KISHIYAR KABILAH Book 2 Complete Hausa Novel
Leadersu da ake cewa maman iyabo itace ta iso har gaban hjy khadijatu tana wani diri tana kumfar baki tana zaxxare mata ido tafara mata magana cikin bada oda da doka.
Sai cewa take lallai hjya khadijatun barauniyar y’aya ce,ta sace yayan da ba ita ta haifesu ba, snn kungiyarsu tana umartan ta akan tay gaggawar maidawa alaji bello jimada ragamar kulawa da yayansa da jikokinsa idan ba haka zasu dauki mataki mai muni akanta dan bazasu taba yarda ayiwa dan uwansu haka ba.
Wasu dattajan daga cikin matan suka fara mata gorin cewa ai ba itace ta haifesu ba amma tazo ta mallakesu ta rabasu da ubansu sabida kwadayin abun duniya.
Wasu sukace asiri kawai tay musu shiyasa ta juya kansu akan ubansu sabida mugunta irinta kishiyar uwa.
Masu rashin kunyar cikinsun kuwa harda debo toka da fenti wai zasu watsa mata ajikinta acewarsu ita matsafiyace..
Har sun hargitso kusa da ita Hajy khadijatu, brother kazim yay wuff cikin razanasu kamar zai haura kansu da duka, nan tay sauri wajen hana brother kazim turesu kasa sabida yadda taga ranshi yabaci sosai batason yay rashin kunya ko yaji ciwo wa wata tsohuwa dan matayen duk sun kusa haifansu awajen, ranshi na baci sosai kawai saiya bar wajen a mugun fusace ya koma can gefe jikinshi na ɓari sabida bazai iya tsayawa snn yay shiru ba
Brother hamzat ne yace musu su tattara tsoffin kafafuwansu subar musu tsakar gidansu ko ya kira musu polisawa atafi dasu.
Shugabansun sai tafara masa masifa tanayi har kamar zatayi fada dashi
Duk su anty adixat sai suka tsoma baki aka fara hayaniya awajen sosai dasu.
Ahaka hjy khadjatu ta fahimce cewa duk dai shirinsu anty mojushola ne dan kawai Alaji bello da matarsa su dawo zama acikin mansion din tare da yayansa.
Murmushi tay dan bataga amfanin pulling wann gangamin draman ba,aganinta ko dakansu sukazo gidan akayi magana idan yaransa suna da niyya ai zasu dawo dashi..but is bcos they clearly want to humiliate her, suna son dai lallai suga tana cikin kunci da bakinciki..
Allah yasa itama dai ta haihu da ace bata saka nata dan agidan ba da hala batasan wani irin cin mutunci zasu mata ayau ba.
Suna cikin wann hayaniyan saiga Ahmed nan ya fito cikin gaggawa da alaman hayaniyar ne ya fitar dashi shima yazo adede lokacin matar tana cewa zata shafawa hjy khadijatu toka wai haka dokarsu na matan kungiyar yake, sukan yaɓa maka wani shaida na penti ko toka ajikinka as a reminder na cewa zasuzo su dauki mataki akanka idan baka dena aikata muguntawa mijinka ba.
Takaici duk ya ishe hjy khadijatu Dan wann shine acuceka snn ahanaka kuka. Itace akayi wa rashin mutuncin amma wai itace akazo ake lakawa laifin komi.
Kafin kace kobo har Ahmed ya hargitsa taro ya shiga cikinsu ya fara kkrin kwace ruwan pentin zai watsa ma shugaban nasu brother hamzat ne ya rikesa da sauri.
Anata kkrin controlling dinshi can sai akaji dirin masifa daga baya sister zainab ce ta shigo.
Tunda matayen nan suka hangota daga gate tana zuwa sukadan fara rusuna masifarsu dan sunsan batada kunya kona miskala zarratin kowa yasanta area scatter ce.
Tana zuwa tafara binsu daya bayan daya tana zakwalo asirinsu tana tonawa da karfi acikin balbalin masifa na tsaurin ido da rashin mutunci,acikinsu daga wanda suka kashe kishiyoyinsu, sai wanda suke cin amanan mijinsu, sai wanda suke juya kan surakunansu,sai wanda suka lalata destiny din yayan kishiyoyinsu,sister zainab saida tabisu one by one tana fadin musu nasu matsalar tana tono musu asirinsu harda wayanda suke ci da shi akarkashin yayansu mata karuwai.
Nan danan wajen ya dauka da shiru bakinsu duk ya mutu sai borin kunya ya tashi aka fara boye roban fenti da toka
Saida kura ya lafa snn hajya khadijatu ta tsaya tay addressing din shugaban nasu datake ta cika bakin cewa zasuje su shirya su dawo da yan jarida…”hjya tace musu. Suyi duk abunda zasuy amma susan da cewa zata iya kaiwa kararsu gaba cos they are invading in her personal life, tace musu ita ba kabilarsu bace bare suce zasu treating dinta da wani law na kungiyar kabilarsu. Snn tace ma shugaban nasu cewa tasani cewa ita cikkiyar mace ce bata kasa ba, dukkan wani matsala dake wakana a familynta zasu yi resolving din kayansu da kansu batare da saka hannun kowani kungiya ba..tay warning dinsu agaban kowa tace duk sanda suka kara dawowa mata gida duk abunda tay musu sune suka jawo.
Haka suka tattara sauran borin kunyarsu suka bar gidan suna babatun cewa zasu dawo tare da yan jarida kuma zasu yadata duk duniya domin agani cewa ta raba yaya da mahaifinsu ta hanyar asiri.
Hajy khadijatu bata sake kulasu ba tay calming kanta acikin gaggawa snn ta umarce dukansu akansu shiga cikin gidan ayi breakfast din tare.
Adiaha ta kammala aikinta kenan ta fito tazo ta samu lkcin har angama hayaniya sai binsu da ido kawai takeyi da mamaki ganin yadda kowa acikinsu yake famar haɗa rai sunata mita da masifa kasa kasa da yarensu.
Ahmed da sister zainab dake sunfi kowa masifa da iya bori har aka zuba musu abincin ma basuci ba, bayan an kammala cin abincin hjy khadijatu batace ma kowa uffan ba ta kama hanyarta ta haura sama can dakinta.
Brother kazim da brother hamzat ne suka bita saman dansu je su bata hakuri.
as usual sister zainab saida ta daka ma Adiaha wani tsawar da saida ta razana ta missing step ta fadi kasa ta mugun buga yatsarta,ihu tay tsabar taji zafi, Ahmed na kallonta ya tashi yanajan tsaki yabar wajen baice mata komi ba…
Su anty adizat ne suka dinga bincike suna shige da fice har saida suka samo asalin gaskiyar abakin kawayen kafayat musammn ma business patner dinta zikirat.
Sunsan kafayat bata boye ma zikirat komi dan haka suka bugi cikinta sukaji labarin cewa ai itace ta matsawa alaji bello cewa saidai adawo da ita cikin mansion tace musu jiyan ma bai kwana agidansa ba sabida tsabar tasakoshi agaba tahanasa samun kwanciyar hankli.
Ranar dai haka aka wuni agidan ana memeta wann maganan kafayat kuwa tasha buhun barkwanon tsinuwa da zagi awajensu bana wasa ba.
A fanninsu anty mojushola kowa duk a tsarge suke da tunanin abunda zai iya biyowa baya har yamma ya rufa suna dar dar da basuji an nemesu ba. .
Hajy khadijatu taji babu dadi aranta ammq bata yanke wani hukunci har sai washe gari bayan ta samu nitsuwa ta nemi shawara awajen babban dadarta hajiy maimunatu.
Dacan anata ra’ayin tay tunanin kawai tabar musu gidansu inyaso sai babansu ya kawo musu matarsa suzauna tare tunda dama dan itace duk akeyin fadar akai, tasan kuma idan ta umarce yaran da suyi hakuri suzauna da ubansu kobabu ita zasu iya mata biyayya duk dama zai musu wuyan amincewa.
Tana kammala fadawa
Hjya maimunatu plan dinta tace mata sam bata amince mata ba dan inhar ta tafi tabar gidan shirinsu ne zai lalace, haryau tanakan bakanta na koyawa alajo bello wayo acikin ruwan sanyi. Gani take kmr in har sukabar yar yarinyar nan ta kore yar uwarta a dakin mijinta acikin sauki haka sunyi abun kunya.
Zama tay ta gaya mata yadda zatabi da komi dalla dalla bata boye mata komi ba snn sukayi sallama.
Bayan tay wasu tunani na wasu yan awowi sai can wajajen bayan ishai ta aika aka kirawo mata brother kazim ta zaunar dashi a falonta tay masa nasiha sosai snn ta umarce shi akan da ya dawo da mahaifinsa kawai ita batada wani matsala dasu.