HAUWA KULU Book 1 Complete Hausa Novel
Saidai cikin daren, a gidan Malam Isa, inda aka baiwa su Inna mafaka, Inna ta canza shawara, ba ita ba shiga kotu a rayuwarta saboda abun duniya, a wurin mutanen da shiga kotu na nufin karshen tozarci ga mutuncin su kenan, meye abun duniya wanda duka mutuwa za’ayi a bar shi a inda yake?
A gidan Malam Isa suka kwana dakin matar sa Mai kosai, da asubahi ta kama hannun Hauwa ta dora kayan su a kanta, suka faki idon kowa suka bar gidan Malam Isa. A lokacin shi yana masallaci sallahr asubahi, matar sa kuma tana daka tana jan rago (munshari).
Kai tsaye Inna da Hauwa suka naushi hanyar fita daga BADALAR Kofar Na’isa, ba don sun san inda suke nausa kafafun su ba, ko suna da wurin zuwa, burin Inna kawai su yi nisa da kusa da duk wata Badala ko Kofa da Zakari yake ciki ba kofar Na’isa da Kofar Dan agundi kadai ba, kasancewar kofofin biyu suna makwabtaka da juna. In haka ne kuwa sai dai su bar duka kwaryar BADALOLIN KANO bakidayansu, kafin su iya yin nisa da Zakari, in ba haka bata tabbata zai sake biyo su ne ya batar da ita itama in ta tsaya shari’ah dahi a kotu, kamar yadda take da kyakkyawan zargin shi ya batar da dan uwan sa mijinta Malam Bilyaminu!
Hanyar da ya bi ya batar da shi dinne bata sani ba har gobe. Ta san dai ko don ya ganewa idon sa irin tagayyarar MISKINIYAR ‘yar dan uwan sa a rayuwa da ya hana dan sa mai lafiya ya aura ta tabbata Zakari zai sake biyo su. Don haka dole ta dauke HAUWA-KULU suyi nisa da BADALOLIN KANO bakidaya, don dai ta nisance shi, ta kuma kare Hauwa daga kiyayyarsa da zalincinsa da hassadarsa.
Daga yau tayi kudurin zamewa Hauwa GARKUWA daga dukkan abinda zai cutar da ita musamman kanin Uban nan nata, Zakari, wanda yau ta kara tabbatarwa baya nufin su da alheri. Tayi kudurin cika burin masoyin su na hakika wato “Dr. Sarham” akan Hauwa, na ta tsayawa Hauwa komai runtsi ta samu rabauta daga ko ilmin sakandire ne, ba tare da ‘makanta’ ta zame mata shinge (barrier) ga neman ilmi da cigaban rayuwa ba.
Tayi kudurin in har tana raye, da yardar Ubangiji sai Zakari ya ci arzikin dan uwansa Bilyaminu a rayuwa. Idan kuma malam Bilyaminu baya raye, ita SAFIYA UWAR HAUWA tana raye! Aka ce Uwa mafi Uba… koda uban Sarki ne.
**** **** ****
Tafiya suke ba tare da sun san inda suke jefa kafafun su ba, tsabar bacin rai yasa Inna bata ko gajiya da tafiyar da suke dirka, amma Hauwa tun ba’a yi nisa ba ta sare, tace “Inna na gaji”, Inna tace “daure Hauwa, bana so makwabtan mu su biyo bayan mu su cimmana, bazan zame wa kowa nauyi ba, ba kuma zan zauna cin arzikin kowa ba sai na Ubangiji, don haka bazan zauna a gidan makwabta in hada su fada da iyalin su ba, musamman Malam Isa, kin dai san halin Mai kosai ba taso a rabe shi”.
Hauwa ta daure suka cigaba da tafiya har suka yi wa kofar Nasarawa fintinkau, ita kanta Inna bata san ina suke jefa kafa ba, kofofin cikin gari kawai take so su bari, sai da garin ya Allah ya waye rana ta fito, yunwa da gajiya suka sa Hauwa ta ce “to Inna dan tsaya in huta ko na minti biyu ne”.
Suka tsaya a daidai sakateriyar gwamnati ta Audu Bako, suka zauna suna hutawa. Sai lokacin Inna ta tuna da kudin da Jamilu ya bata, cikin kunshin kayan ta, saboda yawan kudin ta san ba cikin hayyacin sa ya bata su ba, domin sun kai naira dubu biyu. Ta saka hannu cikin bakkon su, ta tabbatar suna nan, sai ta ce,
“tashi Kulu mu hau abin hawa zuwa tasha, na tuna akwai kudi cikin kayanmu”.
Kulu ta kwalalo manyan idanun ta waje, ta ce “tasha Inna? Kano zamu bari? Kanon Dabon? Gari ba Kano ba dajin Allah Inna.
Ai ni da kike gani na nan Inna, ban iya zuwa ko’ina in bar mahaifata KANO saboda wani Kawu Zakari. In muka yi hakan ai ya ci galaba a kan mu kenan, ya raba mu da KANO farin cikin mu, tushenmu, tsatson mu, cibiyar mu, jihar mu ta gado.
Ni dai Inna ko a karkashin gada ne zan dinga kwana in dai ina cikin kwaryar Kano, ruhina yana Kano, zuciyata tana mahaifata, in muka bar Kano Baba ya dawo ina zai gan mu? Kuma makaranta ta fa Inna?”
Sai ta fashe da kuka cike da tsoron, halin da karatunta zai shiga. A da kam, bata karaya ba, amma yanzu ta fara karairayewa, karfin halin ta ya kare, kuzarin jikin ta ya kau, data fara hango illar da Zakari ke son yiwa rayuwar su tunda muhalli shine rayuwa, ta san yanzu itada karatun sai wani babban ikon Allah, a lokacin da ya zo gangara tunda basu da matsuguni, bata san me Zakari ke nufi da su ba sai yanzu, me yake nufi kuwa banda su koma yin bara bisa titi da kwana a kasan gada? Matattarar duk wani abin cutarwa a matsayin su na mata ba maza ba. Inna ta rasa yadda zata yi da Kulu, don kukan nata har da gunji da majina ita atafau bata barin Kano saboda Zakari. Inna ta ce,
“to Kuluwa sai ki gaya min ina zamu je in muka zauna a Kanon, gida dai kina gani akan idon ki aka rushe shi, takardun gidan na hannun su, don haka ni banida sauran buri a zaman kasar Kano da cikin BADALOLInta”.
Hauwa-Kulu tace “ko kan dutsen Dala da Gwauron dutse ne mu hau mu zauna, ai dai muna cikin Kano, kuma can babu mai rushewa, sannan idan gari yaw aye zan iya zuwa makaranta komai nisan dutsen in dawo in tadda ke anan”. Inna ta ce cikin takaici, to “huda-huda, mungu Park uwar ‘yan boko, ana ta makwanci da abinda za’aci ma babu, kina ta zancen wata makaranta?
Da idon uban wa zaki je makarantar daga kan dutsen Gwauron Dutsen?”
Da ace cikin nutsuwarta ta ke, da kuwa ta tada ballin Inna ta mata gorin ido.
Amma da yake babu nutsuwar ko ta kwabo a tare da ita bata tuna wannan ba, Hauwa tace da mahaifiyarta Inna.
“Inna kada ki manta kin yi ma DAN KI SARHAMU alkawarin duk runtsi ba zaki raba ni da makaranta ba, kin masa alkawarin cika masa burin sa in kammala sakandire, alkawari abu ne mai girma Inna, in ban je makaranta ba Inna ba abinda zai raba ni da “BARA” watarana…. a matsayina na makauniya-miskiniya- musaka!”.
Ai jin furucin Hauwa haka wanda ya taso ya fito kai tsaye daka kasan zuciyarta da jijiyoyin wuyanta da suka mimmike. Inna taji kamar Hauwa ta bata vibe, ta zuba mata allurar karfi da kuzari daga sarewar data fara yi. Sai ta samu kanta da tare abin hawa (ba tare da tunani na biyu ba) ba kuma da ta san inda zasu nufa ba ta dai yarda bazasu bar Kano ba, zama daram! Domin ta yarda HAUWA-KULUnta ta fita gaskiya kuma ruhin HAUWA shine GIDANSU NA BADALA!!!
**** **** ****
MURFIN LITTAFI NA DAYA
Abin tambayar anan shine; shin jarumar cikin BADALA (HAUWA-KULU) zata koma da rayuwar ta cikin BADALAR KOFAR NA’ISA inda ruhinta dana iyayenta yake, ko kuwa ta fito wajen gari kenan tana walagigi???
Shin burin masoyin su na hakika (DR. SARHAM ABBAS SHANONO) zai cika akan HAUWA-KULU na ta samu koda ilmin sakandire ne ba tareda nakasar ido ta zame mata shinge (barrier) ba, ganin cewa tun ba’aje ko’ina ba a bayan tafiyar sa, rayuwa ta juyawa Hauwa da Innarta upside-down???
Wanene “PACE-SETTER” din Barr. H. Bilyaminu kuma sai yaushe zai bayyana a rayuwar ‘yar cikin Badala Hauwa-Kulu???
Shin Hauwa-Kulu zata yi rayuwar aure da tara iyali kamar kowacce mace, ko kuwa nakasar ido zata zame mata shinge (barrier) ga cikar farin ciki da dan adamtaka, kamar yadda take zamewa mafi yawan akasarin masu lalurar idanu irin nata???