HAUWA KULU Book 1 Complete Hausa Novel

HAUWA KULU Book 1 Complete Hausa Novel

GULMA AJALI
A
wannan yammacin a Nurses station na sashen ido a asibitin Murtala ba’a komai sai gulamammaki masu lasisi, na abinda ya faru a kan aikin da sabon likitan ya yiwa maras lafiyar tasa. Su Nos Saratu da Metron Maria an samu abinda ake so, aka maida abin topic of discussion na wannan ranar.
Ko aikin su na ranar sun kasa yi yau, tsabar saboda yadda gulmar Sarham ke cin su.
Metron Maria wadda ita ta halarci aikin warware idanun Hauwa tare da likitan, ta ce “hey! In baku labari dai, kunnen ku nawa?”
Suka hada baki (in chorused) wajen cewa “kunnen mu biyu,” “to ku kara biyu ku sha labari.
Dr. Sarham dai ya karasa makantar da yarinyar nan mai hakiya da yake mana balbali akan su, aikin da yayi mata was not successful at all.
Kuma ya kama bakin sa salin-alin bai ce komai akai ba ya bar asibiti, ba tareda kowa ya san ta’asar da yayi ba, ya ja bakinsa ya tsuke ko sum utu ko suyi rai oho musu”.
Nos Gambo tace “ki bari don Allah?”
Saratu ta yi rantsuwa ta labarta musu abinda ya faru, ta ce “yo dama idon ya gama rubewa fa, maganin su kenan suma, da sun lallaba sun tafi da muka kore su da ta ci gaba da morar dan wani abun a idon, a’a su ga sarakan naci dambun kuturu, ni dama na san idon kiris yake jira a taba shi, shikuma karambanin sa kenan, an ce musu sawun su a likkafa su koma gida su cigaba da barbada farin kwallin su da suke barbadawa suka ki ji, wanda bai ji bari ba ai ya ji hoho, yanzu da ya maidata totally blind ai sa hakura”.
“Ni ai dama na fada muku tsautsayi ne kadai zai saka ni baiwa wannnan yaron idanuna ya saka musu wuka, har yaushe ya bar sakandire ko ince ya bar shan nono a cinyar uwar sa? Da zan bari ya fede min ido? Ai yafi kama da Romeo (Uban soyayya) fiyeda consultatant.
Ban da ilmi a Najeriya ya zama sabatta-juyatta, ya zama abinda ya zama wajen tabarbarewa, ban taba ganin inda dan kasa da shekaru talatin ya zama surgeon ba” wata bakuwa a cikin su mai hankali ta ce,
“ku kuwa ku daina abinda kuke yi bai kamata ba, shi aikin fida ai haka ya gada, ko ayi nasara, ko akasin ta, kafin ayi aikin mara lafiya ya san da haka saboda haka nema ake saka hannu bisa yarjejeniyar amincewar iyaye da makusan ta, so ko mutuwa ta yi bashi da alhakin hakan. Yayi iya kokarin sa Allah ne bai yi ba.
Idan fitsari banza ne kaza ta yi mana? Kuna ta zagin sa da kushe shi alhalin bai ci muku ba bai sha muku ba, ku ku je kuyi karatun fidar idon mana? Shin wai kyawun Dr. Sarham da gayunsa ne ya koma masa abin hassada a bakunan ku ko me?”.
Da wannan ta kashe bakin su murus, bayan sun musa da cewa ina abin yake da zasuyiwa hassada abu tsololo kamar karan raken takanda. Wata kuma mara kunya a cikinsu ta kada baki tace “ai irinsa sun fi dadin sha’ani a gado, ba’a dakin tiyatar ido ba”. suka kwashe da dariya. Har suka tashi aikin ranar basu bar wadannan zantukan ba na shegantaka har daya na cewa ya kamata a kwace licence din sa na aikin likitanci tunda daga zuwa ya fara da makantar da ‘ya’yan mutane, saboda rashin iya aiki. (Ni kuma nace gulma-ajali mai yin ki kadai zaki kashe).
***** ***** *****

“DESTINY TORMENTS….”

(DA KARFE SHIDDA NA YAMMA A GIDAN PROF. ABBAS SHANONO)

M
awakin ya sake cewa “Destiny torments my heart…” cikin baitin wata waka ne da Dr. Sarham yake saurare daga kwancen da yake a yammacin ranar, bayan komawarsa gida daga kwace idon Hauwa.
Yana kwance har kusan magriba a rigingine a tsakiyar matsakaicin gadon dakin sa. Sai ya ji shahararren mawakin zamanin wato ‘R-Kelly’ kamar dashi yake. Don zuciyar sa duk ta takura. Ya shiga kunci na babu gaira babu dalili. Ya yarda abinda ya faru dashi a kan aikin da ya yiwa Hauwa Bilyaminu kaddara ne, wadda ta rigayi fata, ba don haka ba ai yaji ‘warning alarm’ a cikin kansa, mai cewa ya bari kada yayi aikin nan babu nasara a cikin sa sam, don haka tunanin sa yafi karkata ga cewa sakacin sa ne ko gangancinsa.
Amma kuma da aikin kaddara ai, altogether.
Allah ya riga ya rubuta Hauwa Bilyaminu zata makance a hannun sa. But this written destiny really touched and tormented his heart.
Ace ka zama sanadin nakasar idanun wani dan adam kwata-kwata, duk da cewa dai aikin likita irin wannan (a mutu ko a rayu) ne, sannan ba za’a tuhume shi ba, tunda ya tafiyar da komai a kan ka’idar aikin sa ne, amma IDO fa ake zance, wannan kwayar tsokar guda biyu mafi amfani da muhimmanci ga halittar dan adam, sannaan in har kana da zuciyar ‘yan adamtaka a cikin kirjin ka da humanity a tare da kai, dole zuciyar ka ta tabu, da ganin yadda fuskar Innar Hauwa ta shiga tashin hankali a lokacin da Hauwa tace,
“bata ganin komai a gabanta sai duhu”.
Wanda tayi ta kokarin danne tashin hankalin data shiga din saboda shi. To shi tashi zuciyar ba tabuwa kawai ta yi ba da tausayin su da ‘disappointment’ akan aikinsa, ta kekkece ne, sannan ta tsatstsage ta yayyage ta yagalgale (into pieces at the same time). Ta yadda a gaban Innar Hauwa duk dauriyar da yake yi sa sai da idonsa ya kada, kwalla ta cika idonnasa, a fakaice ya yi kokari maida kwallar, ta hanyar juya musu baya ya zuba dukkan hannayen shi cikin aljihu yana maida kwallar sa, bai san Innar ta gane halin da yake ciki ba.
Hakan ya faru ne lokacin da ya ji Hauwa tana cewa.

“Shike nan yanzu Inna sunana Makauniya? Ba zan sake ganin fuskar ki data Baban mu ranar da ya dawo gare mu ba? Kema na daina ganin ki kenan daga yanzu?”
Yana iya tuno kalaman Innar Hauwa gare shi, da ta ga yasa hankici yana tsane kwallar da yake ta hadidiyewa cikin idanun sa a wayance, yanzu kam tafi karfin sa, ta baiwa kanta ‘yanci ta digo, a lokacin yana rubutu cikin fayil din Hauwa sai hawaye ya diga a kai, wannan ya faru a kan idon Innar Hauwa.
Sai Innar Hauwa ta bagarar da tasirin maganganun Hauwa suka yi mata a ranta, ta maida kulawarta a kan shi inda ta dube shi cikin lallashi tace “Haba likita? Kaida zaka bata karfin guiwa? Shi Dan adam ai baya tsallake kaddarar sa. Ita Hauwa-Kulu kaddarar ta kenan.
Abin yi a yanzu gaba dayanmu shine mu yi mata fatan Allah yasa makanta ta zamo kaffara a gare ta. Idan makantar nan jarrabawarta ce ta dan wani lokaci Allah ya yaye mata ya bata ikon cinye wannan babbar jarrabawa, idan kuma ta har abada ce Allah yasa ta zamo silar shigarta aljannah. Nakasa ai ibadah ce ga wasu kebabbub bayin Allah!”.

Amma duk da tawakkali irin wannan wanda Innar Hauwa ta nuna, Dr. Sarham ji yake yana blaming kan sa, kamar rashin kwarewar sa ce ta saka Hauwa a wannan halin na rasa abinda yafi komai dadi ga rayuwar mutum, wato idanun ta.
Zai fi yarda idan aka ce sakacin sa ne, laifin sa ne, rashin kwarewar sa ko iyawarsa ce. To ko dai gaskiyar mutane ne da suke cewa yayi kankanta da zama mai ceton rayuwar idanun al’ummah?
Yaushe tasirin maganganun jahilan matan nan magulmata zai bar ransa ya sake ne? meyasa ma kunnen sa sarkin ji, ya zuko masa abinda ba alkhairi bane a gareshi kuma wanda zai dame shi?
Don haka koda ya baro su a asibitin ya dawo gidan su a ranar, wato gidan mahaifin sa, da matsanancin duhun zuciya ya shigo, mahaifiyarsa kanta ta fahimci cikin matsananciyar damuwa Lelen Abba yake. Tun daga bakin kofa kanwar sa Sumayya ta soma tarar sa da zance yadda suka saba saboda shim aba laifi akwai hira musamman da kannen sa, Sumayya tana gaya masa ta yi (passing exams) din ta, kawai ya zo ya bata kyautar da yayi mata alkawari bata son a bata lokaci har kyautar tabi ruwa tunda shi yayi alkawari. Amma ga mamakin Sumayya yau Lelen na Abba ko kulata bai yi ba, yayi fuska kamar ba shi ba, don ko kallon ta bai tsaya ya yi ba, balle ya bata lokaci wajen taya ta murna yadda ya saba in taci na daya a kowanne zangon karatu, balle har ya ce su fita ‘kingsway’ ta zabi ‘gift’ din da ya yi mata alkawarin.
Kawai sai yasa kai ya wuce zuwa dakin sa abinsa, yana cewa a ransa baki da matsala, ko sannu da gida yau bai iya ya yi mata ba itada sauran jama’ar gidan bakidaya.
Sumayyah bata daddara ba, ta sake kwasar faranti data shake da abinci ta biyo shi da abincin rana har dakin sa. Da yake ta gan shi cikin damuwa sai tayi tunanin yi masa abincin da ta san ya fi so, wanda dole zai kula yayi godiya, wato tuwon alkama miyar kubewa busassa. Miyar ta ji busashshen kifin banda da cryfish, ga lafiyayyen farfesun kayan ciki ta hado masa da shi da yaji kayan kamshi da attarugu, komai zai ci sai ansa tarugu da tafarnuwa, sune abinda ke sawa yaci abinci sosai ta sani, duk ta jera a kan tray ta biyo shi da shi har daki.
Sai ta samu kofar tasa ma a kulle da mukulli, wato ya kulle kan sa, don baya son kowa ya dame shi. Musamman ita Sumayya sarkin naci da zuba zance, ya san saita biyo shi, saboda da shi kadai take shiri ta kuma fi sabawa cikin gidan, bata iya zama idan ba kusa da shi ba.
Wannan kulle kan sa da yayi a daki tun dawowar sa gida da hantsi har bayan la’asar ya dami mahaifiyar sa Barr. Mai shari’ah Haj. Maimuna (Mama inji yaranta). Har bayan la’asar suna zuba idon ganin fitowar sa shiru suke ji, ta tambayi Sumayyah ko ya ci abincin ranar data kai masa? Nan take gaya mata cikin tata damuwar,
“ai Mama ko bude dakin bai yi ya dauka ba, dazu na kara dubawa na ga abincin yana nan a bakin kofa inda na ajiye masa”.
A lokacin Yayar Sumayyah mai bin Dr. Sarham a haihuwa wato Aunty Surayyah ta dawo gidan, daga gidan Kakar su Hajiya Kulu. Ba jimawa mahaifin su ma ya dawo daga cikin makaranta inda yake koyarwa wato Prof. Abbas Shanono, nan gidan ya idasa cika ya zama full-house yadda yake a kowanne yammaci in sun dawo daga sabgogin su.
Prof. Abbas ya tadda su jigum – jigum a falo wato dai damuwar Lelen Abba (Sarhamu) ta taba kowa. Don an yi bugun duniya bai bude ba, da Sumayyah ta dame shi da nacin rokon ya bude kofa ya dau abinci, a fusace yace mata in bata bar masa bakin kofar dakinsa ba zai fito ya yi kasa-kasa da ita a wurinnan.
“Yau ban ga Sarham a masallaci ba ko bai dawo bane?” In ji Abba Prof. ya fada yana nazarin ‘ya’yan nasa mata guda biyu da mahaifiyar su wadanda duk suke cikin damuwar abinda ke faruwa da babban Yaya.
A ka’idar Abba Prof. idan ya dawo gida daga cikin Jami’a kullum, kasancewar suna zaune ne a cikin rukunin gidajen manyan malamai na sabuwar Jami’ar Bayero, kafin ya shiga gida masallaci yake fara zarcewa wanda ke kofar gidan sa, mafi yawancin lokuta a can zai tadda Sarham ya riga shi isa, sabida baya wasa da bin jam’I, kuma sautari ya kan riga shi dawowa, zasu hadu a can, su bi jam’i tare, ba zasu shigo gida ba sai bayan la’asar.
Amma sabanin kullum yau har aka idar da sallah bai ga Sarham ba. Wannan abu ya dugunzuma shi, don ya jima rabon da yaga ranar da yana gida bai je masallaci haka kawai ba. Mama ta gaya masa yau sun rasa gane kan sa, ya shigo cikin damuwa daga wajen aiki, ya kulle kan sa tun dazu, har ya kusa dukan Sumayya da ta dame shi sai ya bude ya dauki abinci.
Bata kai ga rufe bakin ta ba sai ga Dr. Sarham ya fito daga dakin sa da saurin sa da hanzari, da mukullin motar sa a hannun sa, tun kayan dazun ne a jikin sa bai canza su ba, (which was unlike him) ya wuni da kayan da ya je asibiti dasu, idanun sa duk sun tasa kamar na wanda ya yi kuka ko ya kwana ido biyu da nannauyan barci.
Ya gaida Daddy da Mama cikin sauri zai wuce, sannan kafin a yi masa kowacce tambaya Sarham ya kama hanyar fita, sai da ya kai bakin kofa sannan yace musu zai koma asibiti ya dawo yayi mantuwa ne ba jimawa zai yi ba. Ya kara da cewa kada su damu ba wani abu ne ya same shi ba, lafiyar sa kalau. Ya dubi Sumayyah yace “ki je ki dauke farantin da kika tokaremin kofa da shi”. Daga haka ya fice. Duk suka bishi da ido har ya fice daga main falon, sun kasa dakatar da shi.
Yana tafe cikin ‘yar karamar motar sa ‘Honda Prelude’ ta yayin samari ‘yan gata mai kofa daya, wadda Abba Prof. yayi masa kyautar ta, bayan kammala karatun sa da dawowar sa gida daga kasa mai tsarki matsayin cikakken likitan ido (at a very young age), yana tafe yana tunanin makasudin sake fitowar sa daga gida yanzu menene?
Tunani kawai ya yi bai kamata ya bar Hauwa da Innar ta su tafi gida ba su ko yi sallama ba, don haka ya baro su a asibitin dazu (absent-minded) ya tafi gida don ya samu nutsuwar ran sa, bayan sallamar da asibiti yayi musu a yau (wato discharge). Son samu ma ya tambayi inda suke, don watan watarana.
A fahimtar sa dai, idanun Hauwa ya gama tafiya kuma ta sanadin sa. Wannan tunanin kadai yana matukar daga hankalin Dr. Sarham kamar ba likita ba, yana kuma azabtar da zuciyar sa, kasancewar bai taba aikin da bai yi nasara ba sai wannnan karon kan na Hauwa, shi ko kiyashi baya so ya ji rauni a hannun sa, watakila don wannan ne karo na farko da yayi aikin ‘cataract’ ya kuma fara da rashin nasara.
Har ya iso asibitin Murtala yana share zufa daga kan goshin sa da farin hankacin sa, da zara-zaran yatsunsa.
Ya karya kan motar zai shiga asibitin kenan sai ya hango Innar Hauwa dauke da dan kunshin kayansu a kan ta, ta kamo hannun Hauwa suna fitowa daga cikin asibitin.
Don haka da hanzari Sarham ya juya kan motar sa zuwa inda ya hange su, yayi gaba da su kadan ya tsaya, sannan ya fito daga motar ya nufe su.
“Inna har kun fito ne?” Sarham ya fada da karyayyar muryar data idasa karyewa a wannan lokacin, idanun sa fal kulawa da damuwa, bayan ya fito daga motar sa, ya maida kofar ya rufe ya tako a hankali zuwa inda suke a bakin titi suna jiran motar haya.
Da far’a Inna ta amsa “Mun fito likita, zamu taka zuwa gida, gashi har ka je gida ka dawo bamu tafi ba muna kailula don tun dazun anka sallame mu.
Kulu ce ta ce in bari ta kara jin karfin jikin ta bazata iya doguwar tafiya a dazun ba”.
Idanun Sarham fal damuwa, ya daga ido ya dubi Hauwan, ga idanu tar a bude, manya dasu, masu haske kamar an wanke su an kuma kara musu lafiya, unfortunately sun koma gululu, kuma ta sanadin aikin hannun sa, sai jujjuyawa kawai suke a kan titi.
Shin ta yaya zai yi ya daina damuwa a kan aikin nan da yayi ba nasara? Naturally shi mutum ne mai phobia na gudun zuciyar mutanen da yasan ya batawa, yawan tausayi ga marassa lafiya da masu karamin karfi, balle ga mata da kuma kananan yara. Shiyasa kannen sa mata biyu ke tsananin jin dadin sa da kaunar sa, saboda kulawar sa garesu.
Sai ya saka hannu ya karbi kullin kayan su da ke kan Innar Hauwa, ya ce “ku yi min alfarma Inna in raka ku zuwa gida, ko don in ga wuri. Ni dan ki ne, wace unguwa kuke?”
Inna ta ce cikin mamaki “anya dan nan ma saka ka wahala haka? Can muke da dan nisa, a can bayan Badalar kofar Na’isa”. Tuni kafin ta gama fada Sarham ya isa ga motarsa ya saka kayan nasu a bayan motar, ya budewa Inna da Hauwa kofar gidan baya.
“Babu komai Inna, don Allah ku shigo in kai ku”. Inna bata da zabi ban da kama hannun Hauwa ta shigar da ita bayan motar, don ta kasa tankwabe tasirin da kirkin sa da kamalar sa da jin kan sa yayi a ranta.
Dr. Sarham ya shigo ya tada motar ya juya ta suka fita daga asibitin Murtala gabadaya. Ba jimawa suka hau titin da zai sada su da Kofar Na’isa. Suna tafe a hanya Inna na nuna masa inda zai bi da su, lokacin da suka shiga cikin Ganuwa.
Hauwa dai bata cewa ko uffan, abinda ya dameta ya dameta, tana dai jin su jefe-jefi suna hira shi da Inna a kan ta. A surutu irinna Inna har tana gaya masa wai Hauwa ‘yar makaranta ce, tana aji biyu na sakandire a GGSS Shekara, ta yi jarrabawar shiga aji na uku yanzu, suna zaman jiran fitowar ta (jarrabawar) Hauwa ta fara apolo.
Can kuma ta nisa tace, “umh! Yanzu kuwa Hauwa-Kulu ai sai zaman gida ko? Tunda dai idanu sun tafi?”.
Ta yi maganar cikin wata irin murya kamar mai neman amsa daga gare shi, a lokacin da bawa ya rasa abinda ya kamata yayi akan wata babbar mas’ala data tunkaro shi ba shiri. Dr. Sarham yayi shiru, yana cigaba da tukin mota, bai ce komai ba don duk wani blame na makancewar Hauwa ya rasa me yasa ya daukeshi bakidaya ya dora shi a kan sa, bayan kuma ba haka aikin likita ya gada ba.
A ka’idar aikin sa bashi da laifi. Amma a humanity da dattaku irin nasa ji yake shine sila, shine ‘cause’ kuma shine ‘at fault’.
Daidai lokacin suka iso lokon gidan su Hauwa. Daga inda mota bazata iya shiga ba, Inna ta nuna masa inda zai iya aje motar ta ce sun gode zasu karasa da kan su a kafa daga nan, don gidan na su can cikin loko ne mota bata kaiwa.
“Inna ai har gida zan kai ku, bani kayan in rike miki, zan so ganin gidan naku don watarana in dinga gaishe ki, ina ganin lafiyar idon kanwata”. Inna ta ce “to likita muna godiya kwarai, kamar ka san bata da dan uwa. Allah ya yi albarka ya baka masu yi maka kai ma”.
Daga haka Inna ta wuce gaba Dr. Sarham ya bi bayan ta zuwa cikin lokon su tana rike da Hannun Hauwa’u yana dauke da kunshin kayan su.
Sarham yayi ta mamakin sanayyar jama’ar unguwar da Innar Hauwa yadda duk inda suka bulla jama’ar unguwar ke gaida Innar Hauwa cikin girmamawa suna kuma tambayar ta yaya Hauwa da ido?
Inna sai ta ce “sauki na wajen Allah tunda yanzu Hauwa ido babu!” “Kamar yaya ido babu?” Anan kam saidai tayi murmushi ta sa kai ta wuce su tana mai cewa “da sauki dai”. Ta kasa bayani don kada ta karasa Sarham a blame. Sosai kowa ya kasa ganewa haka dai ake ta jajantawa ana wucewa har suka shiga gidan su.
Dabbobin Inna duk sun bata gidan da kashin su da fitsarin su yayi daka-daka, kasancewar ta kwana biyu bata nan ba wanda ke sharewa, duk sun cakalkala gidan, ga ganyayyaki sun zubo a ka’ina irin busassun ganyen bishiyoyin su na darbejiya da umbrella duk gidan ya yi kaca-kaca.
Inna ta shiga dakin ta ta dauko ma Sarham kujera ‘yar tsugunno tana cewa cikin takaicin yadda ya tadda gidan nasu daka-daka,
“kayi hakuri Likita, gidan namu yayi datti, tumaki sun bata shi kwana biyu da bama nan, sun yi abunda suka ga dama a tsakar gidan nan. Ka ga nan shine gidan namu, ana cewa gidan “gidan Malam Bilyaminu Kofar Na’isa”, ko da nan gaba ka zo ka bata ko ka kasa ganewa, haka zaka ce, ko gidan su Hauwa-Kulu”.
Sarham yayi murmushi yana jinjina surutu irin na Inna, duk surutun sa ya samu Inna ta fi shi iyawa, don haka da alama tasu zata zo daya kamar Kakar sa Haj. Kulu yake jin maganganun nata, ya zauna a kujerar da Inna ta aje masa yana walainiya da kayatattun idanun sa a gidan, sosai yake sha’awar rayuwa irin ta cikin Badala irin wannan, don suma da can a bayan Badalar suke ta kofar Gadon kaya, amma tun sanda aka bude sabuwar Jami’ar Bayero aka maida mahaifin sa gidajen malamai na ‘New Site’, kasancewar a lokacin yana daya daga daidakun tsafaffin malamai masu matsayin Farfesa a tsangayar magani (medicine).
A can baya kafin a gina ‘New Site’ din iyayensa suna zauna ne a unguwar Kofar Gadon Kaya.
Suka sake sosai a tsakar gida suna cafkar hira shi da Inna, (they are all talkatives) kamar wasu yara. Hauwa na daga can cikin dakinta a kwance, kan siririyar katifar audugar ta, tana jin su da rabin hankalin ta, amma rabi baya tare da su sam. Ita kadai ta san me take (going through) wato me take fama da shi a zuciyar ta, wadda ke cike taf da rauni da karaya da rayuwa, idan ta shafa idanun ta taga duhu didim! Idan ta kyafta su taga babu komai a gabanta sai duhu! Shin wai shikenan haka zata dauwama har abada cikin duhun idanuwa bazata kara ganin fuskar kowa da komai ba, har kuwa fuskar Innar ta?
Har kuma tata fuskar a mudubi idan ta kalla bazata gani ba? Ko kuwa rashin ganin nata na dan lokaci ne watarana zai dawo? Ko kuwa tafiyar idon kenan? Duka wadannan tambayoyin da take yiwa kanta bata da amsar ko daya. Allah shine masani, amma hakika tana cikin matsanancin tashin hankali da dimuwa da wannan jarrabawa, wanda sai wanda ya taba rasa wata gaba ko wani sashe na jikin sa ne kawai zai iya relating.
Imanin ta yau ya karu akan mutane masu nakasar ido (visual impairment) da ta dade tana ganin su a hanya ko suna bara. Yau ta yarda makanta ba abu ne mai sauki ba. Tana jin yadda hira tayi dadi tsakanin Sarham da Inna, kamar su kam ba abinda ya dame su da abinda ya same ta.
Sai labarin halin baban ta wato Malam Bilyaminu da Yayan ta Zulkifl Inna take bashi a sanda suke tare dasu, da irin rashin jin Zulkifilu a sanda yake yarintarsa, tace kullum sai yayo tsokana ya dauko mata Magana shi haka Allah yayi shi ba kamar Hauwa ba da ko naman jikin ta zaka yanka sai ta ga dama zata daga ido ta dube ka.
Can ajima sai kaji Inna ta gangaro kanta ita Hauwan, tana gaya masa irin halin ta na kirki da yasa take tausaya mata wannan lalura data sameta yanzu, yadda Hauwa ke taimaka mata da ayyukan gida bata da kiwa (bata da ganda), ga son karatu kamar tsuntsun alhuda-huda.
Inna ta ce cikin mutuwar jiki da yanke tsammani, babbar damuwar ta a yanzu da makancewar Hauwa-Kulun ta, ba makantar bane ba kai tsaye, ko kiranta makauniya da mutane za’a ke yi, damuwar tata shine; ta yaya Hauwa zata yi ta cigaba da karatu?
Wannan magana da Inna ta yi, ba Hauwa kadai ta saka a tunani da damuwa ba har da shi kan sa Dr. Sarham. Kamar wani assignment na lissafi (mathematics) mai wuya yaji Innar Hauwa ta bashi shima. Wanda zai tafi gida dashi domin yayi solving ta hanyar tunani. Don haka koda suka yi sallama da Inna jikin sa duk a sanyaye yake shima, ya fito lokon ya shiga motar sa ya tayar, amma sai ya kasa tafiya, sai ya kifa kansa a kan sityarin motar na tsayin lokaci yana tunanin ta inda zai iya taimaka musu da rage musu.
Ya shiga cikin tunanin ta wace hanya zai bi ya taimaki rayuwar wadannan bayin Allah da ‘yarinyar su tilo, ta nakasa a hannun sa? Yo a hannun sa mana! Da yayi aikin nan da kula yadda ya dace da Hauwa bata makance ba (a tunanin sa).
Iyaka tunanin sa bai ga da me zai iya taimaka musu ba banda a kan sha’anin karatun Hauwa din, don haka ya yanke shawarar baiwa Abban sa labarin su, da neman shawarar sa da karin haske akan ilmin da bai sani ba wato special education. Kasancewar Abban sa mutum mai hangen nesa da yalwar ilmi a bangare daban-daban fiye da shi, ya san a nan ma bazai rasa sani ba.
Shi da Abban sa (are more than father and Son, they are very close and best friends) na junan su tun yana karami. Haka kanwar sa Sumayyah ita ce babbar abokiyar sa a rayuwa, Sumayyah is nice and easy going sannan (talkative like her Bhaiya) yadda take kiran sa kenan, shiyasa tasu ta zo matukar daya, su yi hira suyi dariya kasancewar sa very jovial likita abokin kowa, ba kamar sakuwarsa ba wato Surayyah, wadda ta dauki rayuwar sababbin ‘yan jami’a (JJC) mai tsauri ta sanyawa kanta.
Duk da kasancewar Sumayyah mai karancin shekaru to fa ya shaida ta fi Surayya hankali da hangen nesa, kai dai bar Surayya wajen iya ado, da iya daukar wanka da kuma son kyale-kyalen da zaa ce tafi kowa cikin tsararrakin ta aji. Halayen da ke hadata fada da Bhaiya din kenan a matsayin ta na sakuwarsa a haihuwa, kusan kullum sai an ji kansu, don shi ta rage wuni a gidan su sai gidan Hajiya Kulu kakar su.
Dr. Sarham, in ka cire abokan karatun sa da har gobe in an hadu akan gaisa, bashi da wani shaqiqin aboki da za’a kira aminin sa, duk da surutun sa da sakin fuskar sa to fa ya san a inda yake yin su, baida abokai sam saboda training din da mahaifin sa yayi masa kenan na ya zamo shine babban abokin sa (Abban), saboda gudun kada abokai su bata masa shi. Abba Prof. akwai saka ido akan tarbiyyar yaransa kamar baida wani aiki a duniya sai kula da su, sai ko abokanan aikinsa a Murtala, wadanda yanayin aiki kan hada su akan dole.
Maman sa kan ce “he is very anti-social, yet a parrot”, bashi da saurin yarda da sakin jiki da kowa, sai ko autar su Sumayyah, ko ita kan ta Maman ba komai yake iya gaya mata ba, da ya shafi sirrikan shi, amma tsaf zai iya gayawa kanwar sa Sumayyah komai su kashe su rufe ba tare da iyayensu sun sani ba.
Babu shakuwa mai yawa tsakanin Barr. Maimuna da daukacin yaranta, wannan ya faru kasancewar gabadaya rayuwarta ta sadaukar da ita ga aikin ta na Lauya da zurfafa karatu, don haka su Sarham sun taso kusan a gaban Kakar su ne Hajiya Kulu. Sun fi shakuwa da Hajiyar Gadon Kaya fiye da Maman su, wadda a can baya a gidan su take zaune.
Lokacin da aka maido Prof. cikin gidajen malamai na sabuwar jami’ar Bayero sai Hajiyar Gadon Kaya tace ba zata biyo su ba, domin bazata iya zaman wajen gari ba, a cewar ta a cikin Badala aka haifeta don haka a kwaryar badala take so ta mutu a binneta, don haka Prof. ya samar mata mai aiki mai suna Gambo, ta zame mata abokiyar zama suke zaune tare a gidan sa na Gadon Kaya wanda mallakin sa ne da ya gina da gumin sa. Lokaci-lokaci yana sabunta shi zuwa ginin zamani irin na wancan lokacin daidai da yawan iyalin sa.
Har yanzu Hajiyar gadon kaya na can amma ta tsufa ainun, sun yi sun yi ta dawo ta zauna tare da su ta ki, don haka kusan koyaushe kafar su bata rabo da gidan Hajiya musamman Surayyah, saboda yadda Hajiya ta shagwaba ta, kuma tafi jan ta a jiki duk cikin su.
Wannan ya samo asali ne daga sanda aka haife ta bada jimawa ba Mama tayi wani dogon rashin lafiya mai tsanani na lokaci mai tsaho wanda yasa dole aka dauke Surayyah a nono ba tare da ta isa yaye ba, Hajiya ce ta cigaba da rainon ta a dakin ta da madarar yara har ta yaye ta, sai ta cigaba da zama a wurin ta har bayan da Maman ta samu sauki, aka zo aka haifi auta Sumayyah, amma Hajiya ta rike Surayyah, bata kara bari ta dawo wajen Maman su ba, saidai ta zo da yawo har girma.
Ita kuma Sumayya dalilin shakuwar su itada Sarham ya samo asali da cewa kusan Sarham shi yayi rainon ta, domin akwai rata ta kusan shekaru goma sha biyu a tsakanin su.
In Mama na wajen aiki shi yake kula da Sumayya su tafi makarantar islamiyyar sa tare, har zuwa sanda itama ta isa shiga makaranta, malamai na hanawa azo da kananan yara amma Sarham ba ya jin Magana, gobe sai ya dawo tare da kanwar sa, in har ba za’a bar shi ya shiga aji da Sumayyah ba tofa zai koma bayan tagar ajin su ne shi da ita su make su yi ta leke, korar duniya malamai zasu yi masa ba zai tafi ba, har suka gaji suka kyale shi yake zuwa aji tare da ita, don Mama bata da lokacin kula da ita.
Inda Mama ta zama akasin Prof. Kenan, shi kam yanada lokacin yaran sa no matter what, yana jan yaran uku a jiki, daga yamma zuwa lokacin barci idan ya dawo daga cikin makaranta suma suka dawo makarantar islamiyya zai kasance tare da su.
Ita Mama zaka samu ko ta dawo aiki zata ce ta dawo da muhimmin (case) a hannunta zata yi nazari, tace su zauna a falo kada su dame ta. A haka Sarham da kannen sa biyu mata suka rayu tsakanin ‘yan bokon iyayen su. Sai ya zama cewa a girman su ma Surayya ta fi shakuwa da Kakar su, itada Sarham basa ga maciji, sai fadan sako da sakuwa, yayin da Sumayyah kuma tafi shakuwa da shiri da shi fiyeda Mama.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected