HAUWA KULU Book 1 Complete Hausa Novel

HAUWA KULU Book 1 Complete Hausa Novel

Hakan ya faru ne sakamakon cewa kowa yana da abin yi daga (sana’ar data karbe shi), ta kuma ishe shi rufawa kansa asiri, da biyan bukatun sa na yau da kullum batare da ya ci bashi ba. Kuma ba tareda yayi rayuwar dage ba.
Kusan kowanne mutum a cikin Badalar birnin Kano da kewaye (kauyuka da kananan hukumomi) yana rayuwa ne daidai shi kuma cikin farin ciki, yalwa da wadatar zucci, domin kullum cikin sa a koshe yake da *Gurasa* Tuwo, Dumame, Kunu, da Koko da Kosai (manyan abincin Kanawa).
A takaice, ko da a ce kai ne beran masallaci sabida talauci a zamanin can da nake yarintata a gaban Innata da Babana, zuwa balagata (‘yammatancina) nayi rantsuwa bazaka rasa abincin da zaka ci sau uku a rana ba”.
A kullum ranar Allah tunanin Babana wanda anan unguwarmu ake kira “Baban Hauwa”, dama na kowanne magidanci kamarsa na jama’ar dake zaune cikin kwaryar gidajen ‘Badala’ da ‘ganuwoyin’ garin Kano, shine; na yadda gobe idan garin Allah ya waye, karfe nawa zai yi sammako ya fita kasuwa ko wajen sana’ar sa??
Ba kuma don komai ba sai don samowa cikinsa dana iyalinsa abincin da zasu ci a yinin ranar.
Kowa ya san a lokacin fiye da rabin Kanawa yan kasuwar saye da sayarwa ne. Wannan ne yasa ba’a kwana ana jin yunwa, sannan za’a wuni a koshe. Kuma ba’a tara komai a banki ba, sannan hakan baisa sai an ci bashin kowa ba. Duk da hakan kuma ana zaune lafiya cikin farin ciki. Wannan ita ce hakikanin rayuwar da ake yi a gidanmu.
Ina farawa da baku labarina ni HAUWA_KULU tun daga tushena, ta hanyar dora shi akan katangar zamantakewar gidajenmu na Kanawa, wadanda aka fi sani da ‘yan kwaryar BADALA, yanayin rayuwar iyayenmu na cikin Badala wata irin rayuwa ce irin mai ban sha’awa ga wanda ba Bakano ba.
Rayuwa ce wadda bako zai tafi gaba ya bada labara, tunda an ce wai Allah daya gari bambam.
**** **** ****

GIDAN MALAM BILYAMINU
T
sakar gidanmu mai fadi da yalwa ne sosai, irin ginin nan ne tun na 70’s wato ginin Kanawan zamanin da, Gidan namu yana nan a bayan tsohuwar Badalar nan mai tsohon tarihi daga cikin Badalolin Kano, wato bayan Badalar Kofar Na’isa, a lokacin nan ni Hauwa-Kulu, zan kimanta shekaru na da cewa ina ‘yar shekaru goma.
Yalwataccen gidan namu duk da cewa a can cikin surkukin lungu yake, wanda ainahi mahaifina Malam Bilyaminu ya gaje shi ne shida dan uwan sa Malam Zakari, daga baya rigima ta hada shi da Zakari a kan gidan, wadda har ta kaisu gun mai unguwar kofar Na’isa, aka ce za’aje kotu, inda mai unguwa ya hana, ta hanyar kawo shawarar bai kamata su je kotu alhalin sun fito gida daya ba akan abin duniya kararre, duk da ya san cewa Zakari ne mara gaskiya, don so yake ya gaje gidan shikadai, mai unguwa ya kawo shawarar daya ya sayarwa daya gidan, don a samu maslaha a tsakanin su. Don ya gaji da rabon fada tsakanin Bilyaminu da Zakari akan gidan gadon sunnan.
Don haka Zakari ya sayar masa da gidan, don a lokacin babu ta yi masa yawa yana neman abinda zai ja jari ne, kudin yafi bukata ba wai gidan ba shiyasa yakeso a sayar. Don haka gidan ya zama mallakin Malam Bilyaminu shi kadai bisa shaidar mai unguwa da makwabtansa, bayan ya biya shi kudaden da ya yanka masa da kansa, ko kusa bai zaci Bilyaminu zai iya biyansa wadannan kudin ba, don haka yana karba ya bar masa unguwar, ya koma kofar Dan agundi da zama, inda ya sayi karamin gida a can da rabin kudin, ya cigaba da sana’ar sa ta wankin hula. Malam Bilyaminu kuwa saboda kaunarsa da gidan sai ya kara gyare shi daidai bukatar kowanne talakkan badala.

Gidanmu, gida ne na kasa da turbaya (gidan da aka gina da Laka), wanda aka bi aka sumunce shi tsaf da suminti, aka kuma shafe shi tas da farar kasa yayi haske gwanin sha’awa. Tsafta da iskar shaqa sun wadace shi, kamar yadda tsaftar zuciya ta wadaci jama’ar wannan gidan bakidayan su, wato Mallam Bilyaminu da matarsa Inna Safiya.
A kowanne wayewar gari ko yammaci, zaka samu iska mai dadi da shiga jiki na kadawa a tsakar gidanmu, musaman a lokacin hunturu, wannan ya samo asali daga manyan bishiyoyin da ke girke a tsakar gidan tun ginashi, na darbejiya dana itacen umbrella, zaka ga reshen bishiyoyin dake tsakiyar gidanmu na rangaji, idan iska na kada su, busassun ganyaryaki na zuba a kas.
Amma bazaka gansu sun bata tsakar gidan sosai ba, saidaima ka ga zanen tsintsiya da ya bi nan take ya share su, wanda ke nuna matar gidan, wato Inna (Safiya) wadda kowa ke kiranta da (Innar Hauwa), bata da kyuyar yin shara, abin nufi Innata jaruma ce wurin yawan kauda datti, ko’ina ka shiga a gidanta zaka gan shi tsaf-tsaf gwanin ban kaye da dadin zama, kamar ba gidan dake cikin surkukin lungunan bayan Badala ba.
La-shakka ko lomar tuwon ka ce ta fadi kasa a gidanmu, za ka sunkuya ka dau kayar ka, ka jefa a baka ka ci, ba tare da kyankyamin komai ba, duk da rashin sukunin aljihu na jama’ar gidanmu wato iyayena tofa suna da wannan dabi’ar ta cikar Imani wato “nazafah’. Irin tsaftar da har ake cewa masu ita, ko suna da aljanun tsafta, ba Innar kadai ba, ba Malam din kadai ba har ni dake tasowa sun min wannan horon, kowannenmu ya rike tsafta irin ta malam bahaushe kai har ta zama symbol din gidanmu, bazaka ce ana kiwon dabbobi iri-iri a gidan ba, sabida yadda Innar Hauwa bata gajiya da share shi duk safiya da marece.
Innata na kiwon dabbobin gida, tun daga raguna har awaki da tumaki, a can wani bangare na gidanmu da aka zagaye da langa-langa. Da zarar awakin sun fito daga garke sun sakar mata shi a tsakar gida ko a can garken nasu zaka ga tabi ta share.
Sau tari zaka samu ‘ya’yan bishiyar nan ta Umbrella yellow sharr dasu sun zubo a tsakar gidan mu, don haka yaran unguwa da yawansu da sassafe kafin su tafi makarantar boko suna yawan shigowa rokon Inna “Innar Hauwa Umbrella ta fado?”
Nan zaka ga Innar Hauwa ta debo wankakkun ‘ya’yan ‘umbrella’ ta babbasu, su yi godiya su tafi suna ci da murna da farin ciki fal a fuskokin su.
‘Ya’yan bishiyar (umbrella fruit) sunada farin jini a wurin yaran cikin Badala sabida zakin dandanon su.
Yadda bishiyoyin suka yiwa gidanmu rumfa da manyan ganyaryakinsu zai matukar baka sha’awa, domin ya koma tamkar wani dan karamin lambu, bishiyoyin sun samarwa mamallakan gidan wadattacciyar inuwar hutawa musamman a lokuta na zafi, ko cikin watan azumin ramadana da kuma lokacin da rana ta take sosai, to kuwa tsakar gidanmu zai zame maka muhallin hutawa sabida inuwa da duhuwar bishiyoyin.
Gidanmu ya kunshi dakunan kwana guda uku kacal, daya a gefe na Babane, biyu na kallon sa, wanda daya ya zama na Inna ne, dayan kuma dakina ne nikadai a kusa da shi. Sai madafinmu mai rufin kwano da akayi da langa-langa, sai bayan gida daga gefe na gargajiya.
Duk sha’anonin cikin gida na Innar Hauwa a karkashin bishiyun nan take yin su, kamar su daka, gyaran kayan miya, surfe, wankin kayanmu, kai har da yin kuli-kuli da man gyada, don sau tari Inna da kanta take yi wa kanta mankuli, don wani lokacin na sayarwa sai ta ce an yi kazanta mai yawa a cikin sa, haka ta kan yi duk wasu abubuwan da hannunta kan iya sarrafawa da kanta ne don amfanin ta na gida. Hatta markaden kayan miya ita take nika abunta da dutsen nika. Inna bata da ganda (kiwa) ko kadan, akwai kuzari da koshin lafiya irin na matan da, da kashinsu yayi kwari daga shan surfe da dakau da tukin tuwo, sakamakon hakan kasusuwansu suka yi karfi sosai, gashi bata wasa da shan magungunan gargajiya masu kara koshin lafiya da cire kananan cututtuka irin su shawara (jante) dasu basir.
Girman tsakar gidan zai isa a gina wani dakin guda, ba tare da daya ya gogi sauran dakunan ba, amma mahaifina wato Malam Bilyaminu ya barwa iyalin sa filin su yi amfani da shi don hidimar gida ta yau da kullum da hutawar su, don ya fahimci yadda rayuwar mu tafi bada karfi a zaman tsakar gidan.
Kowa ya san yadda babu wanda ya kai mutanen dake cikin gari da badalolin nan na jihar Kano jin dadin alfarmar dake tattare cikin zaman kwaryar birnin Kano, da kuma jin dadin rayuwar birni gabadayanta. Mutanen cikin Badala, na da rayuwa ta tsaro ga junan su, da hadin kai, da taimakekeniya a tsakani, don suna kaunar juna ne kamar jini guda suka fito, ga kula da hakkin makwabtaka.
A irin wadannan unguwannin na cikin Kano, a tsakanin 1970’s, 1980’s da 1990’s zaki samu akwai saukin rayuwa na ban mamaki, misali arhar kayan masarufi dana abinci, makwabci baya iya cin abinci shi kadai a gidan sa ba tare da ya zuba an kaiwa makwabcin sa ba, ko ya fito da shi majalisa ayi ciyayya don inganta hakkin makwabtaka da zaman tare, da karfafa taimakon juna da zumuncin Allah.
To a unguwarmu ma, wato Kofar Na’isa, irin rayuwar da su Babanmu ke yi kenan kullum, shi da makwabcinsa Malam Isa, kullum bayan sallahr isha’I kowa zai fito da abincin gidan sa su shimfida katuwar tabarmar kaba a kofar gidan Malam Bilyaminu, su sallaci magriba da isha tare, sannan su zauna zaman cin abincin a kwano guda, da hannayen su dana kawo musu ruwa suka wanke.
Akwai wadatar shaguna na kayan masarufi da abubuwan bukatar yau da kullum a kowanne lungu da kowanne kwana na unguwannin Badala, babu abinda ba’a sayarwa.
Iyaye na dorawa yaran su talla ba tare da fargabar wani abu ba, akwai abincin sayarwa iri-iri kuma mai arha mai tsabta da a ke yi a gidaje, ga rijiyoyin burtsatse a ko’ina da rijiyoyin amfani a cikin gidaje, don haka babu batun wahalar ruwa a lokacin, kai duk iya talaucin ka zaka rayu ne cikin jin dadi ba tare da ka sayi ruwan amfani ba a unguwannin cikin Badala.
A hakikanin gaskiya sai kana zaune a irin gidajen nan namu dake cikin Kofofi da Badalolin Kano, shine kadai kake samun duka wadannan alfarmomin masu tarin yawa, kuma shine zai sa a kira ka da cikakken Ba-Kano, ko ka kira kanka da Bakano, ba dan wajen gari ba ko bakon haure a Kano.
**** **** ****

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected