa dan haka ya kira Sayd din kai tsaye wanda a lokacinda kiran ya shigo yana gaban AZIZ LIMBA yana karanto masa bayanan Report da aka aiko musu daga Italy.
Sunan Latif ne ya bayyana Akan screen din wayar Sayd din datake ajiye a gabansu.
Hannu Sayd ya miqa ahankali ya dauki wayar tareda kashewa ya ajiye gefensa yana cigaba da bayanin da AZIZ ke sauraronsa hankali kwance cikin nutsuwa.
Yana gama bayanansa juyawa yayi ya fice yana amsa wayar Pa din Maheer Zad data shigo wayarsa akan haduwarsu da haryanzu baa san lokacin ba..
