HAUWA KULU Book 1 Complete Hausa Novel
Dr. Sarham na iya ganin yadda Hauwa ta runtse marassa lafiyan idanun ta masu cike da ciwon hakiya a kan saitin fuskar sa… (with utmost curiosity) na son ganin hakikanin kamannin sa…..
Lokacin da ya dora hannnu akan idanun Hauwa-Kulu domin fara aikinsa da bisimillah dauke a bakin sa, sai ya ji wani sako na kwakwalwar sa kamar yana yi masa amsa kuwwa akan kada yayi, yana janye shi daga yi wa Hauwa aikin ido, yana ce masa kada yayi wannan aikin, don 10% ne tsammanin waraka wato nasarar wannan aikin kashi goma ne cikin dari. Amma aka ce kaddara ta riga fata!!!
Ya ci gaba da aikin sa cike da fargaba don ji yake tamkar wani dabaibayi ya zo ya dabaibaye hannayen sa ya rikita shi, ya hanashi yin komai daidai, don wannan itace tiyatar hakiyar ido (cataract surgery) ta farko da zai yi a rayuwar likitacinsa…. Amma wannan bai isa ya zama dalilin kwacewar azancinsa da kwarewarsa ba ai.
Lokacin da yayi nisa da yi mata aikin, sai ya ji hannun sa da jikinsa sun karasa rikice masa da karkarwa gabadaya, zazzabi na shigarsa, zuciyar sa ta hau raurawa, ilmi da fasaha da training din abun duk suka kwace daga kwakwalwarsa… ga wani gumi da ya hau yanko masa ta ko’ina, zazzabin da wani irin ciwon kai na kara karfi, ji yayi ya koma tamkar wani dan koyo anan take, ya nemi iyawarsa da jajircewar sa a aikin tiyata da jaruntar sa wajen yin ta duk ya rasa.
A karshe ma Sarham ji yayi ya koma dalibin ajin farko da ko sakandire bai gama ba, exactly dai yadda ma’aikatan jinyar nan masu gulmar sa su Nos Saratu suka suffanta shi, har daya daga cikin su ta ce tsautsayi kadai zai sa ta bashi idon ta.
Watakila kwacewar azancin da ya same shi a take, yana da nasaba da gulmar su Nos Saratu dasu Metron Maria, da ya saka a ran sa ya dameshi tun ranar, da suka saka shi cikin wani hali na rashin yarda da kansa.
Gulmar tasu ta dade tana yawo a cikin kwanyar sa, domin a zahiri sun ci fuskar sa, sun kuma raina matsayin iyawarsa da darajar kwalayen sa kamar yadda suka raina shekarunsa.
Bai san ta ina zancen nasu mara dadi ya samu halartowa cikin kwanyar kan sa ya hargitsa shi irin haka ba, musamman a daidai yanzu yayin gudanar da aikin nasa da ya kamata ya samu nutsuwa fiyeda kowanne lokaci, ya ji ya koma tamkar lokacin da yake cikin ajin sakandire a Science College Dawakin Tofa, ko kuwa sanda yake dan koyo na matakin farko a MBBS, inda ya koyo aikin likita a jami’ar Sarki Abdul Aziz.
**** **** ****
“HAUWA _ KULU”
A
n yi aikin Hauwa lafiya an basu gado domin su yi jinyar idon kafin lokacin da likita zai kwance mata shi, a duba nasarar aikin ko akasin ta.
Makwabtan su Inna da yawa sun zo har asibitin domin duba Hauwa. Tun ranar da ya yiwa Hauwa aikin nan Dr. Sarham bai dawo asibitin ba yana gida ya killace kan sa a dakin sa yana fama da zazzabi da masassara da ciwon kai na damuwa da zullumi, domin kaso 80% na zuciyarsa na gaya masa cewa yayi kuskure a cikin aikin tiyatar da ya yi wa Hauwa.
Ilai kuwa ranar kwance idanun Hauwa ta zo, sai ranar ne Dr. Sarham ya shigo asibitin Murtala Muhammed. Bayan ya gama abinda zai yi a ofishin sa cikin rashin far’a da rashin walwala kamar da (wanda ba halin sa ba kasancewar shi mutum ne mai yawan sakin fuska ga ma’aikata, mai far’a da faram-faram da mutane musamman marassa lafiyan da suka zo gare shi) amma yau bai tsaya ganin kowa ba yana gama abinda zai yi a ofishin sa sai ya nufi dakin kwantar da mata domin ya duba aikin da ya yiwa Hauwa Bilyaminu.
Tun daga bakin kofa marassa lafiya da masu jinyar su ke gaisar da Dr. Sarham A. Shanono, shi Sarham, an yarda likitan kowa ne, sannan marasa lafiya na son shi saboda kirkin sa da far’ar sa, yana dakatawa a gaban kowanne gado yana amsawa cikin mutuntawa da tambayar kufan jiki, saidai fuskar nan ba murmushi kamar na kullum, murmushin nan da baya rabo da kyakkyawar fuskar sa ta fulanin Shanono yau babu shi. Haka yayi ta bin su daya bayan daya yana jin lafiyar su. Kusan kowa ya gane cewa shi din mutum ne mai mutunta jama’a ba Innar Hauwa kadai ba.
Har ya iso ga gadon Hauwa, wadda itace a gadon karshen dakin, suka gaisa da Inna da ke zaune a gefen gadon kan Hauwa bisa cinyar ta, ya tambaye ta ko yaya jikin na Hauwa, ta ce “tun jiya take min korafin ciwon kai, amma Nos dinnan ta zo ta bata magani. Ta nuna daga cikin Nosis din da ke bayan sa, wadanda suke take masa baya su biyu suna gatsine mata fuska na kin zama ba yadda zamuyi dake.
Bai kula da zancen Inna ba don hankalin sa kusan baya jikin sa. Bakidaya ya tafi ga son sanin aikin sa yayi nasara ko a’ah. Ya dauki file din Hauwa ya duba yayi rubutu a ciki sannan ya karasa gaban gadonta, yace cikin murmushin fatar baki wanda bai je ko’ina ba.
“Kululu-Kuluwa, Kuluwa ‘yar gidan Innarta, yau za’a kwance ido, ina fatan kin shirya?” Daga kwance ta amsa “na shirya mana Dr, yau sati guda ban ga hasken rana ba, ka bi ka kunshemin ido da bandeji”.
Ta bashi dariya amma sabida yana cikin fargaba murmushi kawai yayi, ya fara kuncewa. Da addu’o’I a bakin sa. Nos din da ke bayan sa ce ta taimaka masa, suka soma warware bandejin da aka nannade idanun Hauwa da shi da dan almakashin da ke hannun su.
Aka warware bandejin tsaf. Sai ga kyawawan idanun Hauwa tsaf da su garai-garai dasu kamar a wanke babu hakiya, aiki yayi kyau kenan. Amma me?
Dr. Sarham ya tambayi Hauwa su nawa ne a tsaye a gaban ta? Hauwa ta shafa idanun ta ta kyafta su, ta sake kyaftawa kafin ta girgiza kai tace,
“LIKITA AI BANA GANIN KOMAI A GABANA SAI DUHU!”
In kin ji faduwar gaba da tashin hankali a wurin su su duka dake wurin abin ba’a cewa komai. Amma shi Dr. Sarham ba faduwa kawai gaban sa ya yi ba, yankowa yayi daga zuciyar sa ya tsinko daga kirjin sa ya fado kasa yana majaujawa a dandaryar kasa…..
Ko dama ya dade cikin wannan zullumin tun ranar da ya yi wa Hauwa aikin. Jikin say a gama bashi bai yi nasara ba. Ya tabbata yayi kuskure a cikin aikin domin a lokacin da yake mata aikin ya samu kansa cikin wani bakon yanayi na rashin yarda da kai, wanda zai iya cewa ya gusar da consciousness din sa (hayyacin sa) na dan wani lokaci.
Yanayi ne da bai taba samun sa ba a yayin ‘surgery’, ya sha yin aikin da yafi wannan hatsari na ‘glaucoma’ amma bai taba sarewa ba sai a kan wannan, yafi danganta abinda ya same shi a lokacin da fargaba da tsoron rashin yin nasara sakamakon abinda ya tsinkaya ana cewa a kan sa, wanda ya jefa shi a halin rashin yarda da kwarewar sa akan karan kansa, amma ba don bai iya ba din, dadin dadawa bai taba yin aikin hakiya ba sai wannan karon akan idon Hauwa, ya kuma ga yadda hakiyar tayi zurfi sosai taci idanun ta lalata maganan ta, wannan ya jefa shi a fargaba mai yawa ta aikin bazai yi nasara ba wadda bai kamata ta zo masa a lokacin ba a matsayin sa na likita.
Tunda ya koma gida kuma da wannan tunanin ya kasa dawowa asibiti, don ya tabbatar bai yi aikin yadda ya kamata ba, ko yace yayi kuskure a aikin da ya yiwa Hauwa, ko yace kamar hakiyar da ragowa a ciki bai cireta duka ba, a sakamakon gushewar hayyaci da ya samu na dan wani lokaci (at the said moment).
A karshe ya tabbata garesu dai bakidayan su babu ko tantama Hauwa ta makance a dalilin aikin da Dr. Sarham Abbas Shanono yayi mata ba daidai ba, iyakar maganar kenan. Gulmar su ta tabbata aka bai iya di ba. Ga idanun nan tarr a bude, amma Hauwa bata iya ganin ko dan yatsan ta balle inuwar mutum ko hasken rana da take iya gani kafin ayi aikin.
**** **** *****