HAUWA KULU Book 1 Complete Hausa Novel

HAUWA KULU Book 1 Complete Hausa Novel

SHIMFIDA

NIGERIAN BAR ASSOCIATION
(CONFERENCE HALL)

W
ani irin cika dakin taron yayi, da manya da kananan lauyoyi wasu sun zo ne tareda iyalansu, wasu sun halarta babu iyali, a can gefe kuma a muhallin baki na musamman wakilan kungiyoyi ne masu zaman kansu (International NGOs) masu kare hakkin masu nakasa da tabbatar da ‘Equal Rights, Inclusion and Opportunities’ ga mutane masu bukata ta musamman.

Duk da cewa dakin taron bai cika girma ba, amma ya hadiye mutane da yawa da suka halarta. Wasu da yawa ba don taya ta murnar mukamin da aka bata yau suka zo ba, sun zo ne musamman don son ganinta ido da ido (don debe haso da kore shakku), na son tabbatar da jita-jitar da suke yawan ji akan cikar lafiyarta, a matsayin ta na ‘celebrity’ din Najeriya ga duniyar masu nakasa, wadda sunanta ya watsu, ya fantsama a kafafen yada labarai da soshiyal midiya. Haka muryarta ta dade da zamowa familiar (sananniya) ga kowa akan kwato hakkin nakasassu da kare martabar su (physically-challenged people) a arewacin Najeriya.
Wasu kuwa sun zo taron ne kawai ta hanyar ganin sakon gayyata a kafafen sadarwa wato sun zo ne don farin jininta shiyasa kawai suke son ganinta. Kwarai ita din mai farin jini ce ga kowa.
Kungiyoyin kare hakkin masu bukata ta musamman, su suka hada mata wannan taron na gani da ido (meet and greet), domin taya ta murnar karbar shugabancin kungiyar gamayyar lauyoyin kasa da aka fi sani da suna ‘Nigerian Bar Association’.
Wadannan kungiyoyin sun tsaya mata ne a dalilin tsayuwar ta tsayin daka wajen kare hakkin nakasassun arewa, da tsayawa cigabansu da ilminsu dana ‘ya’yansu, karkashin hadin guiwarta da ‘Sustainable Development Goals’ da kuma aikin da ta zaba na zama lauyar marassa ‘yanci da physically-challenged persons.

Bayan kasancewarta ‘SDG ADVOCATE’ har ila yau, lauya ce ita mai zaman kanta, wadda aikinta yafi karkata ga tsayawa ‘less-privileged’ da wadanda basu da halin daukar lauya ko akaci zarafinsu adalilin nakasa ko aka take hakkinsu na ‘yan kasa a dalilin nakasa, itace kan gaba wajen kare hakkin nakasassu a duk fadin arewa.

Lokacin data durkako dakin taron, wato (ta doso) cikin shiga ta kamala da kwarjini, hannunta yana makale cikin nasa, suna taku a hankali zuwa inda aka tanadar musu don tsayuwa tare. Sai aka mike don nuna girmamawa a gareta, da yawa yau da suka samu ganinta a zahiri sun ce a zukatansu “hakika *HAUWA* ganin ki ya fi jin ki!”
Duk da cewa wannan karon ma da bakin gilashin nata a idanunta. Hakan bai boye zahirin cikar zatinta da cikar kamalarta da iya adonta ba.
Bayan an zauna an nutsu, ta karbi lasifika ta fara da rero godiya ga duk mahalarta taron, da sauran zaqaquran lauyoyi ‘yan uwanta, da kungiyoyin da suka hada mata wannan muhimmin taron gani da ido da gaisawa, kungiyoyin ne masu tabbatar da cewa, mutane masu bukata ta musamman sun samu rabauta daga duk wani matsatsi na rayuwa karkashin tallafin ‘Sustainable Development Goals’ da take yi wa aiki partially, ta sake godewa kungiyoyin nan da suka roki ta fito yau, duniya ta ganta, a wannan ranar mai muhimmanci a gareta, kasancewar muryarta kadai aka sani a kafafan sadarwa, sun roki ta baiwa al’umma labarin ta, maiyuwuwa ya zamo ‘inspiration’ ga al’ummar da suka samu kansu cikin kwatankwacin irin ‘situation’ dinta.
Kungiyoyin sun hada da manyan kungiyoyin kare ‘yancin masu nakasa da tabbatar da cigabansu wato kungiyar ‘AGILE’, da kungiyar ‘Sight-Savers’, sannan kungiyar ‘Action Against Hunger’ da ‘PERL (Partnership to engage, Reform and Learn) ‘.
Ta kuma godewa manema labarai daga gidan rediyon BBC, karkashin jagorancin wakilin yada labarai na BBC a Kano, da gidan rediyon VOA karkashin jagorancin wakilinsu HAMZA MUSTAPHA MAWONMASE.

Sama da kowa, above all, and above all, tace tana godewa Uban ‘ya’yanta, wanda ta kira da suna “My PACE-SETTER….”.

Zazzakar muryarta ta cigaba da karade dakin taron ta cikin bututun lasifika, wadda murya ce da dama take familiar (sananna) ga kowa tun kafin bayyanar fuskarta a zahiri a ranar yau, a daidai sanda take cewa;

“Kamar yadda kowa ya sani sunana na yanka Hauwa-Kulu”. Hauwa shine sunan da aka yankamin rago dashi. Sau-tari idan na bushi iska musamman a lokutan nishadi na da son baiwa kaina farin ciki na kan bugi kirji in gayawa kaina da kaina,
“babu wanda ya kaini samun yin kuruciya mai dadi!
Na kan yi tunanin ai nafi duk tsararrakina jin dadin dabdalar kuruciya, dalilina na fadar haka shine nayi kuruciyata ne a zamanin da hankulan kasarmu da jihohin arewa bakidaya suke a kwance, sannan kuma dukkan iyayena Uwa da Uba suke a raye tare, ina jingine jikin su musamman Innata, ina rabar ni’imar dake tattare da kulawar Uwa da ta Uba a tare, cikin rayuwar rufin asiri irin ta kowanne talakkan Bakano.
Nayi yarintata a sa’ilin da muke cikin shekarar nan mai tarin abubuwan bada labari a kasarmu ta Najeriya, zamanin da sojoji suka kwace mulki daga hannun sibiliyan koko in ce musu (farar hula) cikin shekarun (late 80s), wanda lokacin da wayona mulkin Najeriya ya koma hannun mulkin soja, bayan mulkin (Alhaji Shehu Shagari)”.

Hauwa ta cigaba da cewa “a lokacin ana gudanar da wata irin rayuwa ne mai matukar sauki da hadin kai a tsakanin alummar jihar Kano, har ma da daukacin kasar Najeriya gabadaya irin wanda yayi karanci ko kuma ace babu shi sam! A halin da muke ciki a yanzu.
Ni Hauwa-Kulu nayi ‘yammatancina a zamanin mulkin Shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida.
A wancan lokacin da muke zance, kwanciyar hankali shine babban arzikin da al’umma suka mallaka, suka Kuma wadatu da shi ba tarin dukiya ta yaki-halak yaki-haram ba.
Koko ince a lokacin Ubangiji yayi mana ludufin arzikin kwanciyar hankali da wadatar zuciya sama dana komai, wanda yafi tarin dukiyar yanzu alfanu ga dan adam alhalin babu kwanciyar hankali, godiyar Ubangiji ya wadaci zukatan al’ummar BADALAR Kano da kewayenta, saboda kowanne talakkan birni a zamanin, in kayi duba na tsanaki zaka ga cewa ya iyawa talaucin sa, dai-dai gwargwado kuma daidai misali jama’a basa cikin halin wahala da kaka-ni-kayi; tunda kowa yafi karfin hatsi, wato duk tsananin talauci ba zai sa a kwana da yunwa ba, saboda ba’a damu da cewa lallai sai an ci mai dadi ba, ko sai an sha koko da sukari, ko sai an ci abinci mai maiko da nama, ko sai an sha shayi da madara, gidan talakka da gidan mai kudi kusan duk irin rayuwa daya ake yi babu banbanci, abinci iri daya ake ci, babu yi wa juna rowa, haka suttura kusan iri daya ake daurawa tsakanin matayen cikin badala duka, daga na masu kudi har na talakkawa.

Sanin kowa ne a lokacin babu ta’addancin ‘yan kasa da zaluncin shuwagabanni sosai, shiyasa ake cikin kwanciyar hankali da koshin ciki, wato babu masifar talauci da yunwar da har zata tunzura matasa sana’ar nan ta satar mutane da yin garkuwa dasu, sannan babu hadama da gasar rayuwa tsakanin mazauna badalolin Kano, kamar gasar motocin hawa, dana dogayen gine-gine, ko gasar sanya suttura mai tsada a tsakanin matan badala. Wannan a takaice shine misalin irin zamanin da ni Hauwa na taso a cikin sa, wato zamanin da duniya take a kwance lumui.
Babban kwanciyar hankalin da ake ciki a lokacin shine; al’ummar 70s da 80s basa cin bashin bankuna don su rayu, irin yadda ake ci a zamanin yanzu kamar yadda ake cin dussa, wai don biyan bukatun yau da kullum wadanda ba masu karewa bane.
Ga daukar zunubin kudin ruwa.
Shiyasa zaka ga duk tsananin talauci a lokacin iyayenmu basa cikin fargaba da zullumi, irin wanda tunanin bashi ke haddasawa magidantan yanzu, mai haifar da cututtukan kwakwalwa irin na damuwa da akeyi a zamanin yanzu wanda yake yiwa magidanta illa.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected