ABU NAKA BOOK 3 BY SODANGI
SHEKARU GOMA DA AUREN SU MUS’AB
Mus’ab yana zaune a falonshi yana rubuce-rubuce, ya isa ya yi qiba ya yi jajur saboda wadataccen kwanciyar hankalin da ya samu shi da matarshi, a yanzu sun daina zancen haihuwa da damuwa kan al’amarinta, iyaka dai kullum a cikin addu’a suke, suna kuma ta shan magani na asibitin da na Hausa, saboda kullum iyayensu a cikin aiken magungunan suke. Tun ma ba Gwaggo Habiba ba, in da duk aka ce mata ga mai magani za ta je ta karvo ta kuma aike musu.
Saddiqa ta shigo falon cikin kwalliya da qamshi mai daxi, kana ganinta za ka tabbatar eh, ta dace da zama matar Mus’ab.
Can gefe ta je ta zauna tana cin kilishinta, a hankali ya xago ido, ya ce, “Haba Aisha wannan wane irin rowa n? Kin yi min rowar qamshimki to kilishin ma ba za ki yi min ta yi ba?”
Ta yi murmushi ta ce, “Kilishi kai ka ce bai maka daxi ba”.
Ya ce, “To na ji ke fa?”
Ta taso daga inda take ta zo gare shi, ya ware hannayenshi duka biyu ta shiga cikinsu ya mayar ya rufe, tsawon lokaci suna wasanninsu kafin ya gaji ya miqe tsaye xauke da ita a hannunshi ya nufi xakin kwanciyarshi, tare da faxin muje daga ciki zan fi ganin fasalin kwalliyar taki. Gabanta ya faxi, sai dai kuma ta yi maza ta shanye.
Yana daga kwance yana kallon ta bayan ya kammala abin da zai yi.
“Kina da matsala amma kin qi ki yarda a tsakanin duk lokacin da na kusanceki sai na gane dauriya kawai kike yi kina haquri dani, amma na tambaye ki kin ce ba haka bane”.
Ta yi murmushi ta ce, “Me ka gani?”
Ya harare ta bai tanka ba.
Ta sake wani murmushin ta ce, “Ni bani da matsala”.
“To ai shi kenan tunda abin da kika ga ya fi miki kenan. To maganar tafiyar fa?”
Cikin nutsuwa ta ce mishi, “A’a, Yaya ba bana son binka bane, amma ina so Gwaggona ta zo ta yi min baqunta, shekaru goma ne fa tunda ta aurar dani amma ba ta tava sanin xakina ba, in ma kunya ne ya hanata zuwa xakina, to yanzu kam ai na girma na isa a zo min baqunta”.
Ya jawota jikinshi ya qanqame, ya ce, “To in surukinta take kunya fa?”
Ta ce, “Eh, ai shi yasa nake so in yi amfani da lokacin tafiyar taka sai ta zo mu sake a gidan, tunda ta san baka nan”.
“In dai tafi kenan in barki”.
Ta ce, “Eh, ina maka fatan alheri”.
Kwana biyu bayan nan Gwaggo Habiba ta iso gidan don yiwa Saddiqa baqunta kamar yanda ta nema a dalilin tafiyar Mus’ab xin zuwa qasar Bulgeria kan wani aiki da aka tura shi, inda zai je ya yi watanni uku.
Saddiqa sai kaiwa da kawowa take yi tana tarairayar Gwaggonta wacce ta mayar tamkar wata jaririya saboda tattali da kulawa, ta sake kewayeta da nau’o’in abin sha bayan ta kwashe na cin. Ta dawo ta zauna kusa da ita suna hira.
“Iko sai Ubangiji, gaba xaya mijinki ya canza Saddiqa, xan kwana biyun da na yi tare daku a gidan nan kafin ya tafi sai na ga gaba xaya ya zama kamar ba shi ba, na ce hala shi yasa kema kika sauya. Rabon da ki yi kyau irin wannan tun farkon zuwanku gida”.
Saddiqa ta yi murmushin jin daxin yabon da aka yiwa mijinta, ta ce, “Don ma bani da lafiya Gwaggo”.
Da sauri Gwaggo ta tambaye ta cewa, “Baki da lafiya me ya same ki?”
Ta xan yi shiru ta rasa ta inda za ta soma maganar.
Gwaggo ta kalleta ta ce, “Ni kuwa ai ba wacce za ki voyewa al’amarinki bane in dai ba kina nema ki canza bane”.
Da sauri ta ce, “A’a, Gwaggo ba haka bane, wani abu ne ya same ni babu halin Yaya ya tavani sai cikina ya qulle ya yi ta faman ciwo, in yi ta murqususu ina wahala, sai da qyar zan samu ya sakeni bayan na yi gumi na yi kashirvan. Ko jiya da daddare Gwaggo ba rashin kunya zan yi miki ba, na yi haquri da shi ne kawai don na san wayewar garin yau xin nan tafiya zai yi”.
Jikin Gwaggo a sanyaye ta ce mata, “To amma ba ki gaya mishi ba?”
A hankali cikin nutsuwa ta ce mata, “Shima ya gane don ya gane ina fargabar ya tavani, na dai qi yarda ne kawai sanda ya yi min maganar”.
“To me yasa kika qi yarda Saddiqa? Matsala irin wannan ai ba za ki yi shiru ba”.
Cikin nutsuwa ta ce mata, “Gani na yi mun samu nutsuwa bai cika ma yin maganar asibiti ba in ba dubiya muka je ba, maganin da kuke aiko mishi kawai yake sha. In na ce mishi bani da lafiya sai kuma ya ta da hankali ya ce shine yasa min ciwon.
Sannan kinga wani qullutun dake nan gefen marata Gwaggo ba ki ji ciwon da yake yi min ba, duk abin da nake yi qarfin hali ne kawai, in na nuna mishi wannan ai ban san tashin hankalin da zai yi ba”.
Gwaggo tasa hannu tana tava gefen marar tata, abin da ta jin ya yi mummunar faxar mata da gaba.
“Gareka muke bauta ya Ubangiji, gareka kuma muke neman taimako”.
Kalmomin da take ta furtawa kenan. Cikin nutsuwa ta kalli Saddiqa ta ce, “Wannan ai ba abin voyewa bane, kar ki sake yin haka, yanda duk kika kai da gudun tashin hankalinshi ai dole ya san damuwarki, in kika voye mishi wa za ki gayawa? Shirya mu tafi asibiti yanzu”.
“To ko zamu bari sai gobe Gwaggo tunda yamma ta yi?”
Gwaggon ta kalleta, ta ce, “Ke shirya mu tafi za ki yi ta zama da ciwo ne? In ta kama mu kwana a can ba sai mu kwana ba”.
Dr. Usman ya gama duba Saddiqa, ya kalleta cikin nutsuwa ya ce mata, “Sauka ki zauna a can”. Ya nufi wajen zamanshi ya zauna Gwaggo tana binshi da kallo.
“Ciki ne!”
“Na’am”.
Kamar cikin firgita Gwaggon ta faxi hakan. Hankalinshi a kwance ya sake faxin, “Ciki ne ya fita ne daga cikin mahaifa yana so ya kawo matsala, in ba wanke shi aka yi ya fita gaba xaya ba za ta samu lafiya ba”.
Gwaggo ta soma kuka, “Wankewa ya fita likita bayan duk wannan wahala da aka yi?”
Ya ce, “Eh, to ina ganin kamar ya fi sauqi tunda an samu lafiya ai za a sake samun wani, in kuma kin fi so a gyara mishi zama sai a gyara. Sai dai za ta yi ta wahala don za ta yi ta zama cikin dokoki”.
Ta ce, “Eh, gara a gyara”.
Gwaggo tana zaune kan kujera tana jiran a fito da Saddiqa daga xakin da ake yi mata gyaran cikinta, cikin zuciyarta kuwa kiran sunayen Ubangiji take yi tana qara yi mishi tasbihi.
Sun dawo gida Saddiqa tana kwance saboda umarnin likita na kar ta yi wani aiki ko kuma motsi mai qarfi na tsawon sati biyu. Gwaggo ce take kai wa da kawowa a cikin gidan, sai ji da Saddiqan take yi kamar ta lasheta don farin ciki.
Kusan kullum raba dare take yi tana roqon Ubangiji ya tabbatar da wannan ciki ya zaunar da shi lafiya, ya tsare mai xauke da shi daga duk wata wahala. In kuma lokacin haihuwar ta zo yasa a samu haihuwar cikin sauqi, abin da za a haifan kuma yasa ya zama mai albarka.
Sati uku Gwaggo Habiba ta yi maimakon biyu da ta zo da niyyar yi, tana komawa gida kuma Abu ta taho da niyyar zama, ba za ta koma ba har sai Saddiqan ta haihu ta yi mata jego.
Ran nan da asuba misalin qarfe huxu da rabi na asuba Mus’ab ya bugo mata waya.
“Wash! Yaya daga bacci fa ka tasheni”.
“Ai gara in tasheki Aisha don ki qara sanin nima ba wani baccin nake yi ba, ba ki san irin haushin da nake ji ba da na yarda na baroki a gida, na riga na saba a tattaleni sai in rinqa jin na takura da yawa, ga shi kwanakin sun qi gudu balle in samu in yi in dawo in same ki”.
Ta yi murmushi ta ce, “Ka yi a hankali Yaya kar ka damu kanka da son sai ka yi sauri, magana guda xaya dai da zan yi maka ita ce, ka taho da goron albishir mai girma, don za ka dawo ka samu abin da zai faranta maka rai irin farin cikin da baka tava yi ba a rayuwa”.
Ya yi dariya ya ce, “Kin mai da maganar wasa Aisha tunda kika faxi hakan, ni yanzu da wani farin ciki da zan yi wanda ya kai na ranar da Kawu Gixe ya bani ke balle har ya fishi?”
Ta ce, “To ai shi kenn Yaya mu bar maganar kawai sai ka dawo”.
Ya ce, “To shi kenan sai na dawon”.
Cikin Saddiqa ya shiga wata na shida lokacin da aka soma shirye-shiryen dawowar Mus’ab.
Ran nan tun safe ya iso gidan a dalilin saukar asuba da ya yi, ga mamakinshi bai ga Saddiqa wajen taren shi a airport ba, sun iso gida bai ganta a qofar gidan ba.
Ya shiga falo yana zaton ganinta, Abu ya gani. Cikin mamaki ya buxe baki ya ce, “Hajiya Abu nake gani a gidan ko mafarki ne?”
Tana murmushi ta ce, “Ba mafarki kake yi ba nice”.
“Kar dai ki ce min kema zumuxin dawowar nawa ne ya saki yin wannan doguwar tafiyar don ki tareni”.
Ta sake wani murmushin ta ce, “Zumuxin yi maka albishir da taryen abin alherin da ya samemu ne ya kawoni Mus’abu, ni kam ai ba jiya ko yau na iso gidanka ba, watana biyu kenan. Matar gidan ce kawai ba ta yarda a gaya maka ba”.
Kan Mus’ab ya xauke jin kalaman Abu, amma don ya sauwaqewa kanshi komai sai ya tambaye ta.
“Ina Aishan take Abu?’
Ta nuna mishi xakinta, ta ce, “Ni na hanata tashi tarenka na ce ta jiraka nan inda take za ka zo ka sameta saboda ta bi dokar da likita ya sanya mata”.
Gaban Mus’ab ya yi mummunan faxuwa, kar dai lalurar da ya bar Aisha tana vovvoye mishi ce ta yi riqan da har likita yake doka a kai?
Da sauri ya faxa xakin nata, qamshi da ni’imar dake ciki bai hanashi kaxuwa da ganin da ya yi mata a kwance ba.
“Me ya same ki Aisha?”
Ya yi tambayar a sanyaye. Ta saki lallausan murmushi tana daga kwancen ta ce, “Qaraso mana Yaya, so nake in jika a jikina”.
Tana faxin hakan ta ware hannayenta nuna alamar shi take sauraro. Ya yi maza ya qarasa gareta, nan take suka soma tumurmusar juna, sai dai basu je ko’ina ba ya ja ya tsaya yana kallon ta cikin kixima.
“Mene ne wannan Aisha?”
Ya yi tambayar yana mai kallonta. Ta saki lallausan murmushi a hankali cikin yanayi na raxa ta ce mishi, “Ciki ne, cikin da kake ta fatan ganinshi a gidanka ne yau kake ganinshi, shine albishir xin da dama nake gaya maka na tanadar maka”.
Yasa hannu biyu ya qanqameta a jikinshi tamkar dai ba a cikin hayyacinshi yake qanqamar ba saboda tsananinta.
“Haqiqa kin yi min albishir Aisha da abin da tuni na haqura da ganinshi a gidana, don haka nima zan yi miki tukwuici da abin da ba ki tava tsammanin samun shi ba”.