HAUWA KULU Book 1 Complete Hausa Novel

HAUWA KULU Book 1 Complete Hausa Novel

Ya iso gida wajen karfe tara na dare. Jama’ar gidan su dama ga al’adar su karfe tara na dare na yi sun baje daga falo kowa ya nufi makwancin sa. Amma Abba na nan bai tashi ba, yana nan zaune a kujerar da yake zama a falon yana jiran ganin dawowar sa, yana sauraron labaran kasa da ake yi a gidan talbijin na NTA yana kuma duba tangamemen agogon dake like a bango.
Sarham yayi sallama a babban falon mahaifin sa, inda Abba Prof. ya amsa masa, ya shigo ya zauna daga kasan kafafun Abban, ya ce “Abba sannu da gida” Abba yace “yawwa, kai kuma sannu da yawon dare, daga ina kake haka? Ka bar ‘yan kannen ka cikin damuwa, ka birkice musu wuni guda, me ke faruwa da kai yau?”
Sarham ya yi ajiyar zuciya ya ce “Abba ina kofar Na’isa, wata marainiyar yarinya na yi wa aikin ido, Abba cikin rashin sa’a zan ce ko kaddara ko tsautsayi ko gangancina ne ban sani ba, ta makance gabadaya, maimakon a samu lafiyar da ake nema”.
Muryar Sarham kamar zai fashe da kuka don damuwa, zaka iya karantar tsantsar karaya da sarewar da yake ciki a cikin sautin nasa.

Prof. Abbas Shanono, ya dubi babban dan nasa Sarham cikin kulawa, yace “haba Muhammad Sarhamu! Be a man mana! Sai kace ba likita ba? Da haka zaka cigaba da aikin likita kana karaya akan rashin nasarar aiki irin haka? Ai dama aikin likita ba a hannun ku yake ba, a hannun Allah yake, sai abinda ya hukunta ga marar lafiya.
Never blame yourself a kan duk wani unsuccessful surgery. Ka sa a ranka ka yi iya yin ka, sauran, wato samun lafiya ko akasin ta, yana hannun Ubangijin halitta”.
Maganar mahaifin nasa ta dan kwantar masa da hankali, at least shi bai ce masa bai iya ba, bai ce don shekarunsa ba masu yawa bane, bai kuma ce laifin sa bane this is soothing, a hankali Sarham ya ce.
“Abba kuma shikenan idan yaro ya makance wato ya samu nakasar ido ba zai yi karatu ba sai ‘bara?’”
Abba Prof. yace “in ji wa? Ai akwai cigaba yanzu sosai akan ilmin masu nakasar ido, akwai makarantu na musamman da gwamnati ta bude domin koyar da su kyauta (public special schools) can ya kamata iyayen ta su kai ta, har anan Kano akwai special school dominyara mau nakasa daban-daban”.
Sai Sarham ya ji tamkar Abban sa ya bashi amsar ‘assignment’ din da ya baiwa kansa, ko yace Inna ta bashi, na yaya zai yi Hauwa tayi karatu, sannan kuma Abba ya bashi mafita akan damuwar sa kan matsalar Hauwa, at least zai iya taimaka musu da wannan wato ya tsaya a kan karatun ta, nan take ya yi wani kuduri mai girma ga zuciyar sa shi kadai; na daukan nauyi da takalihun alhakin ilmin Hauwa Blyaminu na sakandire har sai ta kammala in har yana raye, in dai da gaske makafi suna iya yin karatu da rubutu su samu ilmi kamar kowa, da yardar Allah zai tsayawa Hauwa, tunda shi ya samu yayi har gashi ya tsaya da kafafun sa yana kuma da albashin sa, to zai tsaya ya ga cewa Hauwa bata tagayyara a fannin ilmin sakandire sanadin makantarta ba.
Wannan wani alkawari ne da Dr. Sarham ya yi wa kan sa a zuciyar sa, da yake fatan Allah ya bashi iko da tsawon ran cika shi.
Sai washegari wajen karin kumallon su akan dining suka hadu da Maman sa da sauran kannen sa biyu wato Sumayyah da Surayyah. Bayan ya gaida iyayen nasu shikuma kannen sun gaishe shi yadda suka saba ya ja kujerar sa ta dindindin a dining din ya zauna. Mama ta tambaye shi me ya faru da shi ne jiya?
Nan yake gaya mata labarin aikin da yayiwa Hauwa da yadda yake blaming kansa kamar yadda ya gayawa Abban sa.
Barr Mama. itama kamar Abban nasa cewa ta yi ba laifin sa bane. Ta kuma kara da cewa kada ya kara sakawa kansa damuwa irin wannan kan aikin sa in har yana son cimma nasara a gaba, don hakan zai iya sawa ya tsani ‘profession’ din nasa da ya tashi da burin sa. Surayya ta gatsine baki ta ce,
“dadi na da mutum daurawa kai damuwar wasu, damuwar da Allah bai dora masa ba, to sai me zai faru don aiki bai yi nasara ba da zaka bi ka wuni cikin damuwa har da kulle kofa da yiwa kai horon yunwa ta hanyar kin cin abinci wuni guda haka Yaya Doctor, ina dalili ina dan mafari?”
Sarham ya jefe ta da harara, Mama ta ce “ke bana son rashin kunya, wa ya saka ki a maganar mu?”
Dagagefen sa inda take zaune Sumayya ta ce cikin jimami.
“Bhaiya, kayi wa Allah ka kai ni in duba ta, haka kawai naji tausayin ta ya kama ni nima, makancewa fa totally, a hannun ka, ai da tausayi da sanya damuwa, dole ka shiga phobia dinka, dama dai a ce a hannun wani liktan ne ba kai ba bazaka damu har haka ba, Allah sarki Bhaiya na!”.
Yace “I know you always pity me Summy, and you are with me especially in such a bad situation (nasan koyaushe kina tausayamin Summy, kuma kina tare dani musammman a lokaci mara dadi). Madallah da wannan kanwa tawa. ‘Karamar su-babbarsu!”.
Haka suka karya kumallon suka tashi, masu zuwa aiki wato Sarham da iyayen su suka shiga motocin su daban daban suka wuce wajen aikin su, Surayya ta wuce cikin makaranta inda take karatu anan cikin jami’ar Bayero, tana aji daya na digiri a tsangayar ilmin lissafi (mathematics).
Sumayya na aji biyu na babbar Sakandire a makarantar Musa Iliyasu College, dake nan daura da sabuwar jami’ar Bayeron, suna fitowa ne kullum tare da Yayan ta Dr. Sarham tun bayan fara aikin sa, sai ya sauke ta sannan zai mika zuwa asibitin Murtala inda bai jima da fara aiki ba, bayan yayi aiki na dan lokaci da asibitin Abdullahi Wase da aka fi sani da asibitin Nasarawa, suka maida shi can don an fi bukatar kwararru a asibitin Murtala fiye da kowanne asibitin gwamnati a Kano.
Wannan ya faru ne jim kadan bayan dawowar sa daga kasar Saudi-Arabia da kadan, inda ya karanci fannin likitancin ido a jami’ar Sarki Abdul Azeez dake Jeddah.
**** **** ****

Bayan ya sauke Sumayyah ta daga masa hannu, ya ja motar sa zuwa asibiti. Koda ya zo ward round na wannan ranar sai idanun sa suka hango masa gadon da “Hauwa-Kulu” ta kwanta jinya. Nan da nan ya tuno su, wadanda dama da su ya kwana ya kuma tashi a ran sa.
Sai ya ji yana son sake zuwa ya duba su, ya ga lafiyar su itada Innar ta.
Haka kawai yake jin Innar Hauwa a ran sa, jinta yake kamar uwa a gare shi, sabida halin kirkin ta da dattaku, da kuma tawakkalin data nuna akan abinda ya samu ‘yar ta a hannun su.
Don haka da ya fito daga asibiti sai ya samu kansa da juya sitiyarin motar sa zuwa unguwar su Inna, da ya isa bayan Badalar kofar Na’isa kasa gane gidan yayi, da tambaya ya isa har kofar gidan su Hauwa don ya kasa ganewa da farko, kansa ma juyewa yayi ya rasa direction abode gidan yayi cikin lungu sosai, amma da yake ya rike sunan maigidan da Inna ta gaya masa kamar ta san zai bata din sai ba’a sha wahalar kai shi har kofar gidan ba.
Dr. Sarham yayi sallama a kofar gidan Mal. Bilyaminu, Inna dake duke tana share tsakar gidan ta amsa sannan ta leko, koda dau taso daukar muryar dama mai kaifi kamar an fike ta anyi sharpening fitar ta gently daga makogaron sa, bakin ta ya koma har kunne da ganin Dr. Sarham, ta dau wankan ta tsaf ta sha wankakkiyar atampa, kodayake dama ta dauki muryar sa, Inna ta bashi iznin shigowa ya sa kai ya rage dogon wuyan sa ya shigo da sallama.
Inna ta amsa cike da fara’a ta shiga lale marhabin da shi, sannan ta dauki tabarmar karauninta ta shimfida masa.
Sarham ya tsuguna har kasa ya sake gaishe da Inna, ya kuma tambayi jikin Hauwa. Inna ta ce cikin damuwa,
“ai tun bayan tafiyar ka jiya zazzabi ya rufe Kuluwa, ko tashi bata iya yi, sallah ma sai na taimaka mata take iya yi daga zaune, ta dauki damuwar duniya ta dorawa kanta a banza akan abinda Allah ya kaddara mata”. Dr. Sarham ya ce,
“ashsha! Kakata jiki bai yi dadi ba ashe, ki barta Inna, dole ne ta damu, amma a hankali damuwar zata bi jikin ta in sha Allah, bari to in koma in samo mata magani”.
Har ya mike zai saka takalmin sa sai ya dubi Hauwa dake zaune a kan tabarma daga gefe, ta jingina da filo, ga idanuwan tarr a bude kal dasu, amma shi a iya dan ilmin likitancin ido da Allah ya bashi, da abinda ya karanta, ya san wadannan idanun na Hauwa’u in ba wani babban kudurar Allah ba sun tafi kenan, wato sun tashi aiki sai ko wani ikon Allah, wanda ya fi gaban ilminsu su likitocin fidar idon.
Ya matsa gaban tabarmar ya russuna yace “sannu Kakus, ina yake miki ciwo? Don in san irin maganin da zan karbo? Ko allura kike so?” Hauwa ta bata rai sosai saboda sunan da ya kira ta da shi kamar wata tsohuwa, haka mafa a asibiti yace mata Kululu bata ce masa don me ba, yanzu kuma yace mata kuskus, ta dan fiddo manyan idanun kamar tana ganin sa irin warning look dinnan, ta yi fuska sosai ta ce masa, “sunana Hauwa’u Bilyaminu ba kuskus sunana ba, kuma ni ai bana tsoron allura inda a hannu za’a yimin, ba sai na kwaye zani ba”, Inna ta ce “an ce miki Kuskus din, ke da baki san wasa ba”. Yayi murmushi ya sake cewa.
“Kakus, idan na ce miki sunan Kakata gare ki, wadda ta haifi mahaifina zaki yarda? I mean you have my Grandma’s name, Hajiya Kulu Shanono”.
Anan kuma sai tayi shiru, don ta san ba karya yake ba, ba kuma zolaya a maganar sa ta yanzu, ta zuba masa gululun idanunta kawai kamar tana ganin sa, yace “to sunan ki daya da Kakata Hajiya Kulu (Hajiyar Gadon kaya), ni kuma Kakus nake kiran ta, idan ban kira ki Kakata ba bazan iya cewa Hauwa ba, don in ta ji na fadi sunan ta haka gatsau, ba sakayawa, sai tayi kuli-kulin kubra da ni”.
Hauwa bata san sanda ta yi dan murmushi ba, sabida yadda Sarham ya fadi kuli-kulin kuburar ya bata dariya matuka.
Ya ce daga yau ni da kaina zan saka miki sunan da ya dace da kyakkyawar diyar Inna kamar ki, kin ga daga Hauwa, har Hauwa’u, har Kulu, zuwa Kuluwa duk na tsofaffi ne Inna ta lika miki, don haka ki lamunce min daga yau in kira ki da “MAIJIDDAH!”.
Ai kuwa nan da nan Hauwa ta washe baki, fararen hakoranta suka bayyana, batun yau take so a kirata da Maijidda ba amma ba mai kiranta da hakan. Dr. Sarham ya ce, “amma bisa yarjejeniyar banni arawa kowa sunan nan, nawa ne nikadai, ni na saka miki, don haka nikadai zan kira ki da shi, ke ko wani kika ji ya kira ki da shi ki gaya masa ba nasa bane nawa ne, ban yarda ko Inna ta kwaikwayar mun ba”.
Inna tayi dariya tana cin goro ta ji Sarham ya kara burgeta, ko ba komai yau ya saka Hauwa murmushi don ta manta rabon Hauwa’u da murmushi (ear to ear) irin haka, watakila tun kafin ta fara ciwon idon yayi na apolo”.
Yadda Sarham yayi ta yi musu hira sai da zazzabin Hauwa ya sauka a take, ba tare da sun san lokacin da ya sauka ba, ko dama damuwa ce ta sanya a ranta ta hanata sukuni har ta saukar mata da zafin jiki, amma duk da haka Sarham bai kyale ta ba saida ya fita chemist din Lamco ya samo mata magunguna da first aid kala-kala ya dawo, har da gorar locozade da daurin gasassar kaza da biredi. Ga kayan shayi ya sayo musu makil, tun daga kan sukari, milo da madara har da lipton.
Lokacin da ya dawo ya tsugunna gaban Inna yana nuna mata komai kasa magana ta yi ta ce “dan nan ya da wahala haka?” Ya murmusa yace “kada ki damu Inna, na neman albarka ne”.
Inna ko ta shiga shi masa albarka kwando – kwando sannan shi da kan sa ya dau kunshin naman ya isa gaban Hauwa, ya bude ya tura mata gabanta, kamshin kazar nan wadda taji kayan kamshi na gargajiya har cikin kwakwalwar Hauwa wadda rabon ta da abinci dama tun kokon safe da ta dan kurba, don ta rasa ‘appetite’ dinta gabadaya, yace “kanwata ci nama ko zazzabi ya idasa tafiya sosai” yana ganin yadda ta hadiye miyau, mukut, a makoshin ta, amma don karfin hali da ki-fadi irin na Hauwa sai tayi fuska, ta ce ita ta koshi, sai ya ce “to in ni ne baki so in ga lomar ki, bari in tafi, Inna zan wuce gida sai an kwana biyu, kin san na zama dan ki yanzu, zuwa gidan mu sai kin gaji kin kore ni”.
Inna tace “wane mutum ya kori mai kaunar sa, likita Allah ya jikan mahaifan ka, idan suna raye kuma Allah ya kara musu lafiya da nisan kwana mai albarka”.
Wannan addu’a tafi komai dadi da ga Sarham, da sauri Dr. Sarham yake amsawa da “Amin-amin ya rabbi Inna, Abba da Mama duk suna lafiya, cikin koshin lafiya. Allah ya karawa kanwata Maijidda lafiya, da Yakanar karbar kaddarar ta”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected