KISHIYAR KABILAH Book 2 Complete Hausa Novel
Deciding tay data nemo makanta nata sabuwar salon domin kuwa zamowa kishiyar Adiaha ba shine zai saka itama ta maida masa kanta kamr adiahan ba.
Hakan yasaka ta riƙe hannunta tana jajjaan baya sosai dashi komin bori komin fushi haka takekin sakewa da shi haryau har kwanan gobe.
Kwana biyun Bayan yan shawarwarin datake samu awajen adda nafisa har Online classes da akeyi na matan aure ta sakata tashiga tana biyan kudin register inda ake musu lectures sosai gameda abunda ya shafi zaman aure da kuma rayuwar mata gabaki daya. (Surayyahms chat 08060712446)
She become so addicted musmmn ma data shiga 2 weeks exlusive online classes na *Diary of Idle woman*”Na Wata shaharriyar marubuciya
*Surayyahms*
Inda take tsintar abubuwan daya dace masu matukar amfani wanda ta rikesu aranta domin kyautata mindset dinta a matsayinta na ƴa mace mai sanin ciwon kanta da darajar kanta.
Dubu daya kacal ta cire ta yi register ta shiga amma bakaramin karuwa datay da ilimin dayake cikin lectures din ba
Yauma tana kwance wajejen karfe 8 da rabi bayan tayi sallan isha’i kayan baccine ajikinta doguwar wando da yar riga, kan gadon nata duk ta baje takaddu da mac book dinta daga gefe da milkshake bowl dinga ta janyo tana zuƙar madaran dake ciki tanamai cigaba da karanta abubuwanda fasihihiyar marubuciya SURAYYAHMS DIN take cewa.
Yau din ma kusan Wani muhimmyar lectures ne
Akeyi mai nunawa mata cewa botsarewar namiji agidan aurensa mafi yawan lefin na matarsa ce.
_Surayyahms tace:_
An ce, hanyar da mace za ta bi ta mallaki zuciyar namiji biyu ne: cikinsa da shimfidarsa. Ni na qara da daya, sun zama uku: kunnensa.
‘Yar uwata namiji wawa ne. Namiji soko ne. Namiji gaula ne. Amma fa a gaban matar da ta san kanta, ta yarda da kanta, kuma ta laqanci mijinta. Lura da kyau, ba cewa aka yi mace mai kyau, asali ko ilimi ba, a’a, macen da ta san ita mace ce, ta kuma yarda da hakan, sannan kuma ta karanci dabi’ar abokin zamanta. Irin wannan mata, ita ce ke zama ji da gani da kuma tunanin mijinta.
_Surayyahms tace_
Na san cewa kin san duk yadda za ki inganta biyan buqatar cikin mijinki da shimfidarsa, don haka ba sai na ce komai a kai ba, musamman saboda ma na san cewa, dubban masanan da suka fi ni cikin mata da maza sun gabatar da bayanai a kai da dama. Inda kawai zan dan qara, shi ma ba don ba a yi ba, sai don ba a cika yi din ba, shi ne bangaren gamsar da kunnuwan mijinki da hira.
Sama da kashi 50 na rayuwar namiji tana ga harkokinsa ne na waje, yayin da sama da kashi 50 na rayuwar mace tana ga harkokinta ne na cikin gida, ko da kuwa ma’aikaciya ce. A nan, ‘Yar uwata, kina buqatar dan zaburowa da cicciba matsayinki. Saboda ki san yadda mijinki yake rayuwa a harkokinsa na waje. Ba fa ina nufin ki yi binciken sirrorinsa ko neme-nemen matansa ba, No! Wato nufina ki san sana’arsa ko kasuwancinsa, ko aikinsa da wasu harkokinsa da ba zai damu ki sani ba. Ki yi qoqari ki san ababe da dama game wadannan. Idan kika sani, sai ki zama abokiyar hirarsa a kai. Ki sa shi jin cewa, kin yi wa harkarsa sanin da dolensa ya buqaci shawararki ko ya yi hira da ke a kai. Da zarar kin samu wannan matsayi, to, kin gama mallake mijinki, amma fa da sharadin kina inganta ciki da shimfidar can, yes!
Snn tace
Yar uwata, soyayyar nan da kike gani wacce ke ba kya gajiya da ita a zubin halittar dabi’arki, wallahi gundurar namiji take yi.
Maza da yawa sun sha yi wa matansu tsaki, ko gwasale, wasu ma har banka wa matan ashar yayin da suka kira su da tsakar rana don su nuna ko su furta mu su kalaman qauna. Saboda a lokacin, ba abin da ke gaban mazan ke nan ba.
Haka abin yake a wani zubin idan miji ya dawo gida. Wai ba ki lura cewa in mijinki ya ga abokansa ya fi sakin jiki da su a hira a kanki ba? Ai ba wai don yana fifita su a kanki ba ne, a’a sam, sai domin kawai hirar da abokan za su yi masa ke ba za ki yi kwatankwacinta ba. To don me ke ma ba za ki koyi hirar ba ‘yar uwata?
Wasu mata sukan ji cewa, ba su da wata hira da za su yi da mazajensu wacce ta wuce qorafin abin da babu a gida da qorafin rashin lafiyar wani ahalin gida da hirar iyayenta da ‘yan uwanta da qawayenta. Ba ruwanta da halin da mijinta yake ciki bare ta yi hira da shi a kai. Irin wannan hali ke sa maza fita waje hira da wasu abokai, wasu ma har su dade a can, daga nan har su hadu da wasu matan da za su qwace miki miji kina ji kina gani. Irin wannan hali ke sa maza fita harkar mata a cikin gida, ko tasa talbijin da kallo ko waya da chatting.
_Surayyahms tace_
‘Yar uwata, rashin koyon ilimin rayuwar harkokin mijinki na waje, da rashin nuna kwadaituwa a kai, gazawa ce babba daga bangarenki. Don Allah ki gyara!.
Yasrah tay shiru sosai ta zuba idanuwanta akan screen dinta tanata karantawa daki daki tare da kallon maganganun nasu dataji suna ratsata sosai…kusan yau din ma gabaki daya nazarin maganganun nan tay kamun ta gaji tay bacci.
Bayan kwana biyu laulayin Adiaha ya fara tsanantawa sosai ta dawo bata iya wasu abubuwan kawai taƙura kanta takeyi da azaba wajen ganin salonta na iya bautawa soyayya da kuma zakewa wajen daɓbaka lamarin mijinta da baisan tanayi ba ya bata wani sabuwar matsayi.
Saidai wnn karon wayar da kakarta take dan mata yanadan taimaka mata dake yanzu ta dawo nigeria sukanyi waya kusan kullum kafin Ahmed ya dawo ahankli har kakan nata ta fahimce abunda take ciki.
Koda laulayin yafara mata yawa sosai kuma taga mijinsu Ahmed babu ruwansa hanklinsa ma ayanzu naga kan samun yasrah ne sai taji aranta kamr tafara gajiya da kkri saidai kuma naciya da dumbin yarda datay makanta na cewa wann salon nata ne kadai zai iya bata sabuwar daraja da matsayi wanda yasaka bata iya nazari mai zurfi akai kwata kwata.
Kullum kakarta takan so ta ja hanklinta amma ina bata fahintar metake cewa.
Acikin satin nan Koda yasrah ta kammala shanye dukkn wasu zakwalan kalamai da hikiman dake cikin dumbin lectures din marubuciya surayyahms ahakli Adiaha ta soma ganin sauyi mai rikitarwa atattare da ita.
Sai taga kmr dukkn wasu abubuwan nuna so da kyaytawa datake ma Ahmed din sam baya bawa yasrahn sha’awa.
Taga komi zatay da nata salon na daban mai mugun daukar hankli take fitarwa.
Wani irin tsantsar kasaita da kuma kamuwar kai da wani irin sanyayyar halayyar shawagaba da Yasran take fitowa dasu sarari bakaramin gigita Ahmed din nasu yakeyi ba.
Dake yanzu tana dan fama da laulayi har mijin nasu ya gano sai tuni yasrahn tafara saka mata hannu a wasu abubuwan aikin gida datake daukawa akanta duk dama haryau aranta sam batason barin mata tanayinsu harsai taga abun yafi karfinta ko inshi Ahmed din ya bata rai ya hana.
Adiaha ta kasa samun nitsuwa ta kuma daburce musammn dataga yasrahn ma ta fara fidda nata salon acikin hkiima da kuma wayewa kwarai dagske.
Sosai salon yasrah ya fara caza mata kai duba da yadda mijin nasu yake over reacting in total opposite da yadda tasanshi all her life.
She had no idea na cewa Halin yaran nan is very important sai dai ba koyaushe taga yasrahn takeyi ba gudun raini kada ace baiwar Allah nan bata da wayo.
wani lokacin haka zataga yasrah tazama masa very firece and classy, wani lokacin very smart bata nuna wautarta a fili