HAUWA KULU Book 2 Complete Hausa Novel
Wannan shine tarihin soyayyar su shi da Madinah wanda ya tuna a wannan ‘yan dakikan da suke kallon debe tsammani shi da ita.
**** **** ****
Da tunanin sa ya zo nan, sai ya dauke kai daga kallon kudar da suke yi wa juna, ya juya da zummar cigaba da tafiya ya bar ta a wurin, ba tare da ya kara tankawa ba.
Madinah bata yi fushi ba, ta hakurkurtar da ranta da cewa fushin fari ba nata bane, Allah na nufin su da wani al’aamri maigirma da ya sake hada su (at appropriate time), ta sake biyo bayan sa jiki babu karsashi, yana saka kafa tana mayas da tata duk inda ya cire tasa, cewa tayi cikin muryar dake raurawa.
“Sarham, yaya bayan rabo?”
Cikin dakiya da tsare gida yace “bayan rabo kuma? Sai tarin alkhairi” “Kamar baka gane ni ba?” Madina ta fada kamar zata fashe da kuka wannan karon, idanun ta na kallon kasa, sun kasa rike hawayen yanzu, suna cigaba da tafiya zuwa dakin karatu, hawaye na tsirgo mata. Sarham yace.
“Madinah kenan, ni kuwa na gane ki, ko ba Madinah Attahiru diyar masu Bankin Musulunci na Duniya bace? Idan na gane ki sai me hakan zai kare ni da shi, ni Sarham dan yaku-bayi?”
Madinah tana hawaye tace “zaka iya fadin komai a kaina ba tare da na ga laifin ka ba Sarhm, laifi kan laifi na san na yi maka amma ina da DALILI na.
Abu daya nake so ka gane yanzu, Daddyna daka sani a da can, to bashi bane yanzu. Wannan sabon Attahiru SoronDinki ne, wanda duniya ta biyar dashi, yanzu ya gane cewa rayuwar kanta da dan adam kansa komai mukami da mulkin sa, da dukiyar da yake tinkaho duka ba a bakin komai suke ba.
To cut it short, Daddyna ya dade yana neman ka ido rufe domin ya nemi afuwar ka, ya kuma baka damar da ya dade yana hana ka”.
Murmushin da Dr. Sarham Shanono yayi irin wanda yafi kama da a kira,
“na dade da baiwa wannan tatsuniyar baya” ne.
A fili kuma yace “Madinah Soron Dinki, takamaimai me kike so da ni yanzu a takaice, da yasa kike min wannan binbinin haka?”
Ai jin haka Madinah ta tabbatar yanzu kam Sarham ya gama da babin ta, yau ita Sarham ke cewa tana masa binbini! Wannan ba Sarham din data sani a baya bane halinsa duk ya canza, wancan jovial ne mai saukin kai da dadin sha’ani, ko dai wani ne mai tsananin kama da shi da irin sautin sa ta gamu da shi saboda yadda ta saka shi a ranta???
Sai kawai Madinah ta durkushe anan inda take tsaye, cikin korran grass carpet (ciyayi) ta saki kuka mai cin rai.
A can zamanin baya Sarham ba abinda ke daga masa hankali irin damuwar Madinah Attahiru, amma wallahi yanzu bai ji ko gezau ba wai an tsikari kakkausa, ya yi kuka har fiye da wannan da take yi yau akan rashin Madinah, da kuma wulakancin da mahaifin ta yayi masa ranar da yace “ba zai taba baiwa dan almajirin gwamnati (dan malamin makaranta) ‘yar sa ba”.
Ita nata kukan kuwa a yanzu ai na jin dadi ne, abinda bai sani ba, kukan Madina yau ya kunshi abubuwa masu dimbin yawa, har da wadanda tunanin sa da tsinkayen sa bai bashi ba.
Bata taba daina son sa ba, a duka wadannan shekarun daidai da rana daya, ta yanke alaqar su ne domin ta samu damar yin biyayya ga mahaifin ta, wanda ba abinda bai yi mata a duniya ba, ya kuma fifita soyayyar ta akan ta ‘yan uwanta maza bakidaya kasancewar ita kenan masa diya mace, kuma auta a cikin ‘yan maza bakwai. Wannan shine dalilin nata.
Sarham bai tsaya Madinah ta gama kukan bay a cika bujensa da iska ya bar wurin, sai dagowa tayi bayan ta share hawaye ta neme shi a filin wajen ta rasa.
A lokacin ta cigaba da tuno rayuwarta ta baya tare da Sarham, abinda ya faru shekaru bakwai da suka gabata, ta tuno asalin ta, haduwar su, lokutan su tare a campus, da abubuwan da suka faru da ita bayan rabuwar tasu…….
**** ***** ****
WAIWAYE ADON TAFIYA! (2)
DR. MADINAH ATTAHIRU
A
salin mahaifin ta Bakano ne dan asalin Soron Dinki, Soron Dinki wata karamar unguwa ce mai tsohon tarihi a jihar Kano, wadda ta haifi fitattun malamai da alkalai a tarihin jihar. Tana nan dab da gidan Sarki (Emir’s Palace).
Mahaifin Attahiru wato Kakan su Madina tsohon Alkalin Alkalai ne na jihar Kano kuma fitaccen mutum akan sha’anin shari’ah a Kano. Tun a tsakiyar shekarun 80’s Attahiru Habibu Sorondinki ya tafi Jeddah kan wani kwas na aikin Banki, tare da matar sa Hajjah Ramlah da manyan ‘ya’yan sa maza uku a lokacin, Abubakar da Omar, da Osman inda daga wancan lokacin ya fara aiki da wani tsohon bankin kasar ta Saudi-Arabia.
Da tafiya tayi tafiya, zamani na garawa da shi a harkar aikin banki a can, har zuwa lokacin da aka bude ISDB wato (Islamic Development Bank) Allah kuma ya zabe shi ya kai shi ISDB a babbar ‘headquater’ din su dake birnin Jeddah. Ya rike kananan mukamai da dama a cikin ta, kafin ya iso wannan matakin na yanzu. Domin kuwa a halin yanzu mahaifin na Madinah Alhaji Dr. Attahiru Soron Dinki yana rike da matsayin (Chief Financial Officer) na ISDB. Alh. Attahiru na auren Hajjah Ramlah, wadda ta kasance ‘cousin’ a gare shi, ta cika masa gida da kyawawan ‘ya’ya maza har su hudu, Abubakar, Omar, Osman da Aliyu, a Kano ta haifi manyan su uku, wato Abubakar, Omar da Osman. Da suka zo Jeddah ba jimawa ta haifi Madinah da Aliyu anan.
Akwai ratar haihuwa sosai tsakaninta da Osman kafin su samu haihuwar auta “Madinah”. Daga Abubakar har Umar har Aliyu da Usman ma’aikatan bankuna ne a kasar Saudi-Arabia, saboda mahaifin su dake da wuka da nama a harkar aikin banki.
An haifi Madinah ne a garin Madinatul-Munawwarah lokacin sun je aikin omrah duk gidan, shi yasa Baban ta ya kira ta da suna Madinah.
Madinah ta ga gata tun daga haihuwar ta har girman ta, Madinah bata taba sanin wahala ko babu a rayuwar ta ba, ta tashi a gida na ilmi da tarin dukiya, wanda ya sa koda ta shiga jami’a maza ke rububin ta, da yawa ko don su rabi alfarmar ISDB, da yawa kuma saboda kyawun ta ne.
Amma wani ikon Allah babu wanda tasu ta zo daya irin coursemate dinta Sarham Abbas Shanono, wani siririn sardidin yaro, dan ajinsu, wanda ta fahimci yafi kowa a ajin su kokari, kamun kai da kula da abinda ya kawo shi, shima kuma ya fahimci Madinah Attahiru tafi duk matan ajin su kokari, ga aji ga kasaita kamar wadda ta hada jini da sarauta, amma shi bata yi masa ko daya sai ma wani ‘special respect’ da take bashi, sai suka hade daga haka, suka zama abokan karatun juna, daga abotar karatu da karawa juna sani abin nasu ya fara, kafin ba da jimawa ba ya rikide zuwa zazzafar soyayyah wadda ta isa a bada labarin ta a ko’ina, amma irin soyayyar nan ta sa’annin juna. Wadda bata fiya ‘actualizing’ ba. Domin kuwa shekaru uku kacal Sarham ya baiwa Madinah Attahiru.
Duk da kasancewar Madinah irin mutanen nan da basa so ka shiga harkarsu, masu halin da kai tsaye za’a ce na nasara ne kamar ba tashin Saudi Arabia ba, amma duk da wannan hali nata bata da wulakanci da raina mutane. Personality dinta kawai za’a ce na nasara ne (musulma mai halin nasara), tanada wani zazzafan hali na kada ka sake ka shiga harkar ta, itama kuma bata shiga harkar kowa, saboda mugun jan ajin ta, ta kasance mace ‘yar I don’t care attitude.
A hali iri na Madinah ko kai waye wajen isa, ko wane irin laifi kayi mata, ko wane irin aibu kake da shi, Madinah bazata zauna tana gulmar ka da wani ba, tafi karfin haka, saboda she is frank, bata iya boye me take ji akan mutum, zata tare ka ne gaba da gaba ta gaya maka, da dai ta zauna tana zunden ka da wani.
Wato dai a takaice Madinah bata iya munafurci ba, sannan bata so a yi mata.
Wadannan halaye nata sun taimaka kwarai wajen ribato zuciyar kyakkyawan Bakanon matashin Sarham Shanono a kan ta, babban jigon son da ya samu kan sa da yi mata shine yadda gatan data ke da shi bai hanata tsayawa tsayin daka wajen yin karatun da zai amfani al’umma ba.
Sarham Abbas da Madinah Attahiru duk abokanan karatun su na MBBS sun san su tare, ko’ina tare suke zuwa, soyayyarsu mai tsafta, mai ban sha’awa ta ‘yan bokon da, ba irin ta wannan gurbataccen zamanin ba, Madinah kullum kawo ta ake a kuma zo a dauketa a motar gidan su, shikuwa a nan kusa da makaranta ya kama hayar gida mai daki biyu (flat).
Sun tsayar cewa da zarar sun yi bikin kammala karatu zasu yi aure, Madinah ta yarda zata bi Sarham Najeriya ta zauna cikin iyayen sa da kannen sa duk da cewa itada kasar Kano sai da ziyarar dangin su kawai su kan shigo ta, ita dinma sai suyi shekara hudu-biyar basu zo ba.
A wani dan tsakani da ya kasance sun kusa zana jarrabawar karshe a MBBS Madina ta baiwa Sarham iznin fara zuwa zance gidan su, ba don komai ba sai don iyayenta su san da zaman sa, kasancewar soyayyar tasu iya makaranta suke yin ta ba wanda ya san shi a gidan su har zuwa lokacin banda Yayan ta Osman dake zuwa kawota da daukan ta.
Zuwa na farko, na biyu dana uku Alhaji Attahiru ya fahimci akwai mai zuwa wajen Madinahr sa, Hajjah Ramlah ma ta gaya masa wani ya fito neman auren Madinah amma bata san ko waye ba, saidai ga dukkan alamu Madinah tana yi da shi, ko daga girke-girken da take faman yi masa in zai zo.
Daddy ya umarci Madinah data turo masa yaron dake zuwa wajen ta yana so zai yi magana ta gemu da shi, ba tare da tunanin komai ba a washegari Madinah ta gabatar da Sarham a tankareren falon mahaifin ta, daga nan ta basu wuri don su gana.
Sarham yayi wani kuskure zai ce ko katobara, koda yake a wurin sa is normal, wato yawo da farar jallabiyya ta larabawa a garin Jeddah, maimakon da zai je gun siriki yayi shiga ta cika ido da kima sai yasa jallabiyyar sa abinsa wadda taji wanki da guga da turaren sa na Oud Abyad. Kallo na farko da Alhaji Attahiru yayi masa yaga yarintar sa da rashin cika ido, sannan kuma babu tantama dan talakawa ne ko daga sittirar jikinsa amma duk da haka bai yanke hukunci daga abinda ya ganar da kansa ba, sai da ya tambayi Sarham.
“Yaro kai dan ina ne?”
“Kano”
“wane gari a Kano?”
“Shanono”
“Waye mahaifin ka?”
“Prof. Abbas Shanono”
“daga jin Farfesa malamin Jami’a ne kenan?”
“Eh!”
“to kai kuma meye taka sana’ar?”
“dalibi ne ni”
“Dalibi dan Farfesa, ilmi na dukan ilmi, amma dame ka shirya rike min ‘ya ta yaro da kai haka? Ko bata fada maka daga gidan data fito ba?”
Sarham ya kasa hadiyar miyau, don bai zaci wadannan kalaman marasa kan gado daga babban mutum mai ilmi kamar sa ba, Daddyn Madinah ya cigaba da cewa “yaran zamani in zaku yi abu sam sam ba kwa tunani, yo me na sama ya ci bare ya baiwa na kasa?
Yaushe zan ajiye ‘ya ta zaman jiran girman ka da yin arzikin ka kafin inyi mata aure?
Ai kawai yaro kaje ka nemi daidai kai diyar malaman makaranta”.
Sarham hatta jijiyoyin kansa saida suka mimmike, suka fito rada-rada, tun kafin ya tashi a wajen ya gayawa ran sa ya hakura da Madinah ko itace autar mata, don mai taba Abban sa ya zauna lafiya a hannun sa sai dukan ruwan sama. Shima don ba zai iya rike shi daga taba jikinsa bane.
Duk da haka wannan tsohon baturen zai ce ko tsohon nasara ya ci arzikin Madinah-Munauwarah. Amma da ba haka ba?! Da yayi masa raddi daidai da nasa. Ya girgiza kai ya mike. A kullum Madinah na cin alfarmomin sunan ta a wurin sa, wato, yana son garin Madinah sosai, duk sati biyu yake ziyara Masjid Nabawy daga Jeddah, don haka ko cikin hira yana gaya mata cewa tana cin albarkacin sunan ta na Madinah garin Manzo, garin da ya zamewa Ma’aiki (SAW) mafaka (refege) kuma wajen yin hijira daga inda yayi masa kunci, don haka sau tari ya kan ce da ita, ko sunyi aure ta bata masa rai komai girman laifin zai iya yafe mata shi saboda sunanta, zata cigaba da cin albarkar city of Madinah, za kuma ta cigaba da samun wannan alfarmar har gobe a wurin sa.
Don haka bai ce komai ba baya ga godiya ga mahaifin Madinah da barin gidan su ba tareda ya tsaya Madinah ta ga yanayin sa na lokacin ba.
Shi uban da kansa ya gaya mata ya sallami wannan yaron, in bata da hankali shi da hankalin sa, ba daga turu aka fito da shi ba, kuma ta sani daga yau ta bar King Abdul Azeez University kenan, don ya fahimci irin ‘ya’yan talakawan nan ne masu hurewa ‘ya’yan manya kunne da ‘I love you’, su dau advantage na iyayen su don su samu abin yi mai maiko, in sun kama kasa su auro daidai su, ‘ya’yansu su koma na ladan noma.
Madinah couldn’t control her tears, ta bi bayan Sarham da gudu amma bata cimmasa ba. A washegari kuma Babanta bai barta ta koma [KAU] ba, yasa Abubakar ya karba mata ‘transfer’ zuwa Yamboa ya kuma je ya kaita da kan sa, yace in ta kara neman wannan yaron ko a waya kota wata kafar sadarwa kowacce iri ce zai saba mata ko ya bar kasar bakidaya da ita.
Madinah na matukar son birnin Jeddah don anan aka haife ta, amma haka Baban ta ya raba ta da shi saboda Sarham zuwa Yamboa.
Madinah na matukar son Sarham, so irin wanda bazai misaltu ba, amma haka ta hakura da shi saboda ta yiwa mahaifin ta biyayyah.
Madinah na matukar son mahaifin ta shiyasa ta zabi farin cikin sa a kan nata, wato ta zabe shi akan soyayyar dake zuciyar ta, ta kuma bi umarnin sa.
Wannan kadai ya nuna Madinah mai biyayyar iyaye ce ta kuma ci ribar biyayyar tun a lokacin, domin duk da zuciyar ta tafi dare duhu, amma haka mahaifin ta yayi ta saka mata albarka, yana ankarar da ita illar auren ‘ya’yan talakawa gasu yara masu gata kuma ‘ya’yan manya kamar ta, yace basu da alkawari ‘yan taking advantage ne kuma basa juyuwa ta sauki ga matan su, taurin kansu kadai dafadin rai ga matayensu sai ta gwammace kida da karatu, sannan basa taba zama da mata daya.
Duk Madinah tayi biyayyah ko a fuska bata taba nunawa mahaifin ta har lokacin Sarham yana ranta ba. ta kuma san duk abinda ya fada akan Sarham ba haka bane, Sarham akasin duka wadannan expectations dinne.
Sai ta tattara komai ta fauwalawa Allah ta maida hankali ga fuskantar karatunta a jami’ar Yamboa, ta manta da komai, a shekara daya da Sarham ya gama nasa karatun itama a shekarar ta fita daga Yamboa University, ta fita da flying colours a specialization nata, ta zama cikakkiyar likitar fidar ido (ophthalmic surgeon) mai lasisin yin aiki a kasar Saudi-Arabia.
Shima Sarham ya fiddo nasa kwalin daga (KAU), ba tare da sanin me kowannen su yake ciki ba. Daga nan ya tattara ya koma gida. Inda ya kama aiki a karkashin gwamnatin jiharsu.
A lokacin ne AVM Adamu Alkali ya fito neman auren ta.
Ba kuma ta kanta ya bi ba, ya tafi ne kai tsaye ta kan mahaifinta, shikuma a sanin irin biyayyar da Madinah keda ita bai bata lokaci wajen neman yardarta ba, saboda wannan shine daidai da ra’ayin sa, irin mijin da yake mata fata yake mata addu’a, gashi Allah ya bata a lokacin da ya dace tayi aure, miji wanda bazai yi kaico da aura masa ita ba, wato na saman da ya ci ya hantse yake watsowa na kasan sa, dama duk wadanda ke jikin sa koda sun kasance suma masu wadatar ne.
Don haka Daddy bai ja lokaci mai yawa ba wajen sanya auren Madina da AVM (Air Vice Marshall A. Alkali), wanda shima dan Kano ne gaba da baya, amma mazaunin jihar Lagos, inda a can yake aikin sojan saman sa.
**** ***** ****