HAUWA KULU Book 2 Complete Hausa Novel
SARHAM
D
a ya fita cikin zafin rai, wata motar Abbansa (Peogeot 504) ya dauka wadda tun saukarsa da ita yake amfani, kasancewar bai kai ga sayen motar kansa ba tun dawowar sa, ya fizgeta a guje ba tareda ya san wajen zuwa ba, yana dai so yayi nesa da gida don shi kansa ya san bai iya fushi ba, baya son ‘yan kannen sa su ga launin fushin sa mara kyau, ana he’s jovial amma in yayi fushi kamar zawayi yake komawa don rashin hakuri, musamman akan Surayyah da baya son wasu halayenta.
Sai ya samu sitiyarin nasa na sarrafa shi, ya dauke shi yayi hanyar titin da zai sada shi da kofar Na’isa. Yana tafe yana gayawa kan sa ya yafewa Surayyah duniya da lahira, ya yafe mata, amma hakika ta ragewa kanta matsayi a idon sa. kuma ‘outing’ din da yayi niyyar fita dasu zuwa Dam, don tayata murnar kammala degree ya gayawa kansa ya fasa.
Duk da Mama ta ce zata bashi hakuri inya dawo, amma hankalin su su duka bai kwanta da fitar sa cikin fushi ba da kuma ganin tsayin lokacin da ya dauka bai dawo gidan ba.
Ya isa kofar Na’isa da yamma lis, ya karya kan motar sa zuwa titin da zai kai shi lokon su Hauwa, yana tafe yana tunane-tunane akan su, ko a wane hali zai same su? Ko Hauwa ta gama makaranatar sakandire yanzu? Ko yaya suke rayuwar haka babu tallafin kowanne namiji? Ko Baban su Malam Bilyaminu ya dawo? Ko yaya idanun Hauwa? Allah Masani! Bai san meyasa zuciyar sa ta damu da al’amarin su ba, take kuma daraja su, yana saka damuwar su a ran sa in ya tuna a hannun sa Hauwa ta karbi shaidar makanta da lasisinta, daga zuwa neman magani. Shi ya san da ace ba shi yayi mata aikin nan ba, da bazai damu ba don an samu mishkila.
Har gobe kuma ya kuma kasa yafewa kan sa a kan makancewar Hauwa, ya ki cire abun a ran sa, duk da ya san kaddararta ce, shima kuma ba yin kansa bane amma har gobe Sarham yana ganin negligence dinsa ne wato (sakacinsa da rashin iya aikin sa), su suka janyo har Hauwa ta kai ga rasa idonta completely.
Haka tunda ya tafi Jiddah yau shekara uku bai taba kasa tuno su ba kullum, har Allah-Allah yake a yi albashi don kawai ya tura musu, ranar Allah dai-dai ce da baya tuna su, tare da yi musu addu’a da fatan alkhairi. Ya san kuma kudin da yake aiko musu daga albashin sa zai ishe su kananan bukatocinsu na yau da kullum da makarantar Hauwa.
Bayan motar Abban sa da ya tuko, shake yake dankam da tsarabar su Inna rankatakaf! Wadanda tun daren jiya ya saka su a mota yana jiran ya samu nutsuwa ya je kofar Na’isa, yayi ido hudu da Innar sa Safiyya, don ba Hauwa yake kewa ba Inna yake kewa. Eh mana, Hauwa da bata son sa kuma take kullace da shi. Hauwa danger Hauwa hukuma.
Har sabuwar waya nokia karama ya sayowa Inna, da alkawarin yanzu in ya koma Jiddah kai tsaye zai ke kiran su. Idan har Hauwa ta kammala sakandire da kyakkyawan sakamako ya fara tunanin bincike akan yiwuwar cigaba da karatun ta a jami’a, idan hakan mai yuwuwa ne.
Zai nemi dai wanda zaiyi ‘coaching’ din sa akan ilmin ‘visual impaired’, ba zai koma Jeddah ba sai ya tabbatar rayuwar su bata da matsala ta zama ‘stable’ kuma Hauwa na kan turba ta tafiya zuzzurfan ilmi.
Wanda shine kadai zai zame mata gata a dukkan rayuwar ta, a matsayin ta na mai nakasar da ake kira mutuwar tsaye.
To amma me? Sai zuwa yake yana dawowa a inda ya san lokon gidan su Inna yake situating, amma baya ganin gidajen da ya sani a wurin sai fili fetal. Da aka zagaye da langa-langa. Ya ilahi! Ko dai yayi batan kai ne? Ko makuwa yayi? ko kuma ya manta hanya ne?
To amma da mamaki ai ace ya mance hanyar gidan su Hauwa, ko shekaru goma yayi baya nan ba uku ba, in dai ba juyewar kwakwalwa ya samu ba ko shafewar tunani wato ‘amnesia’. Kuma dai ga Kofar Na’isan nan dai tana nan bata je koina ba.
Da ya gaji da zuwa da dawowa wato ya gaji da safah da Marwah a cikin mota sai ya fito yayi ta zagaye wajen da kafafun sa, amma ya kasa ganin gidan Malam Bilyaminu, ya kuma tabbatar anan gidan yake, sai ma yaga ‘pure water’ na leda ake bugawa a filin wajen. Kamar an maida wajen kamfanin ruwa leda.
Ya tambayi wani saurayi cikin masu buga ruwan ledan don Allah ko inane gidan Malam Bilyaminu dan Kofar Na’isa? Ya ce da saurayin “kamar na maku, don na jima bana nan”. Saurayin yace shima bako ne a unguwar, amma bari ya hada shi da Malam Isa mai faskare shi da ya dade a unguwar.
Gidan malam Isa ne kawai ba’a rushe ba cikin gidajen wurin don gidan yayi gefe sosai, saurayin ya raka Sarham suka samu Malam Isa a zauren gidan sa yana aikin itacen sayarwar sa, ya yiwa Malam Isa bayanin wanda Sarham ake nema ko ya san shi? Wai gidan Malam Bilyaminu.
Malam Isa ya bar abinda yake yi ya juyo ga Sarham sukayi musabiha, sai ya bashi wajen zama kan buzun sallahr sa yace ya zauna, da ya tambaye shi ko wa yake nema a gidan Malam Bilyaminu? Sarham yace.
“Innar Hauwa”.
Sai Malam Isa ya tambayi Sarham “kana da alaqa da Innar Hauwa ne?” Sarham yayi dan jim! Kafin yace “eh, amma na dade bana kasar, ina fatan ba wani abu ne ya faru da su ba?”
Malam Isa ya nisa yace, “eh toh, samari, ai Innar Hauwa ta gamu da sharrin wani azzalumin kanin miji, ya sayar da gidansu, rana daya muka ga an zo ana rushe gidan, aka maida wurin wajen hayar neman kudi kala-kala, na so ta zauna mu je kotu a kwato musu hakkin su ni da sauran makwabtan su, kasancewar a gaban mu Zakari ya sayarwa da dan uwan sa gidannan aka raba rigima tun a lokacin a gaban marigayi mai unguwa, amma matar nan ta ki tsayawa, ta gudu daga gidannan bamu sani ba, yau kusan shekara uku zancen nan da nake maka, bamu kara jin duriyar su ba ita da ‘yar ta Hauwa-Kulu”.
Sarham ya ji idon sa har rawa yake banda fatar idon dake raurawa itama, da kyar ya iya yace wanene kanin mijin nata? Ya ce.
“Zakari sunan sa, don kawai dan sa ya zo yace zai auri Hauwa-Kulu, shine ya sayar da gidan don ya kore su ko ince yasa aka rushe shi, to ya ci galaba kam don daga ranar da aka zo aka rushe gidan su basu kara waiwayar kofar Na’isa ba, kuma ba wanda ya kara jin duriyar su, ina tabbatar maka bazasu zauna a Kano ba yadda suka fita a tagayyare, wutsiya zage, kuma cikin mummunan bacin rai.
Jifa aka dingayi da komai nasu. Tausayi yasa na tattara tumakin ta da akuyoyin ta na kado su gida na, na hada na nawa na cigaba da kiwata mata, muje in nuna maka su cikin shekaru uku gasunan suna ta hayayyafa ban san ya zan yi da su ba”.
Sarham ya rasa a halin da yake ciki tsakanin tashin hankali da gigicewa, yace da Malam Isa “basu da wasu ‘yan uwa da zasu iya zuwa wajen su?” Malam Isa yace “eh, toh, ai dukkan su ‘yan cikin Badalar nan ne a sanin da muka yi musu, in ma suna da su, to mu bamu san su ba, basu da wasu ‘yan uwa da bamu sani ba, dangi kam sun kare ai, kuma bana jin a zuciya irin ta Innar Hauwa zata yarda ta rabi wani nata in ma tana da shi.
Tun tali-tali tanada wani irin hali, tafi gane rayuwa ta tsayuwa akan kafafun ta fiyeda ta rabu da wani ya taimaka mata, har kuwa bayan batan mijinta, bata taba neman taimakon kowa ba”.
Sarham yace “shin a ina wannan Zakari din yake?”
Zai so kwarai yayi ido hudu da wannan Zakarin, don kwatarwa su Inna hakkin su, zai so kwarai yayi shari’ah da shi, daganan har kotun daga ke sai Allah ya isa! Domin ya kwatowa Inna hakkin ta, a daure shi har sai igiya ta yi rara, amma Malam Isa ya gyara murya ya kuma gyara zama, yace masa “ka manta da Zakari kawai, ka nemo su Hauwa din shine mafi a’ala, ganin Zakari bazai kare ka da komai ba sai karin bacin rai, don zai iya yi maka mummunan bita da kulli, idan ya gano su Safiya suna da wani gatan bayan shi a duniya.
Ai sanin cewa basu da kowa da zai tsaya musu ne yasa yayi musu haka!”.
Sarham yayi shiru, can yace Baba ina so in sake saye filin wajen ne, ina nufin filin gidan nasu daga hannun wadanda suka saya”. Malam Isa yace, ai hakkin mallakar filin ya bar hannun Zakari tuntuni, wannan mai kamfanin ruwan shi ke da wajen yanzu, kana iya tuntubarsa ko zai sayar maka, amma lallai sai ka nunnunka masa kudi”.
Tare suka je har gidan mai kamfanin ruwan ledan da ya kafa rumfa a filin gidansu Hauwa yana sana’ar ruwa, suka gaisa, Sarham yana hadiye hawayen sa yace, so yake ya sayar masa da filin wajen, inyaso ya yanka masa kudin ko nawa ne zai biya shi, ya bashi takardun mallakar kangonnan.
Hakan kuwa aka yi, da mutumin ya ga kudi ya amince, ya yanka kudin da yaga dama Sarham ba musu yace gobe zai kawo masa su (in cash) ya karbi takardun wurin bisa idanun shaidu kwarara da sabon mai unguwa.
Bayan ya bar Kofar Na’isa kasa komawa gida yayi, ya kuma kasa tuka motar, ya koma gefen titi ya kashe motar ya kifa kansa a kan sityarin, yana tuno fuskar HAUWA-KULU da kyawawan manyan idanun ta da ya nakasta mata su bisa kuskure, da kuma murmushin Innar ta. Daga baya ya ja motar ba tareda ya san wurin zuwa ba, haka yayi ta yawo kwararo-kwararo titi-titi a cikin BADALOLIN KANO, ya taho tun daga Kofar Na’isa, ya isa Kofar Gadon kaya, ya bi ta kofar Dukawuya, ya bulla ta kofar Kabuga, daga can ya karya kan motar yayi kofar Kansakali, ya taho har Kofar Ruwa, bai ga ko mai kama da Inna ko diyarta Hauwa ba, ya dawo baya ta cikin gari ya bulla ta Sabuwar Kofa, kafin ya isa kofar Nassarawa ya dawo da baya ya isa kofar Dan agundi yana ta fatan Allah yasa ya ga Inna da Hauwa koda a hanya ne, amma har duhu ya baibaye sararin samaniya, wanda yasa ya daina shaida fuskokin mutane, kuma man motarsa ya kusa kafewa, ko mai kama da su bai gani ba, duk kuwa da irin kallon kurillar da yake yiwa mata da musaki bisa tituna da Kofofin Kano, da cikin unguwannin Badala.
Allah sarki Dr. Sarham! Kafin ya koma gida har rama yayi, yayi zuru-zuru yayi dan wuya sabida yunwa da damuwa da gajiya da bacin rai. Kamar ba sabon ango ba, na Madinah bada kanka a sare! Ya koma gida a jigace, wajen karfe goma na dare, amma sai ya kasa zaman falon duk kuwa da cewa ya gansu a zazzaune duk zaman jiran dawowar sa suke yi har Abba, domin a bashi hakurin laifin Surayyah gareshi.
Ganin yana nema wucewa dakin sa bayan ya gaida Abba da Mama, ba tare da ya ko zauna an yi hira yadda aka saba ba. Abba ya dakatar da shi, ta hanyar bashi kujera da hannun sa ya ce ya zauna, Sarham ya tsaya a tsaye kamar mai ciwon kafa, sai Abba yace,
“lelen Abba daga ina kake haka, kamar an maka dukan tsiya? Ka gan ka kuwa?”.
Sarham bai yi aune ba yaji wata irin hajijiya na neman kayar dashi saboda yunwa da gajiya, ba shiri ya lalubi kujerar ya zauna yace “wash! Abba, kai na!” Ya kama kannasa da hannu bibbiyu. Abba ya ce “sannu, Sumayyah kawo masa ruwa da abinci, hajijiya ai yunwa ce, me ke faruwa?”
Sarham bai san lokacin da yace “Abba na neme su na rasa, ba inda ban dub aba, ba Badalar Kano da ban zagaya ba, ko mai kama dasu ban gani ba, duniyar nan cike take da azzaluman ‘yan uwa Abba, kowanne dan uwa ya samu faraga sai ya ci amanar dan uwan sa in baya nan, why?”
Surayyyah ta saka kuka don ta dauka wannan maganar da ita Sarham yake ta ce “wallahi Bhaiya ban yi da niyyar cin amanarka ba, na tuba ni kam na shiga uku! Ka dauki abinnan da zafi har fiye da kima Bhaiya” wata uwar harara daya zabga mata ya ce a fusace “na saka ki a cikin magana ta? Kin san wa nake nufi ko su wa nake magana akan su?”
Mama ta ce “kayi hakuri Sarham, zancen nan ya wuce don Allah bazata sake ba na mata fada sosai”.
Yace Mama ni ba zancen ta nake ba Mama, already na yafe mata, na fadawa kaina da kaina na yafe mata yafi sau shurin masaki, tun fita ta ban fita da ita a raina ba, zancen su Inna da Hauwa nake,”
“Su waye kuma Inna da Hauwa kuma?”
Abba da Mama har suna hada baki wajen tambaya, da tunanin ko gamo yayi, ya ce “yarinyar da ta makance a hannu na, (excuse me) na makanta ta by mistake, tun daga lokacin kuma nake kula da karatun ta.”
“Au ho!” in ji Mama, ai kuwa ban manta da zancenta ba, da yadda ka shiga damuwa a lokacin, har yanzu idon nata bai gyaru ba? Kuma wai basu da Uba ne?”
Sarham ya baiwa iyayen sa kaf labarin su Inna, tun ranar da suka fara haduwa a asibitin Murtala, da aikin da yayi mata da sabon da ya shiga tsakanin su aftermath wato bayan hakan, da yadda aka yi ya kai Hauwa makarantar (Special School Kano), da yin sallamarsu lokacin da zai tafi Jeddah, zuwa yanzu da ya dawo yaji abun da ya faru da su daga kanin Baban ta, ya kuma gaya musu batan Malam Bilyaminu tun kafin haduwar sa da su.
Mama don tausayi har da kwallah tace “Allah to ya jefa su a hannu nagari, ya kuma bata lafiya a duk inda take, kai kuma ya baka ladan taimako”. Abba yace “amin, Allah kuma ya saka musu. Ya bi musu hakkin su. Amma don Allah ka ci abinci, ka huta, ka nutsu, ka tuna cewa kaifa sabon Ango ne akwai nauyi yanzu a kan ka.
Ya gaya masa cewa sunyi waya da Daddyn Madinah dazu, nan da kwana uku za’a taho da ita Kano, ba sai ya koma Jeddah dauko ta ba, Babanta yace ya daina cewa ango ya zo ya dauketa kasa-ya-kasa tun daga abinda ya faru kan mijin ta na fari, ina ya tanadar mata domin a sauke ta?
Sarham babu wani doki a tare da shi don zuciyarsa bakidaya bakikkirin take, yace shi ginin da ya fara bai kammala ba, sai dai Abba ya ara masa gidan sa na Rimin Gata (nan baya sabuwar jami’ar Bayero) a sauketa acan. Yace amma in son samu ne shi ya fi so Madinah ta zauna a nan gidan su tashin farko, ba don komai ba sai don ta saba da su Mama tunda na dan lokaci ne zasu koma Jeddah.
(A baya baiyi niyyar komawa Jiddah ba amma yanzu Kano ta fice masa a rai). Daddy ya ji dadi sosai, don a yadda na gina rayuwar iyalinsa da so da kaunar juna, kwarai yake so matar duk da Sarham ya aura ta zamo daya daga cikin iyalin sa, baya so don yayi aure yayi nesa dasu, musamman saboda shakuwar sa da kanwarsa Sumayyah, shakuwar dake tsakanin su har tsoro yake kada yayi aure mace ta zamo sanadinta, Abba ya ce,
“shike nan hakan yayi kyau, madallah, ita Sumayyah sai ta koma dakin Surayyah, su zauna tare for the mean time, sai a gyara ma Madinah dakin Sumayyah ta zauna har zuwa lokacin da zaku koma Jeddah din, Abba ya tambayeshi ko ya gama kwas din sa? kuma yaya batun aikinsa na Murtala da yake batun komawa? Ya gaya masa cewa ya gama, amma zai koma bikin kammalawa da karbo shaidar kammalawa, shi da Madina har yanzu basu zauna (officially) sun magantu sun yanke shawarar inda zasu zauna ba. Amma yanzu kam yafi so ya koma Jeddah.
Bayan ya koma dakin sa yayi wanka ya yi sallolin dake kansa sai ya samu kansa da zama dirshan akan dardumar sallahrsa ya rasa abinda ke masa dadi, abun mamaki ga kiran Madinah na ta shigo masa akai-akai don tun bayan da aka daura musu aure basu yi magana ba, amma ga mamakin sa ya kasa dagawa, a lokacin damuwar da yake ciki tasa komai ya fita kan sa, ya samu kan sa da daga hannu yana yiwa su Hauwa addu’a, damuwa tasa a ranar ko runtsawa na awa guda bai iya yayi ba.
Washegari yaje ya kai kudin filin gidan su Hauwa, ya karbi takardun filin a gaban kwararan shaidu dattijan unguwa su malam Isa da sabon mai unguwa, kowa yana ta mamakin ko me zai yi da filin, shi ba dan unguwar ba, ba kuma dan Malam Bilyaminu ba, amma dai ai yace shi dan uwan Innar Hauwa ne.
Wayar da ya sayawa Inna sai ya samu kansa da mallakawa Malam Isa, ya kuma karbi lambarsa yace zasu dinga gaisawa kuma zai dinga turo masa kudin abincin dabbobin Inna da yake kiwata mata, ya fadi hakan ne a lokacin suna cikin garken dabbobin, suna zagawa yaa kallonsu, ya ga yawan su ya karu nesa ba kusa ba akan sanin da yayi musu, sosai ya jinjinawa Malam Isa da iya kiwon dabbobi da zuciyar makwabtaka irin ta mutanen da, ya kuma yanke shawarar taimaka masa akan kiwon dabbobin shima daga ranar da kudin abincin su.
Malam Isa yana ta murnar mallakar waya, saboda a lokacin bata zama a hannun talakawa, ya sakawa Sarham albarka yafi cikin carbi. Da zasu rabu kuma Sarham ya gaya masa niyyar sa, wato yana so ya gine filin nan, so yake ya a gina musu gida kwatankwacin nasu a filin su, gini na zamani, ya ce shi ba mazauni bane don haka zai turo magina kuma zai bar komai a hannun sa da masu ginin, yana so Malam Isa ya kula da ginin har a gama, don zai jima bai dawo Kano ba.
Malam Isa yana ta mamaki, ko meye alaqar wannan matashin mai kirki da kyakkyawar zuciya da su Innar Hauwa haka, haka suka yi sallama bayan Sarham yayi masa kyautar kudi, kuma a washegari aka saka tubulin harsashin ginin gidan su Inna da kudin da jima yana Tarawa don yin nasa ginin gidan.
Kwana uku bayan nan, ba abinda Sarham yake yi sai yawo a cikin garin Kano yana faman neman INNA da HAUWA har tambaya yake yi ko an san su, ya fasalta kamannin su, maimakon ya maida hankali wajen shirin taryar amaryar sa Madinah-Munawwarah mai isowa daga Jiddahn Saudi Arabia.
Amma ko wanda yace ya san mai kama da su bai samu ba. Wannan yasa duk zaman garin Kanon da dokin amarcin dake gaban sa ya kara fita a ran sa. Ya sa a ransa da Madinah ta zo bazasu dade ba kamar yadda yayi niyya zasu koma Jeddah, in yaso ya karbi tayin aikin da aibitin “SAUDI-GERMAN” suka yi masa, wanda a baya yaki karba, don ya so ne ya dawo gida kwata-kwata ya cigaba da aikin gwamnati a manyan asibitocin Kano da ya tabbatar sun fi bukatar sa, in yaso ya bude private clinic nasa na kansa ya hada, amma a yanzu bai san haka zuciyar sa ta dauki su Inna da matukar muhimmanci ba sai yau da take gaya masa rashin su ba zai sa ya ji dadin zaman Kanon bakidayanta ba, duk da gatan iyaye dana ‘yan uwa dake baibaye da shi, ga na cikar buri, wato na mallakar Madinah abar son sa.
Amma duka ya kasa enjoying ko daya. Saboda wasu bare? Ya ilahi, wane irin abune haka??? Shi kansa yana mamakin karfin ‘bond’ din dake tsakanin sa da ‘Inna’ don bazai ce ‘Hauwa’ ba.
Don haka sai mu ce Amarya Madinah ta shigo kasar Nigeria da kafar hagu, don kuwa likitan zuciyarta Sarhamu babu walwala kota kwabo a tare da shi, gabadaya ya birkice da neman Inna da Hauwa, har iyayen sa suka fara damuwa da saka ayar tambaya, suka zaunar da shi suka ce ya gaya musu gaskiya, bayan tausayi da taimako, meye alakar sa da mutanen nan ne?
Ta yaya zai yi sabon aure amma ya raba hankalin sa da nutsuwar sa, ai sai suma ya saka su a damuwa.
Sarham ya ce babu wata alaqa tsakanin sa da su, sai kauna ta fisabilillahi da haduwar jini, yace shi kawai yana tunanin a wane hali suke ciki ne, yana tsoron fadawar su mugun hannu ko fadawa hannun kanin uban Hauwa wanda baya kaunarsu kuma azzalumi ne, sannan basu da kowa da zasu kira nau in ba shi din ba (Zakari).
Mama tayi fuska ta ce daga yau bana son ka kara fita neman su tunda dai ba kananan yara bane, Allah shi yake kula da bayinSa marassa karfi da masu karfi, kafin ka shiga rayuwar su ai babu uban nasu, kuma hakan bai hana su rayuwa mai kyau da shaker numfashi ba. Saidai ban sani ba ko kana da wani dalilin a kasan ran ka a kansu bayan wannan?”
Wai meyasa mutane suke kasa fahimtar sa ne akan Hauwa da Innarta? Zai iya rantuwa babu wani dalili a kasan ransa a kansu bayan wanda ya fada musu. Kwatakwata kenan babu alaqa ta mutunci da zumunci a tsakanin al’ummar Annabi sai mai kunshe da MANUFA? Haka mafa Sumayyah ta taba cewa wai….. abun babu ko dadin ji domin kuwa yadda yake kallon ta muharramar sa haka yake kallon HAUWA-KULU.
Can tsakar kansa ya tsinkayi sautin Abba yana cewa “talakawa nawa ne a Nigeria da suke cikin halin kaka-nikayi? In ka ce duka sai ka tsayawa rayuwarsu ka hada kan ka da abinda ba zai taba yiwuwa ba, tunda dai kayi taimako iya yinka wanda dace ya kamata ka bar su a hannun Ubangijin da ya halicce su haka, ka maida hankali ga abinda ke gaban ka yanzu. Wato sabuwar rayuwar ka ta girma da yah au kanka”.
**** **** ****