VENNETE
KISHIYAR KABILAH Book 2 Complete Hausa Novel

KISHIYAR KABILAH Book 2 Complete Hausa Novel

Haka nan kafayat taci gudu gashi ta daure mata hannu da baki babu halin yin ihu gashi lokcin kowa yana cikin gidansa saboda safiyane sosai.

Haka karnuka suka yayyaga mata nitynta ta koma gidnsu almost half naked babu takalmi tanata kuka tana zage zage.

Ran hjy fatihat ya baci sosai, wato zainab ita kullum tazo saita ci galaba akan yarta kenan?

Acan gidan kuwa alaji bello ya farka abacci wajen karfe 12 na rana dake yau baiji kafayat ta zo da rigimarta bare ta damesa ba, harya fito tsakar gidan yanata neman kafayat din duk wanda suka ga abunda ya faru da safen babu wanda yace masa uffan hanklinsa duk ya tashi dabai ganta ba.

Haka yayi zugum ga kuma can wayarta a daki babu halin kirarta.

Harsaida kafayat ta huce snn ta kirashi a wayar mamanta da yamma can snn ya fahimce asalin abunda yake faruwa da ita ransa a bace yaje har gidansun dakansa ya dauko amaryansa kafayat din suka taho tare har da mamnta hajy fatihat, bayan ishai akazo aka tara kowa aka fara case kusan dukkan yaransa suna nan babu yadda hajiya khdjatu ta iya hakanan tazo ta tsaya ma yaran nata duk dama batace komi awajen ba.

Yau kwanan kafayat shabiyu da dawowa amma kusan kowani rana sai anyi karami ko babban rikici acikin gidan

Yau din ma haka alhaj bello ya kwanta agaban yayansa yana ihu yanacewa _wa lati sa_ kuzo kubugeni..

Dukanku uku Kuzo ku bugeni ku huce takaicinku akaina

Wann rainin wayo ya isheni haka _imọran onilàkaye yii dara_

Duk saida ya daga musu hanklinsu sosai

Nan aka fara warware magana yafara tuhumar kowa akan ketare iyaka, duk yaransa suka taru sukace idan har kafayat din bazatana kama kanta ba suma bazasu hana kowa rainata agidan ba.

Hayaniya aka dingayi 1-1 dan kusan kowa yana da point dinsa mai karfi.

Kafayat ta tubure tace masa sam ai tun farko yaransa sune basu dauketa matar uba ba, su kuma yaran suna tuhumarta da rashin kame kanta acikin gidan nasu. Ahmed ko tari baiyi awajen ba, nashi ido dan baison ma yasaka musu baki ta rainashi, Dake duk tasan mijinta bayanta zai bi hakanan ta dinga kukan makarici tana kawo karairayi har dai tasaka aka mare sister zainab aka saka ta bata hakurin dole snn aka rufe case din mai gabaki daya.

They agreed that kowa zai tsaya adede limit dinsa amma kafayat cewa takeyi aranta yanzu ma zasu fara gani.

Wani irin tijarar bori da mahaifinsu yay musu ranar dukansu saida jikinsu yay sanyi sosai

Kowa acikinsu saida yay wa zagin tass tass yace musu duk wanda ya sake
Masa bori akan aurensaa da kafayat toh ranan zai tsine masa albarka.

Jikinsu yay sanyi sai basuce masa komi ba Musammn ma brother kazim da babu abunda yake memetuwa a idonsa face yadda ya dinga fadi akasa agabansa yana birgima yana cewa suzo su bugesa idan suna jin haushin aurensa da kafayat har akantane yake cewa zai rabu dasu zai tsinemusu albarka.

Sister zainab kuwa tunda akasata ta bawa kafayat hakuri ta dinga kuka tana tsinuwa mai zafi akan babansun tanacewa yaci amanansu ne danyaga mamansu na ainihi bata raye bayan itace silar dukkan wani arzikinsa dayay arayuwa da har dayake tinkaho da sunan sa ayanzu.

Agidan ta kwana wajen hjy khadijatu tanata aikin rarrashinta wai koda zuciyarta zaiyi sanyi.

Duk hanklinta sai ya tashi dataga yadda kafayat ta buga makircin ta saka mahaifinsu yaci musu mutunci sosai ya nuna kamar baisansu ba.

Yau Kusan kwana tay tana waya da yar uwarta dik tausayin yaran ya kamata sosai dan aranta tasan kafayat batada hankli taga bazata iya da ita acikin sauki bane shiyasa takeson ta bada karfinta akan yaransa.

Da asubahin fari bayan ta idar da sallah ta nemi ganinsu asashenta dukansu..

Babu bata lokaci suka hallaro sashenta iya suya yasu yaran jimada.

She make sure dat agidan Babu wani wanda yasan ta nemesu privately dan A dakin daga ita sai Brother kazim da brother hamzat
Da zainab tare da Ahmed daya shigo daga baya.

Dukkansu a dar dar suka gaisheta sabida yadda suka ga fuskarta babu alaman fara’a ko yanayin lallami duk fargaba ya gume musu zuciya,har sun dauka itama masifa zata musu kotace zata rabu dasu na har abada.

Bayan sun gaisheta ta amsa musu babu yabo babu fallasa Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke kafin nan tafara musu magana dukansu cikin nitsuwa da sonta fahimtar dasu yadda ake cin ribar rayuwa.

Saida ta gama musu nasiha mai yawa snn tace musu su dinga danne zcyarsa Dan da akwai matattu dayawa da kalmomin su na raye snn da akwai rayayyu dayawa da ba’ajin kalmarsu dan haka susan irin kalmomin da yakamata suna furtawa.

Tace musu basuda zabi akan abunda zasu ji ko zasu gani yanzu,amma sunada zabi akan abinda zasu iya fada snn Batace musu su amshe kafayat a matsayin uwa ba.

amma tace musu shi
Kalman iyaye bayana nufin wayanda kawai suka haifi y’ay’a bane,
Shi kalmar iyaye itace ake bawa wanda yake kulawa da yaransa da kuma basu tarbiya mai kyau. tace Idan suna son susan matsayin tsoron Allah a zuciyarsu, su fara duba halinsu tukuna, snn ya kasance duk wani abunda zasuyi suyishi dan Allah badan kowa ba.

Game da auren baban nasu tace musu tasan yay musu zafi sosai harda itama,amma su sani cewa iya matsorata sune suke tsoron shiga duniyar soyayya, kamar yadda Masu hankli basu zama acikin duniyarta.

Tace su mance da zancen fushi da sukeyi da auren mahaifinsu dansu huta ma ransu daga walaknci da tozarci dan kuwa yawan hayaniya baida wata riba face kaskantarwa.

Barema ita kanta sai yanzu ta fahince cewa Ba’a tuhumar wanda yay aure da kalmar rashin adalci, tace dan haka Karku zauna kunata tuhumar mahaifinku da kalman yaudara dan yaje yay aure..

Da ace muku yana neman wancan karuwar yana neman wann gara yay auren koda auren baizama irin wanda sukeso din ba.

Tace Idan namiji ya aure mace toh wallh matarsa ce, idan har kuma ba matarsa bace toh kuna zamanku auren nan zai tarwatse basaima kun daga jijiyar wuyarku ba.

Tace ma sister zainab Shirunta shine zai rabata da kowa lafiya.

Tace ma su brother kazim mai hankli shine yasan inda dare yay masa ba. duk kun girma yanzu kun zama abun alfahari na, Bayan darajarku ta dan adam Lokacin ku shine mafi tsada agareku.

mahafinku ya riga da yaci zamaninshi da wata kafin nan ni,shin zaku bata kuriciyarku ne kuna fada dashi dan ya karo wata koko zaku ci naki zamanin cikin kwanciyar hankli?..

Sosai ta musu nasiha mai nitsuwar tare da igniting positive mindset a zuciyoyinsu.

Lokaci guda tasaka suka fara ganin cewa duk wani masifar da zasuyi da mahaifinsu akan kafayat is not even worth it.

Kamar yadda hajy khadijatu ta basu shawarar cewa yanxu lokacine da zasu tashi su cigaba da neman kudi suyi rayuwarsu mai dadi su moreshi dakyau tare da iyalansu hakan kowa yafara tunani.

Bayan sun kammala maganan kowa yay mata alkwarin zai gyara halinshi, snn suka babbata hakuri.

after a while bayan komi ya lafa nan tafara kiransu da daya bayan daya tana samun alone time tare da kowannensu batare da sunsan da hakan ba.

Brother kazim tafara yiwa nasiha akan cewa ya koma America bakin aikinsa dan izuwa yanzu yaci 1 month kenn anan nigeria bayan aikin kamfaninsa nacan yafi kawo masa kudi..

snn ta kara nitsar dashi a matsayinsa na babban yaya, tace masa komin rintsi karya dena kiran mahaifinsa ko ya dena tura masa kudi ko wani alheri, duk wani abunda zaiyi he shud do so with respect.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected