VENNETE
KISHIYAR KABILAH Book 2 Complete Hausa Novel

KISHIYAR KABILAH Book 2 Complete Hausa Novel

Bayan nan suka dawo kasa matar ta dauka mata perfumes da sanitary pads da sauran tarkacen mata ta hada mata dashi.

Adiaha saita fara damuwa ganin kawai kamar kudin mijinta ake kararwa ajikinta itadai tausayin kudinshi takeyi harta fara jin haushi haushin matar aranta.

Matar dake ta lura da ita wawiya ce wani abun ma bata gaya mata in zata dauka..

Wann ranar zai iya zamowa damar ki ta karshe hala har ku kammala rayuwar aurenku a duniya baza’a kara baki wann daman ba.

Matar ce tafara gaya mata haka acikin yanayin wasa musammn dataga tafara daddaure fuska akan wai ana wasa da kudin mijinta..

Kafin nan a bangaren kafayat dake bibiyarsu kuwa har cikin mall din itama tashigo ta samu lokcin suna haurawa sama ta iso cikin mall din a rude itama duk jikinta na rawa, duk ta rasa yadda za’ayi ta bibiyesu, sai ta biya wani attendant da suka dan saba tahau masa karya tace mishi ai Ahmed din mijinta ne ya kawo sistersa ne shoping kuma joint acct sukeyi tare dashi so tanaso ne ayi tracking mata payment details na duk abunda suka saya dan aranta so take tasan nawane zai kashe ma adiaha acikin shoping mall din nan.

She knew he have enough money to spend
Kuma zai iya kashe wa mace ko nawane,yana daya daga cikin abunda yasa bata iya fushi da walakancinsa tun suna tare sabida shi yana da sakakken hannu inhar zai kashe maka kudi dagske zai kashe maka wanda har saika sha mamaki.

Ko Wayar dake hannunta ayanzu ma duk da kudinshi ne hatta rabin kayan datake sawa ajikinta take takama dashi duk shine yake bata kudin siyensu musmmn ma inta zo wajenshi adacan dasuke kawance.

She is aware that Komin walakncin da zai ma mace bazai hanata kudi ba saidan kuma inhar ya tsane mace kuma toh ko guturu ma saiya fishi kankame hannu.

Tun bayan data barsu a mall din gidan mahaifyarta taje duk hanklinta a tashe ta kasa zama ta kasa yin komi idonta nakan waya tana jira a tura mata information wanda ita kanta batasan mezatay dashi ba kawai dai so take tagani.

The highest amount he ever gave her to spend adacan taje tayi shoping ta biya kudin makarntar ta was 1.5 million Banda iphone daya siye mata alokcin.

Adiaha was looking flawless sai gamshi jikinta yake fatar jikinta yay sumul sumul yana wani yauki fuskarta na fidda haske sabida gyaran dayasha.
.
Sumar kanta madaidaici aka tsaga shi gida biyu aka mata coils ata gaban tay kwalliya mai kyau

Shi dayansa ya dawo a mota around 6pm na yamma yazo mall din yabiyasu sauran kudinsu snn ya dauketa suka kama hanyar gida.

She was busy blushng all the way sabida kallon dataga yana mata atake tafarajin karfin gwiwrta ya dawo tafarajin kanta kamar asalin mace..

She is no longer scared of going to any limit of romance with him now, musammn aynzu dataji jikinta yay wani irin kyau da laushi gata tana zuba mayun qamshi.

 

Agidan kuwa tun fitarsu su anty adizat suka kafa chapterta kowa tana tofa albarkacin bakinta acewar anty nurat yanzu suka fara gasa ta tunda munafukace taje ta hɗa musu makirci awajen Ahmed anzo anci musu mutuncinsu..anty adizat ta dinga rantsuwa cewar bazata taba yafewa ba itadai saita walakanta Adiaha musmmn ma da suke tunanin ayadda take dacan haka zata cigaba da kasancewa duk tunaninsu dan ceton ran shafiu datayine yasaka ahmed yau yabi bayanta babu wani abunda zai canja a tsakaninsu tsabar sun gama raina mata wayo aganinsu ahaka zata kare a kaskance tana yawo kamar yar bola acikinsu suna rainata

Yau babu wani samfurin mugunta da keta da basu zauna sun shiryashi wanda zasu nayi a munafurce domin Adiaha ba.

Kafayat da mahaifyarta ne a tsakiyar falonsu suna kan fada akan daga hankli da kafatayat din tay duk taki cin abinci taki zama ta huta sai jeka ka dawo take wai tana monitoring din ahmed da matarsa.

Hjy fatihat ta dinga mata ihu tana cewa ahaka zaki kare kafayat asararriya.
Memakon ki kama aurenki ki haihu da alaji bello ki samu rabonki a familyn jimada kin zauna kina bibiyar rayuwar Ahmed da matarsa..ure internationally crazy bakin ciki ne zai kashe ki

Mutumin da ko kishin ki ma baiji ba? Memakon kin auri ubansa ke kimasa walakanci yanzu shine yake cin ubanki ya hanaki zama gidan miji shikuma yana enjoying life nashi ..kafayat sum evil spirit has definatley use damilare to curse your future .. damilare is ur curse aaaaah kafayat
Bazaki bar shegen yaron nan kiyi rayuwarki ba

Kafayat tace babu ruwanki mumy ni kawai kyaleni bakisan abunda nakeji araina ba, so how did u expect me to feel bayan wata ne take living dreams dina agaban idona tareda Damilare..
He is the love of my life

Hajiya fatihat tace
“Past tense. Not anymore, keda damilare har abada tunda ubanshi yaci gindi naki!

Kafayat ta kara sautin kukan ta, mum meyasa bakida imani ne! im hurting here…Na gaya maki har rike hannunta yakeyi openly, yana bude mata car, he took her to fancy restaurant and later even took her for shoping..

Hja fatihat tace Ya isa haka kafayat kin gaya min wann labari yafi sau dubu daya yau bana son naji kuma..idan haka ya maki zafi kisaka alaji bello jimada yakaiki mana, see me see trouble ooo bashine yana cin gindi naki ba.

Mummy pls stop it wann wawan tsohon ne zakice na fita dashi…god forbid
Menene yake dashi? Dacan ne yake da arziki amma yanxu Baida komi sai pension, da katon burarsa mai kamar karfe, …all the luxury he is enjoying na yaransa ne sune suke spending masa kudi, kuma tunda ya aureni basu son bashi kudi mai yawa saina kashewa..sai inta jiransu sai sun bashi kafin nan ni yabani?Mummy how is it fair? Ko zai kashe min kudin ma bazai kashe min millions ba…but Ahmed and his brother suna da kudi sosai yanada phameuticals business and alot of shares in real estate.

Ahmed aunty is even a big politician yanzu dana auresa yanzu da hala ta bani wani aiki mai kyai awani waje duk kikace min saina auri tsoho toh gashinan ai..am just frustrated, am depressed, i feel cheated. Ahmed is giving away evrything dat belong to me to another woman ..acikin wani irin azaban kuka mai cin rai ta fada hartanajan sheshkka mai zafi..

Tana cikin kukan sai kilau wayarta yay kara alaman shigar sako

Hjy fatihat ne tay sauri zata dauki sakon ta goge dan karta gani hanklinta ya kara tashi, kafayat tay wuf ta fauce wayarta a masife tana kuka, hjy fatihat na kkrin hanata tana cewa kafayat dis will only hurt u kidena bincikan sirrin damilare ina ruwanki da kudin da ya kashe wa matarsa? …

Ko ajikinta ta kwace wayar ta gudu dashi can gefe snn ta bude tex din da sauri sauri tana kallon amount din da Ahmed ya kashe ma Adiaha a mall kuwa ta sake wayar ahannunta ya fadi kasa ta fasa wani irin kara ta zube kasa in total nervous break down.
[6/11, 10:37 PM] SURAYYAHMS: Hajiya fatihat ta karaso kanta da gudu a rude tanamai tattabata kafayat arikice,kafayat meya sameki haka? Ganin ko motsi batayi yasaka ta rasa inda zata saka kanta kawai ta dauki wayar a rude ta duba sakon tana kalla saida idonta ya fiffito waje itama..

Ta rike baki”Haaaaaaa, tayi ihu tare da cewa 2.9 million just like that?..
aje wayar akasa tayi hannunta na rawa rawa..ta koma kan yarta kafayat da fuskat tausayi “kafayat pls wake up errh damilare bashine kadai namiji a duniya bafa
…kafayat Karki kashe kanki da baqin cikin damilare, dagangan fa yake mikii wann abu dan ya kasheki da baqin ciki ki kare alalace,pls dont mind him my doter he is a very wicked child..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected