HAUWA KULU Book 1 Complete Hausa Novel
A karshen shekarar har kyauta aka bata wato ranar hutun karshen shekara ‘prize giving day’ kasancewar a shekarar gabadaya ita ke daukar na daya, kuma tafi kowa zuwa makaranta akan lokaci da kasancewa cikin tsaftar jiki data kayan makaranta.
Hakan yasa Sarham da kan sa kawowa Hauwa tasa kyautar ta musamman don kara mata karfin gwiwa inda ya dauki Sumayya a motar sa suka je Levintis suka yo mata sayayyar kayan kamun azumi rankatakaf. Kayan dadi na kwali dana gongoni iri-iri.
Wannan ne karon Sumayyah na farko da zuwa gidan su Hauwa, tunda jimawa Bhaiyan ta Sarham ke bata labarin su, amma bai taba yarda ta biyo shi ba sai yau, yau din ma don ta taya shi sayayya ne don ta iya provision na kayan kwalama, ta kuma taya shi da daukar kayan zuwa cikin lungun.
Suka yi sallama Hauwa na gindin famfo tana alwalah Inna na daga kitchen, Inna ta amsa musu don ta dau muryar Sarham tun daga madafi, amma Hauwa a cikin cikinta ta amsa, zaka ga dai yadda bakin ta ya motsa alamar ta amsa, Sumayya ta tsaya daga nesa ta saka ma Hauwa ido don jikin ta ya gama bata itace Maijiddan, Hauwa Kulun Badalar kofar Na’isa da Yayanta yake yawan bata labari kullum, wadda yake cewa ya makantar daga kuskuren aikin ido. A kunnen sa yaji Sumayyah ta rada masa cewa.
“Tabarakallah-masha Allah, Subhanallah Ahsanal Khaliqeen da wadannan idanuwa na Hauwa’u. Bhaiya, ashe dai Hauwa-Jidda beauty ce, irin kalar dana ke so na koma (kasancewar Sumayyah fara ce tas)”.
Sarham ya juya ya galla mata harara don ya ji ta sarai. Yace “wallahi zaki koma yanzunnan in baki yi min shiru ba”. Inna ta leko jin maganganun su tana maraba da bakuwa, nan da nan ta saki far’a tace “Sumayyatu ce ko?”
Sumayyah ta washe baki jin farad daya Inna ta kama sunan ta, ko da wannan ta san tana da matsayi mai girma a gun Bhaiya, tunda har wadanda yake mu’amala da su sun san da zaman ta.
Ta ce “ni ce Inna ina wuni?”
Inna ta bata shimfidar karaunin ta ta zauna, inda Hauwa ta tashi, a lokacin ta gama alwalarta ta juyo tana tafe zuwa inda suke kanta tsaye babu ko lalube, tsabar ta dade da sanin kowanne lungu da kowanne sako na gidan su. Sumayyah ta kamo hannunta ta zaunar da ita a kusa da ita, cikin girmamawa Hauwa tace da Sarham “Ina wuni likita, yaya aiki?” Ya dan dubeta kadan kafin yace “an gode Allah Maijidda, ga Yayarki Sumayyah na kawo miki” Sumayyah ta saka hannunta cikin na Hauwa, sai Hauwata rike hannayen nata sosai a cikin nata tana murmushi tace “sannu da zuwa”.
Basu jima suna hira ba Inna ta kammala girkin ta na dambun shinkafa da yaji zogale da soyayyen mangyada ta zubo musu a kwano guda, sannan ta zubawa Sarham yadda ta saba zuba masa a kwanon sa da ta ware masa na samira wanda sabida shi ta dauko shi daga cikin samirunta, shikadai take zubawa abinci a ciki. Ga yaji da yaji tafarnuwa a gefen abincin. Kamar ta san shi da son tafarnuwa, Sumayya ta hadiyi miyau tun kan ta kai loma abincin ya gama yi mata, sannan tsaftar masu gidan ta gamshe ta.
Hauwa kasa cin abincin tayi da Inna ta hada musu itada Sumayyah don bata sakewa da baki amma Sumayyah sosai take kai loma, nan da nan ta tashi da dambunnan. Shima Sarham tuni ya tada nasa sai kwanuka aka direwa Inna.
A ranta Sumayya ta ce “eh, wato dole Bhaiya yayiwa abincin gidan su kaura, yana nan an gargajiyantar da shi da wannan girki mai motsa kunnuwa. Basu jima ba sosai don zasu gidan Hajiya Kulu, Sumayya ta baiwa Hauwa sayayyar a hannun ta inda ta saka mata ledojin a cikin hannun ta ta ce,
“ga nan gift dinki ne inji Bhaiya, ki cigaba da dauko na daya kin ji Hauwan Inna, shi kuma yayi ta kawo additional gift, duk karshen shekara”.
Murmushi Hauwa tayi, tana shafa kayan da ledojin, murmushin na karuwa a fuskar ta, kanta a kasa ta ce “kice masa nagode, Allah ya saka da alkhairi, kema na gode da ziyara Anti Sumayyah”.
Bayan fitar su da kadan itada Inna shiru suka yi. Hauwa tace Inna ni bazan taba komai ba, don bana son abinda za’a zo ace muna kwadayi”. Inna tace “to ban ki ta taki ba Kulu, amma shima ya san bamu kwadayin komai nasa tunda baki roke shi ba kuma ba yau ya fara ba, saidai na yau nima ya tsorata ni, don kayan sun ci kudi da yawa da alama”. “To Inna ki ajiye ni dai bazan taba ba” Inna tace “tsahon shekara guda kenan muna tare da yaron nan, in da wata manufa a tare da shi ko da wani hali nasa mara kyau zuwa yanzu ya kamata in sani, to ban taba gani ba sai tarin alkhairi da nagarta a tare da shi.
Alheri da kyauta wannan na lura halin sa ne na halitta kawai. Don haka ni mahaifiyar ki Safiya na ce ko bayan raina duk abinda Sarhamu ya dauka ya baki da hannun sa ki karba da godiya, ki kuma yi amfani da shi da zuciya daya, wannan yaron bashi da wata manufa akan mu sai zumuncin Allah da ya saka kansa tsakanin sa da mu, don bazan ce wani ne ya saka shi ba ko don neman wani abu daga gare mu”.
**** **** ****
A cikin mota suna kan hanyar zuwa gadon kaya, Sumayyah ta kasa shiru, abubuwa da yawa sun tsaya mata a rai game da mu’amalar Sarham da gidan su Hauwa, babu tudu me ya kawo gangare? Ta saci kallon Bhaiya, wanda ke tukinsa hankalin sa a kwance, ta ce,
“Bhaiya, ina da tambaya, if you permit, may I ask? Tsakani da Allah son Hauwa kake yi?”
Wani irin wawan burki da Sarham ya ci da motar, saida dukkan su suka wuntsulo gaba, suka kusa ci da baka a gaban motar. Saura kadan ya kwadawa Sumayyah mari, domin ji yayi kamar ta yi sabo, amma ya daure ya rike hannun sa yana cewa ba zai taba dukan mace a rayuwar sa ba in sha Allah, balle Sumayyah, da yafi so duk gidan su, kowacce irin katobara zata yi masa kuwa, ba shiri Sarham yayi parking motar a gefen titi.
Cikin matsanancin mamaki da fushin da yake so ya danne yake kallon kanwarsa, yace da Sumayyah “ke kuwa me ya kaiki wannan tunanin mai kama da sabo? Sumayya sakewa ta dake har ta kai da ki raina ni irin haka?
A duniya mutum bazai yi wata kyakkyawar alakar mutunci da zumunci da mutanen da ya san darajar su, suma suka san tasa ba, kuma yayi sanadin janyo musu lalurar da basu da yadda zasu yi da ita sabida raunin su, da rashin namiji tsayayye a cikin rayuwar su, mutum bazai yi tunanin taimaka musu da faranta musu domin Allah ba sai don wannan shirmen?”
Sumayyah idon ta ya raina fata da ganin bacin ran Sarham karara, ta ce “kayi hakuri Bhaiya, ba raini bane hasashe na ne dana kasa dannewa a rai na, na yi la’akari ne da maganar Hausawa da suka ce in kaga kare yana sunsunar takalmi… dauka zai yi.”.
Da sauri Sarham yace “amma kuwa Allah wadaran wannan bahaushen da a wajen sa babu kowacce alaqa ta mutunci da taimako a tsakanin al’umma sai da manufa, babu kyautatawa mara galihu sai a dalilin wani shirmen banza wai SO!”. Yana fadi yana tada motar, da gaske a gareshi so shirme ne, don baiga ranar da so yayi masa ba.
Yana tukin yana maida numfashi, fuskar MADINAH ATTAHIRU na gilmawa a idanun sa. Itace silar bacin ran sa ba maganar Sumayyah ba, ita tayi fami ne akan gyambon da aka samu yayi healing ba tare da ta sani ba.
Sumayyah jikin ta har rawa yake ganin yadda jikinsa har tsuma yake, ta ce “don Allah don Annabi kayi hakuri Bhaiya, ni tambaya kawai nayi bansan ranka zai baci haka ba, kayi hakuri bazan sake shiga abinda ba ruwa na ba”.
Sai kawai ya fizgi motar ba tare da ya kara ce mata komai ba, amma ya fasa kaita gidan Hajiyar Gadon kaya, kofar gida ya maida ita wato can gidan su, New Site.
Tun bai gama tsayawa ba da motar yace, “fice min daga mota malama, daga yau bazan kara fita da ke ko’ina daya shafeni baba, uwar kaudi uwar tsugudidi, fadi ba’a tambaye ki ba”.
Jikin ta nata bari ta bude kofar motar ta fita daga gaban motar, hawaye ya tsirgo mata, zata cigaba da bashi hakuri ya fizgi motar sa ya bar harabar gidan su.
Sumayya ta dade tsaye a wurin, tana nadamar shegen surutun ta, da bata iya gani tayi biris, daga karshe ta share hawayenta ta shiga gida.
Yinin ranar zungur, Sumayyah ta kasa sukuni idan ta tuna Bhaiya na fushi da ita, Aunty Surayya na tambayar ta me aka yi mata take kulubi da hade rai? Sai ta ce a fusace “ina ruwanki dani? Ko ina shiga harkar ki?” Mama tace “ke ko! Ina laifin Yayan da ya damu da kai? Nifa rashin kunyar ki ce take hada ni da ke” Sumayyah ta tashi fuuu! Tayi dakinta ta bar musu falon. Surayyah na fadin “kyaleta Mama ta yi da ‘yar halak.”
Shikuma tunda ya sauketa asibitin Murtala ya koma. Ya shige ofishin sa ya kulle kan sa a ciki.
Maganar da Sumayyah tayi kuskuren furtawa ta tuna masa da shekaru biyar a baya, abinda ya dade da mantawa; ta tuna masa ‘first love affair’ din sa wato MADINAH ATTAHIRU (MADINAH SORON DINKI), ‘yar ajinsu, wadda bai sha da dadi a hannun ta ba dama iyayen ta da sunan soyayya, shiyasa duk inda aka ambaci yana son mace, sai ran sa ya kai makura wajen baci.
Ya so Madinah kamar rai, irin son da ake kira (love at first sight) tun bai gama sanin ciwon kan sa ba, amma Baban ta ya wulakanta shi, don a cewar sa nawa yake a shekaru da matsayi? Sune samarinnan masu hurewa yaran mutane kunne su hana su karatu, bai isa auren diyar sa ba. Sannan Uban sa ma bai isa ba, tunda ba wani bane banda malamin makaranta, ina shi ina auren diyar sa?
A lokacin ko part three na karatun sa bai hada ba. Soyayya ta rufe musu ido, soyayya ce irin ta tashen balaga daga shi har Madinan, sun so juna shi da Madinah kamar daya bai iya rayuwa ba tareda dan uwansa ba, sun yi alkawarin aure da zarar sun kammala MBBS sabuda yadda suka zaku ga son mallakar juna, amma Baban ta sai ya canza mata makaranta ma, duk don ya raba su, ya nesanta Madinah daga gareshi kwatakwata, don yace ya fahimci zai hana ‘yar sa karatun da ya kai ta ta yi a Jami’ar Sarki Abdul Azeez dake Jeddah ne kawai, shine dalilin da a karshe ma ya dauke ‘yar sa ya maida ita Jami’ar Yamboa dake kusa da Madinatul Munawwara, inda acan ne Madinah ta samu ta kammala nata karatun, shikuma ya kammala a King Abdul Aziz University ya dawo kasar sa ta haihuwa, daga lokkacin basu kara haduwa ba shi da Madina ko a hanya ko a waya ko a mafarki.
Baya ko son tuna wata kalma wai ita soyayya saboda abinda Baban Madinah yayi masa, shi ya san tsakani da Allah ya so Madinah ya kuma yi niyyar auren ta da zarar sun kammala karatun matakin farko na koyon likitanci, itama kuma sai ta baiwa mahaifin ta goyon baya dari bisa dari, lokacin da ya maidata Yamboa sai bata kara nemansa ba koda kuwa a email, ko a telephone, ko ta wasika da ake aikawa ta post office a lokacin.
**** ***** *****