HAUWA KULU Book 2 Complete Hausa Novel

HAUWA KULU Book 2 Complete Hausa Novel

WAIWAYE ADON TAFIYA (1)
(DR. SARHAM SHANONO A JEDDAH)

Abinda ya faru shekaru ukun baya shine tun saukar sa a birnin Jeddah cikin wani ikon Allah suka hade shi da ‘ex’ dinsa Madinah Sorondiki a cikin asibitin koyarwa na ‘KING ABDUL’AZEEZ’, inda duk a can ne dukkansu suke kara zurfafa karatu.
Ba zai manta ba kwanansa uku da zuwa ranar nan ya zo wucewa, kamar daga sama ya hangi Madina Attahiru tana shiga wata farar mota kirar ‘Audi’ don fita daga asibitin. Sarham ya mutstsika idon sa, don da farko ya dauka gizo idon nasa yayi masa, irin wanda dare da rana ya saba yi masa a kan ta, har saida ya dinga neman taimakon Ubangiji da sallolin dare kafin ya samu Madinah ta daina yi masa gizo a kowacce kusurwa ta dakin sa.
A ranar da yayi mata wannan ganin a asibitin kusan karamin hauka yayi, bai iya yayi barci a daren ranar ba ko na minti daya, ‘fade memories’ na komai nasu a can baya ya dawo masa sabo, ya dawo da tsohuwar Madinah sabuwa a ran sa.
Amma a washegari da ya sake ganin ta, sai ya kuma tabbatarwa ba gizo idon sa ke masa ba, Madinah ce. Har yau bayan rabuwar shekaru bakwai, tana nan a Madinah ‘yar gayun ta. Fara, doguwar nan sambaleliya da ya sani hamshakiyar ‘yar hutu. Madinah siririya mai yalwar gashin ido dana gira, ta kara tsayi da cikar halitta, ga sabon aji na musamman data kara a kan wanda ya santa da shi a baya, ko dama can Madina classique lady ce balle yanzu da ta ke kusan shekaru Talatin. Tana takunta akan kasa cikin rangaji da rangwada tamkar basarakiya, tabon sallahr nan har yau yana nan a kan goshin ta, ya kara fitowa radau, shi ya kara tabbatar masa har gobe tana nan a “Madinah” mai yawan ibada.
Madinah (Munawwararsa da ya sani) tuntuni mai aji ce, iyayenta sun wadatata da komai na bukatar rayuwa, balle yanzu da ya san ko yaya ta zama babbar likita tana aikin kanta kuma kallo daya zaka yi mata ka san hankalin ta a kwance yake, tana neman cika shekaru talatin.
Abinda bai sani ba shine tana da aure ko bata da shi?
Wannan tunanin, da kuma sanin halin mahaifinta da yayi, su suka sa yayi maza ya shiga taitayinsa, ya soma yaki da fade memories masu neman dawowa muhallinsu saboda ganinta. Sosai ya kama kan sa, bai bari ma ta san ya gan ta ba har bayan sati guda da ganin da yayi matan.
Amma wani coincidence din, ashe ajin su daya a wannan karon ma, itama ta zo yin irin kwas din da yazo yi, duk a specialization nasu na ‘ophthalmology’. Bayan kwashe shekaru biyu tana practicing aiki a Dr. Siddiqah Hospital anan Jeddah.
Ranar da yi mata gani na biyu da yamma ne, ya je shan Gahwah (coffee) a wani Mud’am dake cikin asibitin koyarwar nasu na Sarki Abdulazeez, bayan ya gama sha, ya tashi ya nufi kantar biyan kudi, ya zaro khamsoona riyals dinsa daga aljihu zai biya, kawai ya ji cashier din ya ce ai an biya kudin gahwar da ya sha.
Ya juya cikin tsanaki da mamaki, nan yayi ido hudu da Madinah Attahiru, his ex Madinah Sorondinki, tana masa kallon ashe kana duniya?
Zuciyar sa ta harba. Makwallaton wuyan sa ya motsa, amma ya kasa hadiyar miyau. Donhaka wani abu ya tokare a wuyansa. Madinah muguwa ce ta karshe ya sani in dai akan soyayyah ne, idan ta samu dama zata iya kisa, har lahira kuwa, don haka nisa da ita shi ya fi wa bawa kamarsa kwanciyar hankali.
Juyawa Dr. Sarham yayi cikin daure fuska kamar bai san ta ba, ya soma takawa don barin mud’am (restaurant) din gabadaya.
Madinah ta saki malalacin murmushinta, ta riga ta san halin kayanta bashi da jarumta in dai a kanta ne, tanada yaqinin bazata sha wuya ba wajen dawo da shi ruwa tsundum cikin soyayyah. Ba da sanin sa ba Madinah har sujjadah ta fadi ta yi a nan inda take zaune, (for the second phase) na rayuwarta ta sake haduwa da Sarham Shanono, a muhallin da ta fara haduwa da shi a can baya.
Ta tako cikin kasaitar ta har inda yake tsaye yana shirin barin wurin shan coffee din, ba tare da ko an gode yace ba, daga abinda aka biya masa. Madinah ta sha gaban sa, ta kashe shi da murmushin nan nata kamar na koren furen fulawa, da ya dade da daina gani, zuciyar sa kuma bata bar mararin ganin murmushin ba all those years, Madinah ta ce,
“ai in da alkawari zai zamanto cewa ko gaisuwar musulunci ce akwai a tsakanin mu Dr. Sarham, idan ta SO da KAUNA ta gushe ko tayi fading, a matsayin mu na dalibai duka, sannan ‘yan kasa daya kuma ‘yan aji guda, dana tabbatar abinda nazo yi shi ka zo yi, ba laifi bane don hanya ta hada mu mun tsaya mun yi gaisuwar musulunci”.
Wannan karon ma bai yi niyyar bata amsa ba yasa kai zai wuce abinsa, a ran sa yana fadin “Allah ya shiga tsakanina da ke Madinah!
Mumini na kwarai sau daya maciji yake saran sa a rami guda”. Amma sai Madinah bata yi fushi ba, ta sake shan gaban sa. Ta ce,
“Assalamu alaykum warahmatullah wa barakatuhu!”
Kamar yadda ta dade da sani, Sarham Abbas nada wani hali daga halaye masu kyau, wato baya iya maida gaisuwar musulunci a kwandon shara, ta hanyar kin amsata, wato duk inda ya ji ta sai ya amsa koda ba da shi ake ba, ba don komai ba sai don cika sunnar Manzo SAW.
To yau ma hakan ce ta faru kuma yanzun ma. Sarham ya kasa kin amsawa don cika umarnin addinin musulunci, sai ya ce kasa-kasa kamar yaci madaci,
“wa alaykumus salam warahmatullah wa barakatuhu”.
Daga wannan sai aka shiga kallon-kallo, koko in ce ‘kallon kuda’ kallon debe shakku ko debe tsammanin gizo ido ke yi, kallo ake babu ko kiftawa haka babu kakkautawa tsakanin SARHAM DA MADINAH. Suka yi wa juna kiriii da ido.
Kallon da ya dawo masa da duk abinda ya faru cikin shekarun soyayyar kurciyar su kan idon sa, koko ince, kan idon kowannen su, komai da ya gabata (in the past) ya zo yana gilmawa a idanun kowannen su, tamkar yadda sinasinai ke wulgawa a majigi, suna tariyo kan su, suka kuma shiga warware tsohon kullin dake zuciyar Sarham akan Madina, tamkar ana tariyo tsohon kaset na faifan bidiyo.
A hakikanin gaskiya Sarham na kullace da Madinah kullata mai yawa, wadda ta janyo ya maida kansa ba namiji ba, ta hanyar daina sha’awar soyayya da sha’anin mata gabadayansu.
Madinah tasa ya hada su itada sauran matan duniya yayi musu kudin goro da cewa dukkansu maciya amanar kauna ne, kuma basu san darajar soyayya ba, mata irin Madinah in ka bari ka fada komarsu zasu iya kashe ka har lahira akan soyayya.
Yana tuhumarta ne da rashin alkawari da cin amanar kaunar da suka yi wa juna.
Son data ke ikirarin tana yi masa yayi ittifakin ko kusa bai kai rabin nasa ba, shiyasa ta iya bari har aka raba su cikin matukar sauki haka, kamar kwace goriba a hannun kuturu.
Abu daya ya sani kuma yake da tabbacin sa; Madinah Attahiru, bata taba raina shi ba, wai don shekaru biyu ko uku kawai ya bata a haife, Madinah bata taba raina arzikin mahaifin sa ba, wai don bai tara dukiya kamar nata mahaifin ba, baya ga kasancewar sa malamin makaranta/malamin jami’a.
Yana son Madinah har gobe, domin ta hada duk wasu halaye na kwarai da nagarta da kyawun sura dake sawa a so mace, a yi mata So na musamman. Duk wasu ‘attributes’ da yake so a matar aurensa Madinah ce ta hadasu ita kadai ranta.
Ya ci buri mai yawa a kan Madinah Attahiru, haka ya sha wahala lokacin da ya rasa ta farat daya. Haduwar su ba zato a yanzu, karo na biyu cikin shekarun girmansu, a lokacin da suke da cikakken hankalin su bata nufin komai sai fami a kan gyambon da riga ya warke.
Kafin wannan lokacin sun yi alkawarirrika masu dimbin yawa shi da ita, kai har yawan adadin ‘ya’yan da suke burin haifa ra’ayin su ya zo daya, wato ba masu yawa ba, shi da Madinah kamar Lailah da Majnoun ne. Daga cikin manyan alkawuran su na can baya, har da na yin aure daga zarar sun kammala MBBS, koda basu samu ayyukan yi ba a Jeddah, sun ajiye a ransu zasu yi ko ayyukan philanthropy ne a private clinics na Jeddah don rufa asirin juna indai zasu rayu tare.
Rana daya Madinah bai san ya aka yi ba, bai san me ya faru ba Madinah ta yarda mahaifin ta ya ci zarafin sa, ya kuma canza mata makaranta, duk dai don ya raba su, ya rasa mai yasa Baban Madinah ya ki jinin sa ya kuma raina arzikin su shida iyayensa har haka, tunda daidai gwargwado iyayensa nada abin yin su, da rufin asirin su basa nema a hannun kowa, ko da yake ya taba gaya masa fuska da fuska;
“me na sama ya ci bare ya baiwa na kasa? Kuma yayi yarinta da auren ‘yarsa a lokacin” Shine kawai hujjarsa.
Babban laifin da Madinah ta yi masa shine, bayan an canza mata makarantar, bai kara ji daga gareta ba, Madinah bata kara waiwayarsa ba, bata kara neman sa ba, koda da gaisuwar zumunci ne. Ai yasan Madinah nada email adireshinsa, da adireshin sa na gidan wasika, da lambar talfon din gidan su, amma ko sau daya, bata taba tunanin gwada neman sa ba, wanda ke nufin ta datse duk wata alaqar soyayya da sanayya dake tsakanin su.
Koda ba don maganar alkawarin aurensu ba, ai ta nemi inda yake ta ji yana raye ko ya zarce ta dalilin kisan gillar soyayar da suka taru suka yi masa itada mahaifin ta, tunda dai ta kwana da sanin irin son da yake mata, ba irin wanda zai gushe farad daya bane.
Wannan shine babban laifin da Madina tayi masa da ba zai yafe shi ba wato kin neman sa ko sau daya cikin shekaru bakwai da rabuwarsu, tun bayan komawar ta Yamboa inda a can tayi nata consultancy din, tsayin shekaru biyar, da komawar sa shima zuwa gida Najeriya na dan wani lokaci, inda daga baya ya dawo shima yayi consultancy dinsa ya sake komawa gida.
Wanda ya yi shi ne da kyar da sudin ludayi shikadai a [KAU] a dalilin rashin Madinah tare da shi.
Saboda tunda suka fara MBBS suke tare, har zuwa karshen sa. Karatun dukkansa, da aikin gida (assignment) da halartar lacca duk tare suke yin komai. A lokutan jarrabawa kuwa duk zaka same su tare a library, sun dukufa basa komai sai fatan isa ga ‘goal’ din rayuwarsu. Don haka shekaru goma kenan ya kwashe a cikin hidimar dakon son Madinah Sorondinki, idan har lissafin sa daidai ne; yayi shekaru biyar tare da ita cikin fafutukar hada MBBS, shekaru biyar kuma cikin jinyar soyayyar ta, lokacin da yake consultancy, tun bai san so ba akan Madina ya koye shi, wato tun farkon tashen balagar sa da soyayyar Madinah ya budi idanu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected