HAUWA KULU Book 2 Complete Hausa Novel
Tunda ya hawo jirgi yake tunani, Allah dai yasa Surayyah na kaiwa su Inna kudin da yake aikowa ta account din ta da yace ta dinga baiwa Sumayyah tana kai musu, ta san gidan, don sun taba zuwa tare, ya san dai Innar Hauwa jarumar uwa ce, cikin kowanne hali zata kula da kanta, kuma zata kula da Hauwa-Kulunta, ba zata bari ta zama (drop out from school) ba.
Dan abinda yake tura musu duk wata ya san zai ishe su cin abinci har wata ya zagayo, duk da ya san Inna bazata zauna haka babu sana’a ba, Allah yasa Sumayyahn kuma tana jure kai musu, kodayake Sumayyahn sa ba daga nan ba, wajen aikin zumunci da taya shi son duk abinda yake so, balle wadannan bayin Allah data fahimci sun mamaye rabin zuciyar sa!
Jirgin su ya taso daga Jeddah a washegari bayan sun yi sallama emotionally shi da Madinah a filin jirgi, yanata kissima abubuwa daban daban a ransa, wadanda zai je ya tarar a Kano, akan dai Inna da Hauwa, da rayuwar da suka samu kan su a bayan babu shi. Sarham ya sa a ransa ba zai koma Jeddah dauko matar sa Madinah ba wannnan karon sai ya mallakawa Inna wayar tafi da gidan ka komai kankantar ta, don dai ya dinga jin lafiyar su kai tsaye, ba tare da ya saka ‘third party’ a tsakanin su ba.
**** **** ****
T
axi din da Dr. Sarham ya dauko shata daga filin jirgi bata sauke shi a ko’ina ba sai a kofar gidan su. Wanda ke cikin rukunin gidajen malamai na sabuwar jami’ar Bayero.
Surayyah ce ta fara hango shi daga tagar dakinta, daidai lokacin ta dage labule don samun iska kasancewar ‘nepa’ sun yi mata halin su na dauke wuta tana tsaka da shaqar barcin rana cikin A.C, wani hucin zafi ya tada ta, don haka ba shiri ta tashi ta dage labulen ta don ta samu ‘natural’ iska ta shigo mata, wannan ne yasa duk gidan ita ta fara ganin sa yana fitowa daga mota.
Banda ‘jini’ sunan sa ‘jini’ da Surayyah bazata gane Bhaiyan Sumayyah ba sam, ko ta ce Yaya Doctor yadda take kiran sa ita, sabida girman da ya kara da irin canzawar da yayi a shekaru ukun da ya kwashe a kasar Saudi-Arabia, ilhamarsa da cikar zati sun karu, sun ninku akan wadanda ya bar gida dasu. Yayi haske kadan, fatar jikin sa ta yi ‘fresh’ kamar wanda ya shiga injin wankin fata.
Karadin Surayyah shi ya tashi Sumayyah dake falo a gaban TV tana kallon diramar Hausa, ta yo dakin nata a guje don ta dauka wani abu ne ya same ta, da karfi Surayyah tace, “Summy Bhaiyan ki ne, Yaya Doctor ke shigowa”.
To amma me? Sai ta tuno wani abu, wanda yasa nan da nan ta nutsu, ta daina murnar dawowar Bhaiya, gashi dai ya dawo ‘unexpected’, gashi ta masa babban laifi, tace cikin damuwa.
“Summy na dauka ba yanzu zai dawo ba, na saka a raina kafin lokacin da zai dawo na hada kudin nan na baki sakon nan na mutanen nan kin kai musu duka a dunkule”.
Sumayyah ta ce cikin mamaki “wane sako? Wadanne mutanen?” Cikin damuwar data fi ta baya Surayyah ta ce. “Ki min afuwa Summy, ban taba gaya miki Yaya Doctor yana aiko kudi ta account dina in baki ki dinga kaiwa mutanen nan nasa talakawa da ya likewa na kofar Na’isa ba, ni wallahi na ma manta, sai yanzu dana ganshi na tuna”.
Ta kara da cewa “Summy don girman Allah ki rufa min asiri in ya tambaye ki kice ina baki duk wata kina kaiwa, in yaso zan dunkule duka abinda ke hannu na a yau in baki ki kai musu kafin ya je gidan, wallahi cosmetics (kayan kwalliya) and other stuffs kawai nake karawa da su duk wata, saboda Mama bata yarda ta saya min irin wadanda nake so.”
Idon Sumayyah har rawa yake don bacin rai, da tsoro da mamakin abinda ‘yar uwarta ta aikata, har ta fara hango irin hukuncin da Bhaiya zai mata, ta fara hango shi ya dauke Surayyah da mari kodayae Bhaiya baya duka baya zagi, amma fa bai iya fushi bay a kuma kware da (silent punishment), fatar bakinta ma rawa take yi, ta kasa murnar dawowar tasa ma don haushi da mamakin Yayar ta Surayyah, da kyar Sumayyah tace,
“kin ci amana amma, Yaya Surayyah kin ci amanar Bhaiya, na rantse da Allah babu ruwa na, count me out of your dirty game”.
Daga haka Sumayyah ta fice da gudu tana “Oyoyo! Bhaiya, Mama Bhaiya ya shammace mu”. Sai ga Mama ta fito daga dakin ta itama kan ta ko kallabi babu, tace “really?” Surayyah kuwa bayan gida ta shige ta boye kanta, jikin ta ba inda baya rawa.
Sumayyah ta kusa kai Sarham kasa sakamakon tsallen da tayi ta shako shi da sunan murna. Haba! Sarham sai ya balle da fada blah! Blah! “Sumayyah meye haka? Baki san kin girma bane? Ko an ce miki da da yanzu ma daya ne? Bana son irin wannan haukan welcome din, an wuce wajen, kada ki kara”.
Mama ta iso falon tana cewa “kai mai hali dai baya fasa halin sa, kai kuma daga zuwa sai fada kamar tsiduhu? Shekara uku ba kwana uku ba basu saka ka a idon su ba, ba dole su yi murnar ganin ka bagatatan yau ba?”.
Sarham ya mike ya isa gareta ya kama hannayen Mama ya rike cikin tafukan sa, yana murmushin farin ciki ya kai su ga fuskar sa kan sajen sa, wanda a baya kafin ya tafi bashi da shi yace “My Mommah, I missed you badly kin sani. Amma autar ki bata san ta girma ba, kullum tana nan jiya I yau shiyasa bazan daina fada ba”.
Kafin kace meye wannan gida ya kacame da murnar dawowar Dr. Sarham. Da Abba Prof. ya dawo murnar tafi armashi, a ranar har dare suka raba a falo suna hirar yaushe gamo, amma an nemi Surayyah an rasa a falon, tunda ta zo ta yi masa sannu da zuwa ta gudu gidan Kakar su Haj. Kulu a gadon kaya, don tayi-tayi Sumayyah ta karbi ‘yan kudin da ke hannun ta ta kai Kofar Na’isa, ta roke ta kan ta rufa mata asiri tayi maza ta kai musu tun kafin Yaya Doctor ya huta ya waiwayi zancen, wadanda ko kwatan abinda ta kashe daga abinda yake aikowa din basu kai ba.
Sumayyah ta ki amsa, ta kuma ce in ta takura mata ta cigaba da saka sunanta cikin laifi nan wallahi zata tona ta, “kawai ki yi harkar ki Yaya Surayyah ki rabu da ni, ni ba maciyiya amana bace kuma ba’a shirya rashin gaskiya da ni”.
Duk da ta san Sumayyah ta gaya mata bakar magana sosai amma ta kasa cewa komai wannan karon, girma da mutunci ai madara ne, kuma mutum shi yake rike kayan sa, ta yarda ita ta zubar da girman ta har Sumayyah kanwar bayan ta yau ta nemi zagin ta (in disguise). Don haka Surayyah ta ga gara ta gudu gidan Hajiya, inda ba abinda Sarham ya isa yayi mata in dai a gaban Hajiya ne koda ta bare da ita.
Washegari walima sosai Mama ta hada musu a babban falon ta, ta murnar dawowar Sarham da kammala zurfafa karatunsa, wato kwas din da ya je yi na tsayin shekaru uku a (KAU, Jeddah) ta kasar Saudi Arabia, don haka aka tura direban zuwa Abba Gadon kaya don ya dauko Hajiyar Gadonkaya.
Jin maganar zuwan direba daukan su daga bakin Maigadi yasa Surayyah duk ta damu, lokacin da da aka ce su fito a tafi gidan Abba, Hajiya tace ta shirya su tafi gidan nasu tare, ta yaya ana can ana murnar zuwan dan uwanta da taya shi murnar zama babban likita zata taho ta zauna ita kadai anan kamar mujiya a cikin ‘yan uwanta?
Tace lallai ta shirya su wuce, bazata bar ta ita kadai a gidanta ba.
Da Surayyah ta ga ba sarki sai Allah sai ta fadawa Haj. Gaskiya cikin damuwa, cewa laifi tayi masa fa, bata so ya kure ta, don zai iya dukan ta, Hajiya kuwa ta saka ta a gaba tace sai sun tafi taren, mai dukan mata ita sai ruwan sama.
Mama da hannun ta tayi girke-girken walimar nan, don haka sun kwashi gara mai dadi sosai. Sarham yayi wa girkin Maman sa cin yaushe rabo! Da sweet cook din Mama!? Ba abinda bai ci ya hantse a wajen ba. Da yake magananne ne har gobe tunda ya fara cin abincin nan bai yi shiru ba, yana yi ne yana zuba santi, saida Hajiya Kulu ta saka masa filon kujera a kuturin sa, tace, “gara a saka maka waigi haka likita Sarhamu, Allah yasa dai matar duk da zaka aura mai iya girki ce.
Shin ma ina aka kwana kan maganar aure? Wannan karon kam zan bada cigiyar mata har a masallatai idan bakin jini ne ya hana ka samun mata”. Daga Abba har Mama duk suka bi shi da ido kamar Hajiya ta ci musu albasa ne ta fadi abinda ke ci musu rai, suka dakata da cin abincin suma suna jiran amsar sa da zai fada, da alama dukkannin su suna da wannnan damuwar tuntuni kawai Hajiya ta riga su furtawa ne.
Ai yau Sarham da karfin guiwar sa ya ce “ki kwantar da hankalin ki Hajiya, ba sai kin kai tallata a masallaci ba, an riga an bani mata cikin daraja da kima kuma wadda nake so tuntuni, ku ake jira ku je tambaya da sanya lokaci”.
Mama da Abba har suna hada baki wajen tambayar sa.
“Daga ina ka samo matar kuma ‘yar waye a Kano a ina suke? Tun yaushe kuke tare bamu da labari?”
Yace “Mama zaki iya tuna yarinyar dana ke tare da ita tun zuwana karatu MBBS na farko? Ina nufin MADINAH. Ke ai kin jima da sanin labarin ta, wadda a baya mahaifin ta yace bazai bani ba, to ita din ce dai muka sake haduwa a wannan karon muka sulhunta, mahaifin ta kuma ya bani auren ta already ku kadai yake jira, ‘yar gidan Attahiru Habibu SoronDinki ce”.
Mama da yake ta san zancen Madinah tuntuni nan da nan ta ci magani, fuska a gintse tace “shima ai ya sani” (tana nufin Abba Prof.) ta kara da cewa “ko ba yarinyar da ka kusa kashe kanka a kanta ba, saboda uban ta ya wulakanta ka? Yarinyar da ka zauna shekara bakwai cikin tuzuranci babu aure saboda an hana ka ita, sakamakon cewa sun raina arzikin mu da mutuncinmu? Itace ko ba ita bace?”
Sarham yayi shiru, gaban sa da zuciyar sa na wani irin faduwa, tsoron sa Allah tsoron sa kada Mama tayi (opposing) maganar Madinah, shi kam da ya shiga uku, don in har ba Madinah ya aura ba, babu shi babu aure a duniya (ya fada a zuciyarsa).
Abba ya ce “Lelen Abba rabu da Mama, yi min cikakken banyani, diyar Attahiru Sorondinki wanda na sani ce da gaske? Ina nufin na ISDB? In haka ne kenan jikar Alkalin Alkalai Habibu SoronDinki kake nema kenan fa?”
Sarham ya dan samu kwarin guiwa da hope, domin a muryar Abba kawai ya ji ‘excitement’ na sanin iyayen Madinah da yayi, kamar zai yi na’am da maganar shi kam. Yace,
“sune Abba, his last daughter Dr, Madinah Attahiru”. Da rashin karsashi a muryar sa ya baiwa Abba tarihin su Madinah da iyayaenta kamar yadda ya ji daga bakinta, da kuma na rayuwar su a Jeddah itada mahaifanta da ‘yan uwanta maza, inda a can aka haife su itada wasu daga cikin yayyen nata, da yadda mahaifin ta ya raba su a baya, yanzu kuma su da kan su suka neme shi ba shi ya nemi Madinah ba ta dawo masa ba, har pretending din da yayi tayi mata don kada ya koma mata ya gaya musu, da kiran sa gidan su da Daddyn nata yayi, domin ya bashi hakuri da uzurin sa na hana shi auren Madinah.
Amma abin mamaki duk da wannan labarin da Sarham ya bayar Mama taki saukowa ta amshi zancen Madinah da hannu bibbiyu, musamman da taji wai har aure an daurawa Madinah bata tare ba mijin ya rasu, sai ta kara ninka ‘opposition’ din ta da zancen, inda tace cikin mamaki,
“Sarham! Kai kuma inda Allah yayi da kai kenan saboda soyayyah? Bazawara/widow zaka dauka kana saurayi wanda bai taba aure ba? Bazawara fa kaikuma saurayi? Ni ban yarda wai bata je gidan mijin ba, sun dai rufa ka ne don su sayo mata matsayin budurwa, shiyasa ko lefe aka ce ka bari, kai kuwa saboda Allah me Madinar nan ke da shi da sauran mata da kake gudu suna rububin ka basu dashi?”
Abba yace “Maimuna har gobe baki san SO ba na ga alama, kyale rai da abunda ya afu ga so, aure kuma ai ba kaskanci bane daraja ne, haka mutuwar miji baya nufin darajarta ta ragu, ni ban ga laifi anan ba don yarinya ta taba aure, shin Manzon mu ba da bazawarar ya fara ba?
Yarinyar nan ‘yar manyan mutane ce kuma ‘yar babban mutum, sama da abunda yafi haka zasu iya cewa kafin su bada auren ‘yar su, aka ce tuwon girma… miyar sa nama Maimuna, ko yanzun ba don ta rasa miji bane yasa suka bashi, a’ah, ya ci darajar soyayyah ne kawai Allah kuma ya tsaga cewa ita din rabon sa ce”.
Mama tayi shiru amma ta ki gamsuwa, ta ce “ni kawai ko ‘yar shugaban kasa ce bai dame ni ba, tunda suka raina arzikin mu tun farko nima na raina mutuncin su, saboda basu yi amfani da ilmin su ba anan don wallahi ba yabon kai ba, Sarham dina ya wuce raini, tunda Allah ya bashi addini, nasaba, ilmi da basira to ya gama bashi duk wani arziki na duniya koda kuwa a kan jaki yake yawo”.
Duk aka yi wa Mama dariya Abba yace “Maimunatu Dan farin? Kike wannan zakewar a kan sa babu fulatanci? Ina fulatancinki ya tafi ne?” Ta yi fuska sosai ta ci laya tace “ko rabin farko ne shi ba Dan fari ba, ina son abuna yadda suke so ‘yar su koma fiye, sun dauko sudin kwano sun bashi, ina dalili da gatan sa shima da komai?” Abba yana danne dariyarsa yace.
“Barr. Maimunatu to yaya zaki yi? Tunda shi ya ji ya gani yana son leftover din nasa a haka?”
Sarham dai bai ce komai ba kansa na kasa, kamar yace da kasar ta tsage ya shige, amma ya ji ciwon kalmar nan ta an bar masa sudin kwano, ta kara rura wutar kishin sa akan auren Madina da AVM Alkali. Duk ya daina dokin auren ma, Madinar ta kara bashi haushi, amma baya jin ruwa da iska zai fasa karbar auren Madinah ko da ta haihu goma da AVM wanda ke nufin so na hakika yake yiwa Madinah.
Abba da Hajiya Kulu, suka yanke shawarar wadanda za’a tura Sorondinki daga waliyyan Sarham don gabatar da zancen aure don itama Haj. Kulu tayi na’am da zancen dari bisa dari don kuwa ta san Kakan Madinah farin sani marigayi Alkalin Alkalai wanda tace zuri’arsa ne kaf suka samar da Sorondinki.
A daren Abba Prof. kwana yayi yana lallashin Mama cikin dabara da soyayya irin ta manya akan maganar auren Sarham, yace mata abu daya zata duba kawai; son da Sarham yake wa Madinah, in ta duba wannan to sai ta sakawa ranta salama.
Domin shi ya lura son da Sarham yakewa Madinah mai yawa ne, tunda har ya iya kwashe shekarun nan babu aure saboda rashin ta, kuma jin ta auri wani kafun shi, bai say a ce ya fasa ba.
Ita kuma Mama irin iyayen nan ne masu kishin ‘yayan su, wannan son da ake fadi yana wa Madina shi yafi komai bata mata rai, don a tsarin ta sam bata son Sarham ya auri macen da son da yake mata ya zarta wanda take masa, ko wadda zata zo ta canza masa behaviours da alaqarsa dasu. A ganin ta son da yakewa Madinah yayi yawa har ya zarta nata son, ba don haka ba ai da bata yarda ta auri wani kafin shi ba, tana tsoron kada Madinah tayi amfani da hakan ta bautar mata da shi, ko ta wahalar mata da shi tunda ta zame masa rayuwa dungurungum. Duk da ta san Sarham jarumi ne akan komai nasa ko a cikin maza, kuma tsayayyen namiji ne tun yana yaro akan ra’ayinsa, amma tana tsoron wannnan matsiyacin son da yake yi wa Madinah Attahiru.
Haka Abba Prof. ya samu ya lallaba ‘yan kayan sa, don shikadai yasan abinda yake zuciyar Mama, ya nuna mata in bata cire kishin matar Sarham daga ranta ba zata zubar da girmanta, kuma zata sha wahala don matsayin kowaccen su daban a wajensa, ya roketa kada ta zama fitinannun iyayen mijin zamani masu tsanar surukansu babu gaira babu dalili kawai don yaransu na son su, tunda itama ba haka Hajiyar Gadonkaya tayi treating dinta ba duk da ta san son da Abban yayi matukar yi mata, da haka ya samu ya lallabata har dai ya samu lagonta ta amince aje akai kudin auren, ta kuma sakawa al’amarin albarka.
Washegari waliyyan Sarham suka tafi SoronDinki. Suka dawo da albishir mai dadi na cewa Baffanta yace Juma’ar nan za’a je a daura auren a babban masallacin juma’ah na Kano, su sun shirya tuntuni, su suke jira dama. Suka kuma fadi irin karbar mutunci da saukar girma da aka yi musu, wannan ya kara sauko da zuciyar Mama.
Iyayen Sarham sun gabatar da komai na auren har sadaki ga kanin Baban Madinah tun kafin juma’ar ta zo, kuma Baban Madina yana ta kara jaddadawa kanin shi ta waya ya gaya musu shi baya karbar lefe, sadaki da kudin aure kawai yake amsa. Wannan ma ya kara sanyayawa Mama. Juma’ah na zagayowa aka daura auren.
**** **** ****
Tun dawowar sa Najeriya Sarham bai samu nutsuwa ba ko ta kwabo, sai yau da aka daura auren sa da Dr. Madinah Attahiru bayan saukowa daga juma’ah, mahaifin ta da duka ‘yan uwanta maza hudu sun samu sun halarci dauren auren, Madinah ‘yar dangi ce gaba da baya kasancewar auren zumunci ne a tsakanin iyayen ta, sun kuwa nunawa Hajjah Ramlah zumuncin da karah, don kwansu da kwarkwatarsu zuri’ar Sorondinki sun yi dafifi a ‘main house’ din su, don halartar yinin bikin Madina a ranar da aka daura aure.
Iyayen Madinah su ya kamata a kira masu Kano, ba kuma wai sarauta ce dasu ba domin iyayen ta da dangin ta na uwa dana uba wadanda duk abu guda suke, sun kame duk wasu madafun iko na Kano.
Sai bayan daurin aure ne, da ya samu ya huta ya samu nutsuwa bayan mutane sun watse, a daren daurin auren ya samu ya zauna da Sumayyah yana tambayar ta yaya labarin su Hauwa da Inna?
In ce ko tana zuwa tana gano masa su da baya nan kamar yadda ya bar mata sallahu? Kuma in ce ko duk wata tana kai musu sakon da yake aikowa ta hannun Surayyah?”
Ya tsare ta da kaifafan idanun shi ganin yanda tun bai gama magana ba Sumayya ta shiga cikin rudani da damuwa, na farko dai itama ta mance da su Hauwa, bata kara tunanin zuwa kofar Na’isa ba tun bayan tafiyar sa, na biyu ga abunda Surayyah tayi, wanda ke nufin dukkan su sun zama masu laifi ga Bhaiya, sai dai a ce laifin Surry ya take nata wato, sawun giwa ne ya take na rakumi.
To amma ta kwana da sanin halin Bhaiya baya son yayi maka tambaya wadda a wurinsa mai muhimmanci ce ka zuba masa na mujiya nan da nan zai harzuka, sai duk ta daburce, ta hau inda-inda da in-ina, tana son cewa ba ita bace Surayyah ce, tana kuma son kare Surayyar.
Kawai sai jikin sa ya bashi babu gaskiya acikin al’amarin ta, ko wani abu mummuna ya faru dasu Inna a bayan tafiyar sa, gabansa yayi mummunan faduwa ya fiddo wayar sa ta tafi da gidan ka daga aljihun gaban farar shaddar shi Wagambari wadda ta sha maikon sabunta, Ango sosai, sai walainiya yake yi a cikin farar Excelcior din, yasa dan yatsan sa daya yana dannawa Surayyah kira, tana amsawa yace ta same shi a karamin falon Mama.
Tun daga jin kiran sa itama Surayyah ta hau numfarfashi ta san ta gama barewa, a lokacin suna tare da wanda zata aura a harabar gidan su wato Engnr. Aliyu Barde, wanda dan abokin Baban su ne, iyayen su suka hada su, Aliyu ya fahimci hankalin ta ya rabu gida biyu tun bayan amsa wayar ta, yace “me ya faru ne a wayar?” Surayyah ta dauki excuse daga wajen Aliyu kan Yaya Doctor dinsu yana kiran ta a cikin gida, ko zai bata minti goma?
Egnr. Yace ai tafiya ma zai yi don akwai inda zashi, don haka suyi sallama kawai, sai wajen jibi zai dawo. Don lokacin an saka musu lokacin aure.
Bayan sun yi sallama ya tafi, Surayyah ta taka zuwa cikin gida tana tafe salalau-salalau kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki.
Sarham har ya gaji da jiran shigowar ta ya mike zai biyo bayan ta yana huci sai gata tana shigowa. Tun kafin ta zauna ya jefo mata tata tambayar kamar yadda yayiwa Sumayyah game da sakon su Inna da yake turowa ta account din ta duk wata, yau shekara uku bai taba fashin turowa ba, wanda yace a dinga kaiwa mutanensa na kofar Na’isa.
Surayyah tayi zuru-zuru ta yi wiki-wiki da ido tayi masa shiru, kiris ya rage ya mare ta, don baya son halin ko’in kula in yana maka maganar da a wurin sa mai muhimmanci ce, kayi shiru ka zuba masa ido kamar tsohon maye kana kallon sa.
Da kyar Surayyah ta motsa baki ta ce cikin rawar murya “I’m sorry Yaya Doctor!” Ta kara cewa “I’m so sorry” “Sorry for what?!” Ya tambaya (in exclamation).
Sumayyah kanwarta wadda ta soma hawayen ganin yadda ransa ke hauhawa wajen baci tun ma kafin yaji laifin da Surayyah tayi masa, taga basu da mafita banda ta gaya masa gaskiya, sai tace.
“Bhaiya, maganar gaskiya ko sau daya bata taba bani komai tace in kai musu ba, sai ranar da ka zo take gayamin ai kayan kwalliya take saye da kudin, ni ma kuma ban taba zuwa duba su ba, wallahi na manta hanyar gidan sam, lokunan (are complicated), don haka dukkan mu mun yi laifi Bhaiya, muna rokon ka in ka tashi hukuntamu, to kayi mana sassauci a hukuncin ba don halin mu ba, ka yi mana uzuri da ajizanci irin na kowanne dan adam”.
Sarham ya kasa magana don takaici sai raba ido yake a kan su su biyu, amma kalaman ta na karshe sun yi tasiri sosai a cikin ran sa dake tafasa, ya ciza fatar bakin sa kadan, yana kallon su da lumsassun idanu duk sun zama unease, kada Surayyah ta ji labari, wadda ta kasa zama tana daga tsaye har lokacin amma kafafun ta rawa suke. Da kyar Sarham ya hadiyi miyau, yace cikin sanyin murya.
“My only two and beloved Sisters ne suka ci amana ta haka?!”
Sumayyah ta cigaba da hawaye tace “wallahi Bhaiya babu ruwa na, bata ma taba gaya min ba ni sai ranar da ka dawo.
Ni nawa laifin na rashin zuwan maka ne kawai, da kuma rashin taya ka kula da abinda kake so a bayan idanun ka, wanda ko kadan baka cancanci hakan daga gare ni ba. Kamata yayi ace ko kare ka ajiye don kana son shi ya kamata in kula maka dashi in your absence balle mutane ‘yan adam.
Na yi kuskure Bhaiya, amma na tuba, ka karbi hanzari da uzuri na, ajizanci ne na dan adam da mantuwa, na tuba Bhaiya bazan sake ba”.
Sumayah ta durkusa a gabansa ta daga hannu cikin roko, hawaye na bilbila, Surayyah ta kasa kare kanta amma hakika yau ta ji kunya, ta kuma yi nadama a lokacin da bata da amfani, wato lokacin da ko ta bada sakon ba zai yi masa amfanin komai ba tuda ya riga da ya dawo, gashi ta san ta sirewa dan uwan nata yanzu, saboda rashin amana, koda bai fada ba bai kuma bai doketa ba.
Mama ta shigo da sauri jin kukan Sumayyah, tana tambayar su “me ke faruwa ne haka a falon nan ake kuka har da kururuwa?”
Sarham ya ce cikin kololuwar feeling of disappointment “Mama kin gan su, su duka sun ci amana ta!” Mama ta ce “kada Allah ya nuna mini ranar da zan haifi Da maci amanar dan uwan sa, sun dai yi kuskure wanda ba wanda yake sama da aikata shi, ka yi hakuri Sarham ka yafe musu kaji! Duk da ban san girman laifin ba”.
Sarham ya dubi Surayyah (feeling disappointed) ya ce “Surayyah idan abinda kika yi kyautatawa ne ga zumunci na da ke, na gode. Allah ya saka da alkhairi.
Ke kuma Sumayyah baki yi min laifin komai ba, amma daga yau na san matsayina a wajen ki, na kuma ga ajin da kika ajiye ni, tunda bazaki zame min ‘yar uwar da a bayan raina zata kula da haula ta ko abinda na bari ba”.
Sai ya sa kai ya fita, makwallaton sa har motsi yake don tsananin bacin rai, ba tare da ya tsaya yi wa Mama bayanin laifin da suka yi masa ba.
Mama duk suka saka ta a duhu, ta rasa gane komai, sai da Sumayya ta share hawayenta ta gaya mata komai cikin muryar kuka.
Mama ta kasa tuno mutanen da ake matsalar a kan su, ta san dai ire-iren jama’ar sa ne da baya rabo da kyautatawa, da irin jajibe-jajibensa, amma hakika ta harzuka da abinda Surayyah ta yiwa Yayanta, bata san ko su waye wadanda yake turowa kudin ba duk wata tun daga Jeddah ba, ba kuma tareda ta damu da ta sani ba, amma tunda har ya dauki tsahon shekaru uku yana turo musu kudi duk wata bait aba mantawa ba to masu muhimmanci ne a wajensa, kasancewar ta san halin sa akan son tamakawa mutane da son kyautatawa na kasa da shi da marassa lafiyansa, sai hakan bai zame mata wani sabon abu cikin halayen dan nata Sarham ba, Mama tace.
“Da gaske wannan cin amana ne, kuma zai fi bakanta masa rai ne kasancewar mutane mafiya kusanci da shi ne suka yi masa”, ta dube su cikin fushi ta sake cewa “a duniyar nan in dan uwanka ciki daya bai rike maka amana ya rufa maka asiri ba, in bazaku kashe ku rufe kai da shi ba, ba tareda ko iyayen ku sun ji ba, waye zai yi maka?
Sannnan da wa zaka yarda a duniya, kuma da wa zaka aminta?
Kin yi kuskure Surayyah, ba dan uwa irin naku ake badawa kasa a idanu ba, saboda shi din dan uwa ne har dan uwa guda har da rabi, ko in ce Yayan da babu irin sa, ko don son da yake muku da kulawar sa da kyautayinsa gare ku”.
Surayyah ta gama dukkan nadamar da mutum zai iya, a lokacin da yasan bai kyauta ba aka kuma ankarar dashi. Cikin kuka ta ce.
“Mama don Allah ki bashi hakuri, na tuba na bi Allah na bi shi, zan biya shi duka kudin sa da zarar na fara aiki, dama ban kashe da niyyar bazan biya ba, kawai ya zo ba ‘notice’ dina ne, nayi niyyar in bata ta kai musu kafin lokacin zuwan sa, wallahi zan biya shi”, Mama ta wani harareta ta ce “ta baya ta raggo.
Duk abinda zaki biya shi yanzu bazai karba ba, kuma bazai masa amfanin komai ba. Surayyah an yi bokon banza tunda shi ya koya miki son abin duniya, kayan kwalliyarbanza kayan kwalliyar hofi, saboda Allah da me iyayen ki suka rage ki banda son kyale-kyalen ki na banza da wofi da kika dorawa kan ki tun shigar ki jami’a, da son lallai sai kin hada kafada kin goga da kawaye da suka dauki karyar rayuwa suka dorawa kan su?
Kullum ina nuna miki ‘reality’ akan barin sayen abubuwan nan masu tsada da suka fi karfin aljihun ki ko na iyayen ki, kina ganin kamar ni kaina ban waye ba, tunda bana sayen turare su ‘designer’ sai Humrah sai Oud, har ni zaki nunawa sanin ya kamata akan rayuwar duniya Surayyah? Yaushe aka haifeki har kikayi wayewar??”
Mama tayi ta fada ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, daman tana cike da halin Surayyah din kan irin tsarin rayuwar ta mai tsada, fadan da Sarham bai tsaya ya yi musu ba don bacin rai shi Mama tayi ta yi musu ta wanke Surayyah tas. Wankin babban bargo. Surayya dai sai hakuri take baiwa Mama ganin har tafi Sarham daukar zafi da al’amarin.
Aka ce dan uwa rabin jiki, ganin yadda duk ta muzanta sai ta koma baiwa kanwar ta Sumayyah tausayi, Summy ta ji kamar a maida laifin ya koma kanta, ita a cigaba da yi mata fadan ita kadai, ta koma taya ta suka yi ta baiwa Mama hakuri da rokonta kan ta bashi hakuri in ya dawo, sunyi alkawarin bazasu sake yin kuskure makamancin wannan ba, Sumayyah dai ta ari laifin suka yafa shi tare da ‘yar uwar ta.
**** **** ****