ABU NAKA BOOK 3 BY SODANGI
GARIN MISAU RANAR TALATA DA YAMMA
Direban dake janye da motar su Mus’ab ta yi parkin a qofar gidansu da misalin qarfe huxu da rabi na yamma, Mus’ab yana karanto addu’o’in godiya ga Ubangiji bisa kariyar da ya yi musu suka iso lafiya.
Bai san sanda Saddiqa ta fice daga cikin motar ba, ya shiga gida yana riqe da jakarta da takalminta da ta fita ta bari a motar tana rungume da Gwaggo Habiba tana kuka. Fitowar Malam Abdullahi daga xakinshi cikin hamdala ya dawo dasu cikin nutsuwarsu.
“Sannunku da zuwa, sannunku da zuwa”.
Abin da yake ta faxi kenan. Mus’ab ya ja ya tsaya daga bakin zauren.
“Shigo mana Mus’abu ka tsaya daga can kamar wani baqo?”
Ya bi bayanshi zuwa cikin xakinshi kamar yadda Saddiqa ma ta bi bayan Gwaggonta suka qule cikin nasu xakin.
Mus’ab da babanshi suna gaisawa ita ma Saddiqa ta yi sallama ta shigo, cikin ladabi ta tsuguna tana gaishe shi.
“Iko sai Ubangiji, jiya Habiba take maganarku ashe kuna tafe. To kun zo lafiya ko?”
Ta ce, “Lafiya qalau”.
“Ya ya abokan zama?’
Ta amsa cikin girmamawa, “Duka sun ce a gaishe ku”.
Ya ce, “Madallah, Ubangiji ya yi muku albarka”.
Ta tashi ta fita ta barsu ta sake shigowa, ta ajiyewa Mus’ab kwanon furar da Gwaggo Habiba ta dama mishi da kanta, wanda ba a tava yin hakan ba sai dai tasa ayi mishi.
Saddiqa tana zaune a kicin tana ta taya Gwaggonta aikin abincin da take yi suna kuma hirarsu, duk lokacin da ta kalle ta sai ta ga ita take kallo.
Ta yi murmushi ta ce, “Gwaggo kina kallona kina mamakin rashin zuwana gabanki shekara guda ko?”
Gwaggo Habiba ta ce, “A’a, Saddiqa ba shi bane, aure ai ya wuce haka, ya kan kuma sa ayi abin da ya fi haka. Canzawarki ce take bani mamaki, ban tava zaton za ki zama haka ba, gaba xaya kin sauya min, sai nake tunanin ashe dai yayanku zai riqe aure”.
Saddiqa ta yi ‘yar dariya ta ce, “Uhm! Gwaggo kenan, wai ku me kuka mai da Yaya ne?”
Gwaggo ta tayata yin murmushin ta ce, “Ke dai kawai an godewa Ubangiji ga shi shima……”
Ta fasa faxin abin da za ta faxa xin saboda b ta saba zancenshi da kowa ba. Saddiqa ta gane abin da take nufim, ta miqa hannu cikin ladabi ta karvi ludayin miyar dake hannunta don ta yi mata abin da take son yi, daidai lokacin kuma tana yi mata bayanin Yaya Mus’ab ai masu ganinshi kullum ma suna mamakin yanda ya zama, to balle wanda ya shekara bai ganshi ba, to ya dena komai Gwaggo, baya shan taba balle barasa, duk wani abin da kika sani ya bari.
Cikin jin daxi ta ce mata, “Iko sai Ubangiji, ashe a kan bari?”
Ta ce, “Eh, to shi dai ya daina, na kuma yarda ya daina don baya faxin abin da ba gaskiya bane”.
Wani daxin ya sake kama Gwaggo saboda irin shaidar da matarshi ke bayarwa a kanshi. Ta ce, “Eh, haka dama waxanda suka sanshi nake jin suna faxa, to Ubangiji ya qara shirya mana”.
“Aisha!”
Ta fito ta zo ta same shi. Ya ce, “Gayawa Inna ta yi haquri Baba ya ce muje masallaci magariba ta gabato, sai mun dawo zan zo mu gaisa”.
Ta ce, “To, sai kun dawo”.
Ta koma tana gayawa Gwaggon nata, su kuma suka fita. Malam Abdullahi yana gaba yana ba shi wani labari, shi kuma yana biye a yanayi na girmamawa da amsawa cikin ladabi.
Da daddare xakin Gwaggo Habiba ya cika da jama’a ‘yan sannu da zuwa, qannen Mus’ab mata duk sun zo, ga maqwabta da suka shirshigo ana hira, Abu tana basu labarin irin borin da Saddiqa ta yi ranar da za ta barosu, tana yi kuma tana kuka tare da faxin ni zan biki, ni zan biki ki kaini gun Gwaggona, ana ta dariya.
Ta kalli Saddiqa dake kwance kan qafar Gwaggon nata ta harareta tare da faxin, “Ashe-ashe duk gulma ne da iya shege, jira take yi in tafi in basu wuri ta sa hannu biyu ta rungume al’amarin mijinta, tunda ga shi ba ta zo gaban Gwaggon nata ba sai yau shekara guda har da kwana goma sha takwas”.
Gwaggo Habiba ta yi maza ta ce, “Yanzu kwanakin dawowarki daga can kenan Inna?
Ta yi maza ta ce, “Eh mana, to ko dawowarmu daga aikin Hajji yau wata nawa ne?” Ta hau lissafi.
Gwaggo ta girgiza kai ta ce, “Kai kwanaki suna gudu, Ubangiji dai ya azurtamu cikawa da imani”. Gaba xaya aka amsa “Amin-amin”.
Abu ta sake juyawa kan Saddiqa, hannu tasa ta kai wa kuturinta duka ta ce, “Ke, tashi mki zauna kema kamar kowa, kin zo gabanta za ki yi ta tumurmusar ta, in kin koma wurin miji ki mance da ita. Waxannan mazaunan da kika ajiye in baki zauna a kansu ba mene ne amfaninsu?”
Saddiqa ta soma shure-shure da kuka sai dai hawayen sun qi zubowa.
Gwaggo ta ce, “Ba fa laifinta bane Inna, kuma da kanku kun yi ta faxa bai zauna ba, ga kuma qarin girma da ya samu, to ai ita ma ba ta zauna ba tunda tare da ita yake yin tafiyar”.
Mus’ab ya tsaya daga tsakar gida ya kira Hamida, ta yi maza ta tashi ta fita, ba ta daxe ba ta dawo ta ce, “Anti wai ki je yana kiranki”.
Saddiqa ta xaure fuska ta ce, “Gaskiya ni bana son Antin da kuke ci min, a kirani da sunana kawai”.
Ta miqa hannu ta buxe jakarta tana xiban magunguna. Abu tana faxin, “Ai tunda kika auri tsoho mai tsofaffin qannen da suka haifeki, to dolenki kema ki karvi tsufan”.
Saddiqa ta yi dariya daidai ta xauki kofi da robar ruwan swan tana faxin, “Uhm! Abu kenan, yanzu nan Yaya Mus’ab xin ne tsoho?” Ta fita ta barsu suna dariyarta.
Minti kusan biyar da fitar Saddiqa sai gata ta dwo tana kuka, gaba xaya aka yi tsit! Ana kallon ta.
“Mene ne kuma na wannan kukan da kike yi?”
Tana sharve ta baiwa Abu amsa da cewa, “Wai dole sai na fita mun tafi can gidan mun kwana”.
Da sauri Abu ta ce, “Ke wuce ki shiga xakin uwarki ki hau gadonta ki yi kwanciyar ki ko ‘yar hira ku yi ku xebewa juna kewa kin ji?”
Saddiqa ta yi hanzarin bin umarnin nata ta wuce cikin xakin ta hau gadon ta kwanta, ta barta tana faxanta.
“Haba, ni bana son fitina, fitanannen mutum kawai mara haquri, shekara guda baka kawo yarinya gaban uwarta ba kuma kun zo ba za ka barta ta sake ba?”
Da haka hirar ta watse kowa ya nufi gidanshi.
Washe gari da sassafe Saddiqa ta fito daga wanka kenan tana zaune kusa da Gwaggonta tana shafa, sai ga Abu ta shigo tare da sallamarta.
Ta kalli Abu ta ce, “Gaskiya ko tare dake muka kwana iyakar sammakon da za ki yi kenan ki shigo mana xakinmu”.
Ta zauna kusa da Saddiqan suka gaisa tana kallonta.
“Ni kina da ciki ne?”
Ta ce, “Nima ban sani ba”.
Ta yi tsaki ta ce, “Kar ki sani”. Ta juya wurin Gwaggo Habiba, “Ba ta ce miki komai bane?”
Cikin nutsuwa ta ce, “A’a, ba ta da komai Inna, ta dai ce wai tana da matsalar al’ada. Na ce daga baya kenan hakan ya sameta ko? Tunda ita ai ba mai irin wannan lalurar ba ce”.
Abu ta ce, “To ba sai a karvo mata magani ba?”
Saddiqa ta fito cikin kwalliya sosai sai sheqi take yi, ta yi kyau har ba a magana. Abu sai binta da kallo take yi.
Ta kalli Abun ta yi murmushi ta ce, “Kar ki karvo min magani don ba zan sha ba, Yayana yana kaini asibiti”. Ta wuce ta fita saboda jin isowar Mus’ab, daga fitar nata ta dawo ta zauna.
Mus’ab ya shigo ya nemi wuri ya zauna kan tabarma, ya yi kwalliyar manyan kaya babbar riga da ‘yar ciki da wando na farin yadin voil, ga hularshi ta zauna d ata yi matuqar sakuwa. Tuni qamshinshi ya gauraye ko’ina. Ya shiga yiwa Innarshi bayanai tana sauraro har tana faxin haka ne, abin da baya faruwa a tsakaninshi da ita.
Hatta Abu dake tayata sauraron daxi ne ya kamata. Saddiqa ta tsuguna a gefen Mus’ab riqe da kofin ruwa da kuma magani a hannunta, tana jin ya yi shiru ta yi maza ta ce mishi, “Ga shi ka sha’.
Yasa hannu ya karva ya sha saboda ba zai yi musu da ita a gaban Innarshi ba.
Abu ta ce, “A’a, ni wane irin magani ne wannan kike xura mishi? Ba ki gaishe shi ba ba ki ba shi abin da zai ci ba kin kawo qwayoyi kin ba shi. Haka jiya yana kiranki kika kama xiban qwayoyi. Baka da lafiya ne Mus’abu?’
Kafin ya amsa Saddiqa ta ce mata, “Sai ana ciwo ake shan magani? Kema ba na ga safe da yamma kike sha ba?”
Bai biyewa Saddiqa ya mayar da maganar wasa ba sai ya ce mata, “Bani da lafiya Abu”.
Abu ta kalle shi ta ce, “Wane irin ciwo ne wannan da bai hanaka qiba ba, bai kuma hana fatarka gogewa ta yi kyau ba? Ko kuwa dai irin shagwavarku ta ‘ya’yan yau ku yi ta xirkawa kanku qwayoyi haka siddan?”
Ya ce, “A’a, ciwo nake yi sosai”.
Abu ta riqe baki cikin mamaki ta ce, “To hala ciwon ne ya mai da kai haka?”
Ya yi murmushi ya ce, “Ba shi bane, ina zaune lafiya ne a gidana na yi sa’a Aisha ta karvi lalurata ba ta tayar da hankalinta ba balle nawa ya tashi, ban da haka kuma na daina shan abubuwan da da nke sha, shi yasa kika ga na canza da yawa. Amma ina buqatar ku qara yi min addu’a”.
“To a qara yi maka addu’a baka faxi damuwar da ta same kan ba don mu san irin wacce zamu qara akan wacce dama muke yi”.
Bai vata lokaci ba ya yi mata cikakken bayani.
“Ba za ka haihu ba Mus’abu?”
Abu ta yi tambayar. Nan take kuma ta soma kuka, wani irin kuka mai tsanani tamkar wacce aka yiwa wani abu mai tsanani.
Kanshi a sunkuye qafafuwanshi a harxe yanda dama yake zaune tun farko bai motsa ba. A haka yake jin kukan da Abu ke yi, yake kuma sauraron kalaman da Innarshi ke furtawa.
“Abin da na gudarwa Saddiqa kenan, ga shi kuma shine ya sameta”.
“A’a Gwaggo, A’a, Gwaggo kar ki shiga wannan maganar don ni na warke”.
Abu ta daka mata tsawa ta ce, “Ke tafi can shashasha, wani warkewa za ki yi shi bai warke ba, ina ce shi yake sa miki? To ta ina za ki samu lafiya?”
“Gaskiya ni bana so, Abu bana so, ke ba za ki sasanta magana ta zama mai sauqi ba za ki qara lalatata?”
“Ke matsa can wawuya, wannan maganar taku ai dama a lalace take, a ina kika tava ganin zama ya yi dai-dai tsakanin mai lafiya da mara lafiya? Sokuwa kawai, wai ke ga mai son miji ko? Zai kuwa kai ki ya baro, rashin haihuwa wasa ne? An ce miki in kece ba za ki haihun ba zai yarda ne wata zai je ya kawo in ba ki yi haquri ba ki kasa zama, shi kam ai shi ya jawa kanshi, tun yaushe ne ake baqin cikin wannan shaye-shaye da Mus’abu ke yi? Tun bai isa komai ba”.
Ta bar maganar ta kama kuka sosai.
Cikin nutsuwa Gwaggo ta ce, “In kun gama hutun sai ka tafi ka barta a gida”.
Saddiqa ta yi maza ta ce, “A’a, Gwaggo zan bishi ba yaji na yi ba, ba kuma qarar mijina na kawo muku ba, baqonta muka zo yanda muka zo tare kuma haka zamu tafi tare, ina sonshi”. Ta soma kuka.
Mus’ab ya buxe baki an hankali ya ce mata, “Inna ni zan fita”.
Ta ce mishi, “To”.
Abu ta miqe ta bi bayanshi suka tafi suka bar Saddiqa tana ta faman kuka.
A hankali cikin yanayin rarrashi ta ce mata, “Da kin yarda kin zauna a gida har kafin a ga yanda lamarin zai kasance”.
Ta ce, “A’a, zan bishi, zan je in zauna da shi, bai yi min komai ba, ban ga kuma abin da sauran surukaye suke wa matansu ba wanda shi bai yi min ba. Da nice nake cikin yanayin da na ga Kubrah jiya da kin ce an qwace mishi ni, in muka tafi kuma ni ba zan ma sake…..”
Gwaggo Habiba ta katseta ta hanyar tambayarta, “Kina cikin hankalinki kuwa Saddiqa ko wani abu ne ya same ki?”
“Ki yi haquri Gwaggo ba abin da ya same ni, bana jin daxi ne kawai na yanda ake tafiyar da al’amarin Yaya Mus’ab a gidan nan, sai yaushe za a fara tausayin shi? Duk wani wanda zai yi baqin cikin al’amarin ai tayashi yake yi ba finshi ya yi ba”.
Ta soma ba ta labarin halin da Mus’ab ya shigo lokacin da likita ya ba shi labarin abin da yake ciki, da yanda aka yi ta shawo kanshi har ya samu nutsuwar da yake tare da ita. Har ta gama Gwaggo ba ta sake ce mata komai ba, iyaka dai zuciyarta ta kai matuqar da ba za a iya kwatantawa ba.
“To sai kuma mu zo gabanku Gwaggo shi da kanshi ne ya faxi al’amarinshi sai a turashi a gaba da maganganu masu zafi, Abu tana yi ku kuna yi? Kenan babu mai tausayinshi?”
Gwaggo ta fita ta bar mata xakin ta nufi kicin ta kama aikin abincinta, ita ma Saddiqa ta yi shiri ta fita ta bar gidan.
Mus’ab yana zaune kan tabarma xakin Abu yana cin gasasshiyar masara suna hirarsu lokacin da Saddiqa ta yi sallama ta shiga gidan.
Abu ta yi mata sannu da zuwa kamar ba yanzun nan suka rabu ba.
“Me za ki ci a kawo miki?”
Ta ce, “Masara”.
Ta ce, “Ai kuwa iyakarta kenan, sai dai mijinki ya sn miki. Kai ka san mata masarar ka raba biyu ka ba ta rabi”.
Mus’ab ya kalli Abu ya ce, “To ke ki yi shiru mana ki barta ta yi maganar da bakinta”.
Saddiqa ta yi shiru ba ta yi magana ba. Abu ta lura basa magana da juna da ita kaxai suke yi. Ta yi dariya ta ce, “Au ni fushi da juna kuke yi ne?”
Mus’ab ya ce, “Take yi dai, ni ina fushi ne?”
Saddiqa ta yi maza ta ce, “Waye ma ya fika? Ba ga shi don ka yi fushi wai kana so nima ka bani haushi ba ka je ka aske qasumbarka? To na rantse kanka za ka qarawa haushi, don ba zan sake yin magana da kai ba sai randa ta koma daidai yanda take kafin ka asketa”.
Abu ta qyalqyale da dariya ta ce, “Ai kuwa dai taka ta sameka, kai kuwa me yasa ka yi wannan aski tunda ka san ba a so?”
Ya yi tsaki ya ce, “Abin haushi ne da ita Abu, daga zuwanmu garin nan har ta fara sava alqawuran da ta yi min”. Ya kwashe bayani tas ya yi mata.
Abu ta ce, “Eh to, ba ta kyauta ba, amma kai ma fitana ne da kai, don haka an yi dai-dai dukanku kun yiwa juna shi kenan magana ta qare sai ku sasanta a shirya kawai a kori gaba”.
Ya kalli Saddiqa ya ce, “To kin ji Aisha, Abu ta ce mu shirya”. Ta yi kamar ba ta ji shi ba.
Kwanansu uku da zuwa Misau kullum a gidan Gwaggo Habiba Saddiqa take kwana, tun da ta je gidan Abun ma sau xaya ba ta sake fita ba, kowane lokaci tana manne da Gwaggonta, in tana kicin suna tare, in ma xakin ne haka, ko sallah za suyi ga sallayarta ga tata.
Zuciyar Gwaggo ta yi matuqar jin daxi ganin yanda Saddiqa take matuqar son mijinta, take xai-xai da shi a duk lokacin da ya shigo gidan. Sai dai abin da ya dameta guda xaya ne, maganar da Mus’ab da bakinshi ya gaya musu cewar likita ya tabbatar mishi da cewar da wuya qwarai ya haihu.
To haka za su zauna shi da Saddiqa ba za su haihu ba? Tana yiwa kanta tambayar take yin maza ta kawar da ita ta hanyar mayar da al’amuran gaba xaya ga Ubangiji, don tsananin abin ya wuce duk wani kwatance.
Ranar asabar da yamma bayan sallar la’asar Mus’ab ya shigo falon Innarshi suna tare ita da Saddiqa, cikin nutsuwa ya ce mata, “Inna sanda zamu zo garin nan Aisha ta yi min alqawarin da da muka zo ta qi cikawa”.
Cikin kulawa Gwaggo Habiba ta tambaye shi, “Wanne irin alqawari ne wannan?”
A hankali ya ce mata, “Na gaya mata in mun zo zamu sauka a can gidana ne, daga can ne za ta rinqa zuwa duk inda za ta, amma in dare ya yi za ta koma can ta kwana ta ce to”.
Saddiqa ta yi maza ta ce, “Ba haka bane”.
Gwaggo Habiba ta yi maza ta kalle ta, “Za ki qaryata mijinki ne a gabana?”
Ta yi maza ta yi shiru saboda ganin yanda Gwaggon ta xaure mata fuska.
“Bana son iya shege”.
Ta juya wurin Mus’ab ta ce, “In ka tashi tafiya ka kirata ku tafi, in kuma yanzu kake son tafiyar ma sai ku je”.
Hankalinshi a kwance ya ce, “Na fi so mu tafi yanzu saboda su Bilkisu sun yi min waya wai mazansu za su zo gaisheni na ce to a sameni a gidana”.
Da sauri Gwaggo Habiba ta ce mishi, “Qwarai kuwa su sameka a gidanka, ke Saddiqa xebo mishi girkin da nake yi ki riqe mishi”.
Ta yi maza ta ce, “To Gwaggo”. Ta je ta dawo tana cewa, “To amma Gwaggo ai mun ce zamu Bauchi gobe da sassafe”.
Gwaggo Habiba ta ce, “Eh, in hali ya yi na ki fito da sassafen sai ki fito, in kuma bai yi ba sai ki haqura sanda mijinki ya samu zarafi sai yasa a kaimu”. Ta ce, “To”.
A mota suna tafiya Saddiqa tana gaya mishi kar ka ga ka haxani da Gwaggona ta tilastani binka ka yi zaton ko in munje wani abin arziki zamu qulla ba kulaka zan yi ba”.
Ya ce, “Babu komai Aisha in dai zan samu in tava jikinki ai magana ta qare”.
Washe gari da safe Saddiqa da kanta ta yiwa Gwaggonta waya, “Gwaggo ku yi haquri ba zan samu fitowa daga gidan ba yau su Anti Hamida za su zo wuni. Na ce ko ita ma Kubrah za a yiwa mijinta magana don ta zo tunda ‘yan’uwa za su haxu”.
Gwaggo Habiba ta ce, “To, sai a gwada”.
Baqunta mai daxi su Saddiqa suka yi da kuma tafiye-tafiye masu yawa, har wurin su Ishak da sauran ‘yan’uwa da abokan arziki.
Sati huxu suka yi kafin suka yi shiri suka koma gida da xinbin tsarabar da suka yi ta rarrabawa maqwabta da abokan mu’amala na cikin gari.
Bayan dawowar su Saddiqa gida sun ci gaba da zamansu lafiya a sannu da fahimtar juna dake tsakaninsu.
Mus’ab ya fita hanyar duk wata masha’a, ya mai da hankali kan istigfari, neman gafarar abin da aka aikata a baya da qoqarin gyara na gaba.
A yanzu matsalarshi babba ita ce rashin lafiyarshi, zuciyarshi ta qi yarda ta ji daxin zaman da zai yi da Saddiqa, ita ba haihuwa shi babu, bayan kuma lalurar tashi ce shi ya jawowa kanshi ita.
In shi Gwaggo Habiba ta samu yaxuwar zuriyarta ta wurin wasu ‘ya’yan, to ita Innarshi fa, Saddiqa kaxai ta bari a duniya. Wannan shine abin da ya fi komai damun shi.
Auren nasu ya cika shekaru biyu, yau ma suna gaban likita, zuwa yanzu kuwa an yiwa Mus’ab canjin magani har sau biyu saboda wasu lalurorin nashi da aka sake ganowa.
Sauraron shigowar likitan suke yi don jin sakamakon sabbin gwaje-gwajen da aka yi musu.
Ta xaga ido ta kalle shi cikin sanyin jiki, a hankali ta buxe baki ta ce mishi, “Gabana sai faxuwa yake yi”.
Ya yi murmushi ya ce, “A kan me Aisha?”
Kafin ta ba shi amsa Dr. Usman ya turo qofa ya zo ya zauna a kan kujerar shi, gaba xaya suka mai da hankali wajen sauraron abin da zai gaya musu.
“Ina ganin mun xan samu ci gaba tunda ita Hajiya ba a sameta da wata matsala ba, don haka za ta rinqa shan magani ne kawai na hana haihuwa da qwayoyin cuta.
To kaima kuma mun gano inda asalin matsalarka take, kamar yanda na riga na tava gaya maka ne, ita wannan cutar ta kan yi riqar da take daskarewa har ta toshewa qwai hanyar shiga mahaifar mace, to abin da ya faru da kai kenan, shi yasa magungunan da muke ta amfani dasu basu wani yi aiki na a zo a gani ba”.
“To yanzu babu wani abin yi kenan?”
Ya yiwa likita tambayar. Ya yin da Saddiqa ta yi kasake tana sauraro.
“Eh, akwai abin yi, shine tiyata a buxe wurin a kankare ita jijiyar a cire ciwon daga cikinta, sai kuma ka ci gaba da shan magani zuwa wani lokaci da zamu ga abin da zai faru”.
Saddiqa ta yi shiru in ban da tunanin inda jijiyar take babu abin da take yi.
Sun dawo gida Saddiqa tana zaune tana kuka.
“Ni ban yarda da aiki ba, kaima ka san yinshi hatsari ne, shi yasa ma ka qi tambayar likitan hatsarin shi. Ai ba murxarka ciwon yake yi ba balle ko ka ce yana damun ka”.
Mus’ab ya kalle ta ya xan yi murmushin qarfin hali.
“Hatsari Aisha? Har ya wuce na ina zaune ana cewa in abin ya gagara sai a san yanda za ayi? Me ake nufi? Haka zan zauna duk sanda na je gida sai anyi min kalamai na barazana?”
Ta xan yi shiru kafin ta ce mishi, “Ba dai Gwaggo ce ta yi maka maganar ba Abu ce, ita kuma baka iya nuna mata ka ji haushi balle ta sani, ko ranar da aka yi hakan kuma a kaina fushinka ya qare, ka ce wai na ji daxin abin da ta faxa xin bayan ni ban tava tayar da maganar likita ba a gabansu kai ne”.
Ya yi shiru fuskarshi a xaure alamar ranshi ya sosu, ita ma ta ja bakinta ta yi shiru, dama ta ga abin zai yi nisa ta miqe ta nufi wurinta ta ci gaba da harkokinta.
In har Mus’ab yana da wata matsala a yanzu da ta addabe shi, ta takurawa zuciyarshi, to ba ta wuce matsalar rashin haihuwarshi ba, duk da bai tava ganin wata damuwa a wurin matarshi ba, to amma kuma ya yarda da maganar da Abu ke yawan gaya mishi cewar quruciya da kunya ke hanata nunawa, nan gaba in abin ya yi nisa ba za ta jure ba.
“Hajiya lafiyarta yanzu qalau, mahaifarta kuma a shirye take in aka sa mata qwai za ta xauka”.
Wannan shine kalamin da likita ya yi musu a zuwa asibitin da suka yi na qarshe. Ya waiwaya ya kalli Saddiqa dake ta faman sharar bacci a bayanshi, bacci ne mai nauyi da alama kuma bacci ne na gajiya.
Ya kawar da kanshi daga gareta, cikin wani tunanin wanda daga baya ya ga ba zai fissheshi ba. Ya miqe ya shiga banxaki ya yi wanka tare da alwala ya fito ya fara gabatar da nafilfili.
Washe gari da safe suna tare wurin karyawa, suna kuma hirarsu cikin nutsuwa. Ya sake shigo mata da maganar da ta riga ta ce mishi ba ta son ji.
“Aisha bai fa kamata a ce muna cikin matsala sai mu kawar da ita mu yiwa kanmu qaryar bamu da ita ba. Kin yarda da maganar aikin nan da kike yi sai in ga kamar nine baki damu dani ba”.
Ta yi maza ta xago ido ta kalle shi.
Ya ce, “Eh mana, yanzu ke ba za ki fata da sha’awar ki ganki xauke da cikina a jikinki ba?”
Da sauri ta ce, “Ina yi mana Yaya”.
Ya ce, “To in kina yo don me ba za ki qarfafa min zuciyata ba sai ki rinqa nuna ke baki da matsala, amma kuma kullum kina aiken a kawo miki jariri ki rena? Kullum fa sai kin tura an kawo miki xan da Zainab ta haifa”.
“Ba ina qin aikin bane hatsarinshi ya yi yawa, sai na ce to mu tuntuvi iyayenmu don mu ji abin da za su ce kai kuma ka qi”.
A hankali ya ce mata, “Ina tsoro ne kar su ce basu yarda ba, in suka yi haka kinga ba zan tafi babu izininsu ba, in kuma aka yi sa’a suka amince nan kuma hankulansu za su tashi suyi ta fargaba suna zullumin yaushe za a yi, in anyi kuma me zai faru? Shi yasa na fi so sai anyi sai mu gaya musu tunda lokacin babu sauran zullumi ko fargaba”.
Da irin waxannan kalaman Mus’ab ya rinjayi Saddiqa ta amince da maganar aikin nashi.
Nan da nan ya tasata a gaba suka koma gaban likita don ya sanya ranar da za a yi aikin, inda ya xibar musu kwanaki ashirin da xaya a dalilin akwai magungunan da ake buqatar Mus’ab xin ya yi amfani dasu kafin lokacin.
Duk da Saddiqa a kan ta amince ake yin shirin jikinta a sanyaye yake qwarai.
“Zo ki ji, kawo kunnenki nan ki ji abin da zan gaya miki”.
Ya soma yi mata maganar a kunnen nata cikin yanayin raxa. Ta xago ido cikin murmushi tana kallon shi saboda maganganunshi. Bai rama mata murmushin ba, maimakon haka magana ya soma yi mata cikin nutsuwa yana mai kallon idanuwanta.
“Sanda Innata take raye haka take yi min in na yi mata wani xan abin da ya faranta mata rai, sai ta jawoni kusa da ita ta raxa min wani abu mai daxi a kunnena. Zan tafi tiyatar nan Aisha zuciyata cike da fata da buri na ayi nasara in samu ki haifar min ko da ‘ya mace guda xaya ne da zan yi mata takwara da ita”.
Saddiqa ta qara matsawa kusa da shi a hankali ta cusa hannayenta cikin rigarshi tare da kwantar da kanta a qirjinshi, a hankali cikin kalamanta mai sanyi ta ce mishi, “In ka haifi mace guda to Gwaggona fa Yaya?”
Kwanaki ashirin sun cika saura guda xaya tal! Saddiqa tana xakinta a kwance Mus’ab ya shiga ya sameta, ta yi maza ta share hawayenta tare da sakin fuskarta don kar ya gane abin da take ciki. Shima ya yi kamar bai gani ba.
Matsawa kusa da ita ya yi ya kwanta, ya miqa hannu ya jawota jikinshi yana sansanar qamshinta. Ta yi qoqari ta xan ture shi ya xan matsa kaxan.
“Mene ne haka?”
Ba ta kula tambayar tashi ba ta yi maza ta miqe ta zauna.
“Da ka tsaya mun yi magana tukunna”.
Ya ce, “Ba zan yi ba sai na yi abin da ya kawoni tukunna”.
Bai yarda ya bari ta sake ce mishi komai ba ya shiga sarrafata, sai da suka samu nutsuwa sai ta ce mishi, “Ni Yaya baka da damuwa ne, gobe ne fa aikin nan?
Bai kalle ta ba ya ce, “Bani da ita, takin ma bana son ki gaya min addu’a kawai na ce ki rinqa yi”.
“To ai ni munanan mafarke-mafarken da nake yi ne suke bani tsoro, in zan gaya maka abin da na gani kuma ka ce wai baka son ji”.
“To a ina kika ji an ce a ba da labarin mummunan mafarki? Ina ce addu’a aka ce a rinqa yi mishi?”
Bai tsaya ba ya tsallaketa ya shiga banxaki ya yi wanka ya fito tare da alwala, ya shiga gabatar da nafila. Ita ma ta bi bayanshi, basu daina ba har sai da aka kira sallar asuba.
Yana dawowa daga sallar asuba ta je kusa da shi don ta gaishe shi, ya jawota ya rungume a jikinshi yana shafata.
“Santsin jikinki kaxai ya isheni ni’ima Aisha”.
Ta yi maza ta zame daga jikin nashi ta ce,
“A’a, Yaya kana faxa ne kawai don in ji daxi, amma in da haka ne ai da ka haqura da wannan tiyatar da za ka tafi yau, tunda na gaya maka ni kam Yaya Mus’ab ina sonka rashin haihuwa kuma ba zai rage komai ba a tsakaninmu da kai”.
“Na sani Aisha”.
Ya faxa cikin jin daxin kalaman nata.
“Na sani Aisha, na san za ki iya zama dani da lalurata. To amma mene ne tukuicin son da muke yiwa juna? Ina son ganinki da ciki”.
Ya faxi hakan cikin raxa har ya sata jin kunya.
“An jarrabi zuciyata da son in ganki a hakan, in san nine, mutanen duniya ma su tayani shaida hakan a ce matar Mus’ab juna biyu ne da ita”.
Ta yi murmushi, yana ganin murmushin nata ya yi maza ya miqe ba tare da ya ba ta damar da za ta sake narke mishi ba.
“Bari in yi wanka Aisha in shirya kafin su Idris su iso”.
Kafin ya fito daga wankan sai ga Idris da matarshi Abida sun shigo, ‘yan mintoci kaxan kuma sai ga Sani shima ya iso tare da amaryarshi.
Saddiqa tana tsaye a xakinta jikinta sai rawa yake yi, Mus’ab ya shigo sanye da jallabiya mai ruwan shuxi, silifas xin wanka ne a qafarshi, qamshinshi na kullum yana tare da shi.
Ya kama hannayenta duka biyu ya riqe a cikin nashi, ya sunkuyo da idanuwanshi cikin nata da tuni suka fara zubar da hawaye.
“Ai nima zan bika, zan je ayi komai a kan idona ina gani”.
A hankali ya ce mata, “A’a, Aisha yi haquri ki yi zaman ki a gida, ga ‘yan’uwanki mata nan sun zo za su tayaki zaman gidan zai fi miki sauqi da nutsuwa”.
Za ta yi magana ya yi maza ya ce mata, “Shhhhhh!” Kan ta yi wani abu ya yi hanzarin sanya bakinshi a nata, kusan minti guda kafin ya saketa.
“Kar ki yi min musu, addu’a kawai za ki yi min”.
“To Yaya”.
Cikin rawar murya ta faxi hakan. Bai jira ya ji sauran maganar ba ya yi maza ya fita daga xakin, ya samu su Idris da Sani a waje da suka zo don suyi mishi rakiya.
Saddiqa ta nemi wuri ta zauna a qasa tana ta faman kuka Abida tana rarrashinta.
“Ki yi haquri Aisha, ki yi ta addu’a kawai Ubangiji dai yasa ayi a sa’a”.
Ta xago ta kalleta cikin hawaye ta ce, “Iyayenmu fa basu san da aikin ba, na yi na yi mu gaya musu ya qi, wai yana tsoron kar su hanashi gara in an yi kawai su ji”.
Abida ta jinjina lamarin, nan take kuma sai ta ba ta shawara.
“To yanzu tunda ya riga ya tafi ai sai ki gaya musu su sani, don kuwa ai yana buqatar addu’arsu”.
Ta yi maza ta miqe ta xauko wayarta, lambobin Gwaggonta ta danna, tana jin muryarta ta soma kuka.
“A’a, me ya sameki Saddiqa ba dai wani abin ne ya faru tsakaninki da mijin naki ba ko?”
Saddiqa ta ce, “Eh, Gwaggo”.
Gwaggo ta yi maza ta ce, “Yau to ai yanzu muka gama magana da shi ya kirani muka gaisa, mun kuma xan jima muna magana ban ji alamar damuwa a tare da shi ba”.
Cikin nutsuwa Saddiqa ta tambayeta ya gaya miki daga ina ya kira ki Gwaggo? Da sauri ta ce mata, “A’a, bai gaya min ba, wani abu ya faru ne?” Ta yi tambayar a yanayi na nuna damuwa.
“A’a, Gwaggo babu abin da ya faru, amma shi yana asibiti wai za a yi mishi tiyata”.
Da sauri ta tambaya, “Tiyata? Ba shi da lafiya ne?”
Tana share majina tana maganar, “Lafiyarshi qalau a kan dai maganar nan ne, na yi na yi ya qi ya bari, na kuma ce ya gaya muku wai ba zai faxar muku da gaba ba, bayan haka kuma yana tsoron kar ku hana”.
Shiru Gwaggo ta yi na wani lokaci alamar jikinta ya yi sanyi, a hankali cikin nutsuwa Saddiqa ta jita tana cewa, “To Ubangiji yasa ayi mishi aikin a sa’a”. Ta ce, “Amin”.
Tana ajiye wayar kiran Mus’ab ya shigo.
“Albishirinki Aisha”.
Ta yi maza ta ce mishi, “Goro”.
Yana murna ya ce mata, “Yau hira sosai muka yi ni da Inna da na kira ta”.
Ta ce, “Kai Yaya Mus’ab, wannan ne abin albishir xin, ni ina ce ma za ka ce min an fasa yin tiyatar ne”.
A hankali ya ce, “A’a, Aisha ai likitocin da za suyi aikin ma sun riga sun iso tun xazu, Dr. Usman ya gaya min cewar shi da wasu likitoci uku ne za suyi aikin. Kin san wani abu?”
Ta yi maza ta ce mishi, “A’a, sai ka faxa”.
Ya ce, “To zan shiga tiyatar ne hankalina a kwance bana tsoro ba kuma na fargaba, na kuma yarda cewar duk wani abin da ya faru ko zai faru, to daga Ubangiji ne, na roqe shi ya yafe min zunuban da na yi ta aikatawa waxanda suka zama sanadin da na cutar da lafiyata.
Ke kuma na gode miki Aisha, na zauna dake zama mai daxi, kowane lokaci a cikin tattalina da kyautata min kike, kin yi komai don ki faranta min. Mafi alherin al’amarinki kuma shine, kin zama sanadi na daidaituwar tsakanina da mahaifiyata, in ban fito daga wannan tiya…..”
Ta yi maza ta saki wayar a qasa saboda firgitar da ta yi tare da faxin “Na shiga uku!” Nan take kuma ta soma kuka.
Da qyar ta iya yin shiru saboda rarrashi da kalaman qarfafa gwiwa da su Abida suka yi ta yi mata.
“Gaskiya ba zan iya zaman nan ba gara min kawai muje asibitin”.
Abida ta ba ta haquri. Jimawa can ta sake cewa, “Nifa gara min kawai in tafi don ban ga amfanin zaman da nake yi a nan ba”.
Tasa hannu ta kira layin Mus’ab don ta gaya mishi ya barta kawai ta zo asibitin don ta ganshi. Sani ne ya amsa.
“Hello! Aisha akwai wani abu ne?’
A hankali ta tambaye shi “Yaya fa?”
Ya ce, “Ai tun qarfe takwas da rabi suka shiga dashi, dama shine mutum na biyu a tiyatar da za suyi yau”.
Cikin Saddiqa ya ba da sautin qulululuuu! A lokacin da idanuwanta suka kai kan agogon dake wurin, qarfe goma sha xaya har da kwata, kusan awowi uku kenan da shigarwar da aka yi mishi. Ko a wane hali yake ciki yanzu? Oho! Ta yi maza ta ajiye wayar ta nufi banxaki saboda kaxawar da cikinta ya yi.
Wunin ranar zirga-zirgar da ta yi ta yi kenan. Wajen azahar ta isa asibitin bayan ta riga ta yi sallarta a gida.
A hankali ta tura qofa ta shiga xakin da aka nuna mata cewear shine nashin inda aka bashi, jallabiyar da ya baro gida da ita ne a ajiye a kan gadon.
Ta miqa hannu ta xauka ta ninke ta sanya cikin jakar dake hannunta, ta ajiye jakar a kan gadon ta nufi inda ta hango Sani da Idris a tsaye.
Tana isa wurin ta gane a kusa da xakin tiyata suke tsaye. Su dukansu biyun babu wani annuri a tare dasu, gaba xayansu idanuwansu sunyi zuru-zuru, bakunansu sun bushe.
“Sannu Aisha”.
Idris ne ya yi mata gaisuwar a yanayi na qarfin hali. Ta yi nufin wucewa zuwa inda ta hango qofar da aka rubuta Theater room a jiki, da sauri suka ce mata, “Ai ba a zuwa nan, iyakar wurin tsayuwar kenan inda muke xin nan, ki dawo kawai ki yi haquri ko kuma ki koma can xakin ki samu su Abida in an fito da shi ai nan xin ne dai za a kawo shi”.
Ba ta yi magana ba kuka kawai take ta yi.
Dr. Usman ya zo wucewa tana kallon shi yana magana da su Idris ba ta iya qarawa ta ji abin da suke faxa ba, tana dai kallon fuskokinsu zuciyarta kuma tana raya mata, ta gaji da kallon nasu ta yi qoqarin matsawa kusa dasu don ta ji me yake gaya musu haka wanda bayanin ya qi qarewa.
“Yanzu dai sai mu qara haquri mu haxa da addu’a”.
Qarshen maganar likita da ta ji kenan.
“Me ya faru? Me ake ciki na ji yana cewa ayi haquri?”
Ta yi musu tambayar a firgice saboda ba ta same shi ba ya riga ya wuce. Tun kafin su san me za su ce mata ta fara kuka.
Da sauri Idris ya soma yi mata bayanin “Ba fa wani abu bane mai tsanani al’amari ne da yake faruwa da mutane da yawa, kin san kowa da yanda qarfin jininshi yake, an gama aikin sai dai bai dawo sosai ba ta yanda za su iya fito da shi”.
Yana nan kenan tsakanin akwai da babu. Zuciyarta ta raya mata. Nan take jiri ya xebeta ta tafi za ta faxi, da sauri wata mace dake wucewa ta bayanta tasa hannu ta tare ta, su Abida suka yi maza suka kama ta aka kaita xakin aka kwantar da ita.
“Ki fa kwantar da hankalinki kar kuma shi a fito da shi ke kuma kin samu matsala”.
Kukanta kawai take yi ba ta ko kallon su balle ta amsa.
Awa xaya baya aka fito da Mus’ab. “Gareka nake ya Ubangiji, gareka nake neman taimako”. Abin da yake ta nanatawa kenan.
Gaba xaya ana tsaitsaye a kanshi cikin sauraro.
An fito daga sallar magariba kenan sai ga Kawu Gixe da Abu sun iso asibitin, nan da nan Saddiqa ta xan samu nutsuwa a tare da ita.
“Iko sai mai shi, haka al’amarin yake? To Ubangiji ya ta da kafaxarshi”.
Gaba xaya aka amsa “Amin”.
Kalaman Abu ne wannan bayan ta amsa sannu da zuwa da gaisuwar da aka yi ta yi mata.
“To a nuna min inda zan yi sallah”.
Saddiqa ta wuce za ta nuna mata, ta tarar tuni har Kawu Gixe ya idar. Ta tsuguna a gefe tana gaishe shi.
“Ya ya aka yi aka yi irin wannan aiki haka baku sanar da gida ba?”
Ba ta iya ce mishi komai ba in ban da kukan da take yi, saboda ta riga ta gama tsorata da yanayin da aka fito da shi a ciki.
Har suka bar asibitin ran nan bai wani dawo cikin hayyacinshi ba, ita kam ta so a ce an barta ta kwana a wurinshi Abu ce ta ce gara su tafi wai in sun zauna me za suyi mishi bayan ga likitoci suna ta kaiwa da kawowa, ga kuma Kawu Gixe da Sani suma a nan za su kwana?
Sun dawo gida Saddiqa sai bin Abu da kallo take yi, zuciyarta tana raya mata duk halin da Mus’ab ke ciki hankalinta a kwance yake, da kanta ta xebo abinci ta zauna ta ci ta xora da ‘ya’yan itace, ta yi wanka ta hau gado ta yi kwanciyar ta tana tambayar Saddiqa,. To don kin qi ci kin qi sha sai me? Ina ce duk iya shegenku ne ya jawo hakan? Da kin hanashi ai da bai yi ba.
Saddiqa ta zuba mata ido tana kallon ta cikin matsanancin takaici, ta ma rasa me za ta ce mata.
Dare ya yi nisa sanda ta farka ta duba agogon wayarta uku da rabi ne na dare, ta shafa inda Abu ke kwance ba ta nan, ta tashi ta tura qofar banxaki a hankali don ta gani, nan ma ba ta nan. Ta fito falo ba ta ganta ba.
Har ta zuwa za ta koma xaki sai ta tura qofar xaya xakin, Abu tana ciki a zaune kan sallaryarta hannayenta duka biyu a xage zuwa sama, kuka take yi hawaye sai gudu suke yi a fuskarta.
“Ya Ubangiji, wannan yaro Mus’abu….”
Abin da kawai Saddiqa ta iya ji kenan. A hankali ta mai da qofar ta rufe ta nufi xaki ta je ta kama tata harkar.
Suna idar da sallar asuba suka isa asibitin, har lokacin Mus’ab yana kwance a rigingine kamar yanda suka barshi, bambancin kawai shine a yanzu yana furta kalmomi da wanda ke kusa da shi yake iya ji.
“Cikina, cikina, a san min ruwa in sha”.
Saddiqa ta kalli mahaifinta ta ce, “Baba wai zai sha ruwa”.
Kawu Gixe bai kulata ba sai Sani ne ya yi mata bayani, “Sun ce kar a ba shi komai”.
Tausayin halin da yake ciki yasa Saddiqa ta soma zubar da hawaye. Da sauri Kawu Gixen ya ce mata, “Ke, kar fa ki kawo mana iya shege a nan? Kuka? Ba ki san za a yi hakan bane da kika ingizashi yaje ya yi? Wannan fitina da me ta yi kama? Dole ne sai kowa ya haihu? Waxanda basu haihu ba basa rayuwa ne? Yanzu babu bayin Allah mutanen kirki da su basu haihun ba?”
Abu ta tave baki ta ce, “Uhm! Nima dai abin da na ce mata kenan”.
Sani ya yi maza ya ce, “A’a, Kawu Aisha kuwa babu yanda ba ta yi da shi ba shi ya qi”.
Da sauri Kawu Gixe ya ce, “To me yasa ba ta faxa ba ta ja bakinta ta yi shiru?”
Cikin nutsuwa Sani ya ce, “Kawu ina ganin tuna an riga anyi sai ayi addu’a kawai ayi dace, ita Aisha kam Kawu kowa ya ganta ai ya san ta shiga wani al’amari, tunda ai ko shekaran jiya gidansu ba haka na ganta ba, daga jiya zuwa yau ne fa ta yi wannan zabgewar”.
Kwanan Mus’ab uku kafin ya dawo cikin hayyacinshi sosai ya san abin da yake ciki da waxanda suke tare da shi.
Kowa sai murna yake, yana fara samun sauqi Abu ta yi xib! Ba ta ko kallon inda yake kwance, ko ya yi qarfin hali ya yi mata magana ba ta wani kulawa balle ta amsa.
Saddiqa ta kalle shi ta ce, “To kai ka yi haquri mana ka yi shiru dole ne sai ka kula Abu?”
Abu ta galla musu harara dukansu biyun, ta ce, “To ni don ba a kulani ba sai me? Ni ai bake ba ce ya dena kulani mana. Fitinannun mutane masu neman fitinar tsiya, ana zaune lafiya ku tada mutane a tsaye”.
A hankali ya buxa baki ya ce, “Ki yi haquri Abu, Aisha ba ta da wani laifi nine na hanata gaya muku, in ta bi umarnina kuma ai ba laifi ta yi ba”.
“To amma kai me yasa za ka yiwa kanka irin wannan abin, kai baka san haquri ba?”
Ya xan yi murmushi ya ce, “Zuciyata ce Abu ta qi ta yi min daxi, babu abin da take so irin ta ga Aisha da ciki, ko ganin mace mai juna biyu na yi sai in ji inda a jikin Aisha yake da ya ya zan ganta ta yi?”
Ta kawar da kai tare da tsaki ta wuce ta yi tafiyarta ta barsu su biyu. Ya miqa hannu ya yafito Saddiqa ta matso kusa da shi, a hankali ya buxa baki ya ce mata.
“Ki yi haquri Aisha, mun sha wuya amma kwanan nan in muna raye da yardar Ubangiji buqatarmu za ta biya, zan ganki kema kina tura cikinki kamar yanda nake ganinshi wurin matan mutane”.
Saddiqa ta yi murmushi ta ce, “Amma dai kuwa kafin ayi hakan Yaya ai kuwa dai kam an sha wuya”.
Ya ce, “Eh, amma ai babu komai Aisha, in dai har buqata ta biya to ai kuma duk wata wahala tarihi ce”.
Ta ce, “Haka ne Yaya”.
An sallamo Mus’ab ya dawo gida a dal8ilin sauqin da ya smau. Kawu Gixe da Abu kuma sun koma gida Misau.