HAUWA KULU Book 1 Complete Hausa Novel
Zaka yi mamaki in ka ji cewa kusan duk wannan gulmar tasa da zunden nasa da suke yi, wato shi sabon likitan nasu, yana sauka ne reras, kuma tiryan-tiryan a cikin kunnen sa kamar an kunna radio yana sauraren su. Bai san sanda ya ajiye biron hannun sa ba don ya kasa cigaba da rubutun, ba wai haushi yaji ba don sun aibata halittar sa, a’ah, kawai abin ya bashi tsoro, cin naman mutum haka a kan kunnen sa da tsakar rana babu ko shakka, ya fiddo ido warwaje ya kuma kara sakin kunnuwa yana sauraren su da al’ajabi da mamaki. Mata sun kware da gulma ya sani, amma ta wadannan ta bashi mamaki kasancewar su Nosis ne dake karkashin sa.
Shima ya yarda kamar yadda mahaifiyar sa ke yawan fada wato shi “SARHAM” mutum ne mai karfin “JI”. Wato jin sa yana da karfi, kamar yadda ganin sa yake da karfi yadda ba’a zato. Kusan komai na halittar sa ma mai karfi ne Ubangiji ya yi masa, idanun sa basa bukatar madubin kara karfin gani (medicated glass) da yawancin likitoci ke amfani da shi.
Sarham hatta takun tafiyar sa wato (gait) din sa shima mai karfin gaske ne, gab-gab-gab… haka zaka ji takunsa in ya dumfaro ko ya durkako inda kake. Kafin ya iso sautin takunsa zai gaya maka isowar sa. Baban sa kan ce, shi din, wato Sarham, “DAN BAIWA NE KUMA NA MUSAMMAN A CIKIN DUKA ‘YA’YAN SA”.
Komai nisan zance in dai yana gefe aka yi shi, to kuwa tabbas Sarham zai jiyo shi tsaf. Wannan wata baiwa ce da Ubangiji ya yi masa da ba kowa yake yiwa ba, wadda a kullum yake gode masa a kanta, wato baiwar kyakkyawan ji da gamsashshen gani, da suka banbanta dana sauran mutane da yawa, shiyasa a kullum kunnuwan sa suke zuko masa abinda ba’a zaci ya ji ba.
Ga shi dai da gaske siriri din ne shi, kuma dogon mutum a halitta, kamar dai yadda suka gulmanta, shima ya san hakan, don har wasu na yawan fadin wai yana dieting ne saboda sirantar sa mai yawa ce a matsayin sa na namiji, amma kuma a zahiri kakkarfa ne ta cikin kasusuwansa, zaka gane hakan ko daga fadin kirjin sa da kaurin kwanjin sa, wanda ke nuna duk safiya yana motsa jikin shi da kyau da hanyoyin motsa jiki irin na bature, ko daga kaurin tsokar damatsan hannun sa.
Kallo daya zaka yi wa Dr. Sarham ka fahimci yana matukar kula da lafiyar sa kwarai da gaske, ta hanyar kula da abinda yake ci, da motsa jini (exercise) bada wasa ba a duk safiyar Ubangiji. Shi yasa yake dan shafal da shi mai dogon hanci.
Sannan tsayin sa bai wuce kima ba kamar yadda Nosis dinsa suka kintata shi a gulmar tasu, kuma kaurin jikin sa ya wuce ace masa kamar na karan-raken takanda, kai shi bai taba jin wani ya kushe halittar sa ba banda wadannan magulmatan matan, iyakaci ana cewa yana ‘dieting’ baya cin abinci saboda kwalisa, amma shima ya san shi dogon ne saidai ba kamar karan-rake kamar yadda yaji suna cin naman sa ba.
Don haka ba tantama in aka yi la’akari da kalaman bakinsu, da bayanin da mai dan hankalin cikin nasu tayi a kan karatun sa, za’a fahimci tabbas sun yi masa farin sani ba kirkirowa suka yi suka fada ba, har da abinda ya bashi mamaki cikin zunden nasu, wai a Baban sa Farfesa ne na tsangayar ido, kasancewar bai dade da zuwa Murtala ba, kuma shi dai ya san bai taba abota da kowa a asibitin nan ba, balle su ma’aikatan jinya mata wadanda a karkashin sa suke.
Sai yayi dan murmushi kawai wanda ya motsa gefen kuncin sa na dama, ya cigaba da rubuce-rubucen da yake yi a cikin wani fayal na mara lafiyar da ya kammala dubawa ya fita, yace a ran sa.
“A zauna a kafa tebur saboda kai, ana rage maka zunubi haka ai ka isa ne, wanda bai isa ba ko kallon sa ba mai tada kai yayi”.
Yana cigaba da rubutu yana murmushi cikin mamakin gulma ta rashin aikin yi irin na mata musamman ma’aikatan jinya.
Dr. Sarham Abbas Shanono kenan. Siririn wankan tarwadan matashin likitan da bai fi ace a bana ya gama makarantar sakandire ba, sabida duka-duka bai fi shekaru ashirin da takwas ba.
Hayaniyar Malaman jinyar sa, da ta dattijuwa Innar Hauwa data dage bazata tafi ba sai ‘yar ta Hauwa’u ta ga likita, koda kuwa dukan ta zasu yi karewar rashin kunya, tace ban haife ku ba? ta kuma ce ai asibitin ba nasu bane na gwabnati ne, don haka basu isa ba da zasu hana ta ganin likita, inji dattijuwar, don sun kure hakurin ta, wannan hayaniyar ta hana shi fuskantar rubutun ma da yake yi yadda ya kamata. Gashi kuma a kofar ofishin sa ake ta wannan taqaddamar.
Su Nosis din sun dage da rashin mutuncin tunda ta bari sai da ido ya rube zata zo asibiti, to ta je ta nemi sandar yi wa ‘yar ta jagora zuwa bara. Amma bazata batawa likita lokaci ba, a lokacin da ba abunda zai iya tabukawa wadannan idanun da hakiya ta gama canyewa murus.
Innar Hauwa har da kukan ta, don taga alamar fada ba zai bi da su ba, tana rokon su da muryar ban tausayi su bar ‘yar ta ta gan shi kada ta makance, ta yarda ta yi laifi amma a taimaka musu su ga likita don Allah, ta tuba. Kuskure ne ta riga ta yi. Nan gaba zata kiyaye. Amma ma’aikaciyar jinyar nan ko a jikin ta, ta dora kafa daya kan daya akan kujera tana karkadawa ta hana su shiga ta yi rantsuwa da Jesus din ta, ba zata bari su batawa likita lokaci a kan idonnan da sun riga sun kashe shi a banza ba.
“Me ke faruwa haka? Hayaniyar me kuke yi mata haka? Ke Maria, meye haka kike yi? Wannan ya dace da ma’aikacin jinya? Sister Saratu wannan matar bata girme ku ba?”
Dakusassar muryar DR. SARHAM, irin ta mai fama da sabuwar mura, ta karade wurin, yana maganar yana furzar da dan tari, don sosai yake fama da mura daga jiya zuwa yau da ya dan sha ruwan sanyi, jikin sa baya son sanyi ko kadan.
Muryar tasa ta dira a kunnen su da sigar tambaya daga inda yake tsaye a jikin kofar ofishin sa, hannayen sa duka biyu zube cikin aljihun bakar Jacket din sa, yana dan yamutsa fuska cikin gajiya da alamun jin yunwa, don tun safe yake aikin duba marassa lafiya har zuwa yanzu da agogo ya buga karfe biyun rana, wato lokacin cin abincin ranar sa kenan da zuwa yin sallahr azuhur, lokacin tafiyar sa gida yayi kenan. Don haka ya fito ne don tafiya gida.
Yana sanye da bakaken ‘suit’ da ya zanzare kugun sa a cikin su, ya dora bakar jacket a kan su, wadda ta sauko har zuwa gwiwar sa, ta bada suurar cikakken dan gayun likita kuma dan kwalisa dashi na wancan zamanin, masu yawan yin zanzaro da belt.
Bafullatanin Shanono mai kakkaifar murya, amma a halin yanzu ta dushe, ta dakushe da alama yana fama da ‘Catarrh’.
Yanayinsa na Kanawan usli ne, amma yanayin zubin jikin sa na Fulani ne, sabida sirantar sa da ta zabge masa cika ido kai bazaka ce yayi shekaru ashirin da takwas din da yake da su bama.
Sister Saratu ta hau raba ido tsakanin Innar Hauwa da Likita Sarham, ta ki cewa komai, don a dan zamansa da su na dan gajeren lokacin da bai wuce sati biyu ba da aka yi masa transfer daga asibitin Abdullahi Wase (Nassarawa hospital) zuwa nan wajen su, sun fahimci halinsa na kirki yayi yawa a kan marassa lafiyan sa, (he’s very compassionate and caring to his patients), shi yasa a halin rashin mutunci irin nasu suke cewa ya fiya iyayi da kidifiri.
Ilai kuwa ya fahimci komai tun ma kafin su bashi amsa, don ya san ba yau suka fara ba, wulakanta marassa lafiyan da suka rainawa ajawali halin ma’aikatan su ne, daga zuwan sa zuwa yanzu ya gama shaidar hakan, kuma yana cikin sahun likitocin da suka san darajar dan adam, basa yarda da hakan, sai dai in an yi ne a bayan idon su.
A fusace ya soma fadin “wato Metron Maria, Sister Saratu, Nos Mairo ba zaku daina wulakanta bayin Allah ba ko? Shin anya kun san aikin ku? Wannan ba shine halin da aka san ma’aikacin jinya na hakika da shi ba, hakan cin amanar aiki ne babba, kuma tozarta dan adam ne.
Ina ‘humanity’ din ku da aka hore ku da shi matsayin ku na ma’aikatan jinya, dana kiwon lafiya?
A gaskiya na gaji da halin ku, ko jiya na raba ku fada da patient. Idan baku yi hankali kun yi aikin da ya kawo ku yadda ya kamata ba wallahi duk sai na yi reporting din ku”.
Ya dubi Innar Hauwa data sunkuyar da kai kasa tana tsane ido, yace.
“Baiwar Allah me ya faru? Waye babu lafiyan?”
Innar Hauwa ta ji dan kwarin guiwa ya shige ta, saboda a cikin muryar sa mai dushewa da rashin karsashi saboda mura, akwai (caring) wato kulawa da darajja dan Adam, ta rausayar da kai gefe ta ce,
“dama yarinya ce na kawo tana ciwon ido, to sun ce ban zo da wuri bane shiyasa bazan ga likita ba, shine dalilin da nake ta basu hakuri”.
Tausayin matar ya kama shi, ya dubi yarinyar da take rike da hannun ta, yadda hakiya ta cinye rabin idon sai da tsigar jikin sa ta tashi, zuciyar sa ta tashi, ga kwantsa babu kyawun gani, da sauri ya dauke idon sa daga kallon yarinyar, ga kafafun su futu-futu da kura tabbacin sun sha tafiyar kasa mai nisa kafin su iso asibiti, sai ya karbi katin su daga hannun ma’aikaciyar jinyar da katin ke hannun ta wato Nos Maria, ya kuma yiwa Inna umarnin su biyo shi a baya zuwa cikin ofis din.
Sai lokacin Inna ta gane shine likitan da ake musu rowar gani.
“Iya yaya aka yi aka bar idon yaci hakiya sosai har haka?”
Dr. Sarham ya tambayi Innar Hauwa, yana haska cikin idanun Hauwa da ‘yar tocilan din sa mai tsananin haske, yana magana cikin tsantsar damuwar da ta kasa boyuwa a muryar sa, yana cigaba da haska cikin idanun bayan ya gwale su sosai, Inna bata iya ta ce komai ba amma ‘guilt’ ya bayyana akan dattijiyar fuskar ta ainun.
Dr. Sarham ya gama duba idon Hauwa da tocilan din sa, ya kuma gama nazarin sa gabadaya duk cikin dan lokaci, sai ya koma ya zauna a bakar kujerar sa mai juyawa, itama yace ta zauna a kan kujerar zaman maras lafiya da ke fuskantar sa, ya bude mata fayil a take don ya gama gano Hauwa na bukatar aikin ido na gaggawa kawai, don a cire hakiyar. Ya sunkuyar da kai yana rubuce-rubuce a cikin fayil din ta, kafin ya gama ya dago ya dubi Inna.
A hankali kuma cikin tsanaki, Dr. Sarham Abbas Shanono, ya shiga yiwa Innar Hauwa bayanin amfanin zuwa asibiti da wuri, da zarar an ga alamun ciwo, ba sai ciwo ya ci ya cinye ba, cikin tausasawa da lallashi da fasahar harshe irin nasa yake mata magana, ya gaya mata yanzu ba abinda za’a iya yiwa Hauwa a ceci idanun ta illa cataract surgery watau (fida don cire hakiya) ta gaggawa.
Likitan ya saka musu ranar aiki jibi-jibin nan, ya kuma fada musu kudin aikin. Duk da Innar Hauwa ta tsorata da yawan kudaden bata nuna ba ko a fuska. Duk da ta san kuwa bata da su a ajiye.
Da suka koma gida Inna ta shiga cikin matsananciyar damuwa, na farko bata da kudin da likita ya bukata a yanzu, ko jarin wake da shinkafar ta ba zai yi kwatan su ba, abu na biyu tana ganin bazata iya bari a farkawa Hauwan ta ido ba haka kawai. A je garin neman gira a rasa ido. Ko a jangwalo wani abun da yafi karfin su.
Amma Hauwa ta dagewa Inna ita dai tana so ayi mata aikin nan. Inna ta gaya mata abinda take tsoro da kuma rashin kudin aikin a hannu, nan Hauwa ta dinga magiya har da kuka, tana rokon Inna ta amince in yaso ko dan taure daya ne cikin dabbobin ta a sayar a biya. Komai ya faru daga Allah ne.
Haka kan dole Inna ta amince da shawarar ta, don bata son kukan Hauwa ko bacin ranta. Ta fidda Akuya budurwa aka sayarwa mahauci. Washegari, wato ranar da aka basu, da sassafe suka koma asibitin Murtala.
Likita da abokan shiga tiyatar sa suka gama shirin yi wa Hauwa aiki, aka nemi Inna da ta saka hannu, Inna ta saka hannu amma da ganin ta zaka fahimci a matukar firgice take, gani take kamar aka shiga da Hauwa tiyatar nan bazata fito a raye ba, Inna ta soma hawaye tana sharewa da habar zanin ta, tana kankame da hannayen Hauwa.
Ganin haka Dr. Sarham ya shiga yi wa Innar Hauwa maganganu na kwantar da rai yana cewa “kada ki damu Innar mu, lafiya zan maido miki ita, da iznin Ubangiji, da kiyayewar sa, da albarkar sa za’a yi aikin nan lafiya a fito lafiya, in sha Allahu.
Idanun Hauwa’u su koma tangaras, kamar yadda suke a baya su rabu da hakiyar da ke cikin su, hakiya musiba ce ga ido, kin ji ko Inna?”.
Ta daga masa kai, ba don ta gamsu ba, amma bata fasa zub da hawayen ba.
A haka aka shiga da Hauwa dakin tiyata. Ko kafin masu allura su yi mata allurar tafi-da-ran ka wato (anaesthesia) fuskar Dr. Sarham Hauwa ta kurawa ido tana cewa a ranta inama tana ganin sa tar-tar, domin ta ji dadin abinda ya cewa Inna.
Haka ta cigaba da kallon saitin fuskarsa kamar tana ganin sa sosai, alhalin inuwar sa da karshen tsayin sa kawai take iya gani, bata san me yasa take son sanin yaya kamannin sa na halitta suke ba, ko don tausasan kalaman bakin sa ne da yadda yake lallaba mata rikitacciyar Innar ta, domin a lokacin bata ganin komai dadai ama dai tana ganin haske cikin idanun ta.
Murmushin da Dr. Sarham yayi mata a lokacin kamar ya san me take ciki da zuciyarta ne, taji sautin murmushinsa a kunnen ta, ji tayi kamar ya fahimci ba abinda take son gani a lokacin sai hakikanin kamannin fuskar sa, ba don komai ba sai don ta kwatanta su da kyawun kalaman bakin sa.
Ta kasa manta sautin murmushin nasa. Haka kalaman karfafawa marar lafiya zuciya cikin mutumtawa wadanda Dr. Sarham ya yi mata a lokacin, bata jin har abada zata manta su. Ya bata ‘hope’ na cewa zata rayu, kuma zata warke cikin yarda da amincewar Ubangiji; wanda ya saukar da cuta kowacce iri tare da maganin ta.
Tsananin tsoron da Dr. Sarham ya gani cikin idanun Hauwa-Kulu, da karkarwar da jikin ta ya fara lokacin da za’a yi mata allurar ‘anaesthesia’, ita ta saka shi dakatawa daga abinda yake yi wato saka safar hannu, ya sake matsowa daidai kanta har tana iya jin kamshin balaraben turaren sa, cikin taushin murya da lallashi Dr. Sarham yake cewa,
“Relax Hauwa’u. Zamu yi aikin nan lafiya da iznin Ubangiji kinji, kuma zaki samu lafiya Insha Allahu, zaki warke, saki ranki kin ji ko Hauwa’u?”
Daga haka aka soka mata allurar ‘tafi-da-ran ka’ wanda hakan yasa Hauwa runtse idanun ta, kuma ta tafi cikin barcin ne da mafarkan kamannin LIKITA SARHAM! Da fatan ko a lahira Allah ya hada fuskokinsu.
Don gani take kamar ta tafi kenan, duk kuwa da ‘hope’ din da ya bata, har abada ba zata farka ba.
Wato dai Hauwa ta tafi barcin ne da kintacen fuskar Likita Sarham a zuciya da kwakwalwar ta, na wani irin kintace, da dakace, da kuma hasashen ko shin yaya kamannin sa na zahiri suke?
Idan aka yi la’akari da irin kyawawan furucinsa/kalaman sa???