ABU NAKA BOOK 3 BY SODANGI
ABU NAKA…
3
HAFSAT C. SODANGI
Haqqin Mallaka (m)
Naquin mallakar littafin na Hafsat C. Sudan ne (Mrs. Yunus Abdullahi Davai)
Shekarar Bugu:
2006
An sake Bugawa A:
2015
Alura
An xan yi gyara a cikinshi kaxan saboda wasu dalilai, sai dai yana nan a kan tsarinshi na farko.
Na gode.
11/8/2006
TA`ZIYYA
Ubangiji ya ji qan HAJIYA AISHATU BALARABE (JAZAN). Marubuciyar litattafan ABOKIN HIRA da rahamarsa. Ubangiji ya kyautata makwancinta, in tamu ta zo kuma yasa mu cika da imani.
Amin.
ABU NAKA…-3
A
garin Misau gidan Gwaggo Habiba ranar Laraba da hantsi, Abu tana zaune kan kujera ‘yar tsugune a tsakar gida, ya yin da Gwaggo Habiba take zaune gabanta kan tabarma tana kuma goga mata goronta bayan ta gama gyara mata farcenta da ta yanke mata.
“Ni kuwa Inna sai nake ganin kamar bakya jin daxi saboda rashin walwalarki ta yi yawa, tun bayan kai Saddiqa gidan mijinta da kika yi har yanzu baki dawo cikin sukuninki ba. Sannan a zaman yanke miki farcen nan da na yi sai na fahimci jikinki yana vari tamkar wani abu ya tsorataki”.
Abu ta kalli ‘yan yatsun nata da aka ce suna vari kafin ta yi maza ta xauke qafarta daga kusa da ita, ranta a vace ta soma magana cikin faxa.
“Kin ga fa shi yasa jiya da shekaran jiya duk ban zo gidan nan ba, saboda yawan tasani a gaba da kike yi kina tuhumata zuwan Malam kan wai ya ganni ko bani da lafiya ne jiya, shi yasa yau ya zo kuma tun ban gama hutuwa ba za ki fara. To jikina ba zai yi vari ba ni ba tsohuwa ba ce?”
Gwaggo Habiba ta yi murmushi ta ce, “Haba Inna yaushe kika yi tsufan da jiki zai rinqa rawa haka?”
Ta xan kawar da fuskarta gefe ta ci gaba da yin bayani a nutse.
“Ni dai a zuciyata na san akwai xayan biyu in ma dai kina voye min halin da kika baro Saddiqa da mijinta a ciki, ko kuma ke xin baki da lafiya baki yarda kin gaya min ba, amma ki yi haquri”.
Abu ta zovara baki ta ce, “A’a, mene ne na vacin rai kuma daga magana, ko don an mai dani kububuwa don faxa?”
Suka ci gaba da wata hirar. Zuwa can Gwaggo Habiba ta ce, “Ni dai Inna yawan mafarkin Saddiqa da nake yi yana damuna”.
Gaban Abu ya yanke ya faxi, mafarkinta na daren jiya ya faxo mata. A firgice qwarai ta tambaye ta kema kina mafarkin ne?
Gwaggo Habiba ta xaga ido ta kalli Abu cikin nazari da lura, a hankali ta buxa baki ta ce mata, “Dama kina mafarkinta ne Inna baki tava gaya min ba? Kema ashe hankalinki bai kwanta da yanayin da kika barotan a ciki ba”.
Ta soma kuka, kuka kuma mai tsanani.
Abu ta yi hanzarin abka mata da faxa don ta kawo qarshen kukan nata.
“Sai na daina zuwa gidanku tunda haka kuke ke da mijinki, kun tasa Mus’abu a gaba bakwa mishi fatan alheri kullum burinku…..”
Ba ta kai ga qarshe ba ta tsaya saboda jin maganar da Gwaggo Habiba ke faxa.
“Zan tafi can garin in gano halin da Saddiqa ke ciki, zan je in gani da kaina in bai yi min ba zan xauko ta. Saddiqa marainiya ce ba ta da kowa sai ni, nice uwarta nice kuma ubanta. Yaya Gixe ne ya cuce mu ni da ita, shine ya xauke ta ya baiwa mutumin da ya fi mu sanin ba zai riqeta ba, baqin ciki kawai zai cusa mata. To ba zan barshi ba, dama tunda na ga ina munanan mafarkai a kan ta na san…….”
Abu ta katse ta da cewa, “Babu wani mafarki kina dai son zuwa wurin xanki ne kawai, in kuma kika fito ma kika ce za ki je ganin Mus’abu wa zai hana ki”.
Gwaggo Habiba ta zuba mata ido cikin kaxuwa wasu sababbin hawaye suka zubo mata masu zafi saboda takaicin kalaman na Abu, sai dai babu yanda za ta yi.
Cikin nutsuwa ta ce, “Haba Inna, ni kuwa me zai sa ki gaya min haka? Kin sani sarai in ban da Saddiqa tana wurin nan babu abin da zai sa qafata ta taka gidan nan”.
Abu ta ce, “Oh’oh! Ni za ki kawowa wayo, in so kike a dubo miki Saddiqa ba wurinshi za ki ba, ba kya tunanin in je in gano miki in zo miki da wani sabon labarin”.
Ta miqe tana jan zanin ruhuwarta tana tafiya, fita gidan take nufin yi tana kuma qarasa zancenta, “Ba fa hanaki zuwa gidan nashi nake nufin yi ba, ai ba a raba xa da uwa”.
Takaici ya kama Gwaggo Habiba, can cikin maqogwaronta har wani xaci take ji saboda vacin rai, sai dai babu halin ta tanka.
“In kin je ki gai da Mus’abun”.
Ta faxi daidai tana fita.
Da daddare Gwaggo Habiba tana tare da mijinta Malam Abdallahi a gefen tabarmar da yake zaune yana cin abincin shi, yana kuma sauraron bayanin da take mishi na yanda suka yi da Abu.
Sai da ya ji ta yi shiru sai ya yi murmushi ya ce, “To ai sai ki haqura ki tura ta xin tunda ta ga za ta iya wannan wahalalliyar tafiyar”.
Gwaggo Habiba ta kalle shi cikin nutsuwa ta ce, “To amma Malam wane bayani Inna za ta zo da shi in dai a kan wannan yaron ne? Ka santa sarai halinshi na zahiri ma in za a faxa ranta vaci yake yi, ko yanzu ma kuma na fi zaton akwai abin da take tsoron kar a je a gani wanda yasa take faxanz uwan da na ce zan yi balle a ce ita ta zo ta faxa da kanta”.
Ya ce, “Eh, duk da hakan cikin biyu ne za ki zavi xaya, ko ita xin ta tafi ne ko kuma a haqura gaba xaya tunda ga irin kalaman da take furtawa”.
Gwaggo ta ce, “Ni kam gara in dangana in yi ta yi mata addu’a Ubangiji ya kuvutar min da ita daga dukkan sharri”.
Ya ce, “Eh, hakan ma yana da kyau”.
AJAKUTA
Mus’ab yana tsaye a falon cikin tashin hankali da fargabar rashin ganin Saddiqa a cikin gidan.
“Ke Zainab”.
Ya sake qwala mata kira da sake fitowa da gudu hawaye suna zuba a idonta
“Kin leqa nan maqwabta zuwa wajen su Abida ba ta nan?”
Ba ta iya amsawa ba saboda yanayin da ta ga Mus’ab a ciki, in ban da rawa babu abin da jikinta ke yi, ga shi kuma kusan awa xaya da rabi ne tunda suka nemi Saddiqa a gidan basu ganta ba cikin gida da cikin Ajakuta babu ita babu dalilinta.
“Kika ce kinga tana waya?”
Ta gyaxa kai nuna alamar eh, haka ne.
“Me kika ji tana faxa?”
Ya sake wata tambayar.
“Ban ji tana magana ba sauraro kawai na ji tana yi”.
Gabanshi ya sake faxuwa da ya gane wayarshi da Sarah ta saurara.
Anya Saddiqa tana garin nan ma kuwa?
Kai tsaye tambayar ta fito mishi daga cikin zuciyarshi. Kar dai gudu ta yi za ta koma Misau?
Bai jira jin amsar da zuciyar tashi za ta ba shi ba ya yi waje da gudu ya nufi cikin motarshi, sai da ya tabbatar ya xaure kanshi tamau da belt xin dake jikin motar sannan ya shiga tayar da ita, cikin zuciyarshi kuwa addu’o’I yake ta karantowa iri-iri na neman tsari da taimako wurin Ubangiji.
Mus’ab yana tafiya cikin matsanancin gudun da ba zai kwatantu ba, duk da kashedin da zuciyarshi ke yi mishi saboda yanda iska ke kaxa motar duk da mota ce mai nauyi.
Wayarshi ta yi qara a karo na uku, ya yi kamar ya sake yin buris da ita sai kuma ya yi tunanin to ko dai wani cikin masu taya shi neman ta ya ganta? Ya yi maza ya miqa hannu ya xauki wayar ya karata jikin kunnenshi.
“Hello!”
“Mutanen nan fa sun qi yarda su karvi cikiyar da muka kai musu, wai sai bayan awa ashirin da huxu da vacewar ta tukunna”.
Muryar Sani ce ta yi mishi wannan bayanin. Bai tanka ba ya mai da wayar mazauninta ya ci gaba da tuqinshi, cikin zuciyarshi kuwa mamakin hukumar ‘yan sanda yake yi wai basa karvar labarin vacewar mutumin da ya shekara goma sha takwas sai bayan awa ashirin da huxu da vacewar tashi. Ko mene ne dalilinsu na yin hakan? Oho!
Ya kwatanta yawan awa ashirin da huxu abin da za su iya yiwa Saddiqa sun isheta ta je har Misau ta zauna ta huta, ta ma kwana tana baiwa Gwaggonta labarin Mus’ab da abubuwan da ta gani a tare da shi.
In har Saddiqa ta samu nasarar isa gaban Gwaggo anya auren shi da ita zai xore? Tambayar da ta zo cikin ranshi kenan.
Tafiya mai tsanani ta awowi uku da mintoci arba’in kafin ya iso wata mararraba ta motocin da suka fito daga kudu suka nufi arewa, a nan ya yi parking cikin surquqin bishiyoyin da suka lulluve wurin, ya fito daga cikin motarshi riqe da kwalin sigarinshi a hannu da fankon ashana, cikin zuciyarshi yana tunanin a irin tafiyar da ya yi in dai Saddiqa motar haya za ta shiga kuma direban mai hankali ne, to ya wuto shi a baya, yana lissafi tare da raba awowi da mintocin tsakanin abin da ta yi kafin isarta tasha da shigar ta mota, da sallamar direba, har kawo isowarsu wannan mararrabar da ya ja ya tsaya.
To in kuma vuya ta yi a cikin garin fa?
Wata zuciyar ta aiko mishi da wata tambayar. Wurin wa? Ya sake tambayar kanshi. Nan da nan ya kori wannan tunanin.
A sanin da ya yiwa Saddiqa gida kawai za ta dosa ba za ta tsaya neman mavoya cikin mutanen da ba ta sani ba.
Da wannan tunanin ya isa wurin ‘yan sandan dake lura da wajen waxanda suka tsare hanya suna ta faman karvar naira ashirin wurin qananan motoci, hamsin ko xari wurin manya, gwargwadon dai irin lodin da ka zo da shi.
Barka da aiki Yallavai”.
Mus’ab ne yake isar da gaisuwarshi wajen xan sandan dake zaune kan wata mota a gindin wata bishiya mai yawan ganye da inuwa, wanda shi ke shugabantar wannan Road Block xin.
“Yauwa barka dai”.
Ya amsawa Mus’ab gaisuwar tashi bayan ya gamsu da kallon da ya yi mishi.
“In ce ko lafiya?”
Ya tambaye shi.
Mus’ab ya sanya hannu cikin aljihunshi ya zaro hoton Saddiqa da ya saka a ciki daidai yana cewa, “Lafiyar ba ta da yawa yallavai”.
Ya miqa mishi hoton yana cewa, “Matata ce ta baro gida ina kyautata zaton za ta biyo ta hanyar nan in har ba ta riga ta wuce ba, taimako nake so ka yi min na in tsaya tare daku”.
Ya yi mishi bayanin abin da yake so suyi mishi.
Xan sandan ya zubawa hoton ido ba tare da ya ce komai ba, tamkar dai wani nazari yake yi. Bai barshi ya kai qarshen tunanin nashi ba ya zaro bandir xin xari biyar-biyar ya jefa kan kujerar motar yana cewa, “Wannan a baiwa yara su sha kunun zaqi”.
“Ai ba sai ka yi wannan wahalar ba don za ayi maka xan wannan taimakon, su mata waxansu irin mutane ne, al’amarinsu har mamaki yake bani, ga shi dai duk wahalar da muke yi a rayuwarmu mafi yawancinta a kansu muke yi, amma basa gani balle su yaba mana, sun fi so kowane lokaci su rinqa tayar mana da hankali. Ni wani lokacin idan abin takaicinsu ya ishe ni sai in ji tamkar a raba mana wurin zama a ce ga garin mata ga na maza, su yi harkarsu muma muyi namu kowa ya yi harkar gabanshi ba ruwan wani da wani ko kuwa?”
Mus’ab ya yi murmushi daidai lokacin da ya gama fitar da hayaqin sigarinshi daga bakinshi, ya ce, “To amma yallavai da anyi hakan anya duniyar za ta yi mana daxi kuwa? Ai ina ganin da bamu yi jarumtakar da muke yin ba ma”.
Yallavai ya yi tsaki mai qarfi ya ce, “Ai kuma tsiyar kenan”.
Ya diro daga kan motar ya nufi cikin motarshi kamar zai ajiye sandar hannunshi, nan kuwa yana nufin sanin abin da Mus’ab ya ajiye mishi ne. yasa hannu ya xauka ya adanasu kafin ya fito, ya kalli Mus’ab cikin yanayin murmushi ya ce, “Amma wannan kunun zaqin ba zai yi musu yawa ba kuwa?’
“A’a, haba Yallavai wannan wuni da kuke yi a rana”.
“To an gode, bari in haura can wajan nasu don in ga irin aikin da suke yi”.
“To Yallavai”.
Mus’ab ya yi godiya, ya koma inda ya voye motarshi a surquqi ya zauna yana hangen abin da su Yallavai suke yi a inda yake voye.
“Park well!”
Tun Yallavai bai qarasa isa ba ya shiga ba da umarni, nan da nan motoci suka yi ta yin parking a gefen hanya.
Qananan ‘yan sanda suka shiga sosai leqa motoci, har duba but saboda umarnin Yallavai. Shi kuma hankalinshi yana wajen fasinjojin motocin ko zai dace da ganin yarinyar da hotonta ke sunne cikin aljihun wandonshi.
Ta kowanne vangare motoci sunyi dogon layi, ga matsanancin bincike cikin zafin rana Yallavai sai xigar gumi yake yi amma babu alamar zai gaji.
Mus’ab yana zaune cikin motarshi cikin fargaba da zaquwa daxewar lokaci ne ya dame shi, anya basu riga sun wuce ba ma kuwa? Ya tambayi kanshi.
Yawan harbawar da zuciyarshi ke yi ya hana shi ci gaba da zaman cikin motar, ya fito ya nufi bakin hanyar shima.
“Yallavai na ce anya basu riga sun wuce ba kuwa?”
Ya yi tambayar a yanayi na damuwa. Ya zubawa agogonshi ido tare da nazarin daxewar da suka yi a wurin suna cajin motocin.
Ya xago ya kalli Mus’ab ya ce, “Ina ganin har yanzu ba zamu fidda rai ba, ai ka san ba daga gida kai tsaye za ta kamo hanya ba, sai ta je tasha tukunna. Don haka ka qara haquri a wurinka don ba zamu so tsayuwarka a cikin mu ba”.
Mus’ab ya sake kunna sigarinshi ya sanya a baki, kafin ya sake gangarawa wurin zaman shi. A daidai wannan lokacin wata mota ta iso wajen peogout qirar station wagoan, ta bi bayan sauran motocin dake tsaitsaye.
Yallavai ya nufe ta da sauri zuciyarshi tana dakan uku-uku, anya ba ita ba ce wancan? Zuciyarshi ke tambayar shi.
Cikin hikima ya qara kallon hoton don ya qara tabbatarwa. Ita ce. Zuciyar tashi ta qara tabbatarwa. Yasa hannu ya buxe qofar motar.
“Fito nan”.
Ya nuna ta da sandar dake hannunshi.
Mutumin dake jikin qofar motar wanda sai ya fita kafin ta samu damar fitowa, wanda tun shigar shi motar hankalinshi yake kanta, iyaka dai bai ga fuskar yi mata magana ba, don haka ya mai da nutsuwarshi kan mujallarshi yana sauraron zuwan lokacin da zai dace da yi mata maganar.
Ya xago kanshi ya kalle shi ya ce, “Ta fito ta yi maka me?”
Gaba xaya jama’ar motar suka zubowa Yallavai ido.
“Common fito nan”.
Ya ba da umarni mai zafi don tuna musu ko shi waye?
Mutumin dake varin nashi ya fito ya tsaya gabanshi suna kallon juna.
“Wai kai waye da kake ja da hukuma? Ka kuwa san matsayin wannan abin da kake yi?”
“Ban sani ba Yallavai sai ka gaya min”.
Ya yi mishi bayani a yanayi na gatse.
Yallavai ya rabu da shi ya mai da hankali wajen baiwa Saddiqa umarnin fitowa”.
Mai mujallar ya kalle shi ya ce, “Haka kawai za ta fito ba tare da ka yi mana bayanin dalilin fitowar tata ba? Me yasa baka ce kowa ya fito ba sai ita wannan yarinyar?”
“Ita wannan da kake gani ta gudo ne daga gidan mijintaa, shi yasa zan fito da ita don in mayarwa mijinta da ita”.
Jin wannan bayani na Yallavai yasa wurin ya kaure gaba xaya fasinjojin cikin motar, waxanda mafi yawancinsu maza ne suka firfito suka kewaye Yallavai, daga masu gyaran zanzaro sai masu naxe hannun riga tare da faxin, “Wannan ai shine zance, ka tsare mu cikin jeji ka fitar da tsaleliyar budurwa a cikinmu ka ce wai za ka mayarwa mijinta da ita. To a wane matsayi, waliyi ko wakili?”
Hargowa ta jawo hankalin sauran jama’a suma suka firfito, masu isowa ma kowa ya zo sai ya yi parking ya fito don ganin abin da ke faruwa, duk wanda ya iso sai ya buqaci sanin me ke faruwa? Tun ana bayani na gaskiya har aka koma qara gishiri a kai.
Mus’ab ya iso wurin don ya kasa fahimtar abin da ke faruwa, cincirindon jama’a yasa ko motar ba a gani daga nesa, da qyar ya kutsa kai ya smau ya isa wurin da abin ke faruwa.
Yallavai wanda tuni ya gundura da lamarin ya shiga fargaba saboda cincirindon mutanen dake kewaye da shi waxanda suka zamo mishi barazana, don ya san kes suke jira su afka mishi, don sun riga sun tunzura.
Yana ganin isowar Mus’ab ya yi maza ya ce, “Yauwa ga ma mijinta nan ya zo da kanshi”.
Gaba xaya wuri ya kaure da hayaniya, “Haxin baki ne da shi suka haxa baki”. Wasu har suna cewa, “Za ma ku sani, mu nan da kuke gani ba za a kawo mana wannan iya shegen ba”.
Yallavai ya yi maza ya ciro hoton dake aljihunshi zai nuna musu don ya samu ya wanke kanshi daga zargin da jama’a ke mishi.
Wani mara kunya a ciki ya yi maza ya fige hoton ya raba shi biyu ya jefa shi a baki ya tauna ya haxiye yana cewa, “Hoto kuma har wata shaida ce”.
Mus’ab ya yi shiru yana kallo cikin nazarin al’amarin, kafin ya zaro karan sigarinshi ya sanya a baki ya kunna yana zuqa a hankali yana kallon Saddiqa dake amsa tambayoyin mai mujallar.
“Kin san wannan da ya ce wai shi mijinki ne?”
Ta girgiza kai nuna alamar ba ta san shi ba, ta kuma qara da cewa, “A’a”.
“Za ki iya tunawa kin tava ganin shi ko da sau xaya ne a rayuwarki?”
Ta tave baki ta ce, “A’a”.
Mus’ab ya gama sauraron ta zuciyarshi cike da mamaki, bai ce mata komai ba sigarinshi kawai yake sha cikin nutsuwa. Ya miqa hannu ya jawo Saddiqa daga cikin motar ba tare da wani ya lura da lokacin da ya yi hakan ba, sai kawai ganinta aka yi a tsaye yana riqe da ita ya mayar da qofar motar ya rufe.
“Ba fa za ka je ko ina da yarinyar nan ba”.
In ji mai mujallah.
“Kai waye da za ka hanani yin hakan?”
Mus’ab ya buqaci sani. Yasa hannu a cikin aljihun gaban rigarshi ya zaro kati (conplimentry card) xinshi ya miqawa Mus’ab ya karva ya gani.
Lauya ne mai zaman kanshi, ya saki katin ya faxi a qasa sannan ya yi mishi lalataccen kallo tare da tambayarshi “To sai me?”
Kallon da tambayar suka tunzura shi ya ce, “Sai ka san ba za ka ko ina da ita ba tunda ko matarka ce sai ina tana son zama da kai, don haka ni zan tafi da ita in kaita gaban iyayenta, in kana sonta sai ka bita can ka same ta ku sasanta, amma baka tsare mu a jeji ka cireta a cikin mota ba bayan mun san mugaye sun yi yawa”.
“Kana da wata shaida ne Yallavai da za ta nuna ita xin iyalinka ce?”
Wani daga cikin fasinjojin ne ya yi tambayar.
Mus’ab ya kalle shi a nutse cikin kwanciyar hankali ya ce mishi, “Babu”.
“To tunda shi da kanshi ya ce babu shiga mota mu tafi kin ji, ya tsai damu yana vata mana lokaci”.
Mai mujallah ne yake wannan bayanin.
“Wasu mutanen basu da hankali, mace ba ta son su sai suje su baiwa iyayenta kuxi su aura musu ita a kan dole”.
Saddiqa ta yunqura za ta shiga motar Mus’ab yasa hannu ya kama hannunta ya riqe.
“Da kin sallame su sun tafi kar ki yi ta vata musu lokaci”.
Ya zuba mata ido yana kallon cikin idonta.
Ita kuma ta fara kuka tana faxin “Ka sake ni, ka sakar min hannuna ban sanka ba”.
Ta shiga kici-kici da qoqarin qwatar kanta daga gare shi.
“Malam in ma matarka ce ba ta sonka”.
Mai mujallah yasa baki, ya kuma yi nufin taimakon Saddiqa ta qwaci kanta wurin Mus’ab.
Mus’ab ya yi maza ya saki hannun Saddiqa dake hannunshi, cikin zafin nama ya taqarqare ya danqarawa mutumin naushi mai qarfi a muqamuqi, abin da ya yi sanadin faxawarshi kan mutanen dake tsaitsaye bayanshi suka tare shi daga kaiwa qasa. Ya taso fuskarshi cike da mamaki.
“Ni ka buga? Za ka yi dana sani, za ka gane ku…..”
Kafin ya qarasa faxin abin da yake so ya faxan Mus’ab ya yunqura ya sake kirva mishi wani wawan naushi. Wuri ya kaure da hargowa, jama’a suka kasu kashi biyu dake qoqarin shiga tsakanin daben dake shirin aukuwa tsakanin Mus’ab da mai mujallah saboda tasowar da ya yi zai rama dukan da ya yi mishin.
Haquri suke bayarwa a sasanta al’amarin cikin ruwan sanyi ba tare da anyi tashin hankali ba.
Mus’ab yana riqe da karan sigarinshi da yake qoqarin kunnawa yana kuma sauraron maganganun da kowa yake yi, ya yin da hankalinshi da nutsuwarshi suke kan duk wani yunquri na Saddiqa.
Wani dattijo ya iso wurin yana faxin, “Haba Yallavai ya ya kuna wuri kai da yaranka amma kuma rikici yake nema ya tashi a gabanku kana kallo?”
Yallavai ya yi mishi bayani kan yanda Mus’ab ya zo wurin ya nemi taimakon shi da duk abin da ya faru, don haka shi a ganin shi yanzu tunda abin ya zama haka, to sai a xunguma ayi can gaba inda za a samu hukumar ‘yan sanda a awurin.
Mus’ab ya ce, “Shi daga inda yake tsaye ba zai qara taku xaya zuwa gaba ba tunda ya riga ya ga abin da ya fito nema, sai dai ko a xunguma a koma gari na baya tunda shima ya wuto ofishin ‘yan sandan a can”.
“Dubi nan yaro”.
In ji dattijon. Mus’ab ya mai da kallon shi gare shi da girmamawa.
“Gaya min gaskiya ka ga tsayawa nan ta yi yawa, inda muka dosa nan ba nan kusa bane arewa fa zamu. Me ke tsakaninka da wannan yarinyar?”
Mus’ab ya kalle shi cikin girmamawa ya ce, “Baba qanwata ce, kakanninmu xaya, mahaifinta wan mahaifiyata ne a wurinshi na girma, shine kuma ya bani ita matata ce”.
“Kai ku tafi ku barshi da matarshi kowa ya shiga mota ya nufi inda za shi”.
In ji dattijon. Mutanen da tsayuwar ta riga ta gundiresu suka nufi motocinsu suna tsaki tare da faxin “MATA! Hum sai a barsu kawai”.
Mai mujallah kuwa tsayawa ya yi ya ce, “To ai ita yarinyar ba ta gaskata maganar ba balle mu yarda da gaskiyarshi”.
Dattijo ya kalli Saddiqa ya ce, “Yarinya ba ki yi kama da mutuniyar banza ba, abin da ya faxa gaskiya ne ko akwai gyara a ciki?”
Ta ce, “Gaskiya ne”.
Ya kalli mai mujallah ya ce, “To kai ka ji”.
Nan da nan jama’a suka watse aka bar Saddiqa da Mus’ab suna tsaye cirko-cirko, hatta Yallavai ya koma wurin sauran ‘yan sanda sun koma kan aikinsu.
Mus’ab ya kalli Saddiqa cikin murmushi ya ce, “To ya ya kenan? Waxanda kika sani sun tafi sun barki da wanda baki sani ba, ya ya kenan? Za mu tafi gida ne ko kuwa?”
Ta yi kamar ba ta ji ba, ta soma kuka. Ya kamo hannunta ya jata zuwa inda motarshi take, ya buxe ya sanya ta a cikin wurin mai zaman banza ya rufe, sannan ya juya ya koma nashi wurin ya shiga ya zauna.
Sai da ya kunna sigarinshi ya sanya a baki kafin ya juya kan motar ta nufi inda ya fito, bayan ya yi sallama da su yallavai.
Sun fara tafiya ko wani nisa basu yi ba Saddiqa ta soma kwara amai, nan take ya tuna kalaman Innarshi.
“Saddiqa da kake gani warin sigari ma sa ta amai yake yi balle a ce ta ji warin barasa a jikin mijinta”.
Ya yi maza ya wurgar da sigarin tare da sauke gilasan motar saboda samun tsarkakakkiyar iska.
“Ki yi haquri Aisha na mance bakya son hayaqin sigari”.
Ba ta yi magana ba in ban da kukan da take yi, duk da tsayuwar da ya yi don ta gyara jikinta ta kuma xan huta.
Mus’ab ya biyo Saddiqa xakinta da shigarsu gidan.
“Ina kika samu kuxin motar da kika biyasu?”
Ta yi shiru ta qi yin magana.
“Ni dai na san tun zuwanki wurina ban tava baki kwabo ba, da abokaina suka zo ganinki suka baki kuxi ma na karve, saboda dama ni zuciyata ba ta kwanta dake ba, na daxe ina ganin kamar za ki iya aikata abin da kika aikatan, shine kika gudu ashe ba kuskure na yi ba.
Wato ke kina nufin za ki iya yin dalilin da mahaifiyata za ta qara yin fushi dani? Kina nufin bayan duk abin da kika sani na tsakanina da ita za ki iya yin dalilin da zai fi haka rashin daxi?
In bakya sona ai ba zan tilasta ki zama dani ba, ni wani irin mutum ne da yake girmama abin da yake son shi. Ko da kika ga na bi hanyoyin da na bi wajen karvar auren ki na lura da quruciyar dake gareki ne, sai kuma na ga ni za a gwada min qarfi, amma in bakya sona ai zan iya yin haquri ba zan so kaina a kanki, zan mutunta al’amarinki in bi son zuciyarki tare da adalci a kai.
Amma ai babu wulaqanci ko tozartarwa a tsakanina dake, ki tashi daga nan ki je ki shiga cikin qartin maza ki nufi Misau ki je ki cewa iyayenmu me?”
Cikin matsanancin vacin rai yake jero kalaman nashi, don haka bai ko saurari kukan da take yi ba.
“Waye ya baki kuxin mota?”
Ta yi shiru.
“Ko shi wannan mutumin ne ya biya miki?”
Ta yi maza ta ce, “Eh”.
Ya zuba mata ido shi ba abin ya xauke ta da mari ba. Ya yi qarfin halin sake tambayar ta.
“A ina kika san shi?”
Ba tare da ta kalle shi ba ta ce, “Tare da shi muka zo daga Misau”.
“Ke da shi da Abu?”
Ta ce, “Eh”.
“Zancen banza kenan”.
Ya miqa hannu ya kamata, ya ce, “Ai duk inda mavoyar kuxin naki suke sai na gansu yau, tunda na ganeki”.
Ya soma cire kayan jikinta yana watsarwa, ita kuma tana kici-kicin hana shi da qoqarin rufe abin da take ganin shi ta fi qin ya gani. Ba tare da ya saurari kukan ta ba.
Lilita ya tarar xaure kan siket xin ta, ya zubawa likitar ido cikin sanyin jiki. Wannan ai lilitar Inna ce dake zuba cinikin kayan miyanta a ciki. Wato Inna ce ta baki kuxin da za ki gudu daga nan ki koma gida ke kaxai? Wai me na yi? Gaskiya ba zan bar maganar nan ba.
Ya miqa hannu ya ciro lilitar don ya cire kuxin dake ciki, har da qullin magani a xaure.
“TAFXIJAM! Har da magani ta baki ki rinqa saka min?”
Ya zuba mata ido yana kallon ta.
“To bari Kawu Gixe zan kai wa in yi mishi bayanin komai don ya ga irin abin da aka shirya min”.
Jin ya ce, “Zai kai wa Kawu Gixe maganar yasa Saddiqa buxe baki ta ce mishi, “Ba Gwaggona ta bani magani ba Abu ce ta bani”.
Ya ce, “A’a, babu ruwan Abu, ita za ta yarda a qwareni ne? Kuma in ma ita ta bakin na yarda ni gara min magani da a baki kuxin motar da za ki gudu ki bar gidana ba tare da izini ba, ko wannan xan fitan da kika yi kin san iyakacin mutanen da kika tayarwa da hankali? Ba gara a tara miki magunguna ba, za ki ba masu mota magani ne su xauke ki a motar haya?”
“Is any one at home?”
Wannan kalmar da Mus’ab ya jiwo ita ta katse shi, a lokaci guda kuma ta jefa shi cikin fargaba da faxuwar gaba mai tsanani saboda fahimtar muryar da ta yi maganar.
Jennifer ce, to me ya kawo ta? Ya fito falon da nufin fita waje inda take, sai kawai ya ganta cikin falon zaune kan kujera riqe da karan sigarinta a hannu tana zuqa, ga kuma kwalbar giyarta a gabanta.
Mamaki ya kama shi, ya ce, “Ya ya haka Jennifer? Ya ya za ki shigowa matata wuri ba tare da kin jira ta baki izinin yin hakan ba?”
Ta kalle shi a lalace kafin ta tambaye shi cewa, “Ina ne wurin nata?”
“Kar mu yi haka dake Jennifer, kashe sigarin muje can wurina sai in ji abin da ya kawo ki, mai nan xin ba ta son warin sigari”.
Ta yi dariya ta ce, “Ba zama da kai ta zo yi ba kenan, any way wannan ku ya shafa, ina fata ba kirana ka yi don ka gaya min abin da matarka take so da wanda ba ta so ba?”
“Ni na kiraki?”
Ya yi tambayar a yanayin dake bayyanar da rashin jin daxin shi, don bai son fitina da ita a lokacin.
“In baka kirani ba me zai kawo ni?”
Ta ja tsaki tare da tofar da yawu tuf! Nuna alamar tir bai isa ba. Hakan da ta yi ya qara fusata shi.
Ya ce, “To na ji na kira ki kin zo, na ji kuma bana son ganinki don haka tashi ki fita”.
Ta ce, “Ai kuma baka isa ba tunda ka kirani sai na huta, sai na shanye barasata”.
Ya yi maza ya ce, “Ba a nan ba”.
Ba ta saurare shi ba ta jawo ledar da kwalbar ke ciki za ta buxe.
“Ba a nan ba Jennifer, kar ki neme ni da magana”.
Ya yi maza ya nufo ta don ganin ba ta fasa ba, nufin shi ya hana ta yin abin da za ta yin ta hanyar fitar da ita daga falon, ta yi zumbur ta miqe, yana isowa gareta ta yi maza ta wanke mishi fuska da wani irin lafiyayyen mari mai qarfi tau!
Ya ja ya tsaya ya zuba mata ido yana kallon ta zuciyarshi cike da mamaki.
“Marina kika yi Jennifer?”
Ta ce, “An mara, kai da kake marin mutane fa?”
Ya ce, “Ai kuwa kin sayawa kanki wahala, don kuwa zan tabbatar da wannan hannun naki ya daxe baki more shi ba”.
Yana rufe baki ya cafke hannun da ta yi marin da shi, yana cafkewa ta soma kururuwa saboda wahala.
“Ka yi haquri Mus’ab”.
Ya ce, “Haba, ai gara kar ki ba da haquri Jennifer, ai kin daxe kina burin marina na kuma daxe ina yi miki kashedin hakan, don haka tunda baki ji ba nima bari in yi abin da na yi alqawari”.
“Na tuba Mus’ab”.
“A’a, ai gara kar ki tuba, in kika yi haka ai baki zama cikakkiyar ‘yar iska ba”.
Saddiqa ta gaji da leqen abin da ke faruwa ta koma gadonta ta hau ta zauna cikin rawar jiki da tsananin tsorata da abin da ke shirin faruwa da hannun Jennifer.
Ban da duk wani mugun halinshi da Gwaggo ta sani bai da tausayi ko na anini. Ta faxi hakan cikin zuciyarta.
A waje Mus’ab ya tari mai tasi ya jefa Jennifer a ciki ya miqawa mai tasin jakarta a hannunshi, ya ce, “Ku tafi ta gaya maka inda za ka kaita, in kun je ka xebi ladan aikin ka a ciki”.
Ya juya ya koma cikin gidanshi inda ya bar Saddiqa.
“Kukan me kike yi Aisha?”
Ya miqa hannu zai tava ta, ta yi maza ta maqure a jikin bango.
“Kar ka tava ni”.
Ta yi mishi kashedi.
“Bana son ganinka kusa dani tsoro kake bani, duk abin da Gwaggo ta gaya min game da kai haka abin yake, sa’a ma ka ci ba ta san rashin tausayinka ba da ta qara tsanarka.
Na sha jin tana cewa, halinka guda xaya da ta sani shine kai xin mai tausayi ne, ba ta sani ba shima tausayin ka daina shi. Abin da ya fi komai bani mamaki cikin lamarin shine, wai Gwaggo ce ta haifeka”.
Mus’ab ya miqe tsaye ya nufi toilet xin dake xakin ya barta tana kuka. Ruwan wanka ya haxa mata ya fito ya kalle ta a nutse qwarai ya ce mata.
“Shiga ki yi wanka tunda kin ce bakya so in rinqa tava ki zan kiyaye al’amarinki qwarai matuqa kika kiyaye nawa, ni wani irin mutum ne da na fi so inda hali in baiwa kowa haqqinshi, ina girmama mace, in kuma ji tausayinta har in yi mata adalci.
Amma kuma bana iya yiwa wacce ba ta san darajarta kanta ba, ko kuma wacce ta nemi shige iyaka”.
Ya juya zai fita tare da faxin, “Amma kin san in har na je na dawo baki yi ba zan yi miki”.
Ta yunqura ta tashi ta shiga toilet xin da nufin yin wankan, shi kuma ya fita waje ya kira qarti da za su tsabtace falon Saddiqa daga qazantar da ya samu na fitsarin da Jennifer ta yi ta sakewa a dalilin wahala da kuma barasar da ta zube.
Saddiqa tana zaune kan kujerar gaban madubi tamkar mai shirin yin kwalliya, sai dai zuciyarta kawai take sauraro. Ko me yasa Kawu Gixe xaukan aurenta ya baiwa Yaya Mus’ab? Anya kuwa Kawu Gixe yana sonta ma kuwa?
Ta zurfafa cikin tunani. Wani abin da Kawu Gixe ya tava yi mata da zai sa ta yarda eh, lallai yana yi mata so irin wanda uba ke yiwa ‘yar da ya haifa.
Shigowar da Mus’ab ya yi ya katse ta. Ya zauna a gefen gadon cikin wata lallausan jallabiya, ga qamshinshi mai daxi yana tashi, da alama shima wankan ya yi.
Tiren abinci da ‘ya’yan itace ya ajiye a gabanta.
“Fara da wannan kafin ki ci kazar”.
Yana maganar ba tare da ya kalle ta ba, bai kuma fasa yanka mata kazar ba duk da zafinta, haka nan yanayin fuskarshi bai sauya ba da alamar har lokacin ranshi a vace yake.
“Kar ki sake yunqurin gudu ki ce za ki tafi gida ke kaxai, ni kaina zan iya mayar dake gida gaban Gwaggonki tunda har yanzu kuna ganin bani aurenki da Kawu Gixe ya yi kuskure ne. To na ji na yarda, tunda ita Gwaggon nine wanda ba ta so, to na ji na yarda, tunda abin haka ne na ji na yarda zan kai ki gaban Gwaggon in baku zavi…..”
Kan ya qarasa ta katse shi ta hanyar hankaxa tiren abincin ya kife a qasa, ta yi maza ta miqe tsaye cikin kuka. Shima ya miqe yana kallon ta tare da mamakin abin da ya yi wanda ya jawo hakan.
“Bana so, ina jin kunyarka ina kuma girmamaka, ka barni in ci gaba da hakan. Muna magana da kai kana sa sunan Gwaggo a ciki, ita ce za ka kai ni gabanta ka bamu zavin auren ka? Ka bani ni da kai mana, ko kuma don ka ga an baka ni ba da yardar ta ba sai kuma ya zama…..”
Ta qara tsananta kukan da take yi.
“Ki yi haquri Aisha, ki yi haquri na yi kuskure da na ambaci sunanta, to amma me yasa da za a kawo ki ba za ta yi miki irin nasihar da take yiwa sauran ba? Sai ta ce in kinga ba daidai ba ki gudu, ba za ta qarfafeki a kan ki tsaya ki taimakeni in gyara halina da take ganin a kanshi ne take qina ba?”
Saddiqa ta galla mishi harara karo na farko da hakan ya tava faruwa a tsakaninsu.
“Nice ma zan taimakeka ka gyara halayenka? Lallai kam”.
Ya xan yi murmushi kaxan karo na farko shima tun bayan da ya neme ta ya rasa a gidan.
“To shi kenan na ji in ba za ki taimake ni gyara halina ba, ai kuma bai kamata ki yi dalilin da mu’amala tsakanina da Gwaggon taki zai qara lalacewa ba ko?
Kin tava tunanin inda kin yi nasarar isa gabanta ke kaxai da sunan gudu abin da zai biyo bayan hakan tsakanina da ita? Ke bakya sha’awar kyakkyawar mu’amala ta shiga tsakanina da ita? Ai har da kwaxayin hakan ya qara sani dagewa a kan auren ki Aisha, don na san tana sonki za ta yi mu’amala mai qarfi da gidana, ko ba don ni ba saboda ke.
Kina tsammanin ina jin daxin abin da ke tsakanina da ita ne? Ita ta haife ni fa, nine namiji guda xaya da take da shi, don me ba za ki gyara tsakanina da ita ba sai ki nemi ya qara lalacewa?”
Jikin Saddiqa ya xan yi sanyi, lura da hakan ya sa shi qara yi mata magana.
“Kawu Gixe da ya bani ke ba kuskure ya yi ba Aisha, ya san ina sonki ne, ya san ba zan iya zaluntarki ba, ya san zan yi miki adalci, ya san babu wani wanda ya fini cancantar aurenki ko da kuwa a ya ya halayen nawa suke, domin nine nake zaune ni da Innata mu biyu sai aka same ki kika shigo cikinmu.
Muna ta murna muna ta ina muka saka dake, muna ta sonki muna renonki cikin kulawa da tausayawa, duk da yawan kukan ki da yawan rikicinki, raina kan vaci in na ga yanda Inna ke wuni hidima da xawainiya, da daddare kuma ki hanata barci da yawan kukan ki, ta yi ta fama dake, ta yi jijjiga tana girgiza ki har sai asuba ta yi kafin ki yi barci, lokacin nan kuma ba lokacin barci bane a wurinta, za ta kwantar dake ne kawai ta miqe ta shiga wasu sabgogin.
Ran nan raina ya vaci haushinki ya yi matuqar kamani na fito na zo na sameta na ce Mama bani fitinanniyar yarinyar nan ki gani ki samu ki kwanta kema ki huta kamar kowa, zan je da ita xakina in rarrasheta, in kuma kin fi so a goyata, to goya min ita a bayana ki xaure min ita ta yanda zanin ba zai kwance ba.
Sai na ga ta yi murmushi ta ce min, kar ka ji haushinta komai ta yi kar ta vata maka rai yarinya ce ba ta da baki, bamu sani ba ko wani abu ke damun ta.
Kalamanta kan sanyani jin tausayinki, in zauna in yi ta taya ta rarrashinki ina tausayi, ina ganin ba laifinki bane damuwa ce tasa kika hana min Innata bacci.
Gari in ya waye in yi maza in yi mata ayykan da zan iya taimakonta dasu, wanki, wanke-wanke, shara, xiban ruwa duk babu abin da bana yi kafin in tafi makaranta, don ta xan samu lokacin kwantawa ta huta da rana, dana……”
Qwan! Qwan! Qwan! Xim! Xim! Xim! Xum! Xum! Xum!!!
Bugun qofa ake yi babu qaqqautawa. Mus’ab da Saddiqa suka zubawa juna ido saboda jin yanda ake bugun qofar. Gaba xaya suka kalli agogon dake xakin, tara saura kwata ne na dare.
“Iko sai Ubangiji, ko waye kuma yanzu?”
Mus’ab ya kalle ta jikinshi a sanyaye.
“Ki yi haquri Aisha bana nufin vata miki rai, ban kuma karvi aurenki don in saki ki yi baqin ciki ba”.
Ya miqe ya nufi inda ake bugun qofar, a zuciyarshi yana tunanin to ko dai Jennifer ce ta turo mishi ‘yan iska don su xaukar mata fansa kan abin da ya yi mata? Ubangiji dai yasa ba wata fitinar ce ta sake biyo shi har gida ba.
Mus’ab ya isa qofar ya xan saurara kaxan don tantance muryar dake magana.
“Anya Baba basu tashi daga gidan nan ba kuwa?”
“Kai tafi can kai ma sakarai dukan qofar ne baka iya ba, kana yi kamar kana tsoro”
“Zan ji tsoro kai Baba in na tarwatsa gilasan gidan nan ya ya zan yi? Masu tsada ne fa”.
Ta ce, “A hau! Babu abin da za ayi maka ai jikokina ne a gidan suna nan a ciki babu wani tashin da suka yi, sun hangame bakuna ne kawai sun kwanta suna bacci, ana bacci kamar na mutuwa to ba a tunanin komai balle a rage dare a xan yi nafilfili”.
“Abu ce”.
Zuciyar Mus’ab ta gaya mishi.
“Me ya sake dawo da Abu yanzu?”
Ya tambayi kanshi cikin tsananin faxuwar gaba.
“Yanzu haka Inna ce ta turo ta”.
Ya juya ya koma wurin Saddiqa ba tare da ya buxe qofar ba, duk da su ma basu daina dukan da suke yi mata ba.
“Aisha, Abu ce ta zo”.
“Abu?”
Ta yi tambayar a yanayi na tsananin mamaki tare da dirowa daga gadonta.
Mus’ab ya juya don komawa ya buxe musu qofar ta yi maza ta ce mishi, “Ka shigar da ita wurinka kar ka kawo ta nan”.
Ya ce mata, “To”.
Mus’ab ya isa jikin qofar yasa hannu yana buxewa tare da tambayar, “Waxanne baqi ne haka basa sallama sai dukan qofa?”
“Kai tafi can ka bani wuri, a ga qato kamar ka a ce wai shi ake bugawa qofa haka saboda yana bacci bai farka ba, ai kuwa dai ya ji kunya”.
Ya yi murmushi ya ce, “Abu kenan, to ba a gidana nake ba?”
Ya shigar dasu qayataccen falonshi daga ita har direban.
“Sannunku da zuwa”.
Ya sake yi musu gaisuwar bayan sun samu wuri sun zauna, shima ya koma wata kujerar ya zauna.
Saddiqa ta shigo falon cikin kwalliyar burgewa, ga shi ta yane jikinta da gyale sai qamshi take yi.
“Wa ya vata miki rai a hanya Abu na ji kamar kina faxa?”
Abu ta harareta ta ce, “Yanzu idonku biyu ake ta buga qofar nan baku fito kun buxe ba?”
Ta yi murmushi ta ce, “Hirar amarci fa muke yi”.
Ta ajiye tiren da ta shigo da shi a gaban Abu ta koma ta sake shiryowa direban nashi ta ajiye mishi, bayan ta gaishe shi ta koma kusa da Mus’ab ta zauna a gefen kujerarshi.
Mus’ab ya sallami direban da ya kawo Abu tare da alheri mai yawa, ya dawo ya sake zama kusa da Abun yana taya ta matsa qafafuwanta da take yi.
“Ai kin wahala da yawa ne Abu, kwanan nan kika tafi kin sake dawowa, wannan tafiyar ai ta yiwa jikinki tsanani. In ce ko dai lafiya?”
Abu ta ce, “Ina fa lafiya, fitinanniyar uwarku mana ta yi sanadin tasowata wai ita za ta zo ta ga halin da na baro mata ‘yarta a ciki saboda hankalinta bai kwanta. Ko da yake dai nima nawa hankalin ba kwanciyar ya yi ba, saboda yanayin da na barku a ciki”.
Ta basu labarin al’amuran duka. Saddiqa ta miqe ta nufi kicin tana cewa, “A’a, Abu ni bana son haka, in za ku yi maganarku ku yi amma ban da Gwaggona a ciki, Gwaggo ce za ta turoki ki zo ki ganan mata halin da nake ciki hankalinta bai kwanta ba, wa take yiwa haka a cikin surukanta? In kin ji marmarin ganina kin zo kawai ki ce kin ji marmarin ganina, amma ba ki ce Gwaggona ta turo ki ba”.
“Ka ji ta ko? Ka ji min ja’irar yarinya ko? Wani marmarin ganinki za a yi? Na sani da uwar taku ta ce za ta zo in barta ta zo da kanta tunda baki ga abin arzikin da na yi ba”.
“Qyale ta Abu mu yi zancenmu”.
“Kun zauna lafiya ne?”
Ta yi tambayar cikin raxa wai kar Saddiqa ta ji.
Ya xan kalle ta a yanayi na murmushi ya ce, “Me kika gani yasa kika tambaya?”
Kan ta sake gaya mishi abin da ta ganin Saddiqa ta fito riqe da kwanon farfesu ta ajiye mata, ta koma kusa da Mus’ab ta zauna.
“To kin ce Gwaggo ce ta turoki ki yi bincike in muna zaune lafiya mene ne? Ina ce dama don kin san zamu zauna lafiyan ne yasa kika gudu kika barni?”
Mus’ab ya ce, “Rabu da ita Abu ba ta so ne in gaya miki gaskiya, sai dai abin da nake so ki sani shine, ko na zauna lafiya da Aisha ko wane irin hali nake ciki ba zan sake daxewa ban zo Misau ba, ba zan barki ki ji marmarin ganina baki ganni ba Abu, saboda na san kina sona”.
Ta ji daxin maganar tashi, nan take ta yi ta sa mishi albarka.
Sun yi hira gaba xayansu har suka kai lokacin da Aisha ta ce mata dare ya yi Abu muje in rakaki ki yi wanka ki sha magani ki kwanta don ki huta gajiyarki”.
Ta ce mata, “To”.
Mus’ab yana zaune a falon cikin tunani za ta dawo ne ko za ta zauna a can, sai gata ta shigo. Kwanukan dake wurin ta kwashe za ta fita dasu.
“Ke nake jira fa Aisha”.
Ba ta yi magana ba ta tafi ta dawo.
“To zo daga nan mana ya ya za ki zauna kuma a can?”
Ta ce, “A’a, nan xin ma ya yi”.
Ya qara gane don Abu ta yi abubuwan da ta yin duka.
“Ina ce nan za ki zo mu kwana?”
Cikin nutsuwa ta kalle shi ta ce, “Saboda me?”
“Saboda shine abin da ya dace ki yi, kema kin sani ko ba a gaya miki ba abubuwan da kike yi min sun yi yawa, bai dace a ce kina yiwa mijinki haka ba”.
Ba ta kalle shi ba ta ce, “Ba ka ce za ka kaini gaban Gwaggona ka bamu zavi ba?”
Ya yi murmushi ya ce, “Wannan maganar ba ta wuce ba”.
Ya taso daga inda yake zaune ya zo wurinta yasa hannu ya sureta, ya ce, “Tunda kin riga kin kawo kanki falon bari kawai in qarasa dake cikin xakin kawai”.
Ya zaunar da ita a kan gadon ya koma gefe ya zauna.
“Ina ce wannan maganar mun gama ta, kuma in bakya so in rinqa sa sunanta a cikin maganarmu ke me yasa kike yi min abin da kika ga dama? Yanzu kina nufin inda kin san zan kai qararki wurinta ta yi hukunci a tsakaninmu za ki rinqa yin irin waxannan abubuwan? Yanzu su Bilki za su yi haka?”
Shi da kanshi ya baiwa kanshi amsar “Ba za suyi ba, saboda sun san mazansu suna da….”
Bai qarasa ba ya yi murmushi saboda kallon da Saddiqan ta yi mishi, ya canza maganar tasu da tambayar ta.
“Me kike ganin za ki yiwa Abu na karyawa da safe?”
Ta ce, “Da zai yiwu waina da miya ko funkaso”.
Ya yi maza ya ce, “To muje kicin xin mana in taya ki ki duba abubuwan”.
Qarfe xaya ta yi lokacin da suka gama haxa qullin masar da na funkason, sannan ya tasota a gaba suka dawo xakin shi, ta shiga banxakinshi ta xauro alwalarta ta fito, ta zo ta zauna a bakin gadon ta yi addu’o’in da za ta yi tun daga suratul Mulk, Qulhuwa, Falaqi, Nasi, Ayatulkursiyu da sauran addu’o’inta, ta shafe jikinta sannan ta wuce can qarshen gadon ta kwanta.
“Amma a irin shirin kwanciyar da kika yi ta hanyar neman lada da albarkar daren ya dace ki yiwa mijinki irin wannan juya bayan? Sannan ko abin arzikin da na yi miki ma yau baki gani ba”.
A hankali ta tambaye shi “Me ka yi min?”
“Ai ba ki ma lura kin gane ba? To babu laifi, yanzu yau rabon da in sha sigari tun yaushe?”
Ba ta kalle shi ba ta ce, “Saboda Abu dai?”
“Abu ai ta saba ganina ina shan sigari Aisha, in don ita ne zan sha iyaka ta roqa min shiriya”.
Ba ta kalle shi ba ta ce, “To na gode”.
Ya ja jikinshi ya isa gareta ya ce, “Tukwici za ki bani ba godiya ba”. Yasa hannu ya juyo da ita gareshi ya yi maza ya qanqameta jikinshi, tsawon lokaci yana sumbatarta tare da lugwigwita duk wata gava ta jikinta, da qyar ta samu ya sake ta.
Ta miqe a hankali ta tashi, ya miqa hannu ya kamota ya ce, “Ina za ki?”
Cikin nutsuwa ta ce mishi, “Xakina”.
“Zo ki yi kwanciyarki ba zan sake tava ki ba”.
Ya juya bayanshi ya barta ita ma ta gyara kwanciyarta. Kusan minti goma sha biyar da kwanciyar tasu ya kira sunanta a hankali, ga zaton shi zai ji tana bacci sai ya ji ta amsa, zuciyarshi ta yi mishi daxi jin ita ma ba ta yi bacci ba.
“So nake na sha sigari”.
Da sauri ta miqe ta zauna a firgice qwarai ta tambaye shi.
“Sigari fa ka ce?”
“Eh, na kasa bacci ne, bana zaton zan iya bacci in ba shi na sha ba”.
“To bari in je xakina kawai”.
“Kina nufin saboda zan sha sigari sai ki nunawa Abu abin da muke ciki ba za ki rufa min asiri a gabanta ba, in ta san mun zauna lafiya ai daxi za ta ji, kin sani sarai saboda ke ta dawo garin nan”.
“Saboda ni?”
Ya ce, “Eh mana, saboda ke”.
Ya faxi hakan daidai lokacin da ya miqa hannu ya xauko ta daga inda take ya kifata a kan qirjinshi, ya kuma zagayeta da hannayenshi duka biyu ta yanda ba za ta zame ta sauka ba.
“Haka Inna take yi miki sanda kike damunta da rikicinki Aisha”.
Tsawon lokaci yana yi mata kalamai masu daxi kafin ya soma tsotson bakinta cikin nutsuwa, babu alamar za ta bijire mishi kan abin da yake yin.
Suna cikin wannan halin suka jiwo kiran sallar asuba daga masallacinsu, don haka suka tashi suka yi shirin yin sallah. Suna idarwa Mus’ab ya shiga xakinshi ya kwanta don ya samu ya xan yi bacci kafin ya fita ofis.
Ita kam Saddiqa kicin ta nufa ta kama aikinta, kafin qarfe takwas tuni har ta gama aikinta ta shirya komai ta yi wanka ta yi kwalliyar ta, ta nufi wurin Mus’ab cikin qamshinta mai daxi don tashin sa daga baccin da yake yi.
Saddiqa da Abu suna falonta suna hira bayan sun gama karyawa, Mus’ab ya shigo yana qamshi, ofis zai fita, bai zauna ba ya ce, “Abu bari in je ofis in dawo sai mu gaisa sosai na riga na makara”.
Ta ce, “To, a dawo lafiya, Ubangiji ya kiyaye”.
Ya ce, “Amin”.
Saddiqa ta vata rai ta ce, “Ba ka karya ba za ka fita?”
“Na makara ne fa”.
Ta xaure fuska sosai ta ce, “Ko kuma kana da wani wurin karyawar ba?”
Ya yi murmushi. Abu kuwa ta galla mata harara tare da jan tsaki. A hankali ya ce, “Ban kunun gyaxar kofi xaya”.
Ta zuba ta miqa mishi ya karva ya shanye, ya yi musu sallama ya tafi.
Mus’ab ya isa ofis ko zama bai yi ba qawayen Jennifer suka tare shi da labarin rashin lafiyar ta da kwanciyar ta a asibiti, sai dai wai ta qi faxin wanda ya yi mata abin. Ya nuna musu jimaminshi kan abin da ya faru, ya kuma ce musu zai dubo ta da zarar ya rage ayukan dake gabanshi.
Suna barin ofis xin ya koma kan ayukanshi, har zuwa lokacin da Sarah ta iso.
Tana zaune a gabanshi ta fiddo kwalin sigarinta daga jakarta ta kunna ta miqa mishi, ya ce, “A’a, Sarah sha kawai”.
Ta zuba mishi ido fuskarta a yatsine.
“Ba ka da lafiya ne?”
Ya ce, “A’a, lafiyata qalau ina dai son rage yawan abin da nake sha ne, matata ba ta son warin taba, kinga yau ma tun a wurin wanka da na sha biyu sai xazu da na sake sha, ina ganin kuma ba zan sake sha ba sai na kusa tashi daga ofis kafin in je gida”.
Ta kalle shi ta tave baki ta ce, “Yana da kyau”.
Tasa hannu cikin jakarta ta zaro wani kati ta miqa mishi ya karva ya duba cikin nazari, kafin ya xago kanshi ya kalle tana murmushi.
“Barthday xin Diana ne ai ka santa, ban yi inviting xin kowa ba in ban da kai, ina fata ba za ka yi min irin na jiya ba na yi ta zaman jiranka baka zo ba”.
A hankali ya ajiye katin hefen tebur xin dake gabanshi ya haxa hannayenshi wuri xaya ya zuba mata ido cikin nutsuwa, ya ce mata, “Ki yi haquri Sarah, gaskiya idan na sake yi miki alqawari ban cika ba ranki zai fi haka vaci, kin san matata yarinya ce qarama ba zai yiwu in rinqa raba dare a waje ba ina barinta ita a gida”.
Ta zuba mishi ido tana kallonshi tare da qoqarin voye vacin ranta.
“Amma kai ne ka ce min don ka yi aure ba wai yana nufin mun rabu bane”.
Ya ce, “Eh, amma ba ina nufin zan ci gaba da irin waxannan abubuwan bane, amma ai ba zamu daina gaisawa ba”.
Ta miqe tsaye ta suri jakarta ta ce, “To sai anjima mijin jinjira”.
Ta fita ta barshi yana kallon qofar da ta buga mishi, tsawon lokaci yana kallon qofar kafin ya miqa hannu ya xauki kan wayar dake gabanshi. Gidanshi ya kira, ya jiwo muryar Saddiqa tana amsa sallamar da ya yi.
A hankali ya kira sunanta.
“Aisha baki ga kamar in dawo gida in same ki yanzu zai fiye mana komai daidaituwa ba?”
Ta gane abin da yake nufi, cikin nutsuwa ta ce mishi, “Eh, to amma sai ka yi min rantsuwar tun zuwan ka ofis yau baka tava wata mace da hannunka ba?”
Ya mai da kan wayar ya ajiye a mazauninta, cikin ranshi yana tunanin irin karvar da ya yiwa Sarah lokacin da ta zo.
Wayar ta yi qara yasa hannu ya xauka cikin mamakin yanda nan da nan daga ajiyewarshi ta bugo.
“Ya ya dai Aisha, in zo xin ne?”
“Ai baka amsa min ba, abin da kake son ci za ka gaya min in shirya maka”.
“Komai kika yi zan ci amma gani nan ma zuwa gidan mu yi maganar gani ga ki. Kin canza shimfixar xakin nan?”
Ta yi kamar ba za ta amsa ba, a hankali ta ce mishi, “Eh”.
“To ki yi min kwalliya irin wacce za ta sani in xan ji sanyi”.
Ta ce, “To sai ka zo”.
Mus’ab yana zaune a gida da daddare suna hira bayan sun gama cin abincin da Saddiqa ta yi musu shi da Abu, ya yin da ita kuma take ta kaiwa da kawowa tsakanin wurinta da kicin, bayan ta sha kwalliya sai sheqi take yi.
“Ni me Saddiqa ke yi ne ta dame mu da zarya?”
Mus’ab ya yi murmushi ya ce, “Abu kenan, gidanta ne fa ki ce kar ta yi zarya?”
Sai da ta gama kawo musu tsiren da ta yi musu na naman rago suka xan yi hira, sai ta miqe ta ce, “Ni zani in kwanta Abu sai da safe”.
Abu ta bita da kallo ta ce, “Ki ce kawai kin gaji da zaman mijinki a nan kina so ku tafi, to ku je sai da safe, tashi ka bita”.
“A’a, Abu ba abin da take nufi ba kenan, baki ga sammakon da ta yi ta toya miki waina da funkaso ba kina ta santinshi”.
Ta gyaxa kai ta ce, “Na gani, gobe ma kuma shi nake so in sake ci”.
Ya ce, “A to, in ba ta kwanta da wuri ba ai sai ta kasa tashi”.
Ta ce, “Haka ne, to ku je sai da safe”.
Kayan baccin da ta samu a kan gadon ta xauka ta sanya saboda tana so ta xan yi mishi abin da zai ji daxi ko da babu yawa.
Ba ta daxe da kwanciyar ba ya shigo, wutar xakin ya kunna hasken ya bayyana, ta yi maza ta ja abin rufa ta rufe jikinta, zuciyarshi ta yi mishi daxi saboda ganin ta bi umarnin da ya yi mata.
Ya canza wutar zuwa mara haske kafin ya isa gadon. Ta yi maza ta kawar da fuskarta gefe saboda ganin yanayin da ya zo gadon a ciki. Ya miqa hannu a hankali ya juyo da ita gareshi.
“Daina juyawa mijinki baya Aisha babu kyau, dakata ki gani, tsaya ki ji abin da zan gaya miki”.
Hankalinta a tashe saboda gane abin da yake son yi da ta yi.
“Ni mu bari sai Abu ta tafi”.
Ta faxi hakan cikin murya mai rawa.
“Ai babu ruwanmu da Abu, Aisha muna wurinmu ne tana nata, ba ta zo gidanmu don ta takura mana ba, ta zo ne don ta tabbatar da zaman lafiyarmu, in ta kama zamu iya zama da ita gida xaya muna sha’aninmu tana nata. Saurareni kawai ki ji”.
Ta kama kuka tana faxin, “Ba ta so”. Sai dai hakan bai sa ya saurara ko ya haqura da abin da yake nufin ba.
Kar dai na wahalar da ita? Ya faxi saboda ganin yanda jikinta ke vari.
“Aisha”.
Ba ta yi magana ba, ba ta kuma bar kukan da take yi ba.
Miqewa ya yi ya shiga banxaki ya zuba ruwan zafi ya zo ya xauke ta ya je ya tsoma a ciki, ya yi mata abin da yake ganin ya dace ya yi mata, sannan ya yi mata wankan sabulu, ya kuma ba ta umarnin ta yi wankan ibada, ya fito ya canza musu shimfixar gadon.
A hankali ta hau kai ta kwanta saboda tsabtace shi da ya yi, a haka suka kwana da Saddiqa, in ban da ajiyar zuciya babu abin da take yi. Ba ta samu rintsawa ba sai bayan da suka yi sallar asuba.
Ganin haka yasa shi gyara mata rufa ya fito ya shiga kicin xinta wai zai toyawa Abu wainar da ta ce yau ma in so samu ne ita za ta ci.
Ba a je ko ina da fara tuyan nashi ba ya kama tari babu qaqqautawa, ita ma Abu ta fito daga wurinta tana faxin “Kai wannan tuya yau dai kam ya yi gardama, ya ya aka yi? Ta jiya ai qamshinta kake ji gwanin daxi ba irin wannan qaurin ba”.
Suna haxa ido da Mus’ab ta ja ta tsaya ta yi turus.
“Au! Haba, yau kai ne mai tuyan ina matar gidan?”
Ya kalle ta ya ce, “Na karveta ne ta xan huta, ko za ki taimakeni ne kema ki karveni?”
Ta ce, “A’a, a na me tunda ka karve ta ai ka iya ne, gara kawai ka qarasa”.
Ta juya tana cewa, “In ban da saunanci mene ne haka? Mace tana can a kwance shememe miji yana kicin yana fama da aikin abinci, sai ya gama ya tasota ta zo ta ci ko?”
Mus’ab ya ce, “A’a, Abu yau dai don Aisha nake yiwa shi yasa kika kira abin saunanci, amma ni kam tun yaushe nake karvarki girgi kina zaune in yi tankaxe, in yi talge, in kaxa miya a gidanki, ai na yi shi ya fi sau nawa?”
Ta ce, “To ai shi kenan ka tsayar da wannan qaurin da yake yi don hayaqinshi yana sirqeni ya sani tari”.
Shi da kanshi ya san qaurin ba mai daxi bane irin na jiya, ga shi kuma duk sun qone, mafi yawancinsu ma sun gutsittsire basu da wani sha’awa, ya kuma san Abu da halinta babu yanda za a yi ta ci abincin da bai mata kyau a ido ba, ko xanxano a baki, don haka ne ya yiwa kanshi qiyamun lailai ya tattara ya ajiye tuyar ya shiga shirya musu wani abin karyawar na daban. Nan da nan ya gama.
Yana tsabtace wurin sai ga Abun ta sake dawowa.
“Ni in ce ko dai ba kukan yarinyar nan na ji jiya da daddare ba?”
Bai kalleta ba ya tambaye ta, “Wacce yarinyar?”
Ta ce, “Saddiqa”.
Idonshi yana kan aikinshi ya ce mata, “Ita ce Abu”.
Ta xan yi shiru kamar ba za ta yi magana ba, sai kuma ta sake tambayar shi, “In ce ko dai lafiya?”
Ya ce, “Lafiya qalau, mafarki ta yi wai damatsirin gidanki sun cijeta”.
Shaqiyancin da ta ji ya shigar cikin maganar ya sata wucewa ta tafi ta ba shi wuri tare da faxin “To madallah”.
Ya gama shiryawa Abu abin karyawar da ya shirya matan a gabanta, ta zuba mishi ido tana kallo, ya xaga ya kalle ta saboda shirun da ya ji ta yi.
Kallon da take yiwa abin karyawar yasa shi murmushi.
“To baki yi min addu’a irin wacce na ji kina yiwa Saddiqa ba jiya da ta kawo miki abin karyawa ba”.
Fuskarta a xaure ta ce mishi, “Addu’ar me zan yi maka bayan ka hana yarinya ta zo ta yi min abin da zan iya ci, wannan duk ai ba abincina bane”.
“Ba hanata na yi ba Abu”.
“To me ka yi?”
Ya xan yi shiru kafin ya ce, “Jiya ne ranar aikinta yau kuma nawa”.
Ta yi tsaki ta ce, “Ai sai ka yi ta yi, jeka ni ka xumami miyar wainar da na ga yarinyar nan tana shiryawa da daddare ka xebo ka haxo min da wainar da ka toya in tsinci wacce zan iya tsomawa cikin miyar in ci ko don sha’awarta”.
Ya ce, “To Abu yanzu kuwa”.
Yana gama kawo mata abin da take so ya yi maza ya nufi wurinshi, bai saurari maganar da take yi na “To ya ya za ku watse ku barni ni kaxai in karya?”
Yana tura qofar xakin ya ga ta buxe ido, a hankali ya matsa kusa da ita.
“Sannu Aisha, bari in kira Dr. Usman ya zo ya xan taimaka miki don tun xazu na ji jikinki da xumi”.
Ta xan kalle shi na xan wani lokaci ta kawar da kai, ya yin da zuciyarta ke raya mata Yaya Mus’ab wane iri ne? Abin kunya ba ya ba shi kunya. Ya kira likita ya ce mishi me?
Sanin da ta yi matuqar tana wurin zai kira likitan ya sata miqewa cikin qarfin hali ta nufi wurinta, in ban da haka da ita kam yau ba ta yarda ta haxa ido da kowa ba.
Tana tafiya yana binta a baya.
“Aisha! Aisha tsaya mana ki saurare ni”.
Ba ta kula shi ba balle ta saurari wata magana.
Abu ta na zaune a falo tana jan carbinta bayan ta idar da sallar walaha, ta kammala addu’o’inta. Saddiqa ta wuceta ta shiga xakinta ta hau gado ta kwanta.
Da sauri Abu ta bi bayan ta.
“Lafiya dai ko Saddiqa? Ko baki ji daxi bane?”
Ta yi tambayar daidai ta xora hannu a kanta.
Ba ta yi magana ba ta soma kuka.
“A’a, mene ne na kuka kuma Saddiqa? In ba a da lafiya saia yi kuka?”
Tana maganar tana nazarinta. Nan da nan ta gano kan al’amarin.
“Uh-uhum! Mus’ab ne ya vata miki rai?”
Ta yi tambayar tare da zama a bakin gadon.
Saddiqa tana jin ta ambaci sunanshi ta kawar da kanta daga kallonta ta juya kallon bango tare da tsananta kukan da take yi.
“Yi haquri, yi haquri, yi haquri shatuwallena, yi haquri ‘yar Gwaggonta ba qwararki ya yi ba, bai kuma zalunce ki ba girma ne ya ja miki, in aka girma ai haquri ake yi, sai kuma a nutsu.
Shi kam ma ai ya yi haquri dake, yau kwananku nawa yana zuba miki ido, Mus’abu ai mai haquri ne. yi haquri kin ji. Ubangiji ya yi miki albarka, ya zaunar miki da aurenki lafiya, ya baki zuriya xayyiba su faranta miki rai kema kamaar yanda kika farantawa iyayenki. Bari ki gani in tashi yanzu zan yi miki maganin ciwon da jikinki ke yi”.
Ta tashi tana shirin abin da za ta yi Mus’ab ya shigo.
“Abu likita ya zo duba Aisha”.
Abu ta galla mishi harara.
“Kai kar ka damu mutane ka ji, duk wahalar da ka gana mata ba ta isheka ba sai ka kira wani likita ya sossoke mata jiki da allura, to babu inda za ta”.
Ta ja tsaki tana harkar gabanta tana mita.
“Shi yasa ko qwari baku da shi, to duk kashi a soke”.
Mus’ab ya yi kamar bai ji kunyar kalaman nata ba, don shi kam yana son sirrin mu’amala tsakaninshi da iyalinshi. Cikin qarfin hali ya ce, “Abu da kun bari an duba ta jikin nata babu lafiya”.
“Ai ba rashin lafiya take yi ba wahalar da ka ba ta ne ya xumama mata jikin, saboda baka da haquri. Ai ni bana son rashin haquri, in aka yi haquri aka bi a hankali ma mene ne wata rana ba sai labari ba?”
Kalaman Abu suka gunduri Mus’ab, ya juya ya fita ya je ya sallami likitan dan ya san Abu ba za ta bar Saddiqa ta fito ba. Ya yi kamar ya bi bayan likitan shima ya yi tafiyarshi don kalaman nata suna sa shi jin kunyarta da yawa. To amma in ya yi haka ita Saddiqa fa?
Ya shiga wurinshi ya gama abin da zai yi ya fito cikin shiri da qamshi, ya sake komawa wurin nasu har lokacin Saddiqa tana kwance, bacci take ko ido biyu bai sani ba.
Ya kalli Abu cikin yanayin murmushi ya ce, “Amma Abu…..”
Bai qarasa ba ya yi shiru, ta gane inda ya dosa. Ta xan taya shi murmushin haxi da cewa, “Babu komai jeka abinka ka dawo za ka zo ka samu matarka ta yi tsaf na kintsa maka ita, ruwan zafi ai shine maganinshi sadidan, sai ko gasasshen nama, farfesu da kuma yaji-yaji, wannan kuwa duk akwai a gidan zan kula maka da ita”.
Ya ce, “To Abu”.
Ya juya zai tafi ta yi maza ta sake kiranshi.
“To zo mana”.
Ya dawo yana sauraron ta. Cikin nutsuwa ta ce mishi, “Zanin gadon naku za ka xauko min in tafiwa uwarku da shi don ya zama mata albishir”.
Mus’ab ya tsuke fuska ya ce, “A’a, Abu ni bana son irin wannan abin da kuke yi tonon asiri ne kawai”.
Nan da nan ta taso cikin fushi, “Za ka bani zanin gadon ne ko sai ka yi dalilin vacin raina a gidanka?”
Ya yi maza ya ce, “A’a, Abu wane ni in vata miki rai”.
Ta ce, “To maza xauko ka kawo min”.
Ya ce, “To”. Ya je ya kawo mata ya juya ya fita ya barta rungume da zanin gadon tana ta faman sanya musu albarka.
Ofis rannan a nishaxi mai yawa Mus’ab yake, ba yau ya fara sanin mace ba a rayuwarshi, amma bai tava samun kansa cikin nishaxin da ya samu kanshi ba jiya.
Kai girma da darajar aure yawa ne da shi, in ban da shaixan ma to me za a yi da matan banza ne? Ya tuna tsawon lokacin da Kawu Gixe ya yi yana fama da shi ya yi aure yana qi, wanda inda tun a wancan lokacin ma ya furta cewar Aishan yake so ya san ba zai hana shi ita ba duk da qanqantar tata.
Sannu a hankali Mus’ab ya yi ajiyar zuciya tare da lumshewar ido, cikin zuciyarshi ya yi tunanin al’amura masu yawa, kafin daga bisani ya saki wani lallausan murmushi, a hankali kuma sai ya furta sunan nata a bakinshi Aisha kenan.
Kafin ya isa gidan da yamma aiken shi biyu, abubuwan amfanin gida yake ta aikewa, cikin zuciyarshi yana tunanin yana zuwa zai tura gidan Idris a kawo mishi Zainab don ta taimakawa gidan nashi.
Abin mamaki yana zuwa sai ya tarar da komai a kintse a kammale a kan tsari, Saddiqa tana zaune a falonta tana cin tuwo miyar kuka da Abu ta yi da naman rago, ga yajin daddawa.
Ya kalli Saddiqa ya kawar da kanshi, har lokacin idanuwanta basu wattsake daga kukan da ta yi ba, iyaka dai ta yi wanka ta kuma yi kwalliya ‘yar kaxan.
Sannu da Abu tana fara’arta ta amsa, sannu da qoqari Mus’abu ka dawo ba?
Ya ce mata, “Eh”.
“To sannu da zuwa, Ubangiji ya yi muku albarka ya rufa muku asiri, ya kuma sa ku gama da duniya lafiya”.
Ya ce mata, “Amin Abu”. Ya juya zai tafi wurinshi.
Ta ce mishi, “Ga abincinka nan a kicin sai ka shiga ka xauka”.
Bai kalle ta ba ya ce, “Aisha ba ta ji sauqi bane Abu? Ki bata ta kawo min mana”.
Ba ta tanka mishi ba don haka ya biya ya xauka ya tafi da shi wurin nashi.
Kwana biyu a jere Abu tana cikin hidimar tarirayar Saddiqa, kulawa da shagwava, har dai Mus’ab ya gundura da abin saboda ko kusa da ita ba ta barinshi yaje.
Ya shiga kicin inda ya hangeta tana gashin nama, ya same ta cikin nutsuwa ya ce mata, “To wai ni Abu ni kuma ni shi kenan ne?”
“Shi kenan kamar ya ya?”
Ta yi tambayar tana kallon shi. Ya xan yi murmushi tare da miqa hannu wajen tayata aikin da ya tarar tana yi.
“To ba kema na ji kiuna ce mata ba cutarta na yi ba, kuma ban zalunce ta ba?”
Ta ce, “Eh”.
Ya ce, “To tunda haka ne ba sai ki lallavata ki xan rinqa turo min ita ba, kina gani fa har yanzu ko magana na yi mata ba ta amsawa”.
Abu ta yi dariya ta ce, “Naqi in lallava maka itan, ai sai daxin ya yi maka yawa, randa na tafi na barku ku biyu a gidanku ka san yanda ka yi ka lallava abinka”.
Satin Abu guda a gidan ta sanar da Mus’ab shirinta na komawa Misau a kwanaki biyu masu zuwa a gaba.
“Da sauri haka Abu?”
Ta yi murmushi ta ce, “Ai na zauna muku Mus’ab ina laifi, in ban da gidanku kai da matarka ina za ni in yi wannan zaman?”
Cikin nutsuwa da girmamawa ya ce mata, “Ai mun gode miki Abu, Ubangiji ya qarawa rayuwarki albarka”.
Daga gefenta Saddiqa ta yi magana a yanayi na sanyin jiki.
“Zan biki gida Abu”.
Abu ta waiwaya ta kalle ta, tuni har hawaye sun fara zuba a idanuwanta.
“A’a, Saddiqa dena wannan kukan ki share hawayenki ki ji abin da zan gaya miki, ki bini gida Misau kina so mujewa iyayenku da abin da zai baqanta musu rai ne?
Ai ni jakadiya ce ta alheri a garesu, zan je musu ne da labari mai daxi mai faranta musu rai. Na zo na same ku lafiya, na kuma barku lafiya har ga albishir mai daxi zan je musu da shi”.
Ta ci gaba da maganarta da cewa, “Aure ai girma ne, girma kuma haquri ne, don haka ki yi haquri ki zauna tare da mijinki, ki yi mishi biyayya, yi na yi bari na bari, ba ki ga irin kai kawon da yake yi a kanki ba? Yana sonki, to in kin tafi ki barshi da wa Saddiqa? Kar ki yi haka”.
Mus’ab ya tashi ya tafi ya basu wuri. Tana ganin fitar Mus’ab ta qara mai da hankalinta wurin Saddiqa.
“Sa hannu biyu ki rungumi al’amarin mijinki, kar ki yarda ki yi wasa da aurenki, kullum ki je ki gaishe shi, kullum ki karkaxe mishi shimfixarshi, kullum ki yi mishi abinci mai daxi. Ki sa ido sosai a kan shi, kar ki yarda hannunshi ya tava wata mace in ba ke ba ce, kar ki yarda ya mai dake qaramar mace, kina gida a zaune shi yana can wurin matan banza a waje. In tafi dake gida to ki barwa wa shi? Ki barwa matan bariki ko? Ke bakya kishi ne?”
Ta tsareta da ido.
“Ni kuwa ai kishi ne dani, ban tava barwa wata mace mijina ba shi yasa ma bayan rasuwarshi ban yarda na sake yin wani auren ba, sai na yi zamana kawai saboda na fi so ko a lahira a ce shine mijina na aljanna cikin yardar Ubangiji”.
Yanda Abu ta yiwa Saddiqa nasiha da kalamai masu daxi, haka ta zaunar da Mus’ab ta yi mishi irin wanda za ta yi mishi, sai dai shi kam ba irin rarrashin da ta yiwa Saddiqa ta yi mishi ba.
“Kar ka zalunceta ka yi haquri da ita, ka yi mata adalci, ka sani ba ta da kowa a garin nan in ba kai ba”.
Ya ce, “To Abu, na gode Ubangiji ya saka miki alherinki a gareni”.
Ta yi murmushi ta ce, “Amin Mus’abu ya saka mana tare”.
Duk kalaman da Abu ta yiwa Saddiqa na rarrashi da kwantar da hankali, da yanda zuciyar Saddiqan ya karvi maganganun da ta yi mata bai hana zuciyarta ta karaya ba har ta yi ta zubar da hawaye tana kuka tare da faxin, “Zan bi ki Abu”. A lokacin da ta ga ana ta fitar da tsarabar da Mus’ab ya yi mata ana jibgawa cikin motar da za ta mai da ita gida Misau.