VENNETE
KISHIYAR KABILAH Book 2 Complete Hausa Novel

KISHIYAR KABILAH Book 2 Complete Hausa Novel

..and how crxy and how difrent its sound.

Tunda ta iso gidan bai ma dawo hayyacinsa ba bare ya tuhumeta yaji dalilin dayasakata ta yanke danyer hukuncin juyowa Abuja ita kuwa atake tay tunanin halama abunda ya keeping dinsa busy kenan baiga texes dinta ba shiyasa ya shareta.

Yasani sarai zata dawo din amma haka ya wani fixge ya kuma dauke kai yay kamr baisan tanayi ba, sai yay banza da batun dawowartan wnda hakan ya balain damun zuciyarta upon dukkan halin kishi da zafi data ke ciki ayanzu.

Acikin kwana biyun bakaramin cin fuska da tijara da kuma bakin ciki ta shaƙa awajensa ba.

Acikin ruwan sanyi ya sakata tagane cewa shifa yanxu ne yasan da cewa ya kwana da ƴa mace snn yasan me ake kira da jin dadin jima’a gabaki daya arayuwarsa.

 

Rikitaccen soyayya da kuma kulawa da yake nunawa yasrah agabanta kwana biyu shine ya sakata tafara amincewa da cewa tabbbas Ahmed banata bane tun asali saidai Amincewa da hakan ne yake kkrin ya zame mata babban aiki yanxu sabida abune wanda ya soma taɓa lafyar kwalarta sosai.

Haka zataje toilet tay kuka tay birgima ta hana idanuwanta bacci cikin tsananin radadin kishi da zafi a boye batare da sannin kowa ba. Worst part of it shine tunda yasrah tafara jinya ya sakar ma Adiahan ragamar komi na aikij gidan.

Zata yi musu komi na kulawa amma bayason ma ta fiye kebewa da matarsa sai yanaganin kmr cinye masa ita ma za’ayi mai gabaki daya.
.
Duk wani mafarkin so da shakuwa datay tunanin samu a wajen Ahmed shine take ganinsa yana rawar kafar bawa yasrah ninkin baninkin sa…
.

Wani bin kakarta kawai take danneta amma abun yakan ma xycyarta nauyin tsiya dan kuwa ko rabuwa da iyayenta datayi akansa bai mata tsananin zafi da ciwo tay dandanasinsa kamr yadda ta dandana saninn dawowarta gidan datay musu acikin gaggawa haka ba.

Wani irin baqin ciki, da cin fuska da kuma tashin hankli shikawai taxo taci karo dashi anan abuna dan kuwa wani abu bai sauya ba haka har saida yasrah ta samu cikken lafiya kafin ta fara samun lafiya a wajen Ahmed.

Abubuwan dataxo ta tarar din sosai ya raɓa mata lafiyar kwakwalwa dan haka ta sauya mood dinta gabaki daya.

Dake tana da kyaun zuciya dacan ta karaya tafara tunanin komawa yolan kawai tabarsu anan ya ji da matarsa dayake rawan kafa akai ita sai ta koma taje tabi shawarar kakarta tay cikkakken gyara koda xasuxo suxauna kowa tashi ta ficceshi.

Saidai kuma tun dataga Ahmed ya fara asalin honey moon yana kuma spoiling din yasra da gifts kala kala sabbi masu daraja na kudi wanda ita kanta batay tsammanin ma yana da irinsu ba sai taji ta sake shigewa cikin yanayn tashin hankli.

Ranar da ya kawo ma yasrah kyautar mota sabuwa kal har yau Adiaha bata mancr cakka mata maganan da yay agaban yasrahn ba.

Kowa na mata murna cikin raha tace mai itama ai daya canxa mata motar taci albarkcin amarya tunda nata ya tsufa sai ce mata yay ai itama ba a sabuwa dal ya sameta ba shiyasa yabata scnd hand dede da ita itama yasrah ya bata sabuwa ne sabida shine dede da ita wannn magann daya cakka mata haryau bakaramin ciwo yake mata aranta ba.

 

Bayan kusan wata guda rayuwarsu ta kasance ahaka kowani rana da irin salon takaicin da Adiaha take kwasa awajen mijin nata wanda baimasan yana kan cusawa xucyarta ba.

Duk sanda ya kwana da yasrah suka samu shakuwr aure tofa ranar saidai fa tay hkri dan sauyawa yakey gabaki daya ya dawo mata zararre.

Wani bin bata iya nitsuwa tay bacci haka nan zata so ta manne musu a kofar dakinsa tanajinshi yana rusa jarabbeb ihu yana santi akan yasrah cikin dare.

Akan yasrah ta fara gane cewa tabbas aikinsa na asbiti bashine number one ba yana da cikken lokci arayuwarsa na dawowa gidan kowani time idan jarabarsa ta cicciyoshi dan Koda da Tsakar rana ne inhar ya samu ya lume daki tare da yasrahnsa toh baya fitowa da wuri.

Wannn ababen da suka dibga faruwa agaban idanunta sosai suka fara sauyata duk da haka ta daure tanata neman mafita makanta gashi kishi yanahata komawa yolan haryau bare ta jr ta nemo gyaran itama.

Bayan yan wasu lokuta bada jimawa ba yasrah ta fara nuna alaman kamr ta samu karuwa na shigar ciki lkcin hjy khadijatu sun dawo abuja da Alhaj bello bayan angama masa duk wata aiki anata jira aga saukinsa nan da wata guda koda zai iya takawa da kafafunsa kamr na dacan.

Tun daga wajen bokaye da kafayat take bibiya tajiyo labarin shigar cikin yasrah tana son tay mata wani abu irin Abunda tayi ma Adiaha amma yanxu babu kudi kuma goddess ta juya musu baya.

Adiaha tasha mamaki kwarai data lura kamr kafayat ne kadai ta soma sanin cewa yasrah ta samu cikin Ahmed.

Tun suna mamakin junansu har kafayat tazo ta cire kunya ta kawo mata shawara akan su hada kai kawai su hana yasrahn aihuwa agidan Ahmed inyaso kowa yay biyu babu azaman auren sun.

Farko ma dixga ta Adiaha tay amma with time da dukaa family aka zo aka fara fahimtar cewa yasrah tana da cikin Ahmed din dagaske shikenan aka kuma maida hankula kan yasrahn duka ana tarairayata.

Tsantsar soyayya da kulawar da Ahemd yake bawa yasrah ninkin baninki yasaka kafayat jin tsananin kishi da borin fushi nan da nan ta kara kaimi wajen shigewa jikin adiaha akan lallai lallai kawai su haɗa kau su hana yasrah aihuwan itama.

Adiaha bata tashi aminta da zancen kafayat ba har saida Ahmed ya fara mata rashin mutunci da cin fuska akan ciwon laulayi da yasrahn takeyi.

Komi akay na laifi sai yana dorawa akanta kamr ma itace nanny din yasrhn yagama raina mata wayo sosai, haka nan yake mata masifa idan yaga wani abu kalilin ya faru akan cikin nn saiyana mata salon maganan banza ciki habaici kan cewa ita kasa samar masa da, haka matayen gidan zasuta gulma suna cakka mata magana cikin raha akan lamarin.

Saidai hankli da nitsuwar yasrah yasaka Adiaha bata iya daukar abun too personal aranta domin kuwa sosai yasrah tana tare da ita akowani hali tanamai sanyayata da kalamai masu dadi da kuma nuna mata jinjina da kyautatawa.

Ranar da aka fara kai yasrah kwaji asibiti kusan kowa saida ya shaida a asibitin cewa Ahmed ya kawo matarso, dan hat yar karamin suprise baby shwer saida Ahmed yay ma yasrah aka rabashe agidan akaji dadi aka babbata kyauta.

 

Adiaha batay ragon azanci ba ta gayawa kakarta halin datake ciki na damuwa da kuma mummunan tsoro data keji ganin yadda Ahmed ya sauyawa akan yasrah gabaki daya akan gindi datake bashi ya naci, toh inaga ace yau kuma ta haifa masa yaro ko yarinya agidan, batajin ma zata samu wani gurbi arayuwarsu kenan nahar bada.

Tunani take koda zata bi shawarar kafayat din ne su yi ma yasrahn wani abu duk dama haryau aranta tana mugun son yasrah aranta sosai shiyasa ma take iya shanye wasu walakancin da ake mata akanta sabida duk abunda Ahmed yake yi mata na cin fuska dede da rana guda yasrahn bata taɓa mata irin haka ba wani binma itace kawai zata lallabeta tay ta bata hiri akansa harsai tay sanyi

Tanajin azaban kishin yasra amma deep within her heart gaskiya bata son ta cutar da ita.

Koda ta gayawa kakarta hakan atake kakar nata ta kawo mata wani sabuwar shawarar da bata taɓayin naxari akai ba.

Saidai wnn ba akan yasrah ba akan kafayat ne..

Nan da nan kakar nata ta soma mata bayani inda ta dada karkatr mata da tunaninta akan kafayat buraimo, nan tace mata ta fara bincikar kafayat akan yawan xubewar nata cikin tukuna, just to make sure if she is clean bata da hannu acikin nata misery din, if not tace mata amfani da ita kawai zatay su cutar da yasrah abaza bayan itama itace ta cutar da ita karshe kuma laifinta za’a gani hala Ahmed ya zo ya tsaneta har Abada in asirinsu yazo ya tonu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected