ABU NAKA BOOK 3 BY SODANGI
GARIN MISAU A RANAR ALHAMIS DA YAMMA
Gwaggo Habiba tana cikin kicin xinta tana qoqarin dama kunun tsamiyar da za suyi buxa bakin azumin nafilan da suke ita da mijinta.
Tsayuwar motar da ta ji ‘jiiyim’ kusa da qofar shigowa zauren gidan yasa ta fitowa da sauri ta zo ta tsaya a tsakar gidan tana kallon hanyar shigowa gidan, cikin zuciyarta tana faxin wannan motar dai da qyar in ba Inna ta kawo ba.
“Assalamu alaikum”.
Muryar Abu cikin fara’a da murmushi ta shigo gidan tamkar ba ta wahala a tafiyar tata ba.
“Lah! Ashe kuwa ke ce Inna, Inna sannu da zuwa, dama tunda na ji tsayuwaar motar dama na ce wataqila kece a ciki, sannu da zuwa, Inna kun shawo hanya”.
Suka nufi xakinta tana shimfixa mata tabarma tana faxin “Tun shekaran jiya muke sa rai dake a gidan nan”.
Abu ta yi murmushi irin wanda ta daxe ba ta yi ba.
“Gidan Mus’abu fa na je a yau xin ma da ya ya na baro shi? Duka yaron nan ki gani in ya gama shigo da kayan tsarabar nan ki samu abin da kika ba shi ya ci, duk da dai ba yunwa muke ji ba”.
Gwaggo Habiba ta yi murmushin jin daxin yanayin da ta ga mahaifiyarta a ciki, ta nufi wajen direban tana faxin “Wannan doguwar tafiyar da kuka yiwo Inna ki ce bakwa tare da yunwa”.
“A’a, baya fa ba ta kaxan, kar dai a ce xan fitar nan da na yi ne Inna ta dawo a bayana?”
Abu ta yi maza ta ce mishi, “Ai kuwa dai nice malama, hala tarin tsarabar da ka gani a tsakar gidanka ne yasa ka gane hakan?”
Ya ce mata, “Eh”.
Ta yi murmushi ta ce, “Aikin Mus’abu kenan”.
Da daddare bayan sallar isha’i Gwaggo Habiba da Abu suna falonta, sun gaisa sun ci abinci suna hira. Ta qosa qwarai Abun ta ba ta labarin yanda ta baro Saddiqa, ita kuma sai ja mata rai take yi.
Malam Abdullahi ya shigo falon ya same su a dalilin ya dawo daga sallar isha’i.
“Gwaggo sai yau?”
Ta yi dariya ta ce, “To yau xin ma da ya ya? Ai dagewa kawai na yi na ce in dai ba tayaku zaman auren naku zan yi ba, ai gara ku barni nima in koma wurin iyalina”.
Malam Abdullahi ya yi dariya, ita kam Gwaggo Habiba sai murmushi take yi, ya yin da kanta ke sunkuye.
“To ya ya kika baro su Gwaggo?”
Ta yi maza ta ce, “Sai alheri, ga tsaraba can ya ce a kawo a rabawa ‘yan’uwa da maqwabta, in kuma gaya maka cewar kai da Kawunshi ku yi shirin tafiya aikin Hajji, ni kuma ni da uwarsu zamu je Umara na ce mishi a’a, ni kam Hajji zan ce don ban sauke farali ba, ga kuma girma ya riga ya kama ni, gara in je tun ban kai ga ba zan iya ba. Ya ce, to sai yanda muka shawarta”.
Cikin farin ciki Malam Abdullahi ya ce, “Eh to, Gwaggo ai sai ku je Hajjin ke da Yaya Gixe mu sai mu tafi Umarar da Habiba”.
Abu ta ce, “A’a, ni da kai dai mu yi Hajji, ita da xan’uwanta suyi Umarar, ai tafiyar da kai za ta fi min dai-dai”.
Malam Abdullahi ya ce, “To, Ubangiji ya yi musu albarka”.
Abu ta yi ta faxin “Amin-amin”. Har ya tashi ya fita saboda sallamar da aka yi da shi.
Gwaggo Habiba dake zaune shiru a gefe ta xago ta sake tambayar ta, “To ya ya kuwa Saddiqa Inna?”
Abu ta kalle ta cikin murmushi ta ce, “Duk wannan labari da nake bayarwa bai isheki ba sai kin ji na Saddiqa ita kaxai? To lafiyarta qalau na barota tana ta hidimar aurenta, ta ce a gaisheki, ga kuma saqo ta ce in kawo miki”.
Cikin sauri Gwaggo Habiba tasa hannu ta karva tana warwarewa ta ga abin da ke jikin zanin gadon ta yi maza ta rufe tana salati, cikin sanyin jiki ta kalli Abu.
“Irin wannan cin zarafin ya yi mata Inna? Wannan ai rashin tausayi ne”.
Abu ta galla mata harara.
“Ke kam ai ba za ki yaba mishi ba, ina can ne fa abin ya faru amma baki kalli haqurin da ya yi da ita ba, kin kuma san a kan ‘yarki ne maza suka fara yin haka. Ya dai ce in gaishe ki in kuma roqa mishi ke ki yafe mishi abubuwan da ya yi miki”.
Ta miqe tana tafiya tana yafa zanin rufar ta.
“Ni gidana za ni in kwana, in yara sun shigo ki xora musu kayana su biyoni da shi”.
Gwaggo Habiba ta bi bayanta tana faxin, “Ki huta gajiya Inna, sai na zo miki ban gajiya”.
AJAKUTA
Mus’ab yana zaune a qofar gidanshi cikin shirin yin alwalar sallar magariba, ya kalli agogon hannunshi bayan ya kalli yanayin sama, zuciyarshi ta raya mishi da sauran lokaci.
Nan take ta sake raya mishi yanzu kam cikin yardar Ubangiji in har komai ya tafi daidai kamar yanda ake fata, to Abu ta isa gida tana can tana bai wa su Inna labarin Aisha ta kai budurcinta, ya san babu wani labari da zai fi wannan daxin bayarwa a wurin Abu.
Ya xan yi shiru kaxan cikin wani tunanin, zuciyar tashi ce dai take sake tuna mishi da irin wunin da ya yi tare da Saddiqa bayan tafiyar Abu a ranar cikin kuka da takura mai yawa, wanda ya yi dalilin da ko aiki bai samu damar zuwa ba.
Son shi ne ba ta yi yasa take waxannan abubuwan ko kuwa? Ya yi maza ya kawar da wannan tunanin saboda dalilai guda biyu. Na farko mu’amalarshi da ita a farko, yanda ta bijirewa auren Sadisu ta nemi a barta kawai ta yi mata yanda ita da kanta ta gayawa Gwaggonta ita xin shi take so, da yanda ita da kanta ba tare da ya nemi ta yi mishi hakan ba ta voyewa Abu halin da suke ciki a lokacin da ta zo gidan.
Waxannan dalilai guda biyu sune suka qarfafa zuciyarshi ya xan ji sanyi, ya kuma qarfafa zuciyar tashi a kan himmatuwa wajen ganin ya shawo kan lamarin nashi.
Hadari ya taso tare da iska mai tsanani, wanda ya yi dalilin da liman ya bayar da umarnin haxa jam’in magariba da isha’i a masallacin.
Ya shigo gida daidai ruwan saman yana saukowa, zuciyarshi ta yi mishi daxi saboda sanin da ya yi Saddiqa matsoraciya ce. Wurinta ya fara isa bayan ya gama rurrufe qofofin gidan.
“Kin yi sallah kuwa?”
Ta amsa mishi da eh. Ya wuce ta yana tunanin irin takurar da ya ga ta yi, ina ma dai NEPA su xauke wutar lantarkin. Yana yin wannan tunanin ya miqa hannu kan mitar gidan ya kashe wutar, duu ya bayyana a ko’ina. Ya wuce ya nufi wurinshi.
Bai daxe da shiga wurin nashi ba ya ji motsin Saddiqa a cikin falon nashi.
“Waye aa nan?”
Ya yi tambayar don ya gane maganar ne ba ta son yi. A hankali ta ce mishi, “Nice”.
“Kina son wani abu ne?”
Ta xan yi shiru kafin ta daure ta ce mishi, “Wuta aka xauke ni kuma bana son duhu “.
Cikin nutsuwa ya ce mata, “Eh, Aisha duhu ai ba shi da daxi”.
“Ko za ka sa a kunna Jean?”
Ya ce, “To, sai dai ruwan ya yi yawa bai kamata in fitar da shi a cikin ruwan ba, saboda kuna Jean ai kinga babba ne mu xan bari mu gani ko ruwan zai yi sauqi”.
Ta yi shiru.
“Ko kina tsoro ne?”
Ta ce mishi, “Eh”.
Ya yi kamar ya ce ta shigo wurinshi sai ya fasa, ya fito ya zo inda take ya kama hannunta ya ce, “Muje in rakaki wurinki”.
Da hikima da lallami ta yarda suka hau gadonta tare suka kwanta, shima kuma ya yi haquri ya kawar da kai daga gareta, don ya fi son shiryawarsu maimakon kara tsoratata. Sai da aka kira sallar asuba ya miqe zai yi alwala ya mai da wutar gidan.
Har wajen qarfe taran safiya ba ta sake ganin ya shigo wurinta ba, ba ta ga yana shirin tafiya aiki ba. Kalmomin Abu suka faxo mata, kullum ki gaishe shi, kullum ki yi mishi abinci mai daxi, kullum ki gyara mishi shimfixa.
Don haka ta miqe ta nufi wurin nashi da nufin zuwa ta gaishe shi. A hankali ta tura qofar xakinshi tare da yin sallama, saboda ganin ba ta ganshi a falon ba.
Ya amsa yana daga kwance a gadonshi, ta kai gwiwowinta qasa a yanayin girmamawa ta ce mishi, “Ina kwana Yaya?” Ya amsa “Lafiya lau Aisha, ya ya gidan ya kwana?”
Ta ce mishi, “Lafiya, me kake so ayi maka na abin karyawa?”
A hankali ya ce mata, “Huta kawai Aisha”.
Ta xan kalle shi ta ce, “Ba ka da lafiya ne?”
Ya zuba mata ido yana kallon ta tare da tambayar ta, “Me kika gani?”
Cikin nutsuwa ta ce, “Na ganka a kwance bayan yau xin akwai aiki, kuma na ce me kake so in yi maka ka ce in huta”.
Bai kawar da kanshi daga gare ta ba ya ce mata, “Bana cikin yanayin da zan ji daxin zuwa aikin yau, saboda na xan takura, in kuma abin da nake so za ki yi min ki zo kusa dani mana ki rage min damuwa ta”.
Ta xan yi shiru kanta a sunkuye, a hankali sai ya ce mata, “Sai na ji kamar Abu ta yi ta yi miki magana a kan kar ki yi wasa da auren ki, na xauka ni da ke zamu yiwa nasihohin da ta yi mana biyayya Aisha”.
Ba ta kalle shi ba balle ta yi mishi wata magana, sai dai hawayenta da suka soma zuba. Ya shure abin rufar nashi ya zo ya kama hannunta ya shigar da ita xakin.
“Zo muje ki gaya min abin da ke saki yawan kuka. Nisa da gida da kika yi? Kina son ganin Gwaggonki ko?”
Ta yi maza ta gyaxa kai nuna alamar, “Eh”.
Yasa hannu ya share mata hawayen.
“Ai na sani, na san kina ganin Gwaggonki nima kuma ba zan hanaki ko in qi kai ki wurinta ki ganta ba, illa iyaka dai kawai zan bari sai kin kwantar da hankalinki mun zauna lafiya tukunna, ko yau xin nan kika yarda muka fara zama lafiya, to ni kuma a shirye nake mu daidaita lokacin da zan kai ki ga Gwaggon naki”.
Da irin waxannan kalaman na dabara ne da yawan nuna na fiki daxewa a duniya Mus’ab ya samu ya shawo kanta cikin ruwan sanyi, ta yarda ta miqa mishi al’amarinta ya samu ya yi yanda yake so da ita, ta kuma jurewa hakan.
Wunin ran nan ko qofar gidanshi bai buxe ba sai da ya yi nufin tafiya sallar juma’a, ana idarwa kuma ya dawo gida. Haka washe gari asabar da kuma lahadi yana gida yana hutawarshi.
“To Yaya yaushe zamu je wajen Gwaggo?”
Sai ya yi maza ya soma lissafi.
“To bari ko kwana talatin da tafiya Abu ta yi don kar a ganmu yanzu ayi zaton ko babu lafiya”.
Ta ce mishi, “To”.
Kwanaki talatin xin suna cika ya xauke ta ya nufi qasar Italy in da ya je ya yi hutun aikinshi na kusan watanni biyu, tafiyarshi ta farko tun bayan dawowarshi daga can inda yaje ya sadu da aminai, abokai da kuma tsofaffin malamanshi da aminanshi.
A lokacin da suka dawo gida kuwa tunanin Saddiqa da tattalinta bai wuce na me za ta yi ko ya ya za ta yi ta kyautatawa mijinta ba.
Watanni biyar sun cika bayan kawo Saddiqa da Abu ta yi har lokacin bai ce ga ranar zuwa gida ba, tamkar ya mance alqawarin da ya yiwa Abu na ba zai bari ta rinqa jin marmarinshi ba ta ganshi ba.
Ita ma Saddiqa mafi yawancin lokaci ta kan tuna Gwaggon nata ne, ta ce kai Yaya yaushe ne za ka samu lokacin da zamu je gida ne? Ina fa marmarin ganin Gwaggona”.
Ya yi tsaki ya ce, “Ai ayyuka ne bari dai mu gani daga nan zuwa qarshen watan nan. In ta ce to. To sai kuma wani jiqon in ta sake tunawa. Daga shi har ita sun zama tamkar basu ba, ko Liman da Mus’ab xin ya tasata a gaba ya kaita gaishe shi mamakin ganinta ya yi, ya cewa, Mus’ab xin yi qoqari ka kai wa iyayenku ita su ganta don su sanya maka albarka. Ya ce, “To malam”.
Suna zaune a falonshi suna hira, sun gama karyawa Mus’ab ya kalle ta ya ce, “Ki gama aikinki da wuri ki shirya in anyi sallar magariba zamu je mu ga Dr. Usman”.
To kawai ta ce saboda ya yi maganar ya fi a qirga, yau xin dai ya zartar da hukuncin tafiyar ne kawai.
Da daddare Mus’ab da Saddiqa suna zaune gaban likita, Mus’ab ya gama yi mishi bayanin abin da ke tafe dasu. Gwaje-gwaje sosai ya yi musu, ya kuma umarcesu dasu kawo mishi wasu abubuwa na jikinsu.
Bayan sunyi hakan ne ya xibar musu kwanaki uku ya ce su dawo don su ji sakamakon gwajin nasu.
Sun dawo suna zaune gaban likitan wanda yake kallon takardun dake gabanshi cikin nazari kafin ya xan xago ya kalli Saddiqa ya ce mata, “Ko za ki xan jiramu a waje?”
Mus’ab ya harzuqa da jin maganar tashi ya ce, “Matata ce fa, me za ka gaya min da ba za a faxa a gabanta ba?”
Saddiqa ta miqe tsaye ta ce, “Babu komai Yay bari in je in jiraka a mota, in ka gama kawai sai ka sameni a can mu tafi”.
Ya bita da kallo har sai da ta fita ta ja musu qofar kafin ya dawo da kallon shi wurin likita.
“Me kake so ka gaya min likita wanda yasa ka korar min mata?”
Likita ya ya kalle shi cikin nutsuwa ya ce, “Ba korarta na yi ba, bana yi maka sha’awar tashin hankali ne da ita, na san a yanda ka renita ta zama haka ba za ka so komai tsakaninka da ita ba illa zaman lafiya da kwanciyar hankali”.
Gaban Mus’ab ya yi mummunan faxuwa, cikin sanyin jiki ya tambaye shi “Me ya faru likita?” Ya tsare shi da ido yana kallon shi tare da sauraron abin da zai gaya mishi.
“Barasa da sigari sun riga sun yiwa kayan cikinka lahani, haka nan ka daxe kana xauke da ciwon sanyi da ake samu wurin matan da basu tsaya wuri xaya ba, saboda baka kula ka xauki matakin da ya dace a kanta ba har ta yi maka illa, ka kuma san ita wannan cutar tana cikin cututtukan dake hana maza haihuwa, don tana toshe jijiyar dake fitar da qwai zuwa mahaifar mace.
To ga kuma wancan matsalar da na ce maka barasa da sigari sunyi maka, ban da wannan ita ma matarka mun same ta da ciwon, sai dai bai riga ya yi mata qarfi sosai ba, na kuma san zai yiwu a wurin ka ta samu”.
Mus’ab ya ji tamkar a sama yake saboda tashin hankali, gaba xaya kunnuwanshi suka daina jin komai in ban da kalaman da likita ya furta mishi sune kawai suke ta nanata kansu.
“Ka yi haquri Mus’ab kar ka xauki abin da tsanani sosai, akwai magungunan da zamu baka in ba suyi ba mu canza wasu, kai dai kar ka bari matarka ta san abin da kake ciki ba wani tabbas ne dasu ba. Kar ka kalli wannan xawainiyar da ka yi a kanta ka mai da ita matar zamani ta bijire maka ba komai bane, musamman ma da yake abin ya shafi haihuwa.
Don haka in ta matsa tana so ta san abin da ake ciki ni zan iya ba da result xin da zai nuna matsalar a wurinta yake, don dai ka samu zaman lafiya a gidanka. A nan asibiti kuma ba za ta samu mai gaya mata komai ba”.
Mus’ab ya miqe tsaye tare da faxin “Na gode likita”. Ya fita ba tare da ya saurari rakiyar da likitan yake yi mishi ba.
Saddiqa tana zaune a qasa gaban Mus’ab, kuka take yi. Ya buxe ido a hankali cikin nutsuwa ya ce mata, “Yanzu nan baki yarda da abin da na gaya miki ba cewar ni lafiyata qalau bani da wata damuwa ba”.
“Ya ya zan yi in yarda bayan ba haka na saba ganinka ba, ni idan na yi maka laifi ne baka son gaya min to ka yafe min”.
Ya miqe zaune a kan kujerar ya ce,”Haba Aisha, ni kuwa a rayuwata me za ki yi min ya vata min rai?”
“To mene ne? Tun daga ranar da muka je asibiti gaba xaya ka canza ka sauya, ka zama wani irin, in bani na yi maka laifi ba waye?”
“To bari mu yi sallah kin ji ana kira, jeki ki yi alwala ki yi taki sallar kafin in dawo daga masallaci”.
Bai jira amsarta ba ya miqe ya fita, bai dawo gidan ba ko da aka yi sallar ya yi zamanshi a waje yana hira tare da jama’ar unguwa.
Saddiqa tana kwance a xakinta saboda ta dena zuwa xakin Mus’ab, shi da kanshi ne kuma ya nuna mata bai son zuwan nata, don haka ta yi qoqari ta kame kanta.
Me ya samu Yaya Mus’ab? Ta yiwa kanta tambayar. Tsawon lokaci tana tunani wani abu ne ya same shi bai son gaya mata, ko kuwa dai haka kawai yake fito mata da waxannan halayen da ba ta tava sanin yana dasu ba.
Ta yankewa kanta shawarar zuwa ta same shi ko barci yake yi ta tashe shi in yaso su yita ta qare, ta gaji da kauce-kaucen da yake yi mata.
Ta jawo zaninta ta xaura kan rigar baccin dake jikinta ta nufi xakin nashi, tun daga falonshi ta soma shaqo warin sigari, gabanta ya faxi, kar dai Yaya Mus’ab ke shan sigari a wannan tsohon daren?
Ta kutsa ta shiga cikin xakin nashi ba tare da ta yi mishi sallama ba, yana zaune a bakin gadonshi da karan sigarinshi a hannu, gefe guda kuma kwalbar barasarshi ce ‘whisky’.
Saddiqa ta zube gabanshi cikin kuka mai tsanani, nan take ya sureta da sauri ya yi waje da ita ya nufi falonta ya shimfixeta a kan doguwar kujerarta.
“Ba na ce ki dena zuwa wurina ba ki gaya min ba?”
Ta ba tanka mishi ba kukanta kawai take yi, ba ta dena ba har ya bar wurin ta ya koma nashi, saboda zai yi shirin sallar asuba.
Kafin ya dawo har ta gama yin shirinta, yana shigowa ya kalle ta cikin nutsuwa ya tambaye ta, “Wannan jakar fa?”
Ba ta kalle shi ba ta ce mishi “Gida zan tafi”.
“Gida ina?”
Ya yi tambayar cikin wani irin yanayi.
Ta ce, “Misau”.
“Na yi miki wani abu ne?”
Ta ce, “A’a”.
“Ban miki komai ba amma kike so ki tafi ki barni, don kin ganni a cikin damuwa kina so ki qara min ita?”
Ba ta kalle shi ba ta ce, “Ai ban santa ba balle ka ce ita ce za ta koreni”.
“Ko baki santa ba ai kin san ina da ita”.
Ta yi maza ta ce, “Kai kaxai ta shafa bana kuma so in jita”.
Ta miqa hannu ta soma jan jakarta za ta fita ya yi maza ya kamo ta ya riqe.
“Kar ki tafi ki barni Aisha, in kin barni da wa kike so in zauna?”
Ta ce, “Da halayenka”.
Ya qi sakinta.
“Me na yi miki Aisha kike nema ki qara min damuwa bayan wacce nake ciki, ban son ganinki cikin tashin hankali ne yasa ban gaya miki ita ba, Aisha ba wai ina voye miki ita bane, ki yi haquri ban gaya miki ita bane saboda ni na jawo komai sai nake ganin ya kamata ne ni kaxai in yi ta damuwar ba in watsa ta zama damuwar kowa da kowa ba.
Duk da hakan kuma ban samu kwanciyar hankali ba saboda na riga na cuci kaina na kuma cuce ki ta hanyar sanya miki cutar da baki san hawa ba baki san sauka ba, ko Innata bana jin za ta yafe min abin da na yi mata, tunda dai ke ce ‘yarta guda xaya da ta bari a duniya”.
“Kai Yaya Mus’ab wacce irin magana kake yi haka?”
“Na cuci rayuwata Aisha, na cuci rayuwata, na cuci rayuwata”.
Saddiqa ta soma kuka sosai saboda kalaman nashi. A hankali cikin nutsuwa ta gama sauraron bayanin da yake yi mata.
“Shine dalilin da yasa ka koma shaye-shayenka ka sha barasa ka sha sigari? Wato duuk ma abin da zai faru ya faru? Wacce irin rayuwa ce wannan? Yanzu ko abinci me daxi ne aka ce ya cutar da lafiyarka ba za ka fita hanyarshi ba balle savo?
Ka yi savo an jarrabeka sai kuma ka ce to tuban da ka yi ma ka fasa? Wataqila har neman matan ma ka koma”.
Ya yi maza ya ce, “A’a, Aisha ai ba zan yi miki qarya ba, ban tava kowa ba, ai kema na haqura dake balle wasu can qazamai. Ki ji tausayina kar ki tafi ki barni ki yi min alqawari kuma za ki taimakeni ki rufa min asiri a kan abin da nake ciki, ki yafe min ciwon da na sanya miki”.
Ba ta kalle shi ba ta ce mishi, “Ni ba kai ka sanya min ciwo ba rayuwata ta san qaddara tana kuma shirye da karvar ta a kowanne lokaci, kuma cikin godiyar Ubangiji”.
Tausayin Mus’ab ya kama ta, ta saki jaka ta shiga kicin don shirya mishi abin karyawa. Sai lokacin ne ta lura da irin ramar da ya yi, lokacin ne kuma ta tuna rabon da ta ganshi ya zauna yana karyawa ko yiwa kanshi wani abin da ya dace.
“Kin barni ina ci ni kaxai ko baki huce bane?”
A hankali ta ce mishi, “Ni bana fushi da kai, ina dai Azumi ne kawai, anjima dai ina so mu koma wurin likitan”.
Da sauri ya kalle ta ya ce, “Me zai mana Aisha? Ya ce ba zan haihuwa ba”.
Ta ce, “To sai kuma a zauna da cuta? Haihuwa ma ai ba shine mai ba da ita ba, ba kuma a wurinshi muke neman ta ba. Ciwon da ya ce muna da shi shine zamu koma wurin shi ya bamu magani”.
Ya ce mata, “To Aisha”.
Mus’ab da Saddiqa suna zaune gaban likita.
“Ta san komai likita na riga na yi mata bayani na gaskiya, yanzu abin yi kawai za ka gaya mana”.
Likita ya gyara zama ya ce, “To magani ne za a baku kai da ita ka san na gaya maka cewar ita cutar cuta ce mai wuyar war…….”
Saddiqa ta katse shi da cewa, “Likita bamu magani kar ka yi bayani, ai ka riga ka yi mishi ya ji ya kuma yarda”.
Ya kalle ta ya ce, “Haka ne, to babu damuwa”.
Ya miqe yaje ya haxo magungunan ya kawo ya shiga yi musu bayani.
“Wannan za ta rinqa sha ne da safe da daddare na tsawon watanni huxu, kar ta yi fashi. Wannan kuma na cusawa ne za ta rinqa sanya shi a gabanta sati-sati har na tsawon sati shida. In ta gama sai ta dawo mu sake yin wani gwajin don mu san halin da take ciki”.
Ya ce, “To”. Ya kwashe su ya miqawa Saddiqa ta zuba a jakarta. Ya sake juyawa wurin likita yana jin bayaninshi.
“Za ka sha magani da safe da daddare tsawon shekara guda kafin mu sake yi maka gwaji don mu ga yanda qarfin ciwon yake”.
Ya ce, “To”.
“Ga wannan na wata guda ne, a haka za ka rinqa karvarshi wata-wata don ba zai yiwu cewa ka je ka ajiye a gida ba”.
Ya sake cewa, “To”.
Ya sake kwashe su ya sake miqa mata, ita ma ta sake xiba ta sake zubawa a jakarta, suka dawo gida.
Saddiqa tana kwance jikin Mus’ab cikin yanayin kwalliyar da ya fi son ganinta a ciki, ga qamshinta a tare da ita.
“Ban qi kowane lokaci ina jikinki ba Aisha, amma in na tuna wai ta hakan ne na sanya miki ciwo sai in ji na haqura”.
Ba ta kalle shi ba ta ce mishi, “Wannan kuma ruwanka, kai ka zavarwa kanka hakan ba ni ba, balle ko ka ce na takura maka. Kuma ma ni daga yanzu kar ka sake yi min wannan maganar tunda muna shan magani maganar ta qare a wurina na barwa Ubangijina”.
Ya ce, “Haka ne Aisha”.
Shekara guda da auren Saddiqa da Mus’ab, tana kwance a xakinta bayan ta karanta katin murnar cikarta shekara guda da zuwanta Ajakuta, wanda Mus’ab xin ya aiko mata da shi, zuciyarta ta shiga tunanin Gwaggonta da daxewar da ta yi ba ta je gabanta ba. Anya na yiwa Gwaggo adalci kuwa?
Tana cikin tunanin Mus’ab ya shigo xakin cikin yanayin da ta san akwai abin da ya yi dalilin dawowar nashi, cikin murmushi yake rage kayan jikinshi yana cewa, “Dawowa na yi ki bani goron cika shekara guda da zama ango”.
Ta kawar da fuska ta ce, “In don wannan ne ai babu wani goron da za ka samu, sai dai ko hukunci. Tunda shekara guda kenan rabon da in ga Gwaggona, tunda na zo kuma baka tava kai mata ni ba ko sau xaya don ta ganni”.
Ya iso gareta yana faxin, “Bari dai yau kam ina ganin ya kamata in tsaya muyi maganar zuwa wurin Gwgagon nan”.
Tsawon lokaci yana jikinta yana yin yanda yaso, har sai da ya kai ga samun yanda yake so ya huta ya koma cikin nutsuwarshi, zai soma yi mata wata hirar sai ta ce mishi, “To, Yaya ai ka ce yau kam za ka zauna mu yi maganar zuwa wurin Gwaggon”.
Yana jin haka ya yi maza ya rage fara’ar dake tare da shi.
“Kin fa matsa min a kan maganar nan, babu halin ki ganni ina hutawa sai kin kawo min maganar zuwa Misau, da wani wanda bai san zaman aure bane? Ina ce kwanan nan Bilkisu da Hamida suka tafi?”
Ba ta kalle shi ba ta ce, “To ai shi kenan zan daina damunka, amma dai in ka dawo gida baka sameni ba kar ka ce ranka zai vaci, don na gaji ina so in je in ga uwata, zuwansu Anti ai ba zuwanta bane”.
Jin haka da ta ce yasa ya shigar da maganar wasa.
“Kina so in xaure muku hanya kenan direban ya rasa inda zai bi”.
Ya sake jawota ya maqale yana faxin, “To ke aikin aure da haqquwan cikinshi wasa ne da za ki ce don kin shekara baki je gida ba sai ki tafi ba da izinin mijinki ba, bari daga nan zuwa gobe zan ga abin da zan iya yi a kai”.
Ta ce mishi, “To”.
Washe gari suna karyawa Saddiqa ta ce, “Yauwa, Yaya Mus’ab ka ce zamu yi maganar tafiya Misau yau”.
Ya ce, “Kai ni Mus’ab”. Ya sauke cokalin dake hannunshi ya ajiye ya kalli Saddiqa ya ce, “Na ga dai alamar in ban yi maganar tafiya Misau xin nan ba za ayi min tawayen da zai hanani shan ruwan da zai tsriga min a gidan nan. Faxi yaushe kike so mu tafi”.
Ta yi murmushi ta ce, “Ko gobe”.
Ya xan motsa kafaxarshi ya ce, “In kinga za ki tafi ba tare da kin tsaya yi musu tsaraba ba sai mu tafi tunda Juma’a ne mu dawo lahadi, amma ni ina ganin me zai hana ki qara yin haquri kaxan tunda zan fara hutuna na qarshen shekara a qarshen wannan watan, in ma bamu yi hutun duka a can ba sai muyi ko da wata guda ne”.
Ta ce, “To, Ubangiji yasa mu gani”.
Ya ce mata, “Amin”.
Tun daga ranar Saddiqa ta kasance cikin shirin tafiya, kullum da irin lissafin da za ta baiwa Mus’ab, Yaya yi haquri na sake tunawa da gida, kaza da kza ta sake ba da wani sabon lissafin, ko na mance da saka gidan su wance su wance ba a lissafin.
Ana gobe za su tafi Mus’ab ya dawo gida bai samu Saddiqa ba, al’amarin ya yi matuqar ba shi mamaki, don kuwa hakan bai tava faruwa ba.
Ya fito waje ya tsaya don ganin ta inda za ta vullo. Kusan minti talatin da tsayuwa kafin ya hango shigowar motar da ta fita a ciki. Tana shigowa ya juya ya shiga cikin falonshi ya ja ya tsaya yana jiran isowarta.
Fusrkarshi a xaure ya tambaye ta, “Ina kika je?”
Ta tsaya tana kallonshi cikin murmushi.
“Haba Yaya, babu ko sannu da zuwa?”
“An qi ayi miki sannu da zuwa, na aike ki ne? Ko kuwa don kina gadarar za ki yi tafiya sai ya zama kowane lokaci za ki rinqa zarar mota kina fita? Kuma ta kai ma har ba za ki gaya min ba ma sai kawai in zo in tarar bakya nan? Ki bari raina ya vaci da tafiyar ki gani in ban hanata ba gaba xaya in ce na fasa in ga qaryar zumuxi”.
Idanuwanta suka cicciko karo na farko da ta ga irin wannan vacin ran a tare da Mus’ab, ta sunkuyar da kanta qasa cikin rawar murya ta ce mishi, “Ka yi haquri magungunan da kake sha na je sayowa don na duba na ga ba za su kai mu dawo ba, sai na ji tsoron kar su qare a inda bamu san inda zamu same su ba, na kuma ta yi maka waya in gaya maka baka xauka ba”.
Ta kasa danne kukan nata, don haka ta yi maza ta wuce ciki ta barshi nan wurin a tsaye yana kallon wayar tashi. Miss call har shida, duka kuma nata ne. Ya bi bayanta zuwa wurin nata.
“To mene ne kuma na kukan? Da kika yi bayanin na yi wata magana ne? Amma ai kema kin san ba qaramin tashin hankali zan shiga ba idan na zo gida ban same ki ba ban kuma san da fitar naki ba, ai sai in yi zaton gudu kika yi kika barni”.
Ba ta kalle shi ba ta xan yi murmushi don ta san zolayarta yake yi.
“Zo nan ‘yar shatuwallena”.
Ya qanqameta a jikinshi.
“In mun je Misau a gidanmu zamu sauka daga can ne za ki rinqa zuwa duk inda za ki kina dawowa gida kina kwana”.
Ta ce, “To”.
Tare suka tafi gidan Idris suka yi mishi sallama, daga nan suka wuce gidan Liman, shima sallamar suka je mishi.