ABU NAKA BOOK 3 BY SODANGI
SHEKARU GOMA BAYAN NAN
Mus’ab mai shekaru hamsin da huxu a duniya, yana zaune a hamshaqin gidanshi dake unguwar G.R.A kan titin T/Valewa a cikin garin Bauchi.
Mus’ab ya ajiye aikinshi ya dawo gida shekaru biyu da suka wuce, ya kuma zavi zama kusa da Kawu Gixe, don haka ya gina wani tafkeken gidan a Bauchi.
Ya yi hakan ne kuma don cika burin da yake da shi na ganin ya sadaukar da abin da ya saura na rayuwar wajen ganin ya bayar da ingantacciyar tarbiya ga yaran da ya haifa, a ganin Mus’ab tarbiya wata aba ce dake buqatar lokaci, haquri, juriya, tausayi, kulawa da kuma soyayya. Haka nan aiki ne da ya hau kan iyaye duka biyu, wato uwa da uba.
Yana zaune cikin hamshaqin falonshi da duk wani abin da ke ciki daga qasar Italy ya shigo da shi, tare da ‘ya’yanshi guda uku, Maryam, Abdullahi da Muhammadu Gixaxo takwaran Kawu Gixe.
Gaba xaya litattafansu suke nuna mishi lokacin da Saddiqa ta shigo cikin falon sanye da doguwar riga xinkin senegal a jikinta, ta yi kyau sai sheqi take yi, ta nemi wuri ta zauna sannan ta kalli yaran ta ce musu.
“Maza ku tashi ku tafi ga Malamin ku ya zo”.
‘Yan samarin biyu suka yi waje da gudu suna rige-rige, ya yin da ‘yar budurwar ta qara lanqwashewa jikin mahaifinta tana tambayarshi.
“Baba ina ce nice mamanka?”
Ya yi maza ya amsa mata tare da zuba idanuwanshi a gareta, “Ke ce mamana Mama”.
Saddiqa ta sake kallon yarinyar wacce ta yi kamar ba ta jita ba, ta ce mata, “Kema tashi ki bisu”.
Ta miqe tsaye ba don tana so ba sai don bin umarni, ta kama hanyar fita daga falon. Mus’ab ya bita da kallo har sai da ta vace mishi daga gani.
Maryam ita ce yarinyar da Mus’ab ya xauki son duniya ya xora mata saboda dalilai masu yawa, farko samunta da ya yi bayan ya xebe tsammani, na biyu takwarar Innarshi ce matar Kawu Gixe wacce take mahaifiyar Saddiqa. Na uku tsananin kamanninta da mahaifiyarshi Gwaggo Habiba, ko cikin ‘ya’yan da Gwaggon ta haifa ba a samu mai kama da ita haka ba. Sai na huxu basirarta, yarinya ce mai kaifin basira, duk shagwavarta da sakarcinta sau xaya tak malami yake faxar abu ta kama.
Ya dawo da kallon shi ga Saddiqa cikin nutsuwa ya ce mata, “Kin korar mun uwata ba ki kyauta ba bayan ina jin xuminta”.
Ta matso kusa da shi cikin shagwava ta langave a jikinshi ta ce, “Tausa nake so Yaya jikina ciwo yake yi min, Yaya ga shi kuma kasala ta dame ni”.
Hanni biyu ya saka ya rungumo ta a qirjinshi, ya sake miqa hannunshi na dama ya tallabo qasan mararta cikin tausayawa da kulawa yake ce mata, “Haquri kawai za ki yi Aisha, ina ganin matsalolin nan naki suna samuwa ne a dalilin za ki sake samo min wata Innar tawa”.
Saddiqa ta yi murmushi cikin shagwava ta ce, “Haba Yaya, ka rinqa samun Innar kenan? Ai gara nima ka yi min kara ka sanya min sunan Gwaggona”.
Ya kalle ta cikin nutsuwar dake qara bayyanar da gaskiyar abin da yake faxi, ya ce mata, “Aisha ke a gareni tamkar wata tauraruwa ce da kusurwowi biyar ke gareta, kusurwar farko tana bayyana matsayinta, kusurwa ta biyu tana bayyana tausayinta, kusurwa ta uku tana bayyana gargaxinta, kusurwa ta huxu ita ke bayyana soyayyarta. Sai ta cikon biyar xin ita ce mai bayyanar da abotarta. Aisha gabana kan faxi in ji tamkar zan razana in na tuna a baya kin tava qina, sai in ce to da za ki sake yin hakan a yanzu a wane hali zan samu kaina?”
Saddiqa ta yi murmushin farin ciki saboda gamsuwar da ta yi da matsayinta wurin mijinta. Ta ce, “Ai a wannan lokacin ina cikin wauta ne Yaya, ban san mene ne so ba, ban fahimci yanda soyayya take ba, ban gane soyayya ta asali ba. Zamana da kai ne ya fahaimtar dani na gane soyayya ta asali, babu ganin girman laifi a cikinta sai yanda za a yi a yafe, babu maganar sauraro a cikinta sai fahimta, babu rabuwa sai yanda za a yi a zauna tare har abada. Ni taka ce Yaya Mus’ab, Innarka ce ta haifar maka ni, dama don kai ta haife ni kar gabanka ya sake faxuwa a kaina, na kuma gode maka da ka yarda ka zaveni na zama nice tauraruwar zuciyarka”.
Sai anjima.
Mu sadu a wani littafin cikin yardar Ubangiji.
Taku.
Hafsat Chindo Sodangi.
Alura:
Sabon littafin MATA DA KICIN XINSU littafi na biyu yana nan fitowa ba da daxewa ba, a neme shi don samun qaruwa har da abincin masu lalurori.