ABU NAKA BOOK 3 BY SODANGI

ABU NAKA BOOK 3 BY SODANGI

SHEKARU BIYAR BAYAN YIWA MUS’AB TIYATA
Saddiqa da mijinta suna zaune lafiya cikin kwanciyar hankali da nunawa juna qauna mai yawa, sai dai har yanzu matsalar gidan ba ta kau ba, buqata kuma ba ta biya ba, haihuwa da ake neman ba ta samu ba.
Bayan tiyatar farko da aka yi mishi, Mus’ab ya sake komawa wata tiyatar nan ma ya tsira da qyar, ita ma dai anyita ne a dalilin jijiya ta toshe, wato dai lalurar farkon ce ta sake dawowa. Har yanzu kuwa babu wata alama da ta nuna an samu nasara, domin cikin shekaru bakwai xin aurensu ba a tava ko da vari ne a gidan nashi ba, sai dai al’ada ta xuake, in anyi bincike a ce wani ciwo ne yake neman tava mahaifa.
Suna cikin rumfa a harabar gidan bayan Mus’ab xin ya dawo daga gudun motsa jiki suna tattaunawa. Ya miqa hannu ya xauki inibin da ya tarar tana ci a tiren silba yana taunawa a hankali.
Saddiqa ta zuba mishi ido cikin nutsuwa saboda ta gane akwai abin da yake son gaya mata.
“Na ga kamar magana za ka yi?”
Ya xan yi murmushin qarfin hali tare da faxin, “Hankalinki nake so ki bani”.
Ta yi maza ta ce, “Dama a wurinka yake”.
Ya ce, “To, kin gane ko?”
Ta ce, “Uhm! Ina jinka”.
Ya yi ajiyar zuciya mai qarfi ya ce, “Yanzu ke Aisha kina ganin zamanmu haka a gidan babu qaruwa ya yi dai-dai?”
Ta ce, “Kamar ya ya?”
Ya ce, “Babu haihuwa mana, ke kin ce ba ki yarda a ce za a sake yi min wani aikin ba, a gabanki ne kuma likita ya tabbatar mana da cewar ciwon nan ya sake dawowa, amma in anyi saurin cire shi ba zai zamo mai tsanani sosai ba. To ina ce gara kawai in je ayi aikin tun bai qara yin qarfi ba?”
Ta zuba mishi ido tana kallon shi a wani yanayi na rashin sanin abin yi, da qyar ta iya buxa baki ta ce mishi, “Ashe maganar sake yin aikin nan bai qare ba?”
Ya gyara zama cikin sakin fuska ya ce, “Ba wai bai qare bane, so nake mu fahimci juna ni dake Aisha, nima ba son aikin nan nake yi ba, to amma ya ya zan yi?”
Ta zuba mishi ido kamar ta yi magana, sai kuma ta fasa. Cikin nutsuwa ta ce mishi, “Ina zuwa”. Da sauri ta miqe ta shiga gida tamkar mai xauko wani abu ta dawo.
Ya zauna nan wajen minti sha biyar bai ga ta dawo ba, ya miqe ya bi ta cikin gida su qarasa maganar. Yana shiga falonta ya tarar da ‘yar guntuwar takarda ajiye a kan kujera.
Ga abin da ya gani a rubuce.

YAYA MUS’AB
Na dai lura babu abin da kake so irin ka ganni cikin tashin hankali da damuwa, ka ganni cikin matsanancin hali. To na gaji ba kuma zan sake yarda ka sake jefani cikin wata fitinar ba, don haka na tafi, daga yau na bar maka gidanka, zan koma gaban masu tausayina”.
Sai wata rana.
Mai qaunarka Aisha.

Mus’ab ya zubawa wasiqar ido cikin kixima, ya rasa me ya faru? Me ya yi da zafi haka har da za a xauki irin wannan matakin? Tsawon lokaci yana tunani ya kasa ganowa.
To ko dai ta gaji da zama dani ne babu haihuwa? Tunda ta san matsalar tawa ce. Ya xauko wayarshi ya danna lambobinta, ta xauka ya jita tana kuka, jikinshi ya yi sanyi maimakon vacin rai zalla.
“Aisha me ya faru? Ki dawo mu yi magana”.
“Ka qyale ni kawai, ka barni kawai in huta na gaji, na gaji da ganin fitina gara in yi nesa da ita”.
“Kina ina ne yanzu?”
Ta ce, “Ina kan hanyar tafiya gida, zn tafi Misau zan koma gaban iyayenmu”.
Ba ta jira wata magana daga gareshi ba ta yi maza ta kashe wayar tata. Ya zubawa wayar ido yana kallonta tare da nanata faxin Misau. Cikin kixima.
Saddiqa tana zaune gaban Gwaggonta cikin gajiya da vacin rai, tunda ta isa take zaune gabanta tana kuka, hankalin Gwaggo ya kai matuqa wajen tashi saboda kukan da take yi da kuma halin da ta ga Saddiqan a ciki.
Abu ta iso saboda aiken da Gwaggo Habiban ta yi mata, ganin Saddiqa ya sata mummunar faxuwar gaba, ta nemi wuri ta zauna cikin sanyin jiki tana tambayar ta.
“Lafiya? Me ya faru? Me ya kawo ki gida ke kaxai? In ma rikici kuka yi ai bai kamata ki biyo doguwar hanyar nan ke kaxai ba, in kika yi haquri zai wuce kina xakinki. In abin ya yi tsanani da za ta faxa ma sai a tashi babba ya je”
“Inna ai tunda aka kai mishi ita ba ta tava shiga wannan yanayin ba, in dai kuma ba matsalarsu bane”.
Gwaggo Habiba tana faxin hakan ta kama kuka, duk da a gaban Abu take ta kasa haquri yau kam ta voye damuwarta kan lalurar rashin haihuwar Mus’ab, xa guda xaya namiji da take da shi. A baya ba ta tava tsammanin hankalinta zai koma gare shi har damuwarshi ta zama tata ba irin yanda ta zama a yanzu, ta rasa dalili, xinbin jikokin dake gareta sun kasa sanyaya zuciyarta ta yi sanyi kan rasa xa a gidanshi da aka yi.
“Me ya faru Saddiqa? Yi magana mana, ki gayawa uwarki damuwarki kinga kin sata tana kuka. Yi mata bayani dan ta samu sauqin damuwarta”.
Cikin zuciyarta ita ma ta yi tunanin yarinyar nan wataqila ta gaji ne da lalurar Mus’abu tunda ta riga ta san matsalar tashi ne. tausayin Mus’ab ya yi matuqar kama ta.
Cikin kukan ta ce, “Na gaji, fitinarshi ta isheni, don haka na bar mishi gidanshi yaje ya yi ta yin abin da ya ga dama”.
Ta miqe taje ta hau gadon Gwaggonta ta yi kwanciyarta saboda kasancewar hutun sallah take yi.
Gari ya waye sanda ta tashi ta je ta yi wanka da ruwan xumin da Gwaggonta ta kai mata, ta fito ta zauna tana shafa.
Gwaggo ta kalleta cikin nutsuwa da kulawa ta ce mata, “Kin rame Saddiqa, tunda kika je gidan mijinki ban tava ganin ki na kasa jin daxin ganin naki ba irin wannan karon, ku rinqa yiwa rayuwa haquri, duk abin da kuka gani zai wuce wata rana har ayi ta bayar da labari”.
Ta ce mata, “To Gwaggo”.
Ta miqe ta xauko doguwar riga ta sanya ta rufe kanta da gyale, ba ta tsaya yin kwalliya ba tasa kai za ta fita.
“To ina za ki ba ki karya ba?”
Ta ce, “Da na je na gai da Baba ya ce in na kintsa in je yana son magana dani, kuma na ga shigar Abu ma wurin shi kar in tsare su”.
Ta ce mata, “To”.
An haxu a xakin Malam Abdullahi shi da Abu da Saddiqa, ta sake gai da shi cikin ladabi da nuna girmamawa.
A hankali cikin nutsuwa ya tambaye ta.
“Me ya faru kika baro mijinki kika dawo gida ke kaxai Saddiqa?”
Cikin nutsuwa ta ce mishi, “Baba na gaji da zama da shi ne kawai”.
Gaban Malam Abdullahi ya yanke ya faxi, cikin zuciyarshi ya tabbatarwa kanshi rashin haihuwar Mus’ab ne ya isheta, tausayin Mus’ab xin ya kama shi.
Sai dai kuma nan take sai ya ji zuciyarshi tana raya mishi zai tsaya ya ga an yiwa Saddiqa adalci tunda dai ai ta yi haquri, bana shekaru bakwai ne da auren nasu, amma ba ta tava buxa baki ta yi wata magana ba.
“Assalamu alaikum”.
Suka jiyo muryar Kawu Gixe yana sallama daga bakin zaure. Da sauri Gwaggo Habiba ta fito daga wurinta don taran xan’uwan nata, sai dai ganin Mus’ab biye da shi ya sata kaucewa ta koma zuciyarta ta yi mata qunci ganin yanda Mus’ab shima ya rame har ma gara ta Saddiqan da tashi.
“Kin tarasu ne a nan kina yi musu qarya suna sauraron ki? Za ki fita ki ba mutane wuri ne ko kuwa?”
Da sauri Malam Abdullahi ya ce mishi, “A’a, ba fa irin wannan hukuncin a a zartar a tsakaninsu ba, don tunda ta kawo maganar gabanmu, to gaskiya da gaskiya ne kawai zai yi maganin al’amarin”.
Abu ta yi maza ta ce, “Gaskiya kenan, ke Saddiqa dawo ki zauna ki faxi abin da ya dameki babu zare ido cikin lamarin balle a je ana tsorata wani”.
Ta koma ta sake zama can gefe a rakuve. Malam Abdullahi ya zuba ido yana kallon ta.
“Kin ce kin gaji da zama da shi me kike so ayi miki?”
Cikin nutsuwa ta ce, “So nake a rabamu”.
Gaban Mus’ab ya yi mummunan faxuwa, kanshi a sunkuye ya yi maza ya qara sunkuyarwa.
“A raba ku a kashe auren kike so?”
Ya yi mata tambayar idonshi yana kallon ta.
Ta ce, “A’a, Baba zama da shi wuri xaya ne kawai ba zan iya ba”.
Gaba xayaa kowa a xakin ya samu sauqi, tun ma ba Mus’ab da Abu ba.
“A barni in zauna a gida shi kuma yaje can ya yi zaman shi”.
“Ya yi miki wani mummunan abin kenan?”
Abu ce ta yi tambayar hankalinta a kwance saboda ta gane rikici tsakaninsu ne ya dawo da Saddiqa gida ba rabuwar aure take so ba.
Ta ce, “Bai min komai ba na gaji da zama da shi ne kawai, saboda na gaji da halinshi na son kai, bai san kowa ba sai kanshi, abin da ya ga dama yake yi, in ya tashi yi kuma baya tausayin kowa, ba……..”
Kawu Gixe ya ce, “A’a, ya fa isa haka, ya isa, don sun xaure miki gindin ki yi magana ba yana nufin za ki zaunar damu ki zage shi a gabanmu bane, ki faxi abin da ya kawo ki in ji tun ranki bai vaci ba”.
Kanta a sunkuye ta ce, “Aikinshi zai sake”.
Kawu Gixe ya qara tunzura, ya ce, “To in zai sake aikinshi ina ruwanki, da can ke kika samar mishi wannan xin da yake yi?”
Abu ta kalleta a hankali ta tambaye ta cewa, “Wani garin zai koma bakya so?”
Ta gane dai ba a gane maganar ba, don haka ta gyara da cewa, “Ba aiki ba, tiyata”.
Gaba xaya aka xauki salati.
“Tiyata?”
Abu ta yi tambayar da qarfi. Ta kama baki ta riqe tana kallonshi cikin mamaki.
Saddiqa ta ci gaba da bayani kanta a sunkuye.
“Aikinshi na farko tilastani ya yi na yarda ya kuma hanani faxa muku, da aka ce ciwo ya dawo ya ce zai koma na ce a’a, a haqura har muka yi rikici da shi, na ce to kar ya sake yi min maganar. Ban ankara ba sai kawai na jishi a asibiti wai ana aikin, yanzu kuma sun sake cewa wai ya fara dawowa ya zo yana gaya min zai sake komawa, duk da na ce a’a, na san ba zai fasa ba. Shi yasa na yi hanzarin dawowa gabanku don ban san ranar da zai tafi ba”.
“Kina da gaskiya, Mus’abu ya ci a guje shi”.
Tana maganar tana kuka.
“Wata tiyatar za ka sake komawa bayan duk hatsarin da aka tsallake? Ana yiwa Ubangiji qarfi ne?”
Kawu Gixe ne ya jero mishi tambayoyin yana mai tsare shi da idanuwa.
Kan Mus’ab a sunkuye ya shiga bayani cikin ladabi don ya samu goyon baya. Abu ta katse shi ta hanyar faxin.
“Kai tafi can, Saddiqa ba za ta sake binka ba ka je can ayi ta yi maka tiyata ana maimaitawa kai kaxai, za ta zauna kusa da iyayenku ta samu nutsuwa, ta gaji da ganin fitina, ta gaji da fitinarka. Kai fitinannen mutum ne, a ce mutum bai san haquri ba”.
Ta soma kuka, kuka kuwa mai tsanani da ya yi dalilin da ta fita ta bar gidan ta tafi nata.
Tsawon lokaci xakin shiru babu wanda ya sake cewa wani abu. Kawu Gixe ya kawar da shirun ta hanyar yin magana a hankali, kuma cikin nutsuwa.
“Ina fata wannan maganar da ta yi na kana shirin komawa wani tiyatar ya zama qarya ta yi maka ba gaskiya ta faxa ba”.
Shiru ya yi bai iya cewa komai ba, duk da ya san Kawu Gixen shi yake sauraro. Gajiya da shirun Kawun ya yi ya ci gaba da maganar da ya katse.
“Kar in sake jin ka tayar da maganar tiyata a gidanka balle har aje ga sake yanka maka wani wuri a jikinka, ya isa haka. Abu guda xaya da zai hanani haramta maka komawa asibiti shine, neman magani halal ne, amma ban yarda ya kai ga yanka jiki ba. Muma a nan zamu yi iya namu in mun ji mai magani na halal zamu karvar muku, muna yi muku addu’a zamu qara, in mun sadu da mutanen da alherinsu ya bayyana zamu roqesu su taimaka mana da addu’a.
Mai bayarwar Ubangiji ne, shi kuma in ya yi nufin samun, to kun ne kawai fayakunu. Shi kenan sai ka ga an samu. Ku dai ku dimanci istigifari, ku kuma haxa da haquri. Ke Saddiqa ki je wurin uwarki ki yi mata sallama ku je wajen Inna ku yi mata sallama ku ba ta haquri, don ta tafi hankalinta a tashe”.
Ta ce mishi, “To Baba”.
Ta tashi ta fita ta barshi yana ci gaba da yiwa Mus’ab nasiha kan muhimmancin haquri da miqa wuya ga Ubangiji.
Ya ce, “To Kawu”.
Mus’ab ya shigo falon Gwaggonshi cikin ladabi, ya koma kan shimfixa can gefe ya zauna cikin nutsuwa, qafafuwanshi a harxe ya shiga ba ta haquri.
“Ku yi haquri Inna ba zan sake ba, dama ni wai burina in dai ga Aisha ta haifar muku xa ne ko da guda xaya ne da zai rinqa zuwa yana yi muku zarya a tsakar xakin nan ne kuna ganin shi, to ga shi ta zo ta haxani daku har Kawu Gixe da su Abu duk sun mara mata baya a kan wai basu yarda in sake zuwa tiyatar ba. Shi kenan ni kuma ba zan haifar muku kowa ba kenan?”
Ya sunkuyar da kanshi qasa, hawayen da suka taru a gefen idonshi suka xiga.
Gwaggo Habiba ta yi kamar ba ta gani ba saboda kawar da kanta da ta yi, cikin nutsuwa sai ta ce mishi, “Tashin hankalin dake cikin tiyatar ya yi yawa, ka bar gidanka ya zauna lafiya tunda ita matarka ba tayar maka da hankali take yi ba, kai ma sai ka yi haquri. Ai ana addu’a ba kuma za a daina ba, al’amarin kuma duk na Ubangiji ne”.
Ya ce, “To Inna”.
Cikin zuciyarshi daxi ya kama shi, godiya yake ta yiwa Ubangiji da ya nuna mishi daidaituwar al’amuranshi da iyayenshi, musamman ma mahaifiyarshi.
“Ke Saddiqa tashi mana baki ji mijinki ya shigo bane?”
Ta ce, “Qyale shi kawai Gwaggo, ya riga ya vata min rai ba wani binshi zan yi ba”.
Ta ce, “A’a, a’a, bana son rashin haquri, ina ce an riga anyi mishi faxa ya kuma ce ba zai sake ba?”
Mus’ab ya xan gyara a hankali ya ce, “Nima fa tana vata min rai Inna ina dai yin shiru ne kawai, saboda ni xin babba ne kar a ce bani da haquri”.
“Me take maka?”
Gwaggo Habiba ta buqaci sani.
“Tana takura min ne Inna”.
Saddiqa ta yi maza ta tashi ta zauna tana kallon shi, ya qi kallon ta balle ya ga kallon da take yi mishin.
A hankali cikin nutsuwa ya ci gaba da yiwa Innarshi bayani.
“Magana da baki ne kawai ba ta yi Inna, amma kullum aiyukanta na nuna matsuwarta ne kan son haihuwa, kullum a cikin sayayyar kayan jarirai take, babu halin mu fita mu dawo ba ta sani na sayi kayan jarirai ba wai sun ba ta sha’awa. Sannan ina yi mana qoqarin jariran mu samu ko da guda xaya ne ta zo ta kawo qarata an hanani. To ku gaya mata Inna ta fita hanyata da irin wannan sayayyar, kar kuma in sake dawowa gida in samu tana karkaxe kayan, in na yi magana ta ce wai qura suka yi”.
Daga shi har Saddiqan tausayinsu ne ya qara mamaye zuciyar Gwaggo Habiba, sai dai ba ta bari sun gane ba.
Ta ce, “Ke Saddiqa in kun je gida ki yi kyauta da kayan jariran nan da kika tara mishi a gida, ina dalilin su? Kayan sha’awa yana qarewa ne? In haihuwar ta zo kece mai sayen riga? To bana so”.
A hankali ta ce mata, “To Gwaggo”.
Ta sake kallon Mus’ab ta ce, “Ku dage a kan yin addu’a, in ka ga har ka samu dagewa kan roqon Ubangiji kan wata buqata taka, to qila ya yi nufin biya maka buqata ne, don haka kar ku gaji da addu’a, in za ku kwanta kuma ku rinqa karanta (Suratul Maryam) bayan addu’o’inku na kwanciya sau uku in har da rabon to zamu sadu da biyan buqata”.
Ya ce mata, “To Inna”.
Suka yi mata sallama suka nufi gidan Abu, daga can suka nufi gidansu inda za su kwana washe gari suyi sammakon tafiya Ajakuta.

Previous page 1 2 3 4 5 6Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected