HAUWA KULU Book 2 Complete Hausa Novel
Inna da Hauwa a tsakar gida, Inna na tankaden garin tuwo Hauwa na sallar la’asar akan dardumar sallah anan tsakar gidan su mai yalwa da sanyin sabon siminti, saidai yanzu babu shukokin su na Umbrella da bishiyar dalbejiya, don haka basu fiya zama a tsakar gidan da rana ba sai da yamma irin haka ko da daddare.
Sai sallamar Salele suka ji, yace Inna kuna da bako” Inna da yake ta san Sarham zai zo sai tace “gidan bakon sa ne da zai tsaya a waje ya turo ka? Ko ba sallama yake da kansa ya shigo ba? Yau nake ganin sabon salo banbarakwai wai namiji da suna Hajara, kace ya shigo, kuma daga yau kada ya kara aikomin yaro idan yazo, shi da gidan su?”
Salele ya koma yace da Jamilu Inna tace ya shiga.
Inna da Hauwa sai ganin Jamilu Zakari suka yi a kan su, yayi sallama kamar an jefo shi. Ya shigo tsakar gidan su cikin kyakkyawar shiga ta hawan Polo.
Idanun sa akan Hauwa ya hau sakin Hamdalah a fili kafin ya zube gaban Inna kamar mai neman gafara. Zai fara gaisheta Inna ta ce “tsaya-tsaya, wa nake gani kamar Jamilu? Wai dama kai ne ka aiko Salele?” yace “ni ne Inna” tace “to sawunka a likkafa Jamilu ka juya ka koma inda ka fito, kafin ka janyo min tijara, yau ko gaisuwa babu tsakanin mu wallahi ka ji na rantse ka tashi ka fice mana daga gida, kada ka kara zuwa balle ka janyo min bacin rai Ina fama da ciwon zuciya, zuciyata tayi rauni kuma bata da lafiya bazata iya daukar bakin cikin ubanka ba”.
Inna ta soma hawaye, tana rokon Jamilu ya tafi. Tun ba’a kaiwa Zakari labarin an ganshi a gidansu ba. Jamilu ya mike ba shiru, yana kallon Hauwa da wani sabon so a cikin idanunsa, musamman da yaga ta kara girma tayi wani irin kyau ta yi bulbul da ita, datar ta tayi sumul. Likita Sarham ya tsaya mata da shan (freshmilk) wato danyar madara tana Nan fal firinjinta tun dawowarsu ita take daddaka don bata iya cin abinci sosai.
Jikin sa yana rawa ya soma ja da baya. Tace “ko a lahira wani kan ci albarkacin wani, albarkacin ka Zakari ya ci ban yi karar sa hukuma ta kwatar min hakkina da tozarcin da yayi min a kan ka ba.
Don haka tun muna shaida juna muna kuma ganin sauran mutuncin juna to ka fita daga inda muke”.
Jamilu ya juya a hankali ya fice, saida ya tsaya a zaure ya share zufa da hawaye, shi ya san da gaske yake son Hauwa, son da yake mata ba shi ya dorawa kansa ba Allah ne. Saboda ita har yau ya kasa yin aure, alhalin ba abinda bai mallaka ba na rufin asiri a rayuwar sa.
Daga nan gidan su Inna gidan Hajiyar sa ya wuce, ya kafa mata kahon zuka kan taje ta baiwa Inna hakuri, kada ta hukunta shi da laifin da ba nashi ba. Hajiya Rumanatu na jin an ga su Inna ta dauki mayafin ta tace su je ya kaita. Don dama zaman Jamilu har yau ba aure ya dameta.
A mota Jamilu ya zauna, bayan Hajiyarsa ta shiga gidan, ya kifa kai a kan sitiyari ya rasa inda zai sa kansa da damuwa. Bai san yana son Hauwa bama sai yanzu, data kara girma ta zama cikakkiyar budurwa komai ya kai ya kawo. Hajiyarsa ta shige gidan da sallama.
Inna sai ganin Haj. Rumanatu tayi tayi sallama, Inna ta amsa fuska ba yabo ba Kuma fallasa don ta gaji da nacin Jamilu da uwarsa.
Inna ta yiwa kawarta tun ta kuruciya wato Rumanatu tarba ta mutunci, irin ta tsofaffin kawaye, bayan sun gaisa kafin Hajiya Ruma tace komai Inna ta hau rokon ta kan ta raba Jamilu da zuwa inda suke, ya rabu da Hauwa. Tace, “ku yi hakuri, ni babu wani aure da zan yi wa Hauwa-Kulu fau-fau, balle na dauketa da hannuna na kaita cikin zuri’ar Zakari a hallakamin ita da niyya sabida ‘yan ubanci irin nasa, muddin Zakari yaji labarin Jamilu na zuwa wallahi zai juyo da rashin mutuncin sa kan mu”.
Iyayen suna can dakin Inna suna zantawa suna kuma fahimtar juna, Haj. Rumanatu na mai gamsuwa da hujjojin Inna akan bazata iya aurar da Hauwa ba, ba ga Jamilu kadai ba har ga kowanne namiji ma. A lokacin Salele yazo zai wuce, sai Jamilu ya roke shi ya sadada a hankali don Allah ya kira masa Hauwa su gaisa.
Nan da nan Salele yabi umarnin ubangidan sa ya je yace da Hauwa tazo ana kiranta za’a bata sako, tace a baiwa Inna mana! Yace tana da bakuwa ne sun kule suna sirri. Haka ya kalallameta ta taso ta tako da hijab mai hannu har kasa a jikin ta zuwa soron su.
Sai ta ji muryar Yayan ta Jamilu ya ce “Hauwa!” Ya saki ajiyar zuciya ya sake cewa, “Hauwa nine Jamilu, ni nace Salele ya kira ki, Hauwa ina kuka tafi duk tsayin shekarun nan kusan uku sai dawowa nayi daga Delta na nemeku na rasa? Ko kinsan har yau ban yi aure ba ina tsumayin dawowar ki Hauwa?”
Hauwa ta dan waiga kamar me tsoron ko Inna na wajen, tace “Yaya Jamilu ne da gaske?” “Nine Hauwa’u, I missed you so much, and I truly love you kin sani Hauwa”. Hauwa ta ji duk ta rikice, ta kasa cewa komai domin maganar sa ta yau ta mata gingiringin, ta mata nauyi, rana ta farko da wani da namiji ya furta mata kalmar so da bakinsa da nata, taji kunya har kasan ranta, Jamilu yace.
“Ki bani dama don Allah Hauwa, in turo magabatana gun Inna, in sha Allahu zamu yi aure ko a boye ne in ya so mu bar Kano gabadaya ba tareda Babana ya sani ba, ina mai baki hakuri kan abinda ya faru, na ji komai bayan dawowata kuma ba inda ban neme ku ba cikin Kano da wajen ta ban samu ko wanda yace ya san inda kuke ba.
A kan ki Hauwa Babana ya kusa tsine mini, Inna kua ta kasa gane karfin son da nake miki ba irin wand azan iya hakura bane, don Allah Hauwa ki manta da komai, ki duba ‘yan uwantakar dake tsakanin mu, mu yi auren mu cikin alfarmar zumunci da kaunar juna, dama Bankinmu zasu yimin transfer kwanannan zuwa Ikeja, in yaso sai mu koma can”.
Hauwa ta rasa abinda zata ce, domin Jamilu ya matukar bata tausayi, ya tafi da imaninta, ya kuma gama saye zuciyarta da wannan kauna da ya nuna mata, tayi shiru kawai tana sauraron Jamilun da zuciyarta da kunnuwanta, tana mai yarda da kowacce kalma da kowanne harafi dake fita daga bakinsa, zuwa can ta ce.
“Ni fa Yaya Jamilu banida matsala, amma babu ruwa na a kan maganar aure. Allah ya sani ban rike ka da komai a raina ba, sannan kuma bana kin ka, ina ganin abinda yafi, ka nemi amicewar Inna ba tawa ba, ni din da komai nawa ababen ikonta ne kuma ni mai son yin biyayya ce a gareta, don haka duk wani hukunci da Inna tayi akaina, inaso ko bana so, bani da ja a kansa”.
Jamilu ya gyada kai cikin gamsuwa da kalamanta, at least ya fahimci Hauwa bata kin auren sa koda bata furta tana son shi ba, tofa babu kiyayyarsa ko kadan a tare da ita, ya rausayar da kai yace,
“ni kuma na yi alkawarin zan lallashi Inna, idan ta bani ke zan kuma kula mata da ke kamar yadda zan kula da kaina. I can understand her fear, kuma kwarai nake la’akari da abida take hangowa (taking the marital responsibility of a blind person will never be easy) amma abinda ta manta ni dan uwanki ne, jinin ki ne, I can possibly endure it fiyeda bare, aure sunnar Manzon Allah ne SAW bai yuwuwa ace saboda lalura ta makanta baza’a yi shi kwata-kwata ba tunda ke din ‘yar adam ce kamar kowa mai lafiyar yin aure, ni Jamilu na yi alkawarin zan zame miki miji abin alfahari kuma dan uwa wanda zamu raba rashin idanun ki tare, sannan wanda zai tsaya wajen ganin kin zamewa ‘ya’yan ki uwa tagari a yadda Allah ke son ganin ki, tsan tsaya tsayin daka wajen ganin cewa lalurar rashin gani bai sa kin kasa basu kulawa ba.
Ni da kaina zan taya ki rainon ‘ya’yan mu Hauwa’u”. sai Hauwa ta kai tafuka ta rufe fuska cikin jin kunya tana murmushi kamar tace kasar ta tsage ta shige cikinta.
Maganar Jamilu ta karshe kai tsaye ta sauka a kunnuwan Dr. Sarham Abbas ne, a lokacin da ya kashe motar sa “opel astra’, ya tako zuwa gidan ya sawo kai soron, cikin takunshin nan mai sauti gab-gab-gab na bakin cover shoes ma matukar daraja, ya shigo zauren su Hauwa, yayi harr da idanunsa a fuskokin su.
Yana sanye da shirt fara kal, wadda aka yi rubutun ‘Dolce&Gabbana’ a jikin ta, da bakin Trouser ne na ‘Tokyo Jeans’. Kansa babu hula, sumar nan tasa baka wuluk ta fulanin Shanono ta cika kan sa har ta nannade (curl), a kafafun shi bain takalmi ne sau ciki na bakar fata kirar Italy. Da farko he was shocked, da ganin Hauwa tsaye da namiji a zaure, da abinda kunnuwansa suka jiye masa Jamilu na fade, da kuma yanayin da yaga Hauwa wanda kiri-kiri yana nuna tadin soyayya. Amma da yake shi din shine Sarhamu, sai ya bagarar, yashare, ya hadiyefirgicewarsa yayi kamar bai ji kalaman Jamilu ba, yayi musu sallama da dusassar muryarsa ya kuma baiwa Jamilu hannu suka yi musabiha, ya dan kalli Hauwa yana mamaki yana karawa, sannan ya shige cikin gidan.
Inna ta rako Babar Jamilu zata tafi suka yi kacibusa da shi yana shigowa tsakar gidan, kafin Jamilu ya samu zarafin tambayar Hauwa ko wanene shi ya isa dakin Inna, shigowarsa tasa hankalin Inna ya koma kansa, a gurguje suka yi sallama da Haj. Rumanatu ta wuce, bayan ta tabbatar mata cewa kwarai ta fahimce ta, zata yi iya yinta wajen lallashin Jamilu ya hakura, ko don kwanciyar hankalin Inna da zaman lafiyar su da Babansa dan jidali (Zakari).
Sarham ya zauna a falon Inna yana jiran ta har ta shigo ta zauna akujerar dake fuskantar sa, suka gaisa, sai ya koma cikin kujera ya kishingida yayi shiru, har da dan juyawa ya kalli taga yaga ko Hauwa taji kunyar idonsa na abinda ya tarar tana yi (soyayya) tayi maza ta baro saurayin ta shigo gida ko a’ah? Amma ina! Ko keyarta bai gani ba, tana can suna sallama da Jamilu kamar bazasu rabu ba, Sarham ya mike dogayen kafafunsa a kasa. Bai iya kara cewa komai ba don al’ajabi da mamakin Hauwa.
Can jimawa sai ga Hauwa ta shigo, tana tafe abunta kanta tsaye, babu ko lalube irin na makafi, tsabar ta gane hanyar dakinta, tasa kai zata wuce dakinta taci uban tuntube da kafafun Sarham, saura kadan ta kifa ta ci da baka. Ko sannu bai mata ba balle yayi ‘apologizing’. Cikin fushi tace.
“Inna wa ya saka min kafa zai kayar da ni haka?” Inna ta yi mata shiru, kafin tace “daga ina kike?” tace “Yaya Jamilu ne ya kira ni soro”.
Haba! Sai Inna ta balle da fada kamar ta rufe ta da duka, cewa take “da iznina kika fita zance gun Jamilu? Kece da zuwa zance Hauwa da wane idon zaki ga saurayin?” Saida Dr. Sarham yace “ya isa Inna, kinsan kinada matsalar zuciya, kada ki dinga bata ranki irin haka kan kananan abubuwa har ya tabo zuciyar ki”. Hauwa ta wuce dakin ta a sanyaye, bayan ta gaishe shi. Dr. Sarham yaki ko amsawa balle ya nuna ya san tana gaishe shi, har ta wuce tana mamakin me ta yi wa Dr. Sarham yau?
Gashi dai yau bai kira sunanta da yake mararin kira na MAIJIDDAH cikin farin-ciki, yalwar fuska da far’ar nan tasa ba, bai kuma amsa gaisuwar ta da kulawa da (attention) kamar yadda ya saba ba. to me ta yiwa Likitan Inna?
Ji yayi gabadaya yau ya kasa zama ya dade a gidan yadda ya saba, ya kuma kasa hira da Inna yadda suka saba, ita kadai take ta babatunta, daga karshe da Inna taga shirunsa yayi yawa sai ta dago ta dubeshi tace,
“ko lafiya kake kuwa likita? Na ganka ba’a yadda na saba ganinka ba”.
Sai kawai ya mike yana cewa “bari in karasa gida Inna, kaina ke min ciwo, yanata sarawa, idan na ji sauki zuwa gobe ko jibi in sha Allah zan shigo”.
Inna tace “ni ai ban sani ba, gashi har nayi maka tuwon Acca kuwa, da miyar da kake so ta zogale” Sarham ya juya a lokacin yana saka takalman sa a bakin kofar falon, yace “ba komai Inna, some other time, zan ci”.
Suka yi sallama dukkansu jiki babu kwari ya juya ya tafi. Ko sallama bai yiwa Hauwa ba.
Yana tuki yana hada gumi kashirban, duk da sanyin AC din motar sa. Abun ya daure masa kai matuka. Ya kuma sakashi a damuwar da ya kasa sanin ma’anarta. Yana isa gida yaji ana murnar zuwan Sumayyah, wadda ta zo hutun karshen shekara da barkar haihuwar Waheedah.
Kamar bai ga Sumayyah ba, bayan kuma har ido sun hada a falon, ya dauke kai yasa kai ya wuce zuwa dakin sa bayan yace musu cikin jam’u “sannun ku da gida”.
Mama ta bi shi da kallo, Sumayyah kuma ta ce. “Bhaiya lafiya kalau yake? Kaamr bai ganni ba Mama?” Mama ta ce “oho muku, kun fi kusa”. Surayyah ta ce “nafi tunanin wani ne ya bato masa rai daga waje, baki ga fuskarsa kamar hadarin da ya nausa yayi gabas ba?” Sumayyah sai ta mike ta bi bayan sa zuwa dakin nasa.
Sallama tayi daga bakin kofa, sai da ya bata iznin shiga ta shiga dakin ta same shi zaune akan ‘study chair’ ya rafka uban tagumi, ta ce.
“Bhaiya baka ganni bane ka wuce bamu ko gaisa ba?”
Ya dago ya dubeta da jan ido, a lokacin taga idanuwansa sun kada, yace “a’ah Summy ce yau a gari? Saukar yaushe?” Tace tun dazu na sauka, ta gabana fa ka wuce, har ido mun hada, ka san mun yi hutu shine fa nace bari kawai in taho ganin Hauwa’u”.
Ta zauna a kujerar ‘sofa’ kwaya daya dake dakin, ta ce “Bhaiya duk ka birkice, you are upset, anya lafiya kake kuwa? Na ganka ‘moody’ tunda ka shigo”. Yace “Sumayyah, bansan yadda zaki fassara abinda ya sani a damuwar ba idan na fada miki, ba wani abu bane serious I don’t know why I made it serious, abun ne ya bani mamaki, ya kuma bata min rai, wai Hauwar nan da kika sani ko ido bata da shi, amma ta iya tsayawa zance da saurayi a soro???
Ni ban taba ganin abinda ya bani mamaki ya rikitani irin wannan ganin dana yi ba”.
Sumayyah tana sane tace “Hauwa wacce? Baby Hauwan mu?” Ya harareta, “ke bana son sakarcin banza. Hauwa ‘yar Inna mana, kanwata ta kofar Na’isa” Sumayyah ta wani ce “au ho! Ka ce min kawai Hauwar Inna, HAUWA-KULU ‘yar cikin BADALA!”. Sai ta hau tuntsira dariya tace “Bhaiya, yanzu ganin Hauwa da saurayi shine abinda ya birkita ka haka?”
Sarham ya harareta yace “Sumayyah yaya ina miki magana ‘serious’ za kina dariyar rainin wayo, Hauwa fa, wadda ko ido bata da shi, ina zata kai wani namiji da sunan soyayya?
Ganin ta nayi da wani cousin dinta suna zance fa, zance na saurayi da budurwa! Wai sunan sa Jamilu, dan kanin Babanta ne”.
Ai kuwa Sumayyah ta kara tuntsirewa da dariya sai da tayi mai isarta, shi kuma ya shaka sosai, saida dariyar ta lafa mata ta ce.
“Bhaiya makaho ba mutum bane? Ko kuwa makaho bai san SO da mai son sa ba?
Don tana makauniya shikenan sai akace bazata yi aure ko soyayya ta ji dadin rayuwar ta kamar kowanne dan adam ba? Ko in bata saurari masu son ta ba kai din auren ta zaka yi?
Yau nake ganin ikon Allah, yau ina ganin abinda ya gagari Kakata Kulu, kai ka dafe dahir har da ‘yar ka tubarkallah, shine ita zaka yi mata fatan ta tsufa a dakin uwar ta, alhalin kai ba son ta kake yi ba, wannan fa shi ake kira karfin hali barawo da sallama ko in ce, Bhaiya na, da tsabar son kai tsagwaro. Wani hali da ban san shi da shi ba.
Ni wallahi gani nake ma babu wanda ya dace da ya aureta kamar dan uwan nata, tunda jinin su daya, ya san darajar ta, zai yi hakuri da nakasar ta, ya riketa da daraja a gidan aure, don kai kam Bhaiya, baka da alqiblah.
Ayi magana cibi ya zama kari!”.
Ta sake tuntsirewa da dariya ta ce “sai amara kirazan biki, mu ne manyan kawayen amarya Hauwa’u, a bikin ta da Yayanmu Jamilu”. Sumayyah har da dan gudu-gudunta ta bar dakin, tana cigaba da tillika dariyar shegantaka. Don ta san ta gama kunna shi in ta kara minti uku a gabansa zai iya losing control kai mata duka. Don tana ganin yadda yake girma idanunsa tunda ta soma shegantakarta.
Maganganun ta dinnan, suka taru suka zamewa Dr. Sarham “a warm food for thought!” A tsayin wannan daren bakidayansa kona rabin away a kasa runtsawa.
Sarham sai faman juyi yake a kan gadonsa, daga wannan gefen zuwa wancan, yana tauna maganganun Sumayyah a kwakwalwarsa, yana kuma fassarasu a zuciyarsa cikinma’auni na hankali da tunaninsa. Daren da yazo masa da tarin ‘alterations’ koko ‘revolutions’ wadanda a can baya bai taba hango yiwuwar makamantansu ba.
Ko na minti daya ya kasa rintsawa. Idan ya tuna maganganun Sumayyah. A ganin sa Sumayyah maganganu ta gasa masa masu zafi ta cikin ruwan sanyi, koko yace jirwaye tayi masa mai kama da wanka, don dama tana kullace da shi akan abinda yayi mata, don kawai ta tambaye shi ko son Hauwa yake yi shekarun baya, bazata manta ba yayi mata wulakancin da bata zata ba, kiris ya rage ya doketa. A nata bangaren Sumayyah, ta dade tana kiwon mu’amalar sa da su Hauwa ta rasa alkiblarsa, musamman in ta tuna abinda yayi mata daga ta tambaye shi ko son Hauwa yake? Ta tuna a ranar dukanta ne kawai bai yi ba, shine abinda take nufi da “ayi magana cibi ya zama kari”.
Da gasken gaske ya kasa barci a daren, sai faman tauna maganganun Sumayyah wadanda ya kira jirwaye mai kama da wanka.
Washegari ya samu kansa da kasa zuwa gidan Inna, saboda har zuwa lokacin ransa a bace yake, haka a sauran kwanaki ukun da suka biyo baya ko hanyar kofar Na’isa bai kalla ba, yana like wajen su Waheedah, kamar ya maidasu ciki, don a can yake samun sanyin ran sa, daga zafafan maganganun Sumayyah da haushin Hauwa (a ganin sa bakaken maganganu ne Summy ta gasa masa son ran ta), da suka dade suna dafa shi kamar dafaffiyar masara, kuma ya kasa cewa Sumayyah komai a kai again bayan kuma ita kadai ce zai iya zancennan da ita. Madinah ta samu lokacin sa sosai a wannan satin, don yanzu kullum yana wuni tare da su baya zirga-zirgar gidansu Inna.
Inna na talgen tuwo a yammacin yau da Sarham ya kwashe kwanaki bakwai bai zo gidan su ba, sai ya fado mata a rai, ta dubi Hauwa dake wankin sittirun ta a bakin famfo tace.
“Kuluwa!”
Hauwa ta tsuke baki ta kuma tsuke fuska bata amsa ba, ai ta san in ta ce mata Kuluwa bazata amsa ba, sai ta ce “ni kuwa kin lura da abinda na lura da shi?” Hauwa tace “me?” “Likita Sarhamu, yau kwana bakwai bai zo gidannan ba, tun ranar da ya zo yace min kansa na ciwo, yanzu haka jikin ne ya matsa masa tunda har kika ga yayi wannan dadewar bai zo ba”.
Hauwa ta yi shiru bata ce komai ba, ta cigaba da wankin ta, ashe ba ita kadai ta lura da rashin zuwan nasa ba. Inna ta sake cewa.
“kin ga da ace na san gidan su sai in je in duba shi”.
A nan ne Hauwa ta bata amsa,
“kai su Inna akwai wuce gona da iri”.
“Ba wuce gona da iri bane Hauwa-Kulu, baki ji fadar bahaushe ba? Yace KA GAIDA MAI GAISHEKA KO DA BAZAI AMSA BA!”
Wannnan magana ta karshe da Inna ta yi, ta yi ta ne a kunnen dan halak din wato (Sarham), don a lokacin ya iso tsakar gidan da kasaitattar sallama a bakin sa.
Nan da nan Inna ta bar abinda take yi a madafin ta fito, ta washe baki tana amsawa, “maraba da Da na Sarhamu, likita Sarhamu na ne tafe? Dan halak yanzu nake zancen ka, sai gaka”.
Sarham ya tsugunna a kofar kitchen din yana gaida Inna, Inna ta koma ta kashe wutar tuwon, ta taso suka shiga falon ta tare, suka kara gaisawa, Inna sai taga duk ya rame mata, tace “Likita jikin ne ya boye ka ne?” Ya ce “a’ah Inna lafiya ta kalau, kwana biyunnan dai ban cika fitowa ba, ina can wajen su Hauwa’u karama kullum”.
Hauwa ta shigo da sallama tana dan dafa bango, ta isa kofar dakin ta sannan ta juyo saitin da ta ke jin tashin tattausar muryar Sarham, ta ce cikin girmamawa “Dr. barka da zuwa, ina wuni?”
Ya dago kai ya kalle ta kadan, kayan jikin ta sun dan jike sun manne a fatar jikin ta, Hauwa yar shekara sha takwas ta gama samun duk wani dirin jikin da jikinta zai bayar, da kyakkyawar suffa na abinda ake nema a tare da budurwa ‘teenager’, nata har ya zarta yawan shekarun ta, don tsammani zakayi ta kai shekaru ashirin da daya.
Tun asalinta Hauwa bata da rama haka take ‘yar duma-duma, lubu-lubu (luscious). Dr. Sarham ya yi wata ‘yar ajiyar zuciya ba tareda ya san ya yi ba, yana tuno kwailancin ta na shekaru biyar a baya, wai itace haka yau a gabansa, yace a hankali “lafiya kalau, ina Saurayin ki dan polo dan gayu?” ‘yar dariya Hauwa ta yi, ta shige dakin ta bata ce masa komai ba.
Sai Inna ce tayi kwafa ta ce, “ai ka bar ni da Hauwa da Jamilu kawai, nice maganin su da rashin kangadonsu, da ni suke zancen wallahi, na sa uwarsa Rumanatu tayi musu iyaka, idan yaji toh, in bai ji ba na rantse zan iya kai shi kotu don alkali yayi musu iyaka.
Na fada na kara ni fa bazan taba yi wa Hauwa wani aure ba, balle in bawa dan Zakari.
Allah na tuba ko dan shugaban kasa ne ya zo neman auren Hauwa, wallahi bazani bayar ba, balle dan Zakari tsatson zalunci.
A cikin burika na masu kyau a kan Hauwa, babu batun yi mata aure a ciki, babban burina shine ta yi karatunnan na zamani mai zurfi in dai makafi na iyawa kamar yadda ta fara, ta samu abunda ko bayan raina zata dogara da kan ta, kuma in karfina ya kare kada nata raunin ya bayyana dalilin rashin karfi na, ko in ta Allah ta kasance min hakan ya kassarata.
Ni din nan nice karfin Hauwa, ni ce kuma idanun ta, bazan taba bari a wulakanta min ita da sunan aure ba, ko a ci mutuncin lalurar ta a dalilin aure, shi yasa na gwammace in adanata a gabana, in kula da ita, tayi ta karatu, duk da ni ma ba karatun nayi ba, amma alhamdulillahi ni lafiya ta kalau, zan rayu ko ba ilmin zamani ba tare da na zamewa kowa labiliti ba.
Amma Hauwa fa? Ai duk wanda na bawa auren ta na kware shi, domin na hada shi da aiki da jidali. Itama kuma na sayo mata rashin kwanciyar hankali. Don haka maganin kada a ji, kada a soma.
Gashi bani da matallafi namiji wanda zai tsayawa Hauwa ta samu ta yi karatun nan tunda ni bansan kansa ba, da wannan yau nake baka amanar Hauwa-Kulu Sarhamu, ina mai baka amanar ta don na amince maka, na kuma amince bat un yau kaunar ka damu ta saboda Allah ce.
Don Allah likita ka taimaka min, wajen cikar burika na a kanta, na tayi karatu mai zurfi wanda zai amfani al’umma ya kuma amfane ta duk da nakasar ta. Bana so nakasar nan tata ta zame mata rauni, so nake nakasarta ta zama ado a gareta.
Inna ta soma sharar hawaye ta ce “gashi Bilyaminu ban san inda yake ba, bansan a halin da yake ciki ba, yana mace ne ko yana raye Allah masani, na tabbata da ace yana tare da mu, shima burin sa zai zama irin nawa ne akan Hauwa, don a komai muna kasancewa da ra’ayi daya ni da shi.
Allah ya gani bazan iya baiwa Jamilu auren ta ba duk da na san a shirye yake da ya tsayawa Hauwa, ba don komai ba sai don ubansa, amma ba don yayi min wani abu ba, ko bai cancanta a bashi aure ba.
Ko Hauwa-Kulu zata tsufa ba aure, tana nan a kwibi na, (a kusa da ni) ba inda zata da sunan aure”.
Hauwa daga dakin ta duk tana jiyo abunda Inna ke fadi akan ta, sai ta samu kanta da dimaucewa, don fisabililahi ko ba’a fada ba ta san zuciyarta ta amince da Yaya Jamilu dari bisa dari, yau ga Inna na cewa a dakin ta zata tsufa. Ya Allah! Itafa mantawa take da makantar nan tata, idan har ba bude littafi da zummar yin karatu taga duhu didim tayi ba, mantawa take bata da ido, saboda rayuwar ta cike take da baiwarwaki da kuma alfarmomin Ubangiji masu yawa da wadatar zuci.
Ji take babu wani abu da mai lafiya yake yi a rayuwar duniya wanda bazata iya ba, musamman aure da hayayyafa.
Inna da Sarham sun jima suna hira, yana zaune dirshan a gabanta. Inna nata kashe zuciyar Sarham da kalamanta masu nuna hakikanin MOTHERHOOD a kan diyarta Hauwa-Kulu, yau ya fahimci ba karamin so Inna take yi wa Hauwa ba.
Ya ci tuwon da Inna tayi kafin ya tafi wanda tuwon masara ne miyar yakuwa, ta zuba masa soyayyen manshanu a ciki da yankan naman rago biyu. Ta kuma hada masa lamurje/zobo mai sanyi wanda tasa a firjin Hauwa yayi sanyi.
Dr. Sarham tunda ya bar gidan su Hauwa ba tareda yau ma ya iya tsayawa a kofar dakinta yadda ya saba ya yiwa Hauwa sallama ba, kasa shiga Sorondinki yayi yau, saboda halin da ya samu zuciyar sa a ciki a kan maganganun da suka yi yau shi da Inna heart-to-heart, ta gama fede masa zahirin abinda ke karkashin zuciyar ta akan miskiniyar diyar ta, HAUWA-KULU, wanda dan cikin ta kadai zata iya gayamawa, amma shi yau ta zaunar dashi ta gaya masa duk wani abu dake karkashin zuciyarta a kan future dinta bisa radadin da take ji na nakasar diyarta.
Kai tsaye ta bayan gidan ya wuce ya lallaba ya shige dakinsa, ba tareda kowa ya san da dawowar sa ba.
Sarham ya kulle kansa don kada Sumayyah ta zo ta dame shi da dumi, dama kuma Inna ta ciko masa cikinsa taf da abincin ta, don haka baya bukatar karin cin abincin Mama yau.
Ya kwanta a ranar a tsakiyar gadon sa yana tunanin maganganun Inna, ya kuma debo na kanwarsa Sumayyah na rannan ya kara akan su, wato yayi addition, yana tarawa yana debewa, tsakanin maganganun Inna da maganganun Sumayyah….
Sumayyah ta ce “Hauwa mutum ce kamar kowanne dan adam, tana da right din yin aure da bukatar yin sa kamar kowa ‘in spite of her disability’, Uwarta kuma ta ce ko zata tsufa a gida bazata bata wannna damar ba.
Ba don komai ba sai don tana guje mata wulakanci da tozarci a dalilin nakasar da shi Sarham yayi mata lasisin ta.
Bayan kuma addini da al’ada da ‘yancin dan adamtaka duka sun bata damar yin aure. Shin tsakanain Inna da Sumayyah, waye mai gaskiya akan future din HAUWA-KULU???
A take kaso mafi rinjaye na zuciyar Sarham ya ce “Sumayyah ce mai gaskiya!!!
Ita Inna ba wai bata so Hauwa tayi aure bane a’ah, gudun kada a wulakanta mata ita ne da sunan aure, da guje mata tozarci da dawainiyar aure da take da tabbacin bazata iya ba sabida rashin ido, yasa ta gwammace tayi ta ajiyar ta a daki. Wato abinda ka san bazaka samu ba hada shi da bana so! Amma ita Hauwa din tunda har take kula Jamilu, to ya tabbata tana son tayi auren kenan ko bata furta ba. Don Inna ta gaya masa yadda Hauwa ke sakewa da Jamilu ita kanta abin yana bata mamaki matuka. Sai ya samu kansa da tambayar kan sa to KO DAI HAUWA SON AUREN JAMILU TAKE YI?
Sarham sai yaji ran sa yayi wani iri mummunan baci, a take wani tunani ya bijiro masa, me zai hana shi Sarham din ya aure Hauwa kowa ya huta (ko da baya son ta so irin na soyayyah irin wanda yake yi wa matarsa Madinah, don shi kadai ne solution ga rayuwar ta (shi Sarham din), da zamowa maslaha ga mahaifiyar ta, hakan zai fi alkhairi fiye da auren Jamilu ko wanin sa ga Hauwa. Tunda maganar Hauwa ta dauwama ba aure ba dabara bace so-karbau, a matsayin ta na ‘yar adam mai cikar lafiya da ‘sexual hormones’ kamar kowa dole tana bukatar yin aure.
A take Sarham ya shiga gayawa kansa; zai auri HAUWA-KULU domin wasu dalilai masu tarin yawa da ya dade yana dambarwa da zuciyar sa a kansu, amma ba don kalmar SO ta gitta ko zata gitta nan gaba a tsakaninsu ba. SO guda daya ne a zuciyar sa; kuma na matar sa MADINAH uwar Hauwa-Waheedah ne.
Zai auri HAUWA ne a dalilin ya san ta kullace shi, akan-karan kan sa kuma yana son kankare wannan kullacin nasa dake kasan zuciyarta, har gobe ya kasa yafewa kansa zama sanadin makantar ta. Babu kuma ta hanyar da zai iya kankare wannan tabon nasa daga ran Hauwa in ba ta sanadin aure da hayayyafa ba.
Zai kuma yi amfani da kwarewar sa ta yanzu, wajen ganin ganin ta ya dawo, koda ba duka ba, da iznin Ubangiji.
A karshe ya gayawa kansa zai auri HAUWA domin yana tausayin Inna, kuma yana kaunar ta, don haka zai karbi amanar nan data bashi ne ta hanyar AURE wanda ta hanyar sa ne kadai zai iya cika mata burin ta, na kular mata da ilmin Hauwa da rayuwarta gabadaya, zai yi kokari wajen cikawa Inna burikan ta a kan HAUWA-KULU ne kadai idan ya samu damar auren ta tunda shi ba mazaunin Kano bane. Auren Hauwa gareshi ta kowanne bangare JIHADI ne maigirma kuma solution ga rayuwa da zukatan bayin Allah masu yawa. Ba sai don SO kadai ake aure ba.
Ya san dole ce ta sata yanke hukuncin kin yi wa Hauwa aure, amma ba don bata so ba, tunda burin kowacce uwa shine ta kai ‘yar ta gidan miji, idan ta isa munzali.
Ta amma ta wacce hanya zai fara? Wadanne matakai zai bi wajen ganin tabbatuwar hakan? Ya san dai wannan hukuncin da ya yanke daidai yake da a ce ya daukowa kansa Dala babu gammo. To amma ya shirya kinkimar wannan Dalar, ya dora a kansa, koda kuwa babu gammon babu gudu babu ja da baya, in sha Allahu ruwa ko iska babu mai hanashi aiwatar da shawarar da ya yanke shi da zuciyarsa ta sanya HAUWA’U CIKIN IYALIN SA.
Sai dai kuma ta ina zai fara? Abin nufi ta wane bangaren???
Ta matar sa abar kaunar sa masoyiyar sa GIWAR SA MADINAH? Ko kuwa ta rigimammiyar uwar Hauwa wato INNA SAFIYYA? Wadda ta ci layar ko dan shugaban kasa bazata bawa auren miskiniyar ‘yar ta ba don kada a tozarta mata ita sabida nakasarta?
Ko kuwa ta bangaren mahaifin sa ABBA PROF.? Wanda tun asali alamu sun nuna ko zancen su baya so? Koko ta bangaren MAMANSA Mai Shari’ah Haj. Maimunatu???
Kowanne daya daga cikin wandannan bangarorin ya dosa da hukuncin da ya yanke, ya san babu sauki wai ciwon arne.
Dr. Sarham ya aje numfashi, ya muskuta ya gyara kwanciyar sa ya koma rigingine, daga kwancen da yake yana hararo jan aikin dake gabansa. Ya san da gaske ya daukowa kansa DUTSEN DALA da na GWAURON DUTSE kai har ma da duka KOFOFIN KANO da BADALOLINTA bakidaya ya kinkima ya dora a kan sa.
Shin ko wa zai taya Dr. Sarham saukewa kansa nauyin wannan kuduri da ya dauka? Ni dai na san mutum mai kyakkyawar zuciya da kyakkyawar manufa a kullum mai nasara ne akan duk abinda yasa gaba. Kuma kamar yadda Hauwa tace ne shi din mutum ne mai ‘abstract reasoning’ komai cudewar lamari baya kasa warware abinsa. Don haka ina yiwa Dr. sarham fatan nasara da fatan alkhairi da taya shi fafutukar kaiwa ga cikar kudirinsa na alkhairi.