KISHIYAR KABILAH Book 2 Complete Hausa Novel
[6/2, 4:26 PM] SURAYYAHMS: _Dr. Hassan’s private Hospital Maitama._
Wajajen karfe bakwai da rabi na yamma motarsu Ahmed ya tsaya adede kofar asibitin Dr hassan anan inda yake yawan consultancy, Kusan a rikirkice Ahmed din da brother hamzat dimeji suka fito tare da kinkimo hjy khadijatu Ahnnunsu suka shigo tare da ita cikin asibitin inda ko motsawar kirki jikinta bayayi bare tay wani numfashi.
“Banda inna lillahi wa inna ilaihi rajiun babu Abunda brother hamzat dimeji yake furtawa.
Idanun Ahmed da suka rine sukayi jajizirr sune akanta ya tsura matasu jikinshi na rawa baya iya kiftawa dan ganinta ahakan harji yake kamar ana konashi da wuta ne a taciki.
Sosai idanunshi suka tara ruwan hawaye masu tsananin zafi dan sosai tausayin mahaifyarshi yake cinshi taciki ranshi wanda kallo daya kayi mata zaka san da cewa lallai tana cikin wani hali na shiga shock sabida yadda dukan jijiyoyin jikinta suka tsandare tay fayau.
Lokaci guda nurses sukayo kansu ganin Dr Ahmed dinne dakanshi yake shigowa ciki
A hanzarce suka bar dukkan abunda sukeyi sukayo kanshi..
Saiji kake ana cewa
kuyi sauri, be fast ,Its DR Ahmed Bello jimada, “Its an emergency!
Nan da nan aka kawo gado mai taya aka dorata akai tare da nurses guda hudu abayansu shida brother hamzat suka shiga tayasu turawa har akai da ita dakin dubiya.
Anty adizat dake wajen duk ta rikice ta rasa me zatay guda daya sai jeka ka dawo takeyi cikin tashin hankli.
Nurses da suka biyosaa ciki zasu tabata knan Ahmed ya harzuka ya koma kansu da masifa cikin ynyin sauke musu zafin fushin dake dawainiya dashi, atake yahau daka musu wani birkitaccen tsawar dayasa duk saida sukaja baya arikice.
Ransa a matukar bace ya lumshe idonsa cikin bacin rai snn yace “Leave now, just leave, evrybody get out .. i can handle dis. Bana son gulma..just get out.
A gaggauce kowannensu ta juya izuwa waje suna masu cewa sorry sir, sorry sir dan su basu ma san komi akan abunda yake faruwa dashi ba, nan da nan aka barshi shikadai a room din.
Huci mai zafi yakey shikadansa ya dunkule hannunshi jijiyonsa duka sun harzuka sun tattaso tsabar yadda bakin ciki yake mamaye masa zuciya.
hannun shi da jikinshi duk na ɓari saboda baisan meyake ji aransa ba.
tsananin tashin hankalin ganin mahaifiyarsa a wann yanayin da bai taba ganinta aciki ba hade da rudanin irin daukar fansa da zafin cin amana da kafayat tay masa ayau shine yake damunsa.
He was not expecting this ko acikin mafarkinsa, yasan dai auren kafayat da babanshi na daukar fansa ne akansa amma baiyi tsammanin zata iya aikata gagarumin zalunci da cin amana ga mahaifiyarsa har haka ba duba da yadda take da matsayin uwa a idanunta tun tana yar karama,kai dole ne ma ace ko shedan na tsoron sharrin mata.
Some Women are truly devil incanate, cikin yanayin bacin rai yake shafe kansa yafi sau takwas acikin zullumi kanshi yay bala’in zafi, ɓari ɓari hannunshi da jikinshi yake har ya kammala sakawa mahaifyarsa drip
Ya gwada blood pressure dinta ya ga yahaura yakai izuwa 199°c,duk da yana cikin tashin hankali bai hanashi nutsar da kansa wajen bata kulawa mai inganci ba. He just cant afford to loose her, har imagining yake inhar mahafiyarsa ta mutu yau a sanadiyar kafayat toh daga ita din har babanshin bazasu rayu a duniyan ba.
Kulawa na musamman ya fara bawa jikintan tare da dora dukkan wani nitsuwarsa da kokrinshi akanta dan ta samu lpya.
Ayayin dayake cikin dqkin dubiya brother hamzat ya harzuka ya fita waje da wayarsa a hannu, tacan inda babu hayaniya ya tsaya snn yaa kira dan uwanshi brother kazim awaya suka fara magana
Muryansa Kamar na wanda zaiyi kuka yake maida masa maganan jin yadda shikansa brother kazim din yake tafarfasa sabida tsananin fushi,ji suke kamar wa uwarsu data haifesu akay wa wann zaluncin dan da suka rasa mahaifyarsu hajy khadijatu ne kawai atare da su har suka kaiga wann lokci.
Na rantse maka brother bazan yarda da wann auren ba, kafayat will neva ever be my step mother, who born her? eee..baba must come and answer to us oo!! “Wann abun kunya acikin family har yaushe, i still cant believ this,baba has gone insane, kowa fa yasan cewa da Ahmed da kafayat ta taso suna soyayya,and then boom sai ace mahafinmu ne ya je aureta dan rashin sanin ciwon kanshi? “Wann wani irin rashin kunya ne suke so suyi? Ahhhhh, haaaa oluwa mi oo, me I cant stand dis disgraceful weding ooo, Dolene ya saketa ko mu mudauki mummunan mataki akanta shegiya yarinya azzaluma kawai tazone ta lalata mana family I swear they wll knw no peace in that house daga ita harshi..
Cike da danne fushi Brother kazim yy ta maza cikin nitsuwa yace kar ka daga hanklinka hamzat, calm down first, yanzu kaje ka kula da Ahmed and mother, kuyi iya bakin kkrinku akanta kuga ta samu lpya,cikin sauke ajiyar zuciya yace, “i wish i am here for her gaskiya mother bata cancanci wann cin amanan awajen baba ba, yana maganan tsabar takaici har ajiyar zuciya mai nauyi na kufce masa bazata,daga nan bai iya tsawaita maganan ba, yace yanzu kaje ka tsaya tare da dami i wll handle baba by myself..yasan ai bai kyauta ba, bai aikata mana daidai ba shiyasa yake kin daukar wayarsa tun dazu danaji labari naketa kiranshi baya daukawa but believe me bazan kyaleshi ba, i swear to god haka bazai taɓa yuwa ba, dolene yasan yadda zai yi auren nan ya mutu..the damage has been done to us i know but it shall not be accepted in our family.
Brothe hamzat yace better!! Dan bazamu yadda bafa, bazaiyu ba, bazaiyi ba, wanncan kazamar yarinya bazata dawo uwata ba ooo.
Suna cikin tattauna hakan sai ga motar anty nurat ya iso harabar asibiti, agaggauce tay parking tare da Adiahar suka kusan a lkci guda suna tafiya cikin gaggawa snn sukayo wajensa,yana ganinsu atare saiyay ma brother kazim sai anjima snn ya katse wayar tare da tsura masu ido har suka karaso.
“Gud evening brother” Adiaha ta gaishesa respectully sann taja ta tsaya agefe feeling awkward jin kanta daban ajikinsu
Hanklin Anty nurat atashe tayi gareshi tanamai cewa Akomi, “ya jiki hajiya? what about Damilare? Is he fine? hows mother feeling? Kafadamin mana har Ta farfado ne?i hope ba wani matsalan daya sameta..ina fatan dai babu wani abunda ya faru, tana maganan ne muryanta kamar na wanda zatay masa kuka itama, jin bai amsa ba taji hanklinta ya dadaa tashi, cike da muryan damuwa sosai tace..im asking u dimeji, yaya kamin shiru, “where is Anty adizat?
Ajiyar zuciya ya sauke snn ahankli ya amsa mata jikinshi a sanyaye da cewa komi lpya Ahmed yana can yana dubata aciki yana maganan yana satar kallon Adiaha dake son tay magana amma bata san mema zata fara cewa ba.
Cikin yanyin danne zcyarsa yace “Kuje ciki ku samu anty adizat din a reception”.Zan xo daga baya..Harta juya zata tafi ya jawota gefe murya kasa kasa yace becareful with ur words, karkuje kunata zuba kuna tona mana asiri awaje, haryanzu yarinyar nan bakuwane acikinmu. Daga can ta kalle adiahan snn tace masa “toh naji”.
Bayan nan ta kama hannun Adiaha suka shiga cikin asibitin tana tafiya tana kananan maganganu” hmm dama haka rayuwa yake oo oo,wata macen zatazo gidan miji da albarka wata kuma zatazo mana da fitina da bala’i. Some women are really a bad omen, a cursed hmmm
maganan take kmr ba da ita ba dan Da gefen ido ta juya ta kalle Adiahar snn ta kyabe baki murya ciki ciki tace ..welcome to our family problem iyawo”..this is just getting started.