HAUWA KULU Book 2 Complete Hausa Novel
THE ARABIAN BRIDE
M
adinah na gidan kakannin ta bayan saukarsu a Kano, a daren ranar za’a kawo ta wajen Mama, an gyara dakin Sumayyah da kyau wato inda za’a sauke ta da ‘yan uwanta. Gidan ya dauki kamshin turaren wuta dan Maiduguri ko ta ina mai dadin kamshi, Mama da kawayen ta su Barr. Hannatu Mahdi da ’yan uwanta suka shirya karbar amarya da danginta.
Har falon Mama aka shigar da Madinah-Munawwarah cikin lullubi, kafin a yi addu’a ta musamman ‘yan rakiyar amarya da ‘yan karbar amarya duk suka watse, gidan ya rage sai mutanen gidan kadai.
Rana ta farko dasu Mama suka ga fuskar Madinan Sarham. So beautiful da ita, karshen gayu karshen class, Masha Allah.
Mama ta ce a ranta dole kam Sarhamunta ya kamu ya tsunduma iya wuya, Madinah ko daga cikin lullubi kafin a ganta a zahiri an san matar manya ce kuma ‘yar manya ce.
Tayi fatan Allah ya basu zaman lafiya da zuri’a mai alkbarka. Ya kade fitina, ya basu ikon sauke amanarta da aka damka musu.
Yau Madinah ta samu kanta a gidan surukan ta wato iyayen Sarham suna ta haba-haba da ita. Sumayyah da Surayyah ma ba’a bar su a baya ba wajen kula da bakuwar tasu, Surayyah kuwa duk da ‘yar tsamar dake tsakanin ta da Sarham sai da ta kasa shiru, da ya shigo gaida Mama bayan ya dawo gidan da daddare sosai tace dashi.
“Yaya Doctor, wallahi ka iya zabo mata, class iya class malam, kyau iya kyau, dubi mata kamar hurul- eeni, kamar ita tayi kanta don kyau da gayu.
Wata mummunar harara Sarham ya zabga mata yace “ki fita idona in rufe, ki bar shiga harkata, na rantse Mama ki raba ni da Surayyah”. Sannan ya gaida Mama da gajiyar hidimar jama’a, wadda keta dariyar masifarsa, Mama tace “ban taba ji ko ganin ango yana masifa ba, duk wani ango far’a yake yi da farin ciki banda kai, tashi ka shiga dakin Sumayyah Madinah din tana can”, cikin jin nauyin Mama irin wanda bai taba ji ba a rayuwarsa yace,
“Mama ki barta, sai da safe in Allah ya kaimu zamu gaisa in sha Allah, a barta ta huta, na san ta gaji, gata bata jure hayaniya”. Nan kuwa kunyar idon Mama ya hana shi zuwa yiwa Madinah barka da sauka cikin rayuwarsa.
Sai da ya koma dakin sa yayi shirin kwanciya sannan ya kirata a waya, Madinah ta fito wanka kenan tana saka kayan barci zata kwanta kiran sa ya shigo mata, sai da ta ja aji, don taji haushin kiran data yi masa bai dag aba kuma bai biyo bayan kiran ba, kafin ta dauka da kyakkyawar sallama a bakin ta, maimakon ta ce tayi fushi, saboda bai zo inda take ba tun saukar ta a Kano, ko irin kananan korafin nan na amare da ke cikin lokacin da ake mararinsu, ina! Madinah nata salon daban ne, da wuya kaga bacin ranta akan abu, komai tana kokarin maida shi ba komai ba a rayuwarta (banda kishin Sarham), don ko shi Sarham zai rantse bai san me yake bata ran Madinah ba, sai ta karya murya cikin rangwadarta da zakin muryarta tace,
“daga jin muryar ka mura kake, ina fatan angon Munawwarah yaci abincin dare?”
Sarham yayi wata wawuyar ajiyar zuciya, tuni ya manta da kishin da yaci alwashin gasata akansa da zarar ta shigo gidansa, wato fushin aurenta da AVM Alkali, ya samu kansa da cewa “kayya! Anyway, kin zo lafiya Madinahtul-Munawwarah, ya gajiya ya aka ji da zafin garin mu?”
Madinah tace “garin ku kai kadai? Ai ba’a canzawa tuwo suna. Zafi kuwa ai yana Saudi Arabia”, yace “kiyi min alfarma mu Arabian Bride, na san ke dinnan ma’abociyar tsinkaye, fahimta, da yi min uzuri ce, bazan iya shiga dakin Sumayyah inda kike ba kusa da dakin mahaifiyata ne, ba zan iya tsallake dakin Mama a gidannan in dinga zuwa inda kike ba, amma already nayi kokari nayi mana booking na komawa Jidda, don ni garin Kano ya fita kaina, zamu tashi rana ita yau in sha Allah muje mu ci duniyar mu da tsinke.
Na yanke shawarar karbar aikin nan na Saudi-German”.
Farin ciki mai yawa ya cika fuskar Madinah da zuciyarta, don dama tana cikin tunanin yadda zata iya rayuwa a garin Kano, ta shiga damuwa akan yadda zata iya rayuwa a Nigeria ma in general, tana dai daurewa ne albarkacin soyayya da yadda kowa nata ke lallashin ta, yayyenta kuma suke gaya mata aure babu inda baya kai mutum har bukka a jeji, amma hakika tafi son cigaba da rayuwa a Jeddah.
A can aka haifeta acan ta rayu, acan ta girma. Abinda ta sani ta kuma yarda da shi kawai shine; ko a cikin ruga zata iya rayuwa in dai da Sarham Abbas ne, kuma in dai zasu kasance tare karkashin alfarmar aure da ni’imarsa itada shi har karshen rayuwar su.
Sarham ya katse mata tunani, “kin amince ko?” Da sauri Madinah tace “haba-haba ai nima zan fi son hakan, da kunya kam mu kebe ko na minti biyu ne alhalin Mama da Abba suna cikin gidan, Allah ya kaimu lafiya, ni da ka kara mana wani satin ma a kan dayan ya zama munyi biyu tareda su kafin mu koma”. Yace “no, zamu tafi rana ita yau in sha Allah bana son zaman garin ne”. Ya tambayi Madinah ko me take yi yanzu? Ta ce ta yi wanka ne zata kwanta, ta gaji sosai, tace tun saukarsu a Kano bata huta ba. Sarham ya ce,
“ai kuwa baki ga ta barci ba, kamar yadda nima ban ganshi ba. On this special day, ki tashi ki dauro alwallah ki yi sallah raka’a biyu nima zan yi yanzu, mu godewa Allah da ya cika mana burin mu da cikar alkawuran da muka yi wa juna yau shekaru goma!
Kada ki manta a cikin sujjadar ki ta karshe ki roka mana ‘long life, prosperity, blessed children, unending love, and infinite peace. Madinah ina fatan ki zamo min ‘shelter’ kamar yadda birnin Madinah ya zamowa Annabin mu Shelter, refuge, security, safety and peace!”.
Madinah ta lumshe idanunta cikin farin cikin da bazai misaltu ba, tace “kaima ina rokon ka roka min aljannah, don Hajjah Ramlah ta gaya min aljannah ta yanzu ta tashi daga dugadugan su ta dawo bisa dugadugan ka.
Ka roka min ‘ya’ya masu yawa tare da kai kuma masu albarka, ka roka min Allah ya mallakamin zuciyar Sarham dina, nikadai raina bakidayan ta, don itace kadai ‘weakness’ dina a duniya (zuciyarsa)”.
Finally, daga yau dai, sunansu ya tashi da ‘honorifics’ tunda ya koma Mr&Mrs. Dr. Shanono. Bayan tarihin fafutukar soyayyar shekaru goma!!!
**** ***** ****
A kwanaki bakwai din da Madinah tayi a gidansu Sarham, ta saba da kowa, kuma ta samu karbuwa ba laifi a wurin iyayen sa musamman Abba Prof. da yake ganin girman Kakan ta mai rasuwa Alkalin Alkalai, duk da ba wai sanayya ce a tsakanin su ba, amma yayi masa farin sani a matsayin daya daga cikin iyayen Kano. Ta fannin Mama kuma, ta zauna ne daga gefe tana laqantar Madinah a ma’auni na adalci da son sanin hakikanin halayen ta, inda a dan zaman su tare ta fahimci Madinah wayayyace, Madinah mai ilmi ce, bata da matsala sai ta rashin kawaici a kan Sarham, in bata gan shi ba sai ta ishi kannen sa da tambayar ina yake, wanda ke nuna zata yi kishi akan sa sosai, idan ya fita bazata nutsu ba sai ta ji shigowar sa gidan, tana da bala’in jan aji amma akan Sarham babu ajin ko kadan, don bata iya boye son da take masa a gaban iyayen sa da kannen sa.
Gata da halaye na kowa tasa ta fishshe shi, wato halayen nasara, kai bazaka ce girman kasar larabawa bace, amma kuma duk da haka tana girmama su, musamman su iyayen sa, ta fahimci Madinah ta san abinda take yi yadda ya kamata, tunda duk rashin kawaicinta data fahimta, a duka kwanakin nan bakwai data yi tare dasu, bata tsallake su ta kebe da Sarham ba, ko ta bi shi inda dakinsa yake, ita da shi sai ko a waya, ko in ya shigo ya taddasu duka a falo, sai ya zauna ayi hirar tare da shi, amma baya sakewa musamman in Mama na wajen, tana kallon Madinah na kashe shi da murmushi.
Shi da kan sa Sarham ya fahimci wani abu, wato tun bayan zuwan Madinah, mu’amalar sa da Sumayyah ta ja baya, Sumayyah ta daina shiga sha’anin sa sam, ko wuri ya shigo tana dariya sai ta daina, ta yi fuska. Ta daina kai masa abinci ko gyaran dakin sa wanda aikinta ne. A’ah, tun baya damuwa har ya fara tunanin laifin me yayi mata don wannan ba halin ta bane, me yasa ta daina ajiye masa abinci ko kiransa yazo ya ci, da gyara masa daki alhalin ta san ba wai Madinah ta tare bane, da zata cigaba da yin wadannan hidimomin da tazo ta tarar tana yi masa.
Yau ya fita can karshen layin su yana wata irin romantic waya da Madinah, don hakurinsa kusan ya fara karewa da takunkumin da ya sanya musu, haka suke yi yanzu kullum da yamma in jama’ar gidan basa nan ko suna wasu sabgogin a kitchen, ko can dare in kowa ya kwanta, sai ga Sumayyah ta karyo kwana tana tafe cikin nutsuwa, ta zo har inda yake ta gifta shi bata ce masa ko sannu ba, har ta zarta shi kadan ya kashe wayar ya saka a aljihu, ya ce,
“Sumayyah!”.
Sumayyah ta dan dakata amma bata juyo ba, ta daure fuska sosai, ya ce “ko ba da Sumayyah nake magana bane?”
Ta dawo ta tsaya a gaban sa tana tura baki gaba, ya ce “kin gama hada kayan naki?” Ta ce “hada kaya kuma? Ina zani?” yace “eh, Abba bai gaya miki da ke zamu tafi Jeddah ba, zaki zauna a gida na ki fara MBBS? Tukunnama wai me nayi miki kike gaba da ni haka? What’s wrong with you?”
Sumayyah mai neman kuka an jefeshi da kashin awaki, nan da nan ta soma hawaye na babu gaira babu dalili, tace “wallahi in dai a gidan ku zan zauna to na fasa karatun a can, ni ba don kai da matar ka zan je Jeddah ba, ba ‘yar zaman daki kuka samu ba, zani jami’ar Sarki Abdulazeez ne, zaman karatun kaina, kowa yayi rayuwar sa a inda yake zaune duk da muna gari daya”. Cikin madaukakin mamaki Sarham ya ke duban Sumayyah, da babbar murya yace “Summy! Kina cikin hankalin ki kuwa? Ko kin fara shaye-shaye ne?” Sumayyah ta murgude baki gefe tace “Allah ya sauwake in yi shaye-shaye, kawai dai… ni bazan zauna a gidan ku bane, in ba hostel za’a kaini na zauna ba, to a nema min admission a BUK”.
Cikin kokarin hadiye fushi da bacin rai da ke tunkudo masa Sarham ya ce “to na ji, matsalar ki ce wannan yin karatu a Jeddah ko barin sa bakidaya, amma ki gayamin dalilin ki na kulla gaba da ni, da fita sha’ani na alhalin ba haka muke nida ke ba, sai yanzu da na yi aure, bayan kinsan mata ta bata tare ba balle ta cigaba da yimin hidimar da kike yi min”.
Sumayyah ta ce “Bhaiya, kaima gashi nan aika fada da bakin ka, “KA YI AURE!” Tunda kayi aure ni ba ruwa na da harkar ka gaskiya, kada wataran azo an araba ni dambe da matarka don na fahimce ta mai kishi ce, sannan na san wannan matar taka mai kama da larabawan aljannah, ba zata barni da kai ba sai ta raba mu, ga shegiyar kissa da kinibibi da rashin kawaici a kanka, tana wani kalmashe murya kamar kyanwa, shiyasa tun yanzu na raba kaina da kai, ba sai ta raba mu in zo ina jin zafin ta ba”.
Sarham baki bude yake kallon Sumayyah, yaki yardarwa kansa bata sha kwaya ba, yana ji ana cewa wai kanne na kishi da matan yayyun su, bai taba yarda ba sai yau.
Sai ya kwantar da ido da murya ganin Sumayya na share hawaye kuma, tana tuno irin tsananin shakuwar dake tsakanin ta da Bhaiya, yau ga wata ta zo ta shiga tsakani, ta fita kusanci dashi, kuma ta san ta shigo rayuwar su kenan har abada, bazasu kara samun kusancin da suke da shi ba ita da shi yanzu, saboda matar sa.
Yanzu kam ya yarda Sumayyah bata sha komai ba, ‘inner feelings’ dinta kenan, wanda ya sabawa hankali, shi take fada masa ba karya take ba, ba kuma hassada take yi wa Madinah ba, a’ah tata damuwar ce ta karan-kanta, saboda yadda ta damu da zumuncin da ke tsakanin ta shi.
Yace “Sumayah kada Allah ya baiwa kowacce irin mace da zan aura iko a kaina, ba a kan ki ke kadai ba, har iyayena da Surayyah, kada Allah ya dora min soyayyar da zata rufe min idanu in canza muku da wani abu saboda mace, ko in yanke zumuncin dake tsakanin mu, ko in kasa kyautata muku da kula da rayuwar ku”.
Sarham ya ja mumfashi a hankali, kafin yace “My sister Sumayyah, ki taya ni addu’a kin ji?”
Sumayyah tace “ai son da kake mata yayi yawa ne, Yaya Sarham ban so ka auri macen da son da kake mata ya rinjayi nata ba, don tsaf! Zata raba ka da kowa naka”.
Sarham yace “Sumayyah wannan tunanin ku ne irin na mata, ki bari ki ga kamun ludayin Madinah tukunnah, ina tabbatar miki Madinah daban take da sauran mata, don bata tashi anan ba, kuma bata tashi cikin mata ba sai ‘yan maza, duka wadannan halayen na mugunta bata san su ba, I assured you.
Madinah mai ilmi ce kuma mai hankali, ta san abinda take yi kin ji?”
Da wadannan kalaman ya samu yayi ta lallashin Sumayyah, har ta dan saki fuska ta daina kukan, amma tayi masa rantsuwa akan ita ba zata zauna a hannun Madinah a Jeddah ba, a makaranta zata zauna. Sarham yace “in aka barki kika zauna a makarantar shikenan baki da damuwa?” tace “eh, saboda matar ka ce raina baya so” ya ce cikin rashin jin dadi, “to na yarda, ban kuma isa in sa ki so ta dole ba, amma don Allah Sumayyah kada ki kulla gaba da Madinah akan haka, mai son naka masoyinka ne ba makiyin ka ba, ki bata dama ki ga irin halayenta”.
Sumayyah tace cikin jin tausayinsa “toh!” ya ce “zaki gyara min dakin nawa yanzu? Yau kwana bakwai baki share min ba, ban ci girkin ki mai dadi ba kanwata ta kaina”, tayi dan murmushi tace “zan gyara dakin, for now, amma ka cire ni daga dafa maka abinci da gyara maka daki kaima daga yau, ka koyi cin na matar ka”.
Da wannan suka tako a tare zuwa cikin gida. Sumayyah ta je ta gyara masa dakin sannan ta tafi hada kayan ta da zata tafi da su Jeddah, tana cikin hada kayan Mama ta kirata tace taje ta zo da Madinah, zasu fita ssallama gidan Hajiya Kulu su kuma gaishe ta bata jin dadi.
Sumayyah ta bata rai, tace “Mama why not Surayyah ta kira miki ita? Tunda tasu ta zo daya?” Mama ta ce “ke bana son rashin hankali kishin kannen miji, ki raba kan ki da wahalar da bata da amfani, tunda ke dai bazai aure ki ba, ita din da baki so ita Allah ya halatta masa”.
Sumayyah tana kokarin ta hadiye bacin ranta, ta ce “Mama Allah ya sawwake in yi kishin Yaya na, kawai ni I DON’T LIKE HER! AND I DON’T KNOW WHY?” Sai tasa kuka.
Mama ta rungume Sumayyah tana lallashin ta, a lokacin tayi ta kokarin ganar da ita hakan bashi da amfani kuma kuskure ne, in har tana so ta zauna lafiya da dan uwanta dole taso matar sa wadda bada jimawa ba zata zama uwar ‘ya’yan sa. Ta tilasta mata kan ta je ta kira Madinah da kanta su tafi Gadon Kaya tare.
Ko da ta shiga dakin Madinah na waya da Sarham, ana kalmasa harshe da larabci ziryan, cikin wani ‘accent’ dinta da shi kadai take yiwa magana da shi. Kyabe baki Sumayyah tayi ta ce,
“in kin gama an ce ki zo mu tafi Gadon kaya”. Ta juya tayi ficewar ta.
Batun yau ba Madinah ta fahimci Sumayyah bata yin ta, ba kuma don tayi mata wani laifi ba sai don a matsayin ta na masaniya akan halayen mata ‘yan uwanta psychologically ta gane Sumayyah irin kannen mijin nan ne masu kulafucin zumunci da yayyensu. Wanda hakan ke sawa su kasa shiri da matan su na aure don a ganinsu zasu raba su, amma ta san Surayyah sosai take yin ta, halinta daban dana ‘yar uwarta, itace ‘yar dakin ta, tasu tafi zuwa daya, kullum sai ta zo mata hira.
Madinah tasa a ranta daga yau zata fara kyautatawa Sumayyah. In har kyautatawa na sawa a so mutum, to Sumayyah sai ta so ta, don an ce zuciya na son mai kyautata mata.
Sun je sun gaida Haj. Kulu Surayyah ce ta tuka su a motar Mama su uku, daga nan suka dan zazzaga da Madinah taga gari, sune har Gidan Makama Museum da Gidan Dan hausa, Madinah ta roki Surayyah bayan sun gama zagayen da su je ‘main house’ din su a SoronDinki.
Tun daga gate suka tabbatar sun zo babban gida, kuma tun daga karbar da akayi musu suka yarda gidan su Madinah gidan karamci ne da karrama baki. Sannan ana ji da Madinah a family dinta. Basu jima sosai ba tayi sallama da Kakar ta da sauran ‘yan uwan ta suka koma gida.
Washegari ya kama ranar da zasu koma Jeddah, shiri sosai Mama ta yi musu na kayan abincin da babu a can, su maggi dunkule, ta kuma yi musu dambun nama mai yawa, gasu alkaki, dubulan, nakiya, bakilawa da gireba na cikin garar Madinah da aka kawo, duk tasa an shirya musu a jakunkuna daidai kilo dinsu, Sarham yayi sallama da iyayen sa da Kakar sa Haj. Kulu. Surayyah ta dauke su a motar Mama tayi musu rakiya zuwa filin jirgin malam Aminu Kano, suka tashi su uku wato, Sarham da Madinah, da kanwar sa Sumayyah wadda zata fara karatun medicine karkashin kulawar Yayan ta a birnin Jeddah.
****** ***** *****
S
umayyah Allah-Allah take su sauka a Jeddah, ta kama hanyar makaranta, ta kyale Sarham da matar sa, don ta gaji da ganin salo da rashin kawaici irin na Madinah.
Bayan saukar su a Jeddah hidimar makarantar Sumayyah ya fara yi, tun ma kafin su tare a gidan su, Madinah ta sauka wajen iyayen ta kafin a gama shirya musu gidan su da Saudi-German suka basu a gidajen likitocinsu, cikin kwanaki uku da saukar su har Sumayyah ta fara karatun ta, aka bata daki a hostel din dalibai kamar yadda tafi so, shi kuma yayi ‘documentation’ na karbar aikin sa a cikin kwanakin da asibitin kwararrun ido na Saudi-German.
Dr. Sarham Abbas Shanono ya zama cikakken likitan fidar ido (ophthalmic surgeon), daya daga cikin manyan likitocin idon da Saudi-German ke ji dasu da alfahari su.
Saida ya kammala ‘documentation’ din sa aka kuma gama shirya musu gidan nasu daga dukiyar gidansu Madinah, daga nan gidan su ya dauketa suka wuce babban birni wato (Riyadh) ta jirgin sama domin barje gumin amarci, abinda larabawa suke kira ‘Shahar Al-asal’ wato (honeymoon) da harshen larabci, inda acan Sarham ya gama gane aya da tsakuwa wato AVM Alkali bai yi masa barnar da yake tsoro ba, tuni ya ware aka barji amarci gangariya da matar da yakewa so gangariya, wanda shi kan sa ya san son da yake wa Madinah mai yawa ne, da har wani lokacin yake tausayin kan sa.
Daga ‘first-night’ din su, Madinah ta idasa tashin kan Sarham, domin abinda yake zato ba haka ya sameshi ba.
AVM bai yi masa barna ba, bai kuma bar masa sudi ba, domin kuwa shi ya bare alewar sa a leda.
Suna Riyadh ana barzar amarci a wani babban hotel na kasar, har tsayin sati guda kafin su dawo Jeddah. Dr. Sarham Abbas, ya kama aikin sa ka’in da na’in a asibitin “SAUDI-GERMAN”.
**** **** ****
Kullum amarcinsu sabo dal yake komawa basa taba gundura da juna. Amma duk da haka Madinah tana ta zuba idon taga Sumayyah ta dawo wajen su da zama bayan dawowar su gida daga honeymoon, amma bata gan ta ba, bata kuma ji Sarham yayi maganar dawowar ta wajen su ba ko sau daya, sai ta tambayeshi a wani maraice.
“Ni Dr. ina Sumayyah ne? Sumayyah ba a wajen mu zata zauna bane? Ta yaya muna gari daya amma zamu barta ta zauna a hostel?”
Yace cikin rashin damuwa da maganar “kada ki damu, zabinta ne”. Madinah bata gamsu ba, tace “amma dai Mama bazata ji dadi ba in taji bama tare da ita, kamar mun kasa rike ta zata gani” ya ce cikin kosawa da zancen “Madinah ki yi abinda ke gaban ki kin ji! Ki manta da Summy. Ban san ki da shiga sharo ba shanu ba.
Summy wata irin hutsuwa ce, bata son shiga harkar mutane kamar yadda kema bakiso kowa ya shiga taki in ba ke kika saka kanki ba, itama haka take”.
Ya fadi hakan ne don bazai iya gaya mata gaskiyar cewa Sumayyah bata yin ta ba, wanda gaskiyar maganar kenan, jininsu bai hadu ba, wato bata a layin mutanen dake son ita Madinar, ta bangaren ahalinsa. Amma duk da hakan data fahimta da kanta ba tareda ya fito fili yayi bayanin ‘fear’ din Sumayyah a kanta ba, Madinah bata fasa kyautatawa Sumayyah ba, haka kawai zata yi shopping niki-niki ta dauka a bayan mota ta kai mata har dakinta na hostel din, ko kayan abinci ko na shafa. Daidai gwargwado Madinah tayi kokarin jan Sumayyah a jiki ko don ta samu ‘yar uwa mace, kasancewar nata ‘yan uwan duk maza ne amma abin mamaki ko kadan Sumayyah ta kasa son Madinah, ta ki sakar mata jiki.
Sarham ya sha zama yana lallashin Sumayyah a bayan idon Madinah, kan ta bude zuciyar ta wa Madinah, ta dauka ita da shi ba banbanci, wato ta dauketa matsayin Yayar ta kamar yadda ta dauke shi Yayanta, amma taurin kai irin na Sumayyah akan Madinah ya ki canzuwa, Sarham ya danganta hakan da rashin haduwar jini kawai a tsakanin su, tunda shi kam ai zuwan Madinah bai sa ya canza ma kannen shi ko iyayen shi da komai ba.
To haka Surayyah ma dake can gida tana shan aiken kaya daga Dr. Madinah duk lokacin da ta samu mai zuwa Kano, lazim ne ta yiwa Surayyah aike. Haka koyaushe suna like a waya tasu kam ta zo daya, amma Sumayya kullum ranta kara nesanta yake da shiga harkar Madinah, saidai ta yarda auren sa da Madinah, da kuma uwa uba zazzafar soyayyar da yake mata kamar ya hadiye ta duk basu sa Sarham din ya canza musu ba su kannen sa da iyayen sa.
“Madinah-Munauwarah”, cikin watanni uku ta zama GIWAr mace a gidan ta, shi da kan sa Sarham in yayi nishadi GIWAR SARHAM yake kiranta, Madinah ta samu fada a wajen mijin ta yadda ba’a zato, saboda tarin baiwarwakin da Allah yayi mata musamman na iya masa da duk fitinar sa a shimfida, Madinah ta yarda da gaske ko a cikin maza nata mijin daban ne a fannin shimfidarsa da matar sa, ta iya kalamai masu sanyi da sanyaya zuciyar miji a duk halin da yake ciki, ta kalmashe shi da iya girki na zamani, da iya kula da shi a shimfida, ta kware wajen taya shi kula da tsaftar jikin sa, kula da kannen sa wadanda ta gama lura baya hada kaunar su da komai a ransa saboda irin ‘upbringing’ din da iyayen su suka yi musu kenan na kaunar junan su da hadin kai a junansu, kasancewar basu da yawa a wurin iyayen su.
Madinah irin matan nan ne masu nacin shiga (educational programs) da ake yi a Saudi-Arabia, duk wasu programs irin na (marriage coaches) na mata musulmi masu burin karawa juna sani akan ilmin zaman aure da zamantakewa da ake yi a kasa mai tsarki ko na likitanci komai nisan gari zaka samu Dr. Madinah na kokari ta halarta, wannan ya karawa Madina (exposure) akan ilmin data ke da shi.
Domin bata tsaya ga bangaren karatunta na likitanci kadai ba, a’ah, tana kara fadada ilmin ta a kan zamantakewar aure da zamantakewar al’umma, tana da yawan rubuce-rubuce (wadanda bata wallafawa) akan sha’anin mata da aure musamman da bata fara aiki da kowanne asibiti ba a lokacin, kullum cikin bincike take a yanar gizo kan yadda zata kara inganta kimar ta a gidan auren ta.
Ko wata uku ba’a rufa ba da auren su, Madinah ta fahimci yaron ciki na wata guda a tare da ita.
Ciki irin silent dinnan (mara laulayin nan), cikin data kira da suna DAN SO. Yo dan ta da Sarham ai dole ta kira shi DAN SO wanda tarihin soyayyar shekara goma ne ya samar da shi ‘sharp-sharp’ kamar a dokin kofa tayi tuntube da cikin sa. Koda cikin ya soma girma ya shiga watanni biyar bai hana ta komai daga harkokin ta ba, amma yasa ta fasa karbar tayin aikin da ta samu da Dr. Siddiqah hospital, domin ta zauna a gida ‘fully’ ta raini dan So, ta kuma baiwa ubansa kulawar da zata gusar da hankalin sa daga kan sauran mata.
Addu’ar ta kullum Allah yasa abinda ke cikin ta namiji ne, tana fatan yayo kamannin Sarham, da halayen sa da kwakwalwar sa. cikin ‘yan watannin da ta kasance kullum a gida Madinah ta kara kaimi wajen ganin ta samarwa kanta kyakkyawan matsugunni a zuciyar Sarham, ko dama matsayin ta mai girman ne, to ta kara girman matsayinta ta hanyar kula da shi da bukatocin sa, ta tsare masa cikin sa, ta kware wajen iya girke-giren zamani dana larabawa, ta mallakawa Sarham duk wata kauna, soyayya, kulawa da yardar da diya mace kan yi wa namiji.
‘Yan gidan su Madinah na yawan zuwa gidanta, haka Daddy din ta da kan sa sai ya dauko Hajjah Ramlah a gaban mota ya tuko da kansa su zo ganin ta, musamman da cikin ta ya soma girma, dokin su ga haihuwar Madinah kamar a kan ta zasu fara samun jika bayan kuwa jikokin su sun kai goma daga yayyen Madinah, don cikinsu Usman ne kawai bai yi aure ba.
Amma a wajen Hajja Ramlah da Dr. Sorondiki na auta Madinah na musamman ne tunda ko cikin ‘ya’yan su ita din ta musamman ce. Don haka sayayya sosai ake ana tarawa don jiran haihuwar.
Cikin Madinah na da watanni takwas Hajjah Ramlah tace a dawo da ita Sorondinki ta haihu a can, ita bazata iya zamar mata jego ba (zaman dabaro), da farko Sarham yace bai yarda ba amma Mama ma sai tace a kai ta, ai haihuwar fari ce, normally a wancan lokacin ana zuwa wankan gida. Don haka bada son ransa ba ya fara ma Madinah shirin tahowa haihuwa, don dama sun riga sun gama sayayyar haihuwar su tuntuni, shi yayi, su Daddy sun yi, Sumayyah ma ta tara kayan baby da yawa iya karfin ta ta bashi da zasu taho, koda bata yin Madina tana maraba da isowar dan ta ko ‘yar ta daga Bhaiya.
Sarham yana cike da damuwar yadda zai rayu a gidan su shi kadai ba tareda Madinah ba.
Shi ya kai Madinah gun kakanninta, weekend kawai ya samu yi tare da su Mama ya koma Jeddah.
Tafiyarsa da sati uku Madinah ta haihu, ta haifi lafiyayyar diyar ta mace, mai kama da ita, amma kalar fatar jikin da bafulatanar sumar ‘yan Shanono yala-yala ta Sarham ce, Surayyah ce ta fara kiran sa tayi masa albishir, cike da doki. Sannan Mama ma ta kirashi don duk suna asibiti tareda ita aka yi haihuwar, Daddyn Madinah tuni ya fara shirin tahowa Kano tarbar amaryarsa da aka haifa ranar Laraba, “Laraba Tabawa Ranar Sa’a” inji Haj. Kulu. Tana mai jan hancin yarinyar dan sirit da shi.
Ranar da Daddyn Madinah da Sarham suka sauka a Kano kwana shidda cif da haihuwar, da yammacin ranar ya je gidan su Madinah a Sorondinki ya dauki yarinyar yana kallon ta da wani irin paternal love, kafin Madinah ta fito daga daki, ta sha ado, kamar ba itace ta dawo daga kofar lahira kwana shidda a baya ba, Sarham ya daga kai yana duban ta da wani irin murmushi, amma sai me? Sai kwakwalwar sa ta gaya masa cewa kawai ya saka ma baby din Madinah suna HAUWA’U ya dinga kiranta da Maijiddah, in the memory of his lost blind sister (miskiniya KULU).
Madinah ta fito ta same shi da yarinyar a hannu amma yayi nisa cikin tunani, yana murmushi shikadai, sai da ta sakala hannayen ta a wuyan sa ya dawo hayyacin sa, ya sumbaci goshin yarinyar itama Madinah ya sumbaci goshin ta, Madinah duk ta kumbure a hakan ma ta dan sace, “an sha gumurzun haihuwa an zama uwa”, da ya dube ta yaga yadda hancin ta da bakin ta suka bubbude leben ya zama tafkeke saiya fashe da dariya.
Madinah ta san me yake yi wa dariyar don yanzu itama ta gama kallon kan ta a mudubi kamar ta fashe da kuka, amma wannan yasa ta kara kaunar Hajjah Ramlah, ko ba komai ta ga yadda ta kawo ta duniya ba wasa bane, ta kuma kara girmama lamarin ta fiye da na Daddyn ta. Yo Sarham yana can Jeddah cikin ofishin sa yana shan rabar AC tana labour room tana gumurzu kamar ta sheka barzahu.
Kwafa tayi ta cuno bakin gaba tace “ai na gama daga wannan babu kari” Sarham ya sake darawa ya ce “ah haba Madam Dr. yaushe aka yi daren garin zai waye? Yanzu muka fara saka kwallo a raga, sai kin yi dozen Hajjaju wannan ta ladan noma ce, ki rubuta ki ajiye na gaya miki” ya hada su ita da jaririyar ya rungume su, yayi musu kyakkyawar sumba a bakunan su, sannan ya yi mata sannu da sauka, ya kuma saka mata albarka, daga bisani yace.
“Allah ya raya mana Nana Hauwa’u, AKA Kuluwa, Kulun Majadun”.
Madinah ta zaro ido ta ce “sunan tsofaffi zaka saka mata? Ka rufa min asiri don Allah ka sa mata ko sunan Sumayyah mana”, yace “Sumayyah ce ta taya ni haihuwar ta? ko sanda nake shan yakushi da cizo a Riyadh Sumayyah ta zo ta taimake ni?” Madinah ta rufe ido cikin jin kunya tace “kai don Allah SARHAM!” Yace, “of course, sunan da na ga yayi min daidai kenan, Hauwa’u, Hauwah uwar al’ummar duniya, Hauwa uwar matan duniya bakidaya, uwar bil adama”.
Sai da ya kama hanya a mota zai koma gida yana cikin matsanancin nishadi, akwai contentment mai yawa on becoming a father, ya tambayi kan sa “why HAUWA? Me yasa sai Hauwa zai sakawa ‘yar sa? Bayan in don yake tuna su ne, sunan Inna ya kamata ya saka wato Safiyyah?
Murmushi yayi, a lokacin yazo zai wuce ta kofar Na’isa, yana kallon kofar wadda aka sake ginewa aka sabuntata, bayan hawan sabuwar gwamnati, sai kawai ya tuna da Malam Isa, kawai sai ya karya kan motar sa ya nufi gidan Malam Isa mutumin sa.
Tun daga nesa ya hango ginin da yasa ayi na gidan su Hauwa ya kammala, gini ya fito sosai na zamani, amma ba’ayi fenti ba tukunna.
A zaure ya tadda Malam Isa yana shirya itacensa, ya yi masa sallama, tun daga nesa da Mal. Isa ya hango shi sai ya saki hamdala, Sarham na isowa tun kafin su gaisa yace “Dan nan kana lafiya? Ina ka shiga shekara guda da watanni ina neman ka? Tuntuni nake ta jiran zuwan ka, gashi ban san gidan ku ba, aikin gini tuni an kammala, wayar da ka bani kuma na kasa magana da ita tun lokacin da ta fada ruwan wanka na ta lalace, na sunkuya sai ta fado daga aljihuna ta shige bokitin ruwan wanka, shirun ka yayi yawa baka leko ni ba, in ce ko dai lafiya? Kusan shekara da rabi kenan ban ji daga gareka ba.
Tun bayan tafiyar ka da kadan nake ta son in yi magana da kai abu ya faskara, in labarta maka abinda ya faru.
Wato cikin ikon Allah kwanaki Mai kosai (matar sa) ta je tashar Kano line zata hau motar Zaria ta ce min ta ga wata mata kamar Innar Hauwa tana sayar da abinci a tashar, amma bata yi mata magana ba ta fasa tafiya Zaria tazo ta gaya min, don ta san irin neman da mukeyi mata. A take na bar abinda nake yi na bita muka je amma bamu same ta ba, sai wasu mata guda biyu a wajen dake yi mata aiki, muka tambaye su ko anan Innar Hauwa take, tana da ‘ya makauniya, suka tabbatar mana anan take sana’ar ta saidai ba kullum take zuwa ba yanzu, don bata da lafiya, su suke rika mata aikin yanzu, amma tabbas bamu ga Hauwa a wajen ba.
Wallahi tun lokacin nake so in gaya maka na rasa hanyar isa gare ka, ni kuma ban kara komawa tashar ba har yau, don a washegarin ranar Sunusi dan waje na ya zo ya tafi damu Ikko, can inda yake sana’ar sa, mun jima bamu dawo ba sai jiyan nan muka dawo nida Maikosai”.
Sarham bai cika katse mutum kafin ya kai aya ba, amma hakika yau ya gundura da dogon bayanin Malam Isa, kawai ya ce masa ya ga Innar Hauwa mana ‘short and simple!’ Mikewa tsaye yayi jikin sa yana dan tsuma, yace.
“Sako takalmanka Malam Isa mu je ka raka ni inda ka gan su suna sayar da abinci din”.
Malam Isa ya ce” ai ka bari ka fara duba ginin daka bar min amanar aikin sa ko? Kafin mu je neman nasu, tunda takamaimai bamu sani ba ko har yanzu suna can” Sarham ya kufula, kamar ya kaiwa Malam Isa naushi, don ji yake kamar yayi fiffike ya tafi shikadai.
Malam Isa ya ce “to tunda naga ranka ya baci, bari to in kira Halilu ya zo ya zauna min akan itacen nan, in yaso in muka yi la’asar sai muyi maza mu tafi”. Kawai sai Sarham ya samu kansa da ce masa “ai nayi sallah kafin na zo don Allah Malam Isa, ka daina ja min rai, bani da hakuri wani lokacin kamar zawayi nake”.
Malam Isa yayi dariya yace “ai wallahi sai ka jira ni na yi tawa sallahr, na kuma kora dan farau-farau a cikina, baka ji shi ba kamar bakin akuya tun dazu sai kururuwa yake”.
Sarham ya koma kasa ya zauna, dabas! Kamar kayan wanki, dole ya jira Malam Isa yayi alwallah a gefe ya hau buzunsa ya tada sallah, ya gama ya jawo kwanon sha a rufe ya sha farau-farau din sa ya koshi, sannan ya dubi Sarham wanda ya kai kololuwa wajen hadiye fushi, Malam Isa yayi dariya yace “irin wannan zama a kasa haka duk ka bata farar shaddar ka, wai ni ko son Kulu kake yi ne, don itama haka take da kyau tubarakallah kamar ka, koda idanun suka makance sai suka kara zame mata gwanin kyau” Sarham bai tanka ba don bacin ran bata masa lokaci da yake yi, yace
“in ka gama muje ko Malam Isa”. Yayi gaba ya bar shi yana masa dariyar shegantaka wai matuka zai dace da Kulu, don idan ta yi fushi haka fuskarta take komawa kamar balam-balam yadda ya koma dinnan”.
Sarham yayi masa banza. Ya budewa Malam Isa gaban mota ya shiga ya rufe ya zagaya shima ya shiga, Sarham ya wani irin juya sityarin a guje da hannu daya saura kadan hular Malam Isa ta fado, da haka ya bar kofar Na’isa, suka hau titi sambal.
Malam Isa da yaji sanyin AC ta ratsa shi sai ya hau sakin zance ba kai ba gindi, ya ce “na so hada Kulu da Sunusi, tun tana yarinya, na gayawa Malam Bilyaminu kuduri na, sai cewa yayi “shi yafi so ‘yar sa Kulu ta je makaranta, baya son auren wurin nan da muke yi wa yara, ka ga yanzu da ya barta ta auri Sunusi, da ta tara yara sun kai biyar, don bana tantama Innar ta ma irin sa ce shiyasa suke zaune lafiya baka taba jin kansu, su dai makaranta-makaranta kamar goyon Mungu Park, don har bayan data makance wallahi mutanen nan basu raba ta da boko ba, haka muka ga sun samar mata dan jagora kullum sai ta je, ban taba ganin masifar son boko irin na Innar Kulu ba, bayan ita ko a zaure bata taba zama da sunan karatun bokon ba”.
Sarham ya juya kan mota cikin kwarewar tuki suka shiga tashar Kano line, ko tanka masa bai yi ba yana mamakin surutu maras ma’ana irin na Malam Isa, fadi ba’a tambaye ka ba, da alama bashi da matsala a rayuwarsa sai ta saida itacen sa.
Malam isa ya wuce gaba kuma har zuwa lokacin bakin sa bai yi shiru ba, yana gaya masa shi ya san dama Innar Hauwa bazata zauna babu sana’a ba, musamman ta abinci, don aljanunta na girki da tsaftane. In ta fara girki duk gidan sa sai miyau ya tsinkewa kowa, saboda kamshin girkin ta, yanzu ma ashe shiyasa ta zabi sana’ar abinci, Malam Isa ya kara da cewa Sarham,
“to Allah yasa ba’a tashar suke kwana ba, ko don ‘yar makauniyar nan Hauwa-Kulu, kada mazan tasha su dinga yi mata dan kira”.
“A’uzubillah!”
Sarham ya fada a zuciyar sa, lokacin sun kawo kofar rumfar abincin Inna mata biyu da dattijuwa daya suna ta kula da kwastomomi daya na zuba abincin in anzo saya, sukayi musu sallama, suka amsa suna tambayar su “me za’a zuba musu?” Kai tsaye Malam Isa ya ce nawa kwanon shinkafa da wake da miya da nama?
Sarham yayi masa kallon takaici ya ce “Malam Isa abinda ya kawo mu kenan?” ya ce “au, yi hakuri na manta ne, ‘yammata Innar Hauwa-Kulu muke nema”.
Dattijuwar mai zuzzuba abinci ce ta basu amsa. “Ayyah ai Innar Hauwa jiki ya ki dadi, yau wata guda kenan bata zo shagon nan ba, na ji ance ma bata gari, wani makwabcin su ya kai ta gidan mai maganin gargajiya na ‘ciwon zuciya’, a can wani kauye wai Albasu, don Innar Hauwa sam-sam ta ki zaman asibiti.
Allah ne yayi Innar Hauwa na da nisan kwana da yanzu wani zancen ake akan jinyar ta ba wannan ba”.
Sarham yace cikin yanayina gigicewa “na roke ki da Allah da Manzon sa ki raka ni gidan nata yanzunnan”.
Numfashin sa har gwamuwa yake tsabar yadda ya saka Innar da son ganin su a ransa, dama tace watakila bazasu kara ganawa ba, watakila sallamar su kenan, Allah ya gani yayi duk iya kokarin sa a kan ya san halin da suke ciki a wancan zuwan nasa Allah bai yi sun hadu ba.
Matar ta sallami kwastomomi sannan ta baiwa ‘yammatan sallahun abinda zasu yi mata kan ta dawo, daga nan ta bi bayan Sarham da Malam Isa zuwa mota.
Suna tafe tana basu labarin ai Innar Hauwa ta dade a kwance, watakila tayi shekara tana jinya, shagon ma yanzu ya zama nata.
Don dama haya muke kamawa, a da ina mata aiki ne da ta kwanta ta bar sana’ar sai nikuma na kama rumfar hayar, ba don ‘yar ta makauniyar nan mai kokari ba da tuni Innar Hauwa babu, da tuni ta kashe kanta da ciwo a gida, don bata son maganin asibiti.
Sarham ko magana ya kasa, yana jin ta ita da Malam Isa suna ta maganar kin asibiti irin na Innar Hauwa, yace ai tun sanin da yayi mata a haka take da akidarta ta amanna da maganin gargajiya.
Malam Isa yace “kuma fa akan kin asibiti ne har idon Hauwa ya mutu da hakiya, ni nan ba yadda ban yi da ita ba akan ta kai ta asibiti tun yana apolon sa, sai da ta ga ‘yar ta gama makancewa sannan ta kaita, a lokacin aka ce ido ya mutu, yadda suka je haka suka dawo.
Matar na nunawa Sarham hanya har suka isa wani dan mitsitsin gida a wata unguwa can ciki, kamar duk rabin unguwar kwatami ne, kasancewar unguwa ce ta masu karamin karfi sosai. Amma gidan nata sai suka same shi a kulle.
Sarham kamar ya dora hannu aka yayi kuka, don matuka ya saka ran sa da ganin Innar Hauwa da Hauwa a yau ba sai gobe ba, koma musu yayi kamar sabon kamun hauka, don cewa yayi da matar ba inda zai bari ta je sai ta hada shi da Innar Hauwa, ta ce itafa bata san gidan mai maganin da aka kaita ba, sai yace to su kai shi gun makwabcin nata da ya kai ta Albasu ne koma ina ne, in ba haka ba itada makwabcin na Inna zai yi karar su ga hukuma kan cewa sun batar da bayin Allah.
“Yau nake ganin abun da ya gagari Kakata” in ji Tafada mai Tuwo, daga abun arziki zaka daura min jakar tsaba kaji su bi ni, ni fa tsakanina da Innar Hauwa mutunci ne kawai, Allah ya gani ko a kwanciyar nan da tayi sau biyu ina taya Hauwa kinkimar ta ta kai ta asibitin Kuroda amma bata yarda ta kwana, yadda kake tunanin mu muka batar da su, to akan me? Daga zaman amana???”
Malam Isa ya lallashi Tafada yace, “kada ki damu ba kya ganin a fusace yake? Ina ne gidan makwabcin nasu?” Ta nuna gidan dake jikin na Innar.
Aka yiwa makwabcin su Inna sallama ta hanyar tura yaro cikin gidan sai gashi ya fito, suka gaggaisa da Malam Isa yace “Tafada ya akayi? Tace ga masu neman makociyarka nan, har suna neman kala mana sharri wai mun batar da ita”. Malam Sani Albasu yayi dariya yace, “Innar Hauwa mai jama’a, ho! Tana can kauyen mu gidan Malam Bagobiri mai maganin gargajiya na Albasu, in kuka je Albasu duk wanda kuka tambaya gidan Malam Bagobiri ya sani, ko daga tashar Albasu ne kukayi tambaya za’a kai ku har gidan sa”.
Sarham yace “me zai hana ka daure ka rakamu kawai, ina ganin zaifi sauki, tunda kai ka kai ta?
Malam Sanin ya yarda zai rakasu har Albasu, Amma yace saidai su dawo gobe yanzu yamma tayi.
Sarham, Wanda hakurin sa ya tuke a lokacin sai yace da Malam Isa su je kawai su yi tambayar har su samu gidan. Malam Isa ya yarda don yaga damuwar sa karara, ya yarda cewa wannan bawan Allah Sarham, da gaske ya damu da Innar Hauwa Allah kadai ya san tsakanin su.
Musamman filin gidan su da ya saye dinnan ya hau ginewa, duk da bai yi masa wani bayani ba ya fahimci yana da niyyar sake mayar musu da gidan su ne. Wanda baya ko tantama kulafucin ta da gidan, da unguwar bakidaya, da mutanen ta na arziki da aka raba ta dasu rana daya, sannan da makancewar tilon diyar ta rana daya, da kuma damuwar batan mijin ta Malam Bilyaminu dare daya, su suka taru suka haifar mata da kamuwa da ciwon zuciyar da ake cewa tana fama da shi a yanzu.
Malam Isa ya tuna Innar Hauwa yanzu mijin ta ya fi Shekara biyar da bata, me zai hana ta yarda tayi GAIBA in ya so shi ya aure ta ya rike mata ‘yar ta guda daya ya killace su a gidan sa su daina rayuwar sayarda abinci a Tasha?
Shi kadai yake wannan tunanin na babu gaira babu dalili har suka isa Albasu.
Malam Isa ya tafi tunani bai san har sun shiga garin Albasu ba, sai da Sarham yayi masa magana yace “gamu cikin Albasu” suka tsayar da motar a gefen titi Malam Isa ya tambayi wani mai Amalanke ko ina ne gidan Malam Bagobiri mai maganin gargajiya?”
Mai Amalanke yace “kun baro gida can farkon shigowa gari, ku koma da baya ku tambaya” Sarham yace “in dai ka san gidan shigo ka kai mu, zan baka kudin Babur ka dawo”.
Hakan kuwa aka yi, mai amalanke ya shiga bayan motar yana nuna musu hanya har kofar gidan malamin.
Wato abun babu kyawun gani, Yaa Subhanallah! Marassa lafiya ne rututu a zube a kasa tun daga zaure, cutututuka iri daban daban masu tasa tsigar jiki. Sarham sai da ya dauke numfashin sa na lokaci mai tsaho sabida kazantar gidan da cunkoson marassa lafiya. Tausayi da haushin Inna ya kama shi, wato har yanzu tana nan da halin ta na rashin yarda da asibiti kamar bai isa ace ta dau darasi tun akan Hauwa ba?
Ganin cewa jinin sa na neman hawa, sai ya umarci Malam Isa ya yi musu sallama da malamin, aka ce ai sai sun hau dogon layin ganin sa yanzu kuma dare yayi, saidai su dawo gobe da safe.
Malam Isa yace da Tafada “shiga kawai ki fito mana dasu, ya gansu hankalinsa ya kwanta, don ni kam ban iya kwana garin nan”.
Tafada ta shiga gidan da sallama, wani ikon Allah da Hauwa ta fara tozali, wadda ke bakin kofar dakin da Inna ke kwance, Hauwan kuma nan da nan ta dauki muryar ta, ta kira sunan ta da ‘yar dusassar murya.
“Tafada, kamar muryar Tafada nake ji”.
Tafada ta isa ga Hauwa da sauri, wadda tayi kozai kozai tayi zuru-zuru, rabon ta da wanka yau kwana bakwai, wato tun kawo su da Malam Sani yayi kauyen nan ya tafi, ya kuma karbe duk ‘yan kudaden hannun su da sunan yana biyan mai magani, amma kullum jiya I yau, babu wani sauki a tare da Inna sai na Allah. Yau kam wuni tayi tana suma babu wanda ya tsaya a kanta sai Hauwar da ba gani take ba, itama an gaya mata dai uwarta na suma.
Don haka yau Hauwa ta wuni kuka wurjanjan har ta gode Allah, idan ta rasa Inna, bata san yaya zata cigaba da rayuwa ba.
Tafada ta gaisa da mutanen data gani a zazzaune kafin ta kama Hauwa ta ce “nice Tafada, ina Innar taki wani ke ta son ganin ta tun daga Kano ya sako mu a gaba saida muka kawo shi nan, kamar dai dan uwanku ne”. Babu wanda ya zo wa Hauwa a rai da zai biyo bayan su har nan, cikin ‘yan uwan su duka sai Yaya Jamilu! Watakila yayi ta tambaya ne a kansu har ya gano inda suke.
Tafada tayi mata jagora suka fito, a yadda Hauwa ta lalace ba don yayi mata farin sani ba da bazai gane ita ce ba, sabida yadda tayi baki ta kuma rame, Sarham ya runtse idon sa cikin tausayi marar misali, muryarsa na shakewa da sarkewa yace.
“MAI-JID-DAH!”.
Sai tayi sak! Da rai da kwakwalwarta cikin son tuno inda ta san sassanyar muryar, da kuma inda ta taba jin an kira ta da wannan kebantaccen sunan. Duk fadin duniya mutum daya ne ya taba kiran ta da “Maijiddah”, ya kuma ce sunan nashi ne shi kadai, bai yarda kowa ya kwaikwaya ya kira ta da shi ba wato LIKITA SARHAM!!!
Hauwa-Kulu ta yi shiru na wucin gadi, kwakwalwarta na faman processing tattausar muryar data kira sunanta. Muryar Likita Sarham ce tabbas, wadda ko mutuwa tayi ta dawo bazata manta ‘accent’ dinta ba. Wani kwayan mutum guda daya da komai nisan shekaru bazata taba mantawa da shi ba, saboda kyakkyawar rawar da ya taka cikin rayuwar ta da gudunmuwar da ya basu, a lokacin da rayuwarta gabadaya ta dauko nakashewa. Duk da a cewar Hauwa, shi Sarham din shi ya karasa mata idanu, wato shi ya karasa makantata, amma bayan faruwar hakan ya kyautatawa rayuwar su, ya kuma taimaka ya hana rayuwar ta karasa rugujewa, ya karfafa mata da cewa kada ta bari ta durkushe a dalilin makanta.
Rawar da Dr. Sarham Abbas Shanono ya taka cikin rayuwar su, duk da cewa ta dan lokaci ce, to fa hakika mai girma da muhimmanci ce domin ya nuna musu kauna da mutunci na masu ilmi. Da wuya ka samu mutum irin sa a wannan zamanin da yake yiwa talakawa da yafi matsayi da ajin rayuwa kamar su daukar mutane. Balle don wani tsautsayi ya faru a dalilin aikinsu su tsaya su yi waiwaye a kai. Ta tabbata da ace bai tafi inda ya tafi ba, da ba’a kawo wannan matakin ba a lafiyar Inna, da karatun ta, da komai ma na rayuwar su, ta tabbata zai cigaba ne da tsayawa rayuwar su kamar Baba da Zulkiflu na raye. Da bazai bari Zakari ya tozarta rayuwar su ba ya raba su da farin cikin su.
Bata yi masa farin sani ba, saboda ko sanda yake tare da su kullace take da shi, bata tsaya ta saki jiki dashi ba, balle ta saba da shi, ko tayi masa kyakkyawan sani, amma ko daga sanin nesa nesa din data yi masa a gidan su ta shaida cewa shi din mutumin kirki ne, mai taimako ne, mai yawan alkhairi ne, ya san (human dignity), kuma yana matukar kaunar su sosai.
Sai hawaye ya soma zubo mata, don ji tayi ma kamar BABANTA MALAM BILYAMINU YA DAWO! Tamkar wani ‘SAVIOUR’ (mai ceto) ya iso cikin rayuwar su, koko tace kamar wani Mala’ikan rahma ya riske su, a lokacin da Inna ke kan gargarar mutuwa cikin rashin gata, kuma a lokacin data fidda rai da tashin Inna.
A can cikin kunne da kwakwalwarta, Hauwa ta tsinkayi muryar nan ta Dr. Sarham mai sanyi da gardi tana tsokanarta, zolaya irin wadda baya rabo da ita, kuma ya saba yi mata don ya samu ta kula shi. Aka ce a bar hali a ci me? Dr. Sarham har yanzu yana nan da (jovial personality) din sa. Hausawa suka ce in ka shekara baka ga mutum ba, ranar da kuka hadu, tambaye shi wani abun daban amma banda halin sa.
Wato a nufin bahaushe halin mutum baya taba canzawa sai dai ko mu ce Sarham ya rage wasu daga cikin halayen sa na sakin fuska, da yawan magana, a dalilin girma da nauyin iyali da yanzu ya hau kan sa.
“A yi magana ki ce an yi miki “GORIN IDO”, dubi kwala-kwalan idanun nata a jike jagab, jawur dasu, kamar kosan da ya soyu a cikin mai don kuka, maimakon ta saki far’a tace “Jabbama-jabbama…lale-maraba da bakon KANO. Ko tace YAYA SARHAM SANNU DA ZUWA”.
A’ah ta tsaya tana mana ambaliyar hawaye, watakila anan garin nasu na Albasu, da haka ake saukar bako”.
Sarham ya fada cikin zolayar Hauwa-Kulu, don rabata da hawayen dake ta satatar mata, da kokarin sa na hadiye nasa hawayen. Ba kankanin abu ke sa shi kuka ba, amma a yau ya san in bai yi da gaske ba ‘he cannot control his tears’ a gaban Hauwa, abinda bazai so hakan ba ko kadan. Kokarin gaske yayi da ya iya hadiye hawayen sa a kan idon Hauwa, wadda yake ma kallon kanwa ta jini, kamar Sumayyah, yadda ba zai iya bari Sumayyah ta ga raunin sa ba, haka ba zai bari Hauwa ta gani ba, ba don haka ba da tuni ya sake su sun shatato shima akan kundukukinsa, kamar yadda Hauwan ke faman yin nata, amma fa ita nata na farin ciki ne.
Ganin yanayin wahala da rashin lafiya da ya same su ciki kuma a kauye ya karya zuciyar sa, wanda ba cikin sa ya tafi ya barsu ba.
Cikin muryar kuka Hauwa ta ja sheshsheka ta ce “Likita sannu da zuwa”, tana mai yi ma saitin da muryarsa ke fitowa kallon ga ZULKIFLU YA DAWO.
Sarham ya matso gaban ta har tana iya shako kamshin hamshakin turaren sa na ‘Oud Abyad’ ya ce “to ko ke fa Maijiddah! Amma kawai daga ganin mutane sai ki balle da bokitin hawaye? Ai sai su Malam Isa da Tafada su dauka baki yi maraba da zuwa na ba sam”.
Tayi murmmushi, har kuncinta ya lotsa ciki sosai, wani abu da ke kara ma Hauwa’u kyau, yace “maza je ki kwaso kayan ku, Inna Tafada taimaka min ki dauko Inna don Allah a sa min ita a bayan mota, in yi maza in kaita asibiti, a kula min da ita da kyau”. A yau yana dakacen inama shi ba likitan ido bane, na zuciya ne! So that ya iya duba Innarsa da kansa”.
Hawayen dadi ya sake kecewa Hauwa, don ita ai tayi-tayi Inna ta yarda ta zauna a asibitin Murtala a cigaba da dubata ta ki, tace in mutuwa ce ta isko ta, a barta ta mutu a cikin dakin ta yafi mata, ta fi so ta mutu a gida akan gadon asibiti, kada taje a kai gawarta mutuware a ajiye a firinji, a kuma jinkirta yi mata janaza.
Kuma ita har gobe bata yarda da maganin asibiti ba, don bata ga ranar da ya yiwa idanun Kulu ba, aikin Kulu yasa ta kara nesanta kanta da asibiti, dama dole ce ta kaita a kan Hauwa dinma, shi yasa tunda ta fara ciwon nan suke dambarwa ita da Hauwa akan zuwa asibiti, daga bisani Hauwa ta dauko shatar mota tace mata zasu je asibitin Kuroda a bata magani kadai su dawo, da suka je asibitin, kallo daya likita yayi mata yace kwanciya zasu bata.
Hauwa bata ankara ba sai ji tayi Inna ta tashi tsaye tace ta tashi su tafi, data tsaya yi mata magiya da gardama kan ta tsaya sai Inna ta kamo hanya abinta, ta kyale Hauwa a tebirin likita, dole Hauwa ta taso ta biyo bayan ta tana kira. Tausayi yasa ta dakata ta kama hannun ta, a lokacin suka taho gida.
Hauwa bata daddara ba, washegari tayi ta rokon ta kan su je asibitin Murtala, ta tabbatar mata su bazasu kwantar da ita ba, da kyar da nacin kukan Hauwa Inna ta yarda suka je Murtala, nan suka hau layi har suka samu ganin likita, anan ne likita ya yiwa Hauwa bayanin dole Inna ta kwanta ayi mata aiki a zuciya, domin ta samu rami (hole) a zuciyarta. Ai jin haka Inna ta mike ta fice ta bar Hauwa da likita suna kiranta (again), Hauwa ta biyo bayan ta tana kuka da roko, sai Inna ta dakata da tafiya tace da Hauwa.
“Idan kin manta haka aka ce min za’ayi miki aikin ido ki warke daga hakiya, amma kin warke din?
To ni yanzu in aka yanka min zuciya kina da tabbacin zan mike?
Ba tsoron mutuwa na ke ba domin kuwa a shekaru hamsin me nake jira banda neman hanyar dacewa da cikawa da Imani?
Ke nake ji Hauwa-Kulu, in babu ni, rayuwar ki zata shiga wani hali na garari da walagigi har da da bara akan titi, don baki da mataimaki da mai yi miki jagora bata idanu kadai ba harma da rayuwar ki gabadaya, sai Allah da ya halicce ki”.
Abinda Inna bata sani ba, ko babu ita Innar, ita HAUWA-KULU (modern makauniya ce), bata bukatar dan jagora don zuwa wani waje, kanta tsaye take zuwa ko’ina, iyakaci kai in ka fahimci bata gani kai ka kauce mata, wata irin brainlliant ce mai kaifin kwakwalwa da kaifin basira, gata da ji mai karfi irin na wadanda suka rasa idanun su da kuruciyar su Allah ya bata. Don dai UWA-UWA ce amfaninta yafi ga haka, wato ya wuce ta rayu don ta yi mata dan jagora, sai dai don ta zama GARKUWAR ta a rayuwa bakidaya kuma cikon farin-cikinta ta.
Tun daga ranar bata kara yarda Hauwa ta ja ta asibiti ba, tayi ta kwanciya a gida suna cinye dan jarin nasu a sayen abinci kullum, tunda ba juyawa ake ba yanzu kashewa ake yi yasa kullum daurin kudin su sai kasa yake yi, kafin makwabcinta Malam Sani mai irin ra’ayin ta kan traditional medicine ya ce da gaskiyar ta, tazo ya kaita gidan mai magani inda zata samu magani na kowacce cuta ba tareda an tsaga kirjin ta ba.
Aka fito da Inna daga cikin gidan ranga-ranga da daurin kayan su a bakko, aka sa a bayan motar Sarham, Tafada da Hauwa suka shiga, suka sa Innar a tsakiyar su, wadda bata san ma ko su waye a kan ta ba lokacin. Rabin jikin ta na kwance jikin Hauwa. Malam Isa na gidan gaba Sarham ya ja motar cikin nutsuwa da hanzari suka hau titin da zai maida su cikin birnin Kano.
Suna tafe a hanya suka fahimci Inna ta farfado daga suman data yi, suka yi ta yi mata sannu da jiki. Malam Isa nata yiwa Inna fada da dacin rai, na yadda ta shiga duniya ta bar makwabtan ta masu kaunar ta, wai ace yanzu ta gwammace rayuwar sayar da abinci a tasha a kan zaman gidan sa, yace to yanzu me kika tsinto a tashar duk sana’ar taki ban ga kinyi arziki ba, ban ga kinyi kiba ba, na gan ki tsiya-tsiya rakace-rakace wutsiya a zage cikin ciwo.
Rayuwa bata raggo bace. Haka azzaluman mutane ba’a kyale su su cigaba da aikata zalinci son ransu ga marassa karfi a doron kasa musamman mata da kananan yara kamar Kulu.
Da kin zauna mun tashi tsaye mun hada karfi da karfe mun kwato miki hakkin ki, yadda makwabtanki suka fusata a lokacin da kin tsaya, in yafi karfin ki ai bai fi karfin shari’ah da Alkali ba, cewa fa mukayi ki tsaya zuwa wayewar gari mu shigar da kararsa maimakon mu dau Shari’ah a hannunmu.
Kuma ni da kin zauna kin yi gaiba, na rufa miki asiri na killace ki a gidana karkashin inuwar aure in taya ki kula da ‘yar makauniyar ‘yar ki, amma ina! Ke ga ki kububuwa sarkin masu zuciyar duniya, kika dauki ‘ya ba ido kika bar BADALA!”
Sarham ya rage gudun motar sa a dokar daji, a fusace yace “wallahi Malam Isa in baka yi mata shiru ba zan cillar da kai a dajin nan in ja mota ta, da me kake so ta ji? Da ciwon jikin ta ko da hayaniyar ka?”
Daga haka aka samu Malam Isa yayi shiru, bai kara magana ba har suka isa asibitin Malam Aminu kano.
Tun kafin su iso dama Sarham yayi waya da Dr. Babangida, wani babban likitan zuciya ne (cardiologist) abokin karatun sa a Jiddah da ya dawo yake aiki a nan AKTH, shi yasa aka karbi Inna cikin kulawa daga shigar su asibitin, aka yi imajensi da ita. Kuma da taimakon sanayyar sa da Dr. Babangida yasa ta samu attention din likitoci da yawa suka rufu akan ta, don binciken hakikanin abinda ke damunta.
Sai da suka kwana suka wuni a A&E ana bata taimakon gaggawa kafin a basu daki a kwantar da Inna, amma da Sarham ya zo asibitin a washegari sai yace a maidata dakin ‘Amenity’ ya kuma biya komai aka maida Hauwa da Inna kebantaccen daki wato ‘Amenity’ a sashen mata.
A kwana uku sakamakon gwaje-gwajen da likitoci suka yi wa Inna ya fito, da gaske tana da huda a zuciyar ta, wadda ke bukatar sai an yi mata aiki an cike ramin da zuciyar tayi. Madinah na can gidan kakannin ta tana jego, Sarham na jelen asibiti dasu Inna daga nasu gidan yake zuwa shi yasa bata san me yake ciki ba, sai dai duk sanda ta kira shi a waya zai ce mata yana asibitin Aminu Kano yana da ‘patient’ yana ‘busy’, ta kuma san shi sosai da Dr. Babangida shiyasa ta daga masa kafa, yau kwana uku bai zo Soron dinki ba balle ya ga Baby Hauwa da take kira (Waheedah) tun ranar sunanta.
Kowa ya dauka saboda Haj. Kulu Sarham ya sakawa ‘yar sa suna Hauwa, shi kuwa zai iya rantsuwa ya saka sunan ne don ya dinga tunawa da Inna da Hauwa a lokacin da ya neme su ya rasa.
Hatta a gida sun gane yana zirga zirga, kuma ba a wajen masu jegon ba, ko jiya ya saka Surayyah girki na hanta da koda da ‘vegetables’ da kunun gyada yace ta zuba masa madarar ruwa a ciki, Surayyah ta dauka shi zai ci, bayan ta gama ta gaya masa ta gama, sai yace ta shirya a basket ta kai masa mota, Mama ta bi Surayyah daki bayan fitar sa tana tambayarta ko wa Sarham zai kaiwa abinci? Surayya tace bata sani ba, yace dai yana da mara lafiya a asibiti ne.
Mama tayi wani dan tunani sai ta ce “in kika bibiya bazai wuce mutanen sa na Badala ya gano ba. sune kadai zai dauka da muhimmanci irin haka ya kasa nutsuwa in suna cikin matsala”.
Surayyah ta ce cikin mamaki “ba sun bar Kano ba? Ba sun bace masa ba tuntuni?” Mama tayi dariya tace “ko a ina suke in dai a fadin Najeriya ne na tabbatar miki sai Sarham ya nemo su, ki bar Sarham akan abinda yasa kan sa, ko yake kuma kauna da son taimakawa da zuciya daya”.
Surayyah ta kwana abun yana bata mata rai, na yadda ta zage ta shirya masa abincin nan da kyau, don ita bata son zancen su ma, yadda aka sakata girkin wahalar wasu kauyawa wai su su Innar Hauwa, tarkacen BADALA, don haka washegari da ya saka ta girkin again tayi maza ta ce kanta na ciwo bazata iya ba, dole sai Nancy sabuwar mai aikin Mama ya saka tayi masa ‘potatoe porridge’ da yaji ganyen alayyahu. Da dafaffen kwai.
Ita Hauwan ma da ake kaiwa garar abincin mai dan gina jiki, don a samu ta murmure ta tada komada daga muguwar ramar data yi da mokadewar da kashin wuyan ta yayi a Albasu, sam bata iya ci, bakin ta ya kasa karbar dandanon abincin don bata saba da cin mai lafiya da dadin dandano irin sa ba.
Ruwan bunu (lipton) ko na Milo kawai take iya zubawa a cikin ta ya zauna da dadin rai, ta zama kamar ka bushe ta ta fadi don kamar ma bata da lafiya, nan kuwa yunwa ce kawai ta zaman Albasu ta zauna a jikinta tayi mata illah. Abu daya ke faranta mata in ta tuna Inna na bisa karkashin kyakkyawar kulawar asibiti yanzu, kuma ana tabbatar mata da tana jin sauki kasancewar idonta a rufe yake kuma kullum ana mata karin ruwa kafin ranar da za’a yi mata aiki tazo.
Sarham ya biya komai ranar aikin, ya kuma saka hannu aka yiwa Inna aikin zuciya. Aka yi lafiya cikin nasara ba kamar yadda Inna ke tsoro ba.
A lokacin ne ya samu ya koma cikin hayyacin sa tun daga ranar da ya dauko su Inna sai yau ya samu nutsuwa, bayan an gama aikin an kai ta dakin hutu, inda Hauwa ta cigaba da jiran farfadowar ta.
Sai ranar ya samu ya leka su Baby Hauwa. Madinah bata iya fushi da Sarham ba, ko me yayi mata kuwa, komai girman laifin, amma yau a kwayar idonta ya gane tayi fushin, musamman da yaga tana ‘avoiding eye contact’ da shi, ya san tayi fushi mai ban mamaki ko bata furta ba.
Ya sa hannu ya dauki Hauwa cikin dan kyakkyawan gadon ta tana barci, ya zauna dab da Madinah yace “Likita matar Likita barka da yau, ya kuka kwana? Ya kukan daren uwar bil’adama?” Madina ta amsa fuska ba yabo ba fallasa, sai yace “ba sai an gaya min ba, na san nayi laifi wa GIWAR SARHAM, kuma na karbe shi tun ba’a bani ba (laifin), tun kwanaki uku baya ma fa ya kamata ace na koma Jeddah, amma inada uzurin da ya rike ni mai muhimmanci, kiyi hakuri kin ji Madindin din Sarham! Madinatul-Munawwarah my shelter, my eternal happiness, my home peace, my safety and my security, in sha Allahu nama fasa komawa, sai kin gama wankan jegon ki sai mu koma tare, zan yi amfani da lokacin (as annual leave) dina”.
Amma har ga Allah ya fasa komawa ne saboda lafiyar Inna, yana kuma son daukan ‘measures’ din da ya dace akan rayuwar su Inna kafin ya koma Jeddah.
Madinah da bata iya dogon fushi da Sarham ba jimawa ta yarda da uzurin sa ta kuma saki rai suka shiga hirar arziki da hirar soyayyar su da bata kodewa, suna yi suna kallon kyakkyawar fuskar ‘yar su Hauwa (Waheedah) wadda suka saka a tsakiyar su tana barci da sauke numfashi cikin koshin lafiya.
A lokacin Madinah da Sarham suka hau musu akan wanda Hauwa tafi kama dashi, shi yace da shi take kama completely, ita tace kalar su da gashin su ne kawai iri daya amma fuskar da yatsun, duk nata ne.
Madinah a idon sa kadai ta fahimci ya jima bai ci abinci ba, amma da yake a dabi’ar shi baya dorawa matar sa nauyin ta tashi tayi masa girki a duk sanda yake so, sai bai mata complain ba, ita da kanta da yake ta san kan kayanta, ta gane sosai yake cikin gajiya da yunwa, don tun haduwar sa dasu Inna bai samu nutsuwar cin kyakkyawan abinci ba sam, don haka ta tashi ta hado masa abinci mai rai da motsi, sai da yaci ya koshi suka gaisa da Kakarta Haj. Lailah, wadda ke falo, sannan yayi musu sallama ya wuce asibiti don ya tadda su Hauwa ya ga farfadowar Inna, don haka daga nan Soron dinki can ya nufa.
Saida ya tsaya a hanya ya yi musu sayayya sosai kamar yadda ya saba duk da ya lura Hauwa bata iya ci, yau sai ya saya mata fresh milk da yawa (unsweetened) kafin ya wuce aibitin. Da sallama ya murda kofar ya shiga dakin, bayan Inna tayi masa iznin shigowa, amma Hauwa a ciki ta amsa masa kamar yadda ta saba amsa sallamarsa tun fil azal, ya tadda su tare da Malam Isa ya zo dubata shi da dan gidan Inna wato Saleleh.
Malam Isa har gidan su Salele ya je ya gaya musu an ga Innar Hauwa, shine fa Salele ya biyo shi. Inna ta dubi Sarham tana daga zaune jikin filo. Ba don ba karamin sani tayi masa ba da bata gane shi ba, don ya canza gabadaya daga yadda ta san shi, dan siririn saurayin likitan nan na Murtala, ya girma ya kara cika ido cikin shekaru kalilan, ilmi da kwarjinin addini sun kara bayyanar da cikar zatin sa. Tayi murmushi a hankali, ta ce.
“Inda rai da rabo, likita Sarhamu! Ashe Allah yayi zamu gana?”
Sarham ya ja kujera a gaban ta ya zauna, yana kallon Hauwa tana shafa hoda irin mai like da mudubinnan a jikinta, saura kadan ya fashe da dariya, kasa amsawa Inna maganar data yi yayi saboda dariya dake cinsa, ya nuna wa Inna ita da baki, itama tayi dariya, tace “kuma ayi magana cibi ya zama kari ba!”.
Malam Isa ya juyo garesu yace “dariyar me kuke haka?” Inna tace “kai dai abar kaza cikin gashin ta, daga jiya zuwa yau na kirga shiga wankan ta ya kai goma! Wai biyan bashin wankan kwana bakwai da bata yi ba a kauyen Albasu take yi yanzu, tunda ta samu ruwan dumi da sabulu mai kamshi ai shikenan, har da yi wa Malam Sani Allah ya isa da yayi mata sanadin komawa zaman kauye”. Sarham yayi dariyarsa mai isarsa, har da sunkuyawa da rike ciki, sai lokacin Hauwa ta gane da ita suke.
Ta dan dakata da shafa hodar, duk ta sha jinin jikinta, ga mudubin a hannun ta, kai sai ka rantse tana ganin fuskar ta cikin mudubin, jin sun kara ninka dariyar ta ji haushi, ta mike ta fita daga dakin sai Sarham ya mike ya bi bayan ta don ya bata hakuri.
A jikin barandar dakunan ya same ta a tsaye fuskar ta ta hade kamar kunun kanwa. Tana tsaye kawai harde da hannuwa a kirji. Ya lallaba ya tsaya dab da ita shima ya harde nasa hannuwan a kirji irin yadda ta yi. Ya ce.
“Kuluwa, ni fa ba ke nake yiwa dariya ba, labarin da Inna ta ke bayarwa ne ya bani dariya”. Hauwa tayi narai-narai da idanu kiris ya rage ta fashe da kuka, tace “idan makanta abin dariya ce ai bata wuce kan kowa ba, idan gorin ido abun yi ne, ba komai ku cigaba da yi min”. Sarham ya kama baki cikin jin wani iri a ransa yace “kina nan a Kulun ki, Kululu, Kulun Majadun sarka mai rikicin gangan, har gobe baki canza ba, dama Inna ta ce ayi magana cibi ya zama kari. Yanzu saboda Allah ba dama muyi dariya sai ki ce rashin idon ki ake wa gori?
Idanun nan fa mun fi ki son su dawo, ta yaya zamu yi murna da halin larurar da suke ciki? Kawai dai kina ji da rikicinki ne na gangan.
Kullum addu’ar mu shine su dawo da gani kamar na kowa, idan masu dawowa ne, idan kuma ba masu dawowa bane Allah ya sa rashin su ya zama silar kaffara a gare ki da iyayen ki, ya baki aljannar Firdausi a madadinsu”.
Hauwa ta dan saki rai, sai Sarham yace, “Maijiddah, tunda muka hadu bamu gaisa ba, bamu zanta ba, bamu yi fadan namu ba, koda yake yau mun dan taba. Anyway, nayi kewar ki MAIJIDDAH, bayan a baya na zaci bazan taba yin kewar ki ba, tunda baki damu da ni ba”.
Hauwa ta yi murmushi ta ce a ranta,
“kwarai kuwa, don ni dai kam in ba na dauko littafin makaranta ba, sam-sam bana tuno ka, gara-garama a lokutan da kalamanka masu haska min rayuwa ke sawa in tunaka”.
Unfortunately, bata san cewa a fili ta fada ba.
Sai ji tayi Sarham yace cikin rashin jin dadi da sosuwar rai, “I know, ba tun yau ba na sani ai, Inna ce kawata, uwata, kuma ita ta damu dani. Ni din a wurinki ba kowa bane face…”.
Yayi shiru cikin tsananin damuwa da rashin sanin ta yaya zai yi ya kankare wannan tunanin daga zuciyar Hauwa-Kulu? Wanda ba tun yanzu ba ya lura yayi mugun samun muhalli a cikin ranta?
Hauwa tace “kaima da ita kadai ka damu (Innar), daga zuwan ka ai ko la’akari da halin dana ke ciki baka yi ba ka fara tsokanata a kauyen Albasu, wai idona kamar ana soya kosai cikin mai, baka san cewa kukan farin cikin ganin ka nake yi ba, baka san halin dana ke ciki ba a lokacin, don ji nayi kamar Yayana Zulkifilu ya dawo, kamar farin-cikin rayuwa gabadaya ya dawomin, duhun zuciya ya gushemin, haske ya dawo a cikinta”.
Da mamaki da jin dadi a muryarsa Sarham yace “to kiyi hakuri Maijidda, mu ajiye wannan a gefe, I’m happy to be your sourse of happiness, koda wannan kadai yau kin karramani, yanzu inaso ki bani labarin bayan rabo, da rayuwar ku gabadaya daga farkon tafiyata har ranar zuwan ku Albasu gidan mai magani”.
Hauwa ta nisa, kafin tace “dogon labari ne likita, amma mun sha wahala wajen neman na kan mu a tashoshin mota, mun yi girki iri-iri ba hutu tamkar injin girke-girke a kowacce rana daga safe har yamma hakarkarinmu bai hutawa, ba don komi ba sai domin kada mu yi bara. Allah ya sani, ba abinda nake gudu da nakasata irin bara! Alhamdulillah for being alive, and for everything, musamman karatuna na sakandire, wanda (against all odds) sai da Allah yasa na kammala shi.
A kullum inna sare da karatun, saboda wahalar zirga-zirga ta rashin idanu, kalaman ka nake tunawa suke zame min ‘inspiration’, kuma madubin dubawata a rayuwar lalurar dana tsinci kaina.
Kalaman ka likita sunyi tasiri sosai wajen karafafani domin ina matukar jin dadin su a lokutan da na bukacesu, cewa da ka yi “akwai iyawa cikin nakasa”, kuma ka ce min “ba nakasashshe sai kasashshe”. Wadannan jimlolin naka guda biyu su suka zame min food for thought; su suka sa na dage na jure da zuwa makaranta ba ido. ‘Obstacles’ da ‘hindrances’ da ke cikin lalurar makanta duka basu sa na bari ya salwanta ba.
Babu wani abin karaswa cikin labarin namu a bayan tafiyar ka, sai na bacin rai da wahala na zallan zalunci wanda kanin mahaifina ya sanya mu a ciki, a dalilin kwace gidan mu ya rusa shi. Ni ban sani ba ashe tun lokacin batan Baba, Inna ta fara ciwon zuciya, don likitan dazu ya tabbatar min ramin ya dade a zuciyar ta yayi akalla shekaru biyar, tana dai yin cuwuka a tsaitsaye tana kuma kula da shan magungunan gargajiya dake kara mata ‘immunity’, shiyasa bai ci karfin ta da wuri ba, bamu ankara ba sai da ya kayar da ita kasa warwas.
Likita rayuwar da muka yi gabadaya kaji-ka ji….” ta zayyano masa daga farko har karshe har labarin bugeta da Yaya Jamilu yayi da mota ya kuma dage daga baya zai aure ta, wanda duk shi ya janyo musu komai.
“Yanzu ina Jamilun? Me zai aura a wannan kankanuwar yarinyar? Bana jin lokacin ko SS2 kin gama, haba! This is sheer abuse. To ya san abinda Baban nasa yayi muku?”
Sarham ya tambayi Hauwa, (furious in anger), ji yake idon sa idon Jamilu da Babansa Zakari sai ya shake su. Hauwa ta ce.
“Yaya Jamilu ban kara haduwa da shi ba, bamu kara jin duriyar sa ba tun tafiyar sa Delta, kuma bana jin ya san abinda Baba Zakari ya yi wa gidan mu, saboda a lokacin yayi tafiya, ban dai sani ba ko idan ya dawo daga tafiyar da yayi wani ya bashi labari”.
Sarham ya dade kan sa a sunkuye, yana tunanin ta wace hanya zai gayawa Hauwa ya sake gine musu gidan su, da gini irin na zamani? Jira yake a sallami Inna daga asibiti ya dauke su ya maida su gidan su na asali, ya kuma yi karar Baba Zakari kan abinda yayi, ko ba’a yi masa komai ba hukuma ta shiga tsakanin sa da su”.
Sun dade a wajen suna labari shi da Hauwa, irin yadda bai taba jin tayi magana mai tsayin ta yau ba, sai da mamakin sa ya kasa boyuwa yace.
“Maijiddah, ashe dama kina magana haka? Da ni ne ba kya yi? To meyasa Maijidda? Me nayi miki haka da zafi?”
Ya tsareta da ido cikin tuhumar dalili, kai kace kamar tana ganin sa, Hauwa ta rufe ido cikin jin kunya, ta ce “ai don na dade ban ganka bane, daga yau zan rufe bakin ya koma kamar da” Sarham ya lumshe ido kamar tana ganin sa, idonsa a kan zara-zaran ‘yan yatsunta ya ce “a’ah ban yarda ba, a bude shi muyi ta shan hira abinmu, irin ta Yaya da kanwar sa da sukayi kewar juna, kin san ni mai baki ne, mai yawan hira ne, shiyasa tamu ta zo daya nida Inna. Maijiddah ina so in zama babban Yayanki daga yau, wanda kafin kowa ya ji damuwar ki nine mutum na farko da zan ji.
Zan bar miki waya don mu dinga magana don zan koma wajen aikina babu jimawa, na rako matata wankan jego ne, amma mun koma Jeddah da aiki tun da jimawa”.
Hauwa ta fiddo manyan idanun ta cikin mamaki ta ce “likita dama kana da mata?” Ya yi murmushi ya ce “mamakin na menene haka? Amsarki a baya itace, a’ah, na dai aure ta babu jimawa, bayan na kammala karatun dana tafi yi a Jeddah, a can muka hadu, duk da dai ba haduwar mu ta farko kenan ba”. Hauwa tace itama likitar ido ce?” Dr. Sarham Yayi dariya yace “exactly! Amma ya akayi kika sani?”.
Tace “na dade da sanin likitoci basa aure sai da liktoci ‘yan uwan su, watakila don kada a shafa musu cuta?” Sarham me zai yi ba dariya ba yace “wato shi likita bashi da cuta a jikinsa Maijidda?” Tace “da sauki dai” anan ma ta kara bashi dariya sosai, yace “ni kuwa da har na yi miki takwara, na dauka kema likitar zaki so zama?” Kafin Hauwa ta kara magana sai Malam Isa ya fito yana musu sallama zai wuce gida, tare da Salele.
Salele yaga Sarham, nan da nan ya shaida shi, ya hau yage baki don bai manta shi ba da tarin alherin da ya dinga yi masa don ya dinga raka Hauwa Makaranta.
Suka gaisa da Salele suka yi sallama da su suka wuce, shi da Hauwa suka koma wajen Inna. Hauwa na tambayar sa cikin mamaki.
“Da gaske likita ka yi min takwara da ‘yar ka?”
Zancen a kan kunnen Inna, ta dago tana kallon shi da mamaki itama, tace.
“Sarhamu kayi aure ne banida labari?”
Sarham ya sunkuyar da kai yana dan murmushi yace “eh Inna, har an samu karuwar Hauwa’u, HAUWA-KULU!”. Ya dauko wayar sa daga aljihun sa ya nunawa Inna hoton Waheedah cikin pink shawul daya dauketa dazu. A takaice ya basu labarin yin auren sa da Dr. Madinah bayan ya kammala karatun da ya kai shi Jeddah, da irin neman da yayi musu kamar ya zautu bayan dawowar sa.
A ranar ya jima tare da su suna ta labarin rayuwar su a kurna, rijiyar lemo da kuma unguwa uku, da ta karatun Hauwa da aka samu kammalawa da kyar, da sudin ludayi, ta gaya masa Hauwa ta fiddo da kyakykyawan sakamako sosai, wanda ba kokarin kowa bane nasa ne, madallah da shi, madallah da haihuwar ’ya’ya irin sa, masu zamewa al’umma fitilar rayuwa kuma bango abin jingina, madallah da tarbiyyar iyaye irin nasa, madallah da shigowarsa cikin rayuwar su”.
Sarham (feeling overwhelmed with joy and happiness) saboda ya sha addu’a yau a bakin Inna, ‘yar sa Hauwa ma ta sha addu’a, tace yadda ya tsayawa Hauwa-Kulu wadda a yanzu za’a kira maariniya miskiniya ta samu ilmi daidai gwargwado duk da makantar ido, Allah ya tsayawa tashi Hauwar ko bayan ransa, yasa tayi ilmin da zata zamo mai amfani ga al’ummar duniya.
Ita da kan ta Inna data nisa, taji yadda lafiya ta wadace ta, bata san sanda ta ce ta tuba tabi Allah ta bi asibiti ba! Daga yau ta daina kin asibiti tunda gashi ciwon shekara da shekaru ya tafi cikin sati biyu. Ta kara da cewa Sarham “ashe abin naku dace ne!”.
Sai bayan kwana uku da yin haka aka sallami Inna, Sarham ya zo da mota ya dauke su zuwa gidan su na unguwa uku yace “Inna koda abinda zaku dauka a gidan ku dauka, ku fito ina jiran ku” Inna tace “ai nan ne gidan mu likita, yanzu anan muke zaune tun da jimawa” ya ce “na sani Inna, zaku raka ni unguwa ne bazamu jima ba, amma dai in har kin yarda da ni, to ki kwaso komai naku”.
Inna ta hau kwasar kayan tana kaiwa boot din motar Sarham tana fadin “yarda da musulmi irin ka wajibi ne!”. Haka Hauwa ma, ta dauki kayan ta tsaf, suka kama hanya, Hauwa na gidan gaba Inna na baya. Sarham na tuki cikin nutsuwa da kwarewa, bai tsaya a ko’ina dasu ba, sai a kofar gidan su, gidansu na BADALAR Kofar Na’isa, dama sun riga sun shirya gidan dai dai gwargwado da taimakon Malam Isa da Salele. An zuba komai na amfani mai saukin kudi.
Inna tunda taga an doso kofar Na’isa ta soma hawayen tuna baya, kirjinta ya hau yin sama da kasa, ita ta dauka zai kaita ta gaisa dasu Maikosai ne.
Amma sai ta ga anyi fakin a kofar wani sabon gida a bayan Badala, in har bata yi kuskure ba, kuma idan har ba idon ta ke mata gizo ba nan din lungun su ne kuma unguwar su, da ko daga makanta irin ta Hauwa ta warke itama zata gane su, tunda ga gidan Malam Isa nan ba abinda ya canza shi.
Sai ta kalli Sarham a gigice, bayan ya kashe motar a kofar gidan. Sai a lokacin yayi musu bayani cewa gidan su ne ya karba musu.
“Ka karba mana kamar yaya?” Inji Hauwa, (sounding extremely puzzled). Inna kuma tace “ko dai ka gina mana?” Muryar Inna ta tambaye shi cikin kuka, don dai a kan idon ta taga lokacin da aka rushe gidan nasu wato gidan Malam Bilyaminu.
Sarham yace “Allah ne ya nufa gidanki ya dawo gare ki Inna, ni kawai na taimaka ne, kuma kiyi hakuri zan yi wani shishshigi, a gaskiya zan yi karar kanin Baban Hauwa akan abinda yayi”.
Inna ta fara kukan farin ciki da dariya a tare, ta ce “Dan nan me zan ce maka? Wace irin addu’a ya kamata in yi maka? Na rasa kalma a bakina da zata gode min kai.
Amma ka bar maganar Zakari, ni kam me zai sake hada hanyata da Zakari? Na roke ka ka rabu da shi Allah na kaiwa karar sa kuma na tabbata zai saka mini. Na bar shi da fitowar rana da faduwar ta”.
Ta share hawaye da habar mayafinta ta sake cewa. “Dan nan me zan ce maka?” A karshe Inna ta fashe da kuka tana ce da Hauwa “gidan mu ne Hauwa-Kulu! Sarhamu ya kwato mana da karfin mulkin Allah”.
Hauwa wani irin shock ta shiga na wucin gadi bayan fahimtar hakikanin halin da ake ciki. A yau ma dakacen nan ta kara yi na shekara da shekaru, mai fatan “INAMA TA GA FUSKAR LIKITA SARHAM!”
Suka karasa cikin gidan Inna rike da hannun Hauwa shikuma ya dauko bakko kayan su ya kai su har dakin da ya zama na Inna, an saka katifa a kasan kafet dirkekiya an shimfide ta da sabon zanin gado. A gefe ga kwabar saka kaya an yi mata. Haka dakin Hauwa ma amma ita a daki aka yi mata toilet don kada ta sha wahalar fitowa tsakar gida. Ga safayan daki da ba kowa yace na Baban Hauwa ne duk ranar da Allah ya dawo musu da shi. Sai kamshin sabon fenti da suminti gidan yake yi gwanin dadi.
Dakuna uku ne aka yi musu kamar da, kitchen kuwa da toilets na zamani aka yi masu masu tangaran (tiles) da Inna tayi ta shafawa da hannun ta a gaban Sarham tana shi masa albarka.
Hauwa duk jikin ta yayi sanyi musamman in ta tuna yadda ta ke share Sarham a baya, da kullacin wai ya makanta ta, Sarham is beyond her imagination a kaunar fisabilillah da yake yi musu.
Aka kai Hauwa nata dakin aka nuna mata direction na sallah dana zuwa toilet da madannin flushing. Ga dan karamin firji a gefen katifar ta (bed side fridge) Sarham ya ajiye mata don ya san ta da son shan abu mai sanyi tun baya, kai yau Inna da Hauwa farin cikin ya fi gaban ayi masa kuka ko dariya sai dai kawai ayi kurum, kamar yadda Hauwa tayi kurum!
Bayan sun gama zaga gidan sun zauna suna hira shi da Inna. Ya ce “wai ta yaya ma aka yi takardun gidan suka je hanun Zakari? Bayan kowa ya shaida ya sayarwa da malam Bilyaminu gidan kamar yadda Malam Isa ya bashi labari?”
Inna ta ce “umh, ai in kana neman hatsabibi ka samu Zakari ka gode Allah, maiyuwuwa yana da na kwarai dinne ya bawa Malam na jabu, ko kuma yasa an yi masa na jabu, oho, tunda har gobe na gonar su Baban Hauwa ya gayamin suna hannun sa, gab da batan Baban Hauwa, yace min sai ya karbi hakkin sa gun dan uwansa Zakari, wanda yake boyewa don a tunanin sa ya dauka Malam bai san da su ba.
Ina nufin gonar mahaifin su ta Panshekara wadda girman ta ya kai na naira miliyan daya”.
Sarham ya shiga mamaki mai yawa, ashe shiyasa Baban sa baya son sake aure? Kullum sai yace masa yana tsoron rarrabuwar kan su ne, shiyasa bai yi musu ‘yan uba ba.
Sun dade suna zantawa kamar Da da uwar sa, Hauwa kuwa tunda ta shige daki ta kwanta a sabuwar katifa bata kara fitowa ba don daga baya ma wani ni’imtaccen barci ne yayi awon gaba da ita, irin wanda rabon ta da shi tunda Inna ta fara kwanciya ciwo.
Da ya zo tafiya ne jin ta shiru ya dan leka dakinta, nan ya ganta tayi dai-dai tana kwasar barci da nutsuwa da kwanciyar hankali, numfashin ta yana hawa yana sauka freely, ashe tafi kyau in tana barci irin mutanen da ake kira sleeping beauty. Ya dan kalleta na ‘yan sakanni yana jin ta kamar Sumayyah a ran sa, ya kudurce a zuciyar sa zai tsayawa rayuwar ta, zai ingantata, zai mata abinda idan Sumayyah ce nakasar idanu ta sameta zai tsaya ya yi mata.
Daga nan gidan su ya koma, a falo ya tadda iyayen sa, kallo daya zaka yi wa Dr. Sarham yanzu ka tabbatar yana cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ba kamar watannin baya ba, gashi Madinah ta cika masa ciki da abinci mai dadi, so bai waiwayi abincin sa dake bisa tebir ba ya zauna gun Abba Prof. amma ya killace bakin sa baiyi zancen su Hauwa ba, don ya lura bat un yau ba Abban (is not interested) akan zancen su, musamman da ya ga ya dauki al’amarin su da muhimmancin da yake neman wuce kima, kuma ya tambayeshi meye alaqar su ta hakika ya tsaya yi masa kame-kame. Tun daga lokacin yace,
“to in babu wata kebantacciyar alaqa da musuluci ya yarda da ita, to ya cire damuwar rashin ganin su daga ran sa, ya bar su a hannun Ubangijin da ya halicce su, tunda uban su ma da ya bar su ai basu kasa rayuwa ba.
Don haka baima kowa zancen ya ga su Hauwa ba, bai sani ba tuni Mai Shari’ah wato Barrister (Mama) ta dade da ramfo shi.
Kafin kwana uku duk makwabta sun san da dawowar Hauwa da Innar ta, aka yi ta shigowa ana ma Inna barka da arziki, da dawowar ta gidan ta, ana hirar yaushe gamo, aka yi ta tuna baya ana tattaunawa kan girman yara na yanzu, musamman ‘ya’ya mata da ba wuya sun girma, dubi dai yadda Hauwa ta gandame, ana tattaunawa a kai, kusan duk jama’ar Badalar Kofar Na’isa sun san Inna da abinda Zakari yayi mata saboda kyakkyawar mu’amalar ta da kowa, sannan yanzu sabon gidan nasu ya fito da gidan sosai. Har an sawa gidan suna sabon gida. A yanzu sai ya zamana babu gida mai zubin zamani da kuma kyawun nasu a bayan Badalar ta Kofar Na’isa.
Washegari da suka wayi gari a kwana na uku da tarewar su. Inna ta ce da Hauwa zata shiga gidan Malam Isa su gaisa da iyalinsa, tace saboda ta ga kowa ya shigo mata murna banda Maikosai. Hauwa tace “toh Inna kada ki dade” tace “kada ki damu bazan jima ba”, ta fita.
Tayi sallama gidan Malam Isa, Maikosai, wadda sunanta na ainahi Talatu, ta gama suyar kosan safe ta sayar, tana wanke kayan suyar ta a gindin rijiya ta amsa sallamar Inna, sannan ta juyo don ganin mai shigowa sai ta ga Innar Hauwa, nan da nan ta yi fuska ta juya ta cigaba da abinda take yi ta barta anan tsaye, sai da ta kammala tas ta zo ta zauna ta baiwa Innar Hauwa kujera ‘yar tsugunne, itama ta samu waje ta zauna akan tabarmar kofar dakin ta, suka gaisa kadaran kadahan sai Inna tace.
“Zuwa nayi mu gaisa Maikosai, naga kowa na zuwa muna gaisawa, ke kadai ce ban gan ki kin zo ba, shine na shigo in gaida ke, Allah dai yasa lafiya”, inji Inna.
Mai kosai ta ce “in kinji shiru ai shine lafiya, lafiya ke buya ba rashinta ba, don haka ni lafiya ta kalau, har kin yi GAIBAR ne kin dawo?”
Cikin rashin fahimta Inna tace “menene kuma GAIBA?” Maikosai ta kalle ta a lalace tace “kina nufin ni zaki binne a baibai? Ko ba da hausa nake magana ba? Kin dauka ban ji me kuke shiryawa ke da bazawarin ki Malam Isa Mai Itace ba, na kiyi Gaiba ki dawo ya aure ki?
Allah na tuba ko meye abin likewa tsoho kamar malam Isa oho, yana fama da kakhi da majinar tsufa?”
Inna tace “innalillahi wa’inna ilaihi rajioun, ni Safiya me nake ji haka? Da auren nawa na likewa Malam Isa? Ni Safiyar ko dai wata ce kike nufi kika dauka ni ce?” Maikosai tayi tsaki tace.
“Ahap! Da bakin sa ya gayamin kin dawo zakuyi Gaiba ya aure ki, ko kin dauka akwai abinda yake boye min?”
Inna ta mike tsaye tana fadin “Maikosai baki da lafiya, ina rokon Allah ya baki lafiya”, daga haka ta fice ta barta tana ta sakin maganganu marassa kai bare kafa.
A zaure ta ci karo da Malam Isa zai shigo, cikin far’a Malam Isa yace “a’ah, Innar Hauwa da kan ta yau a gidan mu? Maraba lale”, wani kallo da Innar Hauwa ta yi masa yasa nan da nan ya sha jinin jikin sa, yayi tsuru-tsuru kamar bafaden da yayiwa sarki karya, tasa kai ta wuce abinta ba tareda ta ce masa kanzil ba.
Malam Isa ya fada gidan sa kamar an jefo shi, yana kwalawa Maikosai kira, a zaune ya sameta tana ta kunkuni ita kadai yace “uban me kika cewa Safiya?” Tayi tsaki tace “munafurcin da kuke kullawa na gaya mata na san komai” Malam Isa ya yi salati yace “amma Maikosai anyi dabba a cikin garke, kin jika min aiki, tsakanina da ke Allah ya isa”.
Maikosai ta tafa hannu tace “kace haka mana, saboda kafi so ku cigaba da ninke ni a baibai, saidai inji sallamar kishiya a kaina, duk abinda kuke ciki na sani, da zaryar da kake tayi a gidan su, har kuka yi kulla-kullar da kuka nemo ta kuka dawo da ita unguwar nan duk don kana kulafucin ta”.
Malam Isa bai iya tsayawa ya cigaba da sauraron ta ba ya juya da sauri ya bi bayan Innar Hauwa.
Tana isa gidan shima ya iso sabida saurin da yake yi saura kadan babbar rigar sa ta tadiye shi.
Tana shiga gidan ya doka sallama sai Inna ta dauko mayafinta data rataye a jikin kofa ta fito. Sabanin da da zata yi masa iznin shigowa yanzu sai ta fita ta tadda shi a zauren.
Suka gaisa Malam Isa yanata rawar jiki yana bata hakuri wai bai san me Maikosai ta gaya mata ba. Inna ta dube shi da manyan idanun ta irin na Hauwa masu neman fadowa kasa sabida girma ta ce.
“Malam Isa, mutunci da makwabtaka ne tsakanin mu, ina ganin girman ka da mutuncin dake tasakanin ka da maigidana, da hakkin makwabta da kake saukewa dare da rana, bai kamata kuma ka yi min kazafi ba ban ji ba ban gani ba, yaushe nace zan yi GAIBA? Balle har na aure ka?”
Malam Isa ya hau gumi yana bata hakuri yace wallahi shi da bakin sa bai yi zancen nan da Maikosai ba, ya dai yi zancen cikin hira da Dan ta Sunusi, inda yace masa “da ace zata yi Gaiba….”.
Bayan wannan bai kara komai ba, watakila Sunusin ne ya gaya mata, ita kuma ta canza maganar yadda taga dama, amma ta yi hakuri. Inna tace “baka yi min laifin komai ba sai alkhairi Malam Isa, amma ka sani ko Malam Bilyaminu bai dawo ba bazan yi wani aure ba, daga nan har gaban abada!
Burina kadai a duniya “Hauwa ce”. In rayu tare da ita, in kula da ita, in tsare mata mutuncin ta. Amma bayan wannan bani da wani sauran abu da ya rage min a rayuwa ta sai fatan cikawa da Imani”.
Malam Isa dai hakuri yake bayarwa, ya kuma roketa kan kada hakan yayi sanadin bacin zumunci da makwabtakar su, ya bar zancen har abada ba zai sake tada shi ba, don Sarham ma ya hanashi. Maikosai kuma zai ja mata kunne itama. Inna tace babu komai. Ya wuce.
Daga nan ya gaya mata maganar dabbobin ta daya kiwata mata, suna nan garke guda a cikin kangon gidan sa. Inna ta rasa da me zata godewa wannan karimin makwabci, ta yi masa godiya mai tarin yawa don tana matukar son dabbobin ta. Tace ya bar su anan su cigaba da zama tare da nasa, zata cigaba da bada abincin su. Wanda yayi a baya Allah ya biya shi da aljannah. Nan yake gaya mata ai SARHAMU yafi shekara yana sayen dussar su da harawar su.
Mamakin Inna da Sarham ya kara ninkuwa, ta ji yaron ya kara kwanta mata a rai, wato ba ita kadai ba, ba ‘yar ta kadai ba, hatta dabbobin ta ababen kulawa da darajjawa ne a gare shi. Ya Allah! Da me zata biya wannan bawan nasa banda addu’ar alkhairi mara yankewa gareshi, da iyayen da suka kawo shi duniya da zuri’ar sa???
Sukayi sallama ya tafi, ta koma gida tana labartawa Hauwa abinda ya faru a gidan Malam Isa da zauren su. Hauwa tafi Inna fusata, tace zata je ta tadda Talatu Maikosai ta gaya mata ba abinda zai kawo su gidan ta koda zasu koma kwana a kan kwalbati in sha Allahu.
Inna ta hana ta tace “tura mata aniyarta mutuncin Malam Isan zaki duba, na gaya miki ashe dabbobina duka suna garken sa yana kiwata mini har yau”. Wannan ne ya dan sanyaya ran Hauwa ta daina jin haushin Malam Isa amma sosai ta shaka da Maikosai.
**** ***** *****
RACE COURSE, KANO
A
wajen kallon Polo na Dawakai wato a filin sukuwa (Race Course) dake unguwar Nassarawa, Salele ya ga Jamil Zakari a matsayin wanda ya lashe kofin gasar dawakai (sukuwa) wanda akayi a ranar, dama dai Jamilu kwararren dan Polo ne, sun dade suna haduwa da Salele a wurare mabanbanta na tseren Dawakai, suna gaisawa, don ya san shi tun a jinyar da Hauwa tayi, sanda ya kadeta da mota.
Yau da Jamil Zakari ya lashe kofi Salele ya shiga sahun samari masu kutsawa suna gaisawa da Jamil Zakari Dan Agundi, Salele yana cikin samari ‘yan kallo masu cike da fata da burin watarana su zama manyan ‘yan Polo kamar Jamil Zakari Dan Agundi.
An fara watsewa kenan Jamilu ya shiga farar motar sa kirar (kia picanto) zai tafi sai ya hango Salele yana ‘waiving’ dinsa daga nesa wato yana ta dago masa hannu, har ya kunna motar ya dakata har Salele ya iso da gudu yana haki yana dariya. Jamilu ya fiddo gudar naira dari ya baiwa Salele, wadda a yanzu zata yi kimar kamar ace naira dubu daya. Salele don murna bai san lokacin da ya hau barin zance ba.
“Yaushe zaka zo gidan su Innar Hauwa ne? Sun dawo bada jimawa ba, sun gine gidan su ya koma sabo dal, sun tare tuntuni, jiya ma Innar Hauwa ta shiga gun Innata sun gaisa har Innata ta zo gidan ta yiwa Hauwa kitso”.
Jamilu yayi sakare! Yana sauraron Salele, kafin ya ji zuciyar sa ta harba, tsohon mikin son Hauwa-Kulu da yake kwana yake tashi da shi ya motsa kansa a kasan ransa, bai san sanda yace da Salele ya shigo gaban motarsa su je ba.
Salele ya kame a gaban mota suka dauki hanyar Kofar Na’isa.