HAUWA KULU Book 2 Complete Hausa Novel

HAUWA KULU Book 2 Complete Hausa Novel

L
okacin da mahaifin ta yayi mata bushara da hakan, wato ya gaya mata da bakinsa ya saka auren ta da AVM Alkali, Madinah ko tada kai bata yi ba balle ta ce a’ah, saidai bayan maganar da kwana biyu ta kwanta zazzabi mai zafi, wanda har ya kai ta da kwanciya a asibiti.
AVM yayi amfani da wannan damar ya zo duba Madinah, ranar ne ma ta fara ganin sa a gadon asibiti, ba wani kallon kurilla tayi masa ba amma ta fahimci babba ne sosai, ba za dai tace sa’an baban ta bane amma hakika ya manyanta don zai girmi babban Yayansu wato Yaya Abubakar, babu mamaki ya aje diyar data kusa giramanta.
Madinah ta dauke kai daga duban sa, yayi mata sannu da jiki ta amsa fuska ba yabo ba fallasa, babu wata fuska da zai neme ta da zance, dole ya gabatar da kan sa ya tafi. A washegari manya suka tsayar da ranar daurin aure.
Sadakin Madinah kawai da aka kawo dankunne ne da sarka na ‘Emerald’ wato koren yaqutu, sannan AVM ya yi alkawarin ‘launching’ sabon asibitin ido nata na kanta da zai bude mata a jihar Lagos inda zata zauna da zarar ta sauka a kasar Najeriya.
Iyaye nata shirye-shirye ta kowanne bangare ka’in da na’in, haka ta fannin matar AVM wato Hajiya Juwaira itama tana ta shirin zuwan amarya don ta saba da shiga ta fitar su shiyasa bata ko damuwa idan yace zai kara aure. Amaryar kuwa a lokacin duk da shekarun nan masu dama da suka gabata zuciyar ta na ga Sarham.
Tarihi ba zai manta da soyayyar su ba, amma babu tantama da zuciya daya yau ta hakura da Sarham da aka damka sadakinta, ta yarda zata auri zabin mahaifin ta.
Aka daura auren DR. MADINAH ATTAHIRU da AVM A. Alkali a wata ranar juma’ah, a masallacin Haraam, bayan saukowa sallar Juma’ah, iyaye da dangi aka shiga shirin biki na garari da kasaita kafin lokacin da za’a mika amarya nanjeriya.
Daddy yace ma AVM shi da kan sa yazo ya tafi da amaryar sa bayan kammala biki kenan, bai yarda da mata su rakata zuwa kai amarya Lagos ba irin yadda ake yi a al’adar Kanawa.
Air Vice Marshall Adamu Alkali Sambo, ya biyo jirgin su na sojin sama zuwa birnin Jeddah, irin jirgin su na helicopter, jirgin ya fadi a wani tsibiri/tsauni. A cewar wasu kuma ‘yan uwan sa sojojin sama ne suka harbo jirgin nashi bisa wata matsalar aiki da suke ciki da shi da su kadai ta shafa kuma su suka santa.
Koma dai yaya ne an tabbatar babu wanda ya fita da rai a wannan hadarin jirgin saman daga shi har staff dinsa guda hudu da matukin jirgin na biyar.
**** **** ****

“Innalillahi wa’inna ilaihirajioun…”.
In ji Daddy, kafin ya saki kan wayar a kasa ya durkushe akan kafafun sa, Hajjah Ramlah na tambayar ba’asi amma ya kasa gaya mata mijin Madinah yayi hadarin jirgi akan hanyarsa ta zuwa daukan ta.
Madinah wadda aka gama shiryawa cikin ‘SARI’ na ainahin matan indiyawa, hatta bular nan ta dankunne a hanci an yi mata da karfen zinare, ta zama kamar ba’indiyar gaske, dama tana da irin suffar su, isowar AVM kawai ake jira su daga Najeriya, sai ga Baban ta ya shigo dakin afujajan, yace mata “Madinah kiyi tawakkali”, Dady ya nisa kafin ya sake cewa “Ya ke ‘ya ta mai albarka, Allah ya karbi AVM”.

Albarkar da har gobe ta tabbatar tana bibiyar ta, domin watanni goma bayan rasuwar AVM A. Alkali, ba tare da ta yi masa ko gani na uku ba, mahaifin nata da kansa ya kira ta, har zuwa lokacin bai gama fita daga ‘shock’ da firgicin mutuwar AVM ba, wanda har ciwo ya kwantar da shi, ya kuma maida shi salihin bawa akan yadda ya dauki duniya a baya.
Ita kuwa Madina duk da taji mutuwar, tofa bata kara saka wani tunani na daban akan rasuwar sa ba, bayan na tunanin zuwa karo zurfin ilmin ta a KAU, don har zuwa lokacin ruhin ta bai bar makarantar nan tasu ta baya ba.
A yau da Daddy ya kirata dakin sa domin su yi magana ‘heart to heart’ irin ta Da da mahaifi shi da ita, ta zauna tankwashe da kafafu a gaban sa.
Ya fara da neman gafarar ta, kafin yace “na so in yi abu na son zuciya ta, gashi duk yadda naso faruwar sa Allah bai kaddara gidan ki bane ba.
Gashi ya yanke hukuncin da ya san yafi daidai da rayuwarki.
Na sani Madina biyayya kawai kike yi min, amma zuciyar ki naga wancan yaron, don haka yau bisa umarnina, na amince ki nemo wannan yaron Sarham a duk inda yake, in har yanzu yanada niyyar auren ki ya zo zan bashi. Bana neman ko kwandalar sa”.
Madinah ta girgiza kai ta ce “Daddy! Ai ni tuni na hakura da Sarham, na dade da mantawa da shi, kai ma ina rokonka ka manta da shi, ka sake yi min duk mijin da kaga dama, da yardar Ubangiji wannan karon ma bazan baka kunya ba”.
Shi kuma ya dage Sarham zata nemo, bas hi ba kara yi mata auren dole, auren soyayya yake son tayi wannan karon, da wanda zuciyarta ta aminta da shi, ba auren biyayyar sa ba.
Madina ta yi masa rantsuwa kan bata ma san inda Sarham yake ba a yanzu, don haka tana rokonsa alfarmar ya barta ta koma karo karatu a King Abdulazeez University.
Shikuma babu ja’inja ya lamunce mata, yana mai saka mata albarka.
Mafarin dawowarta KAU kenan, sai gashi ko sati bata yi ba ta hange shi a zaune a mashayar coffee, yana jira a hada a miko masa. Madinah ta mike ta je ta biya kudin coffee din tun kafin ya gama sha ya tashi.

“SARHAM!!!”

Madinah ta fada a hankali, bayan gushewar shekaru bakwai yau ta sake sanyashi a idanun ta, duk da canzawar halittar sa bazata taba kasa gane shi ba.
Wannan sirantakar da rashin kumarin, yanzu duk sun hade da tsoka da muscles, ta bada surar kakkarfan matashi lafiyayye mai wadatar jini a jika.
Wanda zuwa yanzu zamu iya cewa ya gama samun rayuwa daidai da burin sa, hankalin sa a kwance yake, saboda tsarin rayuwar sa ta masu tsantseni da gudun duniya ce tun sanin data yi masa, ba wai irin ta tara yaki halal yaki haram ba, sun tsaya ga iya gumin su, sun tsaya ga cin halal da moriyar ilmin su kadai.
Yayi jiki daidai misali wanda ya karawa tsayin nasa haiba, ya tashi daga siririn yaron nan zuwa (handsome man), son kowa, kin wadda ta san ba zata samu ba.
Madinah (couldn’t control her tears) wadanda (emotion na radadin soyayya) yayi sanadin zubowar su, a lokacin da zai bar wurin ne ta bi bayanshi shine ya yi mata wannan yarfawar. Shin meye laifin ta a duka wannan tsarin da Ubangiji ya yiwa rayuwar ta? Me tayi ma Sarham da yayi zafin da gaisuwar musulunci ma sai da kyar zai amsata tsakaninsu?
Ba mai bata wannan amsar sai SARHAM din. Ta sani bai dace ta bi shi har gidan sa ba, kai baima dace ba mace kamar ta ta dinga bin namiji komai tinkahon sa yana yarfata irin haka, balle ita Madinah Attahiru, da bayan aji har ajujuwa gare ta. Amma haka ta take PRIDE din nata, da kafarta ta taka zuwa gidan da ta san acan yake da zama, bata da tabbacin har yanzu acan din yake, ko kuma ya canza gida, amma dai tace bari ta fara duba can din ko zata dace. Ubangiji da kan sa yace “SULHU ALKHAIRI NE!”

To gata ta zo neman sulhun abin kaunar ta yau da kafafunta, kamar yadda tasan tana cin alfarmar sunan ta kullum a wurin sa, haka yau ma take da wannan kyakkyawan fatan, tana da yaqinin wannan karon ma zata ci wannan alfarmar daga gareshi, wadda tafi ta koyaushe girma a wurin sa, wato ya sauke fushinsa ya tsaya ya saurareta ko na minti biyu ne albarkacin sunanta da yake girmamawa na MADINATUL MUNAWWARAH… Madinah garin Manzo, Madinah mafaka ga dukkan musulmi, duk da tabbas ta san an bata masa, kuma laifi kan laifi ta san ta yi masa. Ko tace sun taru sun yi masa itada Daddy dinta.
Ilai kuwa tana tura karamin gate din ta hange shi daga can saman bene, tsaye a jikin balcony, ya harde hannayen sa a kirjin sa ya juya bayan sa daga kofar shigowa, don haka bai ga shigowar ta ba, da alama yayi zurfi a cikin tunani.
Madinah tana tura kofar cikin sa’a ta taddata a bude, don haka kai tsaye ta sa kai, ta kuma haura ta matattakalar benen ta cimmasa har inda yake.
Kamar cikin mafarki, kamar kuma irin gizon da ta saba yi masa cikin ido biyu, haka ya ga Madinah Attahiru tsaye a gaban sa, (for the second phase) na rayuwar su. Tana sanye da shudiyar abaya kirar Dubai da mayafin ta, ya sha mamakin biyoshin data yi, a irin sanin da yayi mata wajen tsare mutuncin ta da tsare ajin ta, wato tun saninsa da ita… maintaining self-esteem dinta yana sama da komai a gareta, a kuma irin yarfawar da yayi mata dazunnan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected