HAUWA KULU Book 1 Complete Hausa Novel

HAUWA KULU Book 1 Complete Hausa Novel

An sallami su Inna daga gadon asibiti bayan an kwance karayar hannun Hauwa ranar wata lahadi, ta dauka shikenan sun rabu da jelen Jamilu. Amma ina! Ashe wasa farin girki, lokacin nema Jamilu ya maida gidan su wajen zuwansa. Aka ce in kaga kare na sunsunar takalmi….
Wani babban abinda yafi bata mata rai, duk shiru-shirun Hauwa da miskilancinta in da Jamilu suke hira kaji ta har tana kyakyatawa tun daga soro, tana hira rai-rai-rai kamar kanari ita da shi, ta sake da shi sosai abin ki da jini! Asabar da lahadi da baya zuwa aiki a gidan su yake wuni, makale da Hauwa, Inna ta rasa yadda zata yi da Jamilu. Daga baya ya fito fili ya gaya mata shi fa kamun kanwarsa yake yi, da zarar ta kare sakandire zai kawo sadakinsa.
Inna kam bata yi kasa a gwiwa ba ta ce “Jamilu kana wasa! Kaima ka san wannna abu ne da ba zai taba yuwuwa ba, don haka na roke ka daga yau kada ka kara tada wannan maganar mara yuwuwa.
Ni bazan raba ka zumunci da ‘yar uwarka ba, amma bana bayan wannan maganar wai auren zumunci kai da ita”.
Jikin sa a sanyaye ya koma gida ranar, kuma kai tsaye ya yanke shawarar tunkarar mahaifin sa a kan maganar, a yi ta ta kare. Komai ta fanjama-fanjam.
Malam Zakari sai da ya bari Jamilu ya gama bayani kaf cikin kankan da kai, da tsananin ladabi ga mahaifin nasa, sai ya ce masa, “kai kai kai! Kai kuma ta nan ka bullo?
Auren makauniya? Diyar BILYAMINU jafa’i a cikin zuri’a ta? Toh ban shirya haifar jikan da zai zo ya zama dan jagora ba. Ko ya gado makanta ya saka min a cikin zurri’a, ko babu makanta haihata-haihata jinina ya gogi na Bilya jafa’i, jinin jaraba jinin masifa jinin tsiya da rashin arziki.
Idan ka kuskura ka sake zuwa inda suke, idan na ji labari, sai na tsine maka albarka”.
A gigice Jamilu ya bar gaban Baban sa, o ganain gabansa baya yi, shi kuma Zakari Jamilu na tafiya ya saka takalman sa ya fito ya rufo shagon atamfofin sa dake cikin Singa.
Da ya fafuri mota bai tsaya a ko’ina ba sai a Badalar Kofar Na’isa.
Gidan ai ba zai taba bace masa ba, tunda kuwa gidan gadon su ne, Bilyaminu yayi masa karfa-karfa ya raba shi da shi, don haka kai tsaye ya tuna hanya, bayan tsayin shekarun da ba zai iya tuna yawan su ba rabon sa da ko bin hanyar.
Zakari ya yi sallama a zauren Inna, da katotuwar murya mai razana wanda ake yimawa.
Ta na tsakiyar dabbobin ta tana zuba musu dussa, ta ji muryar sa yana kwada sallama kamar zai tada gidan “Safiya, ina Safiyar ne? Diyar masu Danjangabo?”.
Nan da nan zuciyarta tace mata “ZAKARI!”. Don shikadai yake kirata diyar masu Danjangabo don sana’ar mahaifiyarta kenan. Inna ta dago kai cikin mamaki ta tako ta iso soron ta yi tsaye a gaban sa, bazata iya tuna rana ta farko da ya tako kafar sa gidan su ba tun bayan rigimar mallakar gidan, da a karshe ya sayarwa Malam Bilyaminu.
“Ai bai kamata kiyi mamakin gani na yau ba, tunda ke kika takalo ni, kuma kin sanni farin sani kamar kashi nake, sai an kula ni nake doyi”. Zakari ya fada cikin gyara murya da gyara tsayuwa. Inna tace,
“dole in yi mamaki mana tunda dai na san banza bata kai zomo kasuwa” “yo daman ina kuwa zata kai shi? Sai ya ji wuta!
Zuwa nayi in ja kunnen ki, in sake ja, da kwantareriyar murya, in kin ji kin dauka, ki zauna lafiya, in kin ki ji ba kya ki gani ba.
Ki saki kurwar Da na Jamilu ta shakata, don shi ba nakasashshe bane, haka kawai kin ga yaro da maikon sa shine zaki bi dare ki bi rana ki lika masa makauniya ko? Yo Allah na tuba ko Kulu idon ta hudu kinga ta dace da Jamilu yaro son kowa dan gata dan asali, mai ilmi, mai nasaba, Uwar Bilya kuwa ki bincika tarihi kiji inda uban mu ya samo ta, can ne cikin zuri’ar su barbushe da tsimbirbira”.
Inna Safiya ta yi tsaki ta ce “kana tunanin ko Hauwa ta rasa miji saboda makanta, ko tana yawo tsirara saboda talauci, zan dauketa na baiwa dan ka ko shugaban kasa ya zama?
Ai ni martabar diyata da kake gani, duk da take marar ido, miskiniya, wallahi tafi karfin gidan ka, wulakantaccen gida na rashin tarbiyyah, gidan da daga ‘yan daba sai ‘yan shaye-shaye, sai sauta ga wawa rututu. Uba daya uwa kowa da tasa, kurwar ‘ya ta kurr da shiga irin wannan la’anannen gidan na Allah wadai, in sha Allahu”.
Zakari ya kyabe baki duk da ya ji mugun ciwon maganganunta, ya ce “ni dai na gaya miki, kuma aure-aure ai arziki ne, idan fitsari banza ne kaza tayi mana, shi bai iya ya kara ko daya ba saboda talaucin da yasa shi barin gida, ke da aka gudu aka bari bakin jini yasa ba wanda ya taba zuwa ya sunsuna ki da sunan aure, a haka zaki mutu gwauruwa, da makauniyar ‘ya a gaban ki kina mata tsarkin kashi.
Daga yau zan zuba C.I.D a kofar gidan nan, aka kara gaya min an ga Jamilu ya shigo, duk abinda ya same ki ke da makauniyar ‘yar taki ku kuka da kanku, ke kika saya muku da kudin ku, lakadan”.
Ya juya ya tafi, ya bar Inna tana tsaki. Juyawar nan da zata yi sai taga Kulu a bayan ta curko-curko da ita, manyan idanun ta kamar sa fado kasa don tashin hankali, tayo waje dasu bakidaya. Inna tayi kwafa tace,
“gara da kika ji da kunnen ki, irin tijarar ubansa, marar lissafi, gobe ki kara tankwashe kafa kina hira da Jamilu da sautin murya kamar na gyare, a zo a ci mutuncina ban ji ba ban gani ba.
Jamilun da kin riga kin san waye ubansa, ko wanene Zakari ba bakon ki bane ba”.
Jamilun bai san an yi haka ba a washegari ya zo wa Hauwa sallama zai wuce wani ‘workshop’ da banki ya tura su na sati daya a jihar Delta.
A take kuwa aka kira Alhaji Zakari a waya aka gaya masa, ga Jamilu nan ya sake zuwa.
A ranar, duk da Inna na cikin bacin rai, haka ta hadiye shi, ta zaunar da Jamilu a gabanta, cikin lalama ta roke shi Allah Annabi ya rabu da Hauwa-Kulu, kada ya kara zuwa gidan su.
Ta warware musu shi da Hauwan irin tsohuwar gabar da ke tsakanin iyayen su maza tun kafin a haife su, a sanadin ‘yan ubanci kawai, ba wani kwakkwaran dalili. Ta kuma gaya masa ita a yanzu girma ya cimmata, bata fama da ciwukan zamani ko guda daya, don haka bata son abinda zai tada hankalin ta.
Ta ce masa Hauwa kuma ka gani nakasa ta same ta, wadda tasa bazan iya yi mata aure ba sam-sam, balle na kai ta cikin iyalin Zakari, zai iya hura wuta ya babbaka min ita, a karshe Inna tace.
“Jamilu daga ni sai kuma Allah kadai muka ragewa Hauwa-Kulu, ni kadai ce karfin ta a yanzu, don haka ina tattalin rayuwar ta ne bazan iya kaita inda bazata taba samun kwanciyar hankali ba, koda zan mata auren, balle in kaita gidan ku. Balle kuma bazan taba yi mata aure ba in ba idanun ta ne suka dawo ba. Don haka na roke ka Allah da Manzonsa kan a bar zancen nan daga yau, anan inda zamu ajiye shi.
Jamilu na yarda kai mutumin kirki ne, zuciyarka ba irin ta mahaifinka bace, kai daya ne cikin dubu a gidanku, kuma kai mai nufin Hauwa da alheri da soyayya ne, duk da lalurarta ka amince ta zamo maka uwar iyali a haka, babu wata kauna da taimako da soyayya da wani dan adam zai nuna ma Hauwa a duniya da ya wuce wannan a doron kasa. Hakika mun yaba maka, mun kuma gode maka, domin ka so kayi jihadi ne kuma Allah zai baka ladan niyya.
Amma komai zamuyi sai da yardar iyaye zai yi albarka Jamilu ka sani, ina kuma tabbatar maka ba zaka taba samun albarkar mahaifin ka ba in kana tare da Hauwa-Kulu”.
Jamilu Zakari, yasa hankaci yana tsane tulin hawayen idon sa, ya fahimci Inna sosai, yau kam ya fahimci bata kinsa da Hauwa kamar yadda yake zato a baya, ya fahimci abinda ada ya kasa fahimta, wato su iyayen Hauwa da nasa mahaifin, bazasu taba zama a inuwa guda ba, a sanyaye Jamilu yace.
“Inna na ji ki, na kuma fahimce ki, amma ku sani daga ke har Babana; Hauwa ‘yar uwa ta ce ta jini, ba’a raba hanta da jini, ni kadai na rage mata matsayin Uba kuma dan uwa a yanzu.
Maganar aure tsakanin mu na bar ta har abada! Amma ni Jamilu daga yau nine Yayan HAUWA-KULU na halali kuma Uban ta na jini, daga nan har karshen rayuwar ta, ko kuma ranar da mahaifin ta ya dawo na damka masa ‘yar sa a hannunsa.
Kiyi min alfarmar cigaba da zumunci da ita, da kula da ita, tunda na hakura da maganar aurenta, ba don komai ba sai don samar muku kwanciyar hankali amma ba don na daina sonta ba, don ni da kaina na san Babana hatsabibi ne”.
Inna ta rasa kuma me zata ce. Ta rasa Jamilu kowanne irin mutum ne da baya gane abinda za’a shekara ana ganar da shi.
Da zai tafi ya kawo kudi masu yawa ya baiwa Inna, shi kan sa baisan adadin su ba, yace su yi amfani da su kafin Allah yayi masa dawowa daga tafiyar da ta same shi zuwa Delta.
Jamilu ya tafi Delta da kwana biyu aka yi sallama da Inna a zaure, maza ne magidanta su uku, nan suka gaya mata yaya har yanzu bata tashi daga gidan ba?
Inna ta ce “wane gidan?” Sai suka hau mata bayanin wannan data ke ciki yanzu, saboda mai gidan yana so zai rushe shi, zai mayar da wajen kamfanin buga ruwan leda, ko ba a gaya mata an bata notice din tashi na kwana uku ba?”
Inna tayi musu kallon banza ta ce “ban gane ba? Anya nan gidan kuke nema? Nan dai gidan Malam Bilyaminu Kofar Na’isa ne, wanda ya gada daga tsohon sa”.
“Ya gada ko suka gada?”.
Mutumin ya gyara mata zance cikin gatse. Kafin ta bashi amsa yace “to ai shi Zakari ya riga ya sayar mai da gidan a gaban wadannan shaidun”, ya nuna mutanen da suke tare, wadan da ‘yan unguwar ne abokan Zakari, sannan ya fiddo ainahin takardun gidan ya nuna mata, wadanda Innar bata san ina aka je aka samo su ba.
Suka ce lallai suna son gidan su zuwa gobe, don za’a zo a rushe shi goben, da sauran gidajen da aka saya na makwabtan su.
Da fadin haka Inna ta rasa abinda zata yi, sai kawai ta saka kuka tana cewa su koma su gaya wa Zakari ta sallami dan sa Jamilu in dai a kan sa ne zai mata wannan tozarcin. Ko sauraron ta basu yi ba suka tafi.
Har washegari Inna ta kasa gayawa Hauwa maganar nan, tana ta fama da ita a kirjin ta dake faman zabalbala, zuwa yamma kuwa wasu tsagerun samari suka shigo suka soma fatali da kayan Inna suna jefo komai waje. Suka ce suma saka su aka yi. Ga masu rusau nan zuwa, in sun ki fita ta arziki za’a rushe har da su suna ciki.
Yadda ake jifa da kayan Inna a unguwar ya janyo hankalin daukacin jama’ar unguwa, suka taru don neman ba’asi, amma ba wani bayani sai na maigidan ya sayar da shi, ita kuma Inna an ce ta fita ta laluma taki fita. Inna na kuka, Hauwa kuwa don taurin da zuciyar ta tayi idon ta ko kyallin hawaye babu, amma ya kada ya yi jajir, jakar makarantar ta lalubo da gilashin ta da Sarham yayi mata ta sakaya idanunta, ta goya jakar ta mai dauke da komai nata na makaranta ta kama hannun Inna, kamar itace mai idon ba Inna ba, Hauwa tace.
“Kada ki damu Inna muje, Baba Zakari ya kara arziki da gidannan don Allah, in don ni ko a tashar mota da karkashin gada zan iya kwana, in dai idan gari ya waye zan je makaranta, ba kuma zaki bar ni in yi “bara” don bana gani ba”.
Inna ta kasa magana sai kuka, a haka ta yafa mayafin ta ta kulle kayan ta da zata iya dauka a bakko, ta kama hannun Hauwa suka fice daga gidan.
Gidan su mai tsohon tarihi! Gidan da tayi dukkan rayuwarta da ‘ya’ya da mijinta, sama da shekaru talatin. Gidan da ba abinda take so a rayuwarta sama da shi.
Ga Hauwa kuwa wannan gidan na bayan Badala shine farin cikin ta, da shi kadai take tuna ta rayu tare da mahaifinta.
Ko minti goma basu yi da fita ba, masu rusau din suka iso, cikin dan lokaci suka hau rushe gidan Malam Bilyaminu. Kafin dare sai kasar gidan da duwarwatsu, Dabbobin Inna kam tuni sun yo waje da suka ji su a bude babu turke. Sai Malam Isa da ya dawo kasuwa ya ga dabbobin a kofar gidansa aka kuma gaya masa abinda ke faruwa wato Zakari ya kwace gidan ya sayar su kuma wadanda suka saya sun rusa, Hauwa da Inna suna tsaye a kofar gidan sa ake ta rushe gidansu akan idon su, sai ya tattara dabbobin ya kora su wani kango na gidan sa ya rufe su.
Jama’ar unguwa suka yi dafifi suka hana Inna barin unguwar suka ce tunda dare yayi ta shiga gidan Malam Isa zuwa gobe, dattijan unguwa sun ce ta zauna gobe a shigar da karar Zakari a kotu. Don mai unguwa ya dade da rasuwa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected