HAUWA KULU Book 1 Complete Hausa Novel
“APOLO”
W
ani ciwon ido ne na yayi (eye flu) da aka yi annobar sa a wasu shekarun can baya. Wanda daukacin yara da manya dai-dai ne suka tsallake shi.
A wani wata na Junairu da muka shiga, bazan manta ba aka wayi gari da annobar cutar ciwon ido na ‘apolo’ a garin Kano, yaya aka yi yaya aka yi? Ko wane tudu wane gangare aka bi aka samo? Sai gani nima Hauwa na samo nawa rabon na apolo, daga makarantar bokonmu ta Shekara. Amma Inna ta gagara dauka sabida karfin jinin ta da shaye-shayen magungunan gargajiyanta yana bata immunity iri- iri.
Da farko Innar Hauwa bata dauki abun nawa da muhimmanci sosai ba, don haka bata damu ba, duk da idon yayi jajawur ya kuma kankance kamar gauta, abinda yasa bata damu ba shine kusan kowanne yaro ya samu rabon sa na apolo a wancan lokacin, kai har manya ma, don in yaro daya ya samo duk gidan su sai sun raba (dauka). Amma in aka kwana biyu ko uku da kan sa sai kaga yana washewa. Daga nan kuma sai labari ko ba a saka masa maganin komai ba.
Don haka babu wani mataki da Innar Hauwa ta dauka baya ga tunanin cewa in an kwana biyu idon zai washe dan kan sa, kamar yadda yake yiwa ‘ya’yan kowa.
Ciwon idon ya ritsa dani Hauwa-Kulu ina ‘yar shekaru goma sha biyu da haihuwa. Aji biyu na karamar sakandire a GGSS Shekara.
Wasa-wasa abin da ake zaton kwana biyu ko uku zai washe sai gashi ya dauki wata biyu ba abinda ya canza, sai ma idon ya koma ya cabalbale da kwantsa ba kyawun gani, ko buduwa baya yi idan gari ya waye wato na tashi daga barci, in kai mai kyankyami ne kaga idona a lokacin bazaka iya cin abinci ba, kullum kuma ciwon karuwa yake ta yi kamar ana rura shi maimakon ya ragu ko yayi sauki, na kan cewa Innata idan na yi sujjadah ji take kamar kwayan idon zata zazzago (fado kasa).
Daga baya idon ya koma tsiyayar da ruwa da hawaye ko buduwa ya daina yi sosai, yayi jawur yayi luhu-luhu gwanin ban tausayi.
Innata, wato Innar Hauwa na daga cikin mutanennan ‘yan gargajiya da a rayuwar su basu bada yarda da maganin asibiti ba, kai ita ko sunan likita ta ji an ambata sai ta yi tsaki, don haka kullum saidai ta gasa min idon da ruwan zafi da dan gishiri, ta rambade min shi da farin kwalli, in yi ta kuka don azaba, wanda hakan yasa ciwon idon kullum sai karuwa da cigaba da ta’azzara yake ta kara yi.
Watanni uku da fara ciwon, idon ya rikide ya koma min wata kebantacciyar cutar idanu da ake kira ‘hakiya’ (cataract) ta fito ta kwanta tayi babakere a tsakiyar duka idanun guda biyu.
Lokacin ne hankalin Innata ya fara tashi, ganin wadannan Hakiya cikin kwayar idona sun fara girma, kowa ya ganni sai yayi fadan don me Inna ta ki kai ni asibiti? Meyasa ta bar idon ya zama haka? Ayi ta mata fada kamar a ari baki. A kuma gaya mata “ai Innar Hauwa hakiya ba’a wasa da ita fa”.
Amma Inna tayi funfurus. Sai da ta kai na daina fita don zuwa makaranta don fadan da malamai ke yi akan a kaini asibiti amma Inna ta ki ji, sai cewa take ai tana saka min farin kwalli shine babban maganin ciwon ido, a hankali zai tsotse hakiyar gabadaya, amma ina! Abu kullum kamar ana kara iza shi. Har sai da ta kai ta kawo idanuwan nawa gabadaya sun yi fari tas, sabida yadda hakiya ta mamaye su.
Yau muna tsakar gida ina zaune bisa tabarma da littafin makaranta a hannuna, ba tun yau ba na fahimci na daina ganin abubuwa da kyau, yadda suke a zahirin kamanninsu, amma duk da haka na dage ni a dole karatu zan yi wanda ya wuce ni a makaranta, duk da idanuna dake neman zagwanyewa yau don zafi, amma me?
Ko da na bude cikin shafukan takardar sai na ga bana banbance duk wani rubutu dake cikin littafin sai hasken takardar kadai. Sai wasu taurari suna gilmawa ta gaban idona. Wannan ya tabbatar min, kodai ganina ya tafi, ko yana gab da tafiya ya barni.
Cikin tsorata da al’amarin na kwalawa Innata dake madafi tana kwashe tuwo kira, nace, “Inna ki zo, watakila fa Inna NA MAKANCE!!!
Inna na daina ganin komai a cikin littafi na komai ma bana ganewa”.
Mummunar faduwar gaban da ta samu Innar Hauwa a wannan lokacin bata taba jin irin ta a rayuwar ta ba, ko lokacin data gane batan Baban Hauwa, da sanda aka shigo mata da gawar Zulkiflu daga rafi. Watakila sabida son da take wa Hauwa ne, ko kuma don ta saka buri mai girma a kan Hauwa a ran ta???
Burin ta na Hauwa ta yi maza ta girma ta aurar da ita, burinta na HAUWA ta zamo mai zurfin ilmi a rayuwa, irin wanda basu samu damar yi ba su, itada Malam, kuma basu da wasu ‘ya’yan da zasu yi shi bayan ita, burin ta na Hauwa ta samu kwakkwaran abun yi da zai rike su a tsufanta nan bada jimawa ba, koda ta zama malamar makaranta ne. Ta kuma yi aure ta hayayyafa, ‘ya’yan ta su maye mata gurbin ‘ya’ya masu yawa da Allah bai bata ba a rayuwar ta? Ko kuwa don ita kadai ta rage mata matsayin sanyin idaniya a halin yanzu, amma ace yau idanun ta babu? Ba karamin fadar da gabanta hakan yayi ba.
Sai Inna ta bar abinda take yi, ta taso zani na kwancewa ya kusa faduwa ya barta, ta yo kan Hauwa da gudu, tana ambaton “bana son fatan tsiya HAUWA. INNALILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJIOUN”.
**** **** ****
Wannan shine labarin da Barr. Hauwa Bilyaminu ta bayar a safiyar yau a dakin taron da aka hada mata na ‘meet and greet,’ tsakanin ta da kungiyoyin da take da alaqa dasu, kungiyoyi ne da suka tsayawa rayuwarta har ta kawo wannan matsayin, da sauran masoyanta mutanen arewa wato masu nakasa iri daban daban maza da mata wanda yau yayi quenching curiousity da jita-jitar kowa cewa HAUWA BILYAMINU IS A PHYSICALLY CHALLENGED PERSON. Kuma a ranar ne Hauwa take murnar cika shekaru hamsin da haihuwa, sannan a ranar ne ta karbi jagorancin “Nigerian Bar Association”. Wanda yayi daidai da ranar ‘anniversary’ din aurenta da “HER PACE-SETTER…” shekaru dai-dai har talatin da daya.
Barr. Hauwa Bilyaminu Kofar Na’isa, ta bamu labarin asalinta da tushenta ne a wannan muhimmiyar ranar mai tarin achievements a gareta daga hakikanin bakinta, da asalin lalurar ta. Daga nan na kasa hakura da jin me ya faru da sauran rayuwar HAUWA-KULU? Ni Sumayyah Abdulkadir (Takori) na bibiyi labarin Barr. Bilyaminu bayan taron nan, zan kuma labartawa Takorites labarin HAUWA-KULU daga ranar data rasa abu mafi muhimmanci ga rayuwar bil adama har zuwa yau da take bikin murnar zagayowar cikar shekarun haihuwarta hamsin a duniya….
**** ***** *****
M
afarin makancewar Hauwa-Kulu kenan. Makanta mai sunan hakiya da akafi sani da (cataract blindness), ko a ce makanta mai lasisi, tunda kuwa Innar ta ce ta sayo mata da kudin ta.
Don da farko Inna ta dauka Hauwa wasa take yi, amma cikin kwana biyun da Hauwa ta koma lalube da tsakar rana ko da daddare ta fahimci cewa Hauwa da gaske take, tana gab da daina gani, amma dai tana ganin haske da inuwar mutum in ya tsaya a kan ta, dan ko daki sai da lalube take kai kan ta, ko Innar ta kama hannunta ta kai ta don kada ta buge goshi.
Saboda haka ne wannan karon Innar ta tsorata. Dole kanwar na ki, ta tambayi inda zata kai Hauwa aka ce mata ta kaita bangaren ido a Murtala (Murtala Mohammed Specialists Hospital), washe gari tasa ta a gaba sai asibitin Murtala.
Da tambaya suka isa bangaren ido, a kafa suka tako suka taho tun daga kofar Na’isa har zuwa bakin asibitin Murtala. Kusan wannan shine karon Inna na uku da zuwa asibiti a rayuwar ta, sauran biyun duk dubiya ta zo, don ita ba mai yawan ciwuwwuka bace sabida yadda ta tsaya da shan magungunan gargajiya da jike-jiken saiwoyi akai-akai bata yarda tayi wasa da su, don ko haihuwar Hauwa data marigayin Yayan ta bata yarda an kaita asibiti ba, don haka hatta yanda ake karbar kati basu sani ba, saida taimakon wata mata da itama ta kawo ‘yar ta ganin likita, suka samu suka karbi kati suka hau dogon layin ganin likitan ido. Don kuwa a makare suka iso.
Suka kuma gamu da dogon layi don ranar ganin likitan ido ce wato Alhamis.
Sune kusan na karshe a kan layin, suka zauna a kan bencin da aka tanadar wa marassa lafiya masu bin layin ganin likita bayan sun mika katin su, ma’aikatan jinya da yake akwai marassa kirki cikin su, idan suka juya suka kalli idanun Hauwa sai suyi tsaki, su hau maganganu na gugar zana cikin zagin jahilcin mutanen kauye wajen sakaci da zuwa asibiti, sai ciwo ya ci ya cinye a kwaso jiki hajaran majaran wai an zo asibiti, sun dauka daga kauye suke don sun fi musu kama da kauyawa.
Inna na jin su, ta yi shiru ta sadda kai, bata tanka musu ba.
Wata metron zaqaqura a cikin su, ta kasa gugar zanar ma, sai da ta fito fili ta dubi tsakiyar idon Inna ta ce.
“To yanzu saboda Allah baiwar Allah me likita zai iya muku a wadannan matattun-rubabbun idanun da hakiya ta riga ta cinye?
Allah wadaran bakauyen mutum wajen wasa da lafiyar sa!”.
Da sauri Inna ta dago ta dube ta, kafin ta rufe baki dayar ta amshe.
“Taya ni gani, tun dazu nake kus-kus din hakan a raina kika riga ni furtawa, saboda Allah dubi yarinyar nan sai da Hakiya ta gama cinye idon tas, sannan zasu wani dauko kafa budu-budu dasu su zo asibiti, yo wannan ai ta gama makancewa da lasisi, ko me likita zai iya musu a wannan lokacin ina ce aikin banza ne?”.
Inna dai na jin su, amma bata tankawa, duk da ta yarda basu da mutunci kuma basu girmama furfura, amma ita da kanta ta yarda har da sakacin ta wajen lalacewar idon Hauwa-Kulu.
Ta sunkuyar da kai kasa sosai, hawaye fal idon ta, amma bata bar su sun zubo ba. Ta dago ta dube su, su duka basu fi a kira su ‘ya’yan cikin ta ba amma suke mata wannan tanadin. Kodayake kowa ya san yadda ma’aikatan jinya na gwamnati suke, daidaiku ne masu jin kai da kirki ga marar lafiya, musamman ga mutanen kauye da talakawan da suka raina wa ajawali kamar yadda suka raina Inna din, don sun ganta da kodaddiyar atamfa mai barewa, kuma tayi abunda a wurin su jahilci ne da gidadanci.
Sanin halin malaman asibiti da sau tari ake bata labari tuntuni, yau da suka gwada mata sai bata yi mamaki ba kuma bata ji zafi sosai ba, shiyasa ta daure taki damuwa da su, fatan ta kawai su mika katin su ko sa samu ganin likita.
In ya so shima ko me zai ce mata yace mata a shirye take da daukan laifin ta. Fada ne dai ta san zata sha shi har a wurin likitan shima, to in dai a karshe zai baiwa Hauwa magani, ganin ta ya gyaru, ta rabu da wannan hakiya, to babu komai, shima zata jure nasa.
Ba abinda malaman jinya basu ce mata ba na raini da wulakanci, da suka tambaye ta ko tun yaushe Hauwa ta fara hakiya? Ta ce an fi wata uku, suka ce to tun yaushe suke ganin likita? Nan kuma ta sunkuyar da kai ta ce basu taba zuwa ba sai yau.
Sai wata ma’aikaciyar jinyar mara kunyar gaske tayi kamar ta doke ta, yadda ta rufe Innar da fada duk da ta girme ta, ta ce to ba zata mika katin nata ga likita ba, su tattara su tashi su tafi, in yaso su je su karata da farin kwallin da take rambada mata kamar idanun kwatami.
Inna ta kauda kai ta rabu da su. Amma bata yarda ta tafi ba, duk da sun kore ta. sun kuma tabbatar mata bazasu mika katin nata ba. Sai suka rabu da ita suka koma hirar da ta shafe su, suka manta da su a wurin. Lokaci lokaci suna kiran sunan marasa lafiya suna shiga ofishin likita amma basu kara bi ta kan su Hauwa ba, don a wurin su sun gama da babin su.
Hirarrakin da suke yi duk a kan matashin likitan su ne, wanda aka kawo musu ya maye gurbin kwararren tsohon likitan ido wato Dr. Barde Abba, wanda shi kowa ya san kwararre ne. Inna na ganin hirar tasu a matsayin cin naman abokin aikin su.
Don a cikin hirar tasu ta ji suna fadin.
“Ai tsautsayi ne kadai zai sa mutum ya fada hannun sa, da sunan wai yayi masa aikin fidar ido, yayi yarinta kwarai da gaske da zama likitan ido, a ganin su ba’a taba yin yaron likita a tsangayar ido mai kananan shekaru, kuma mai jarumtar hali da karfin hali kamar sa ba, a dai tarihin asibitin Murtala bakidaya da suka jima da sani, don sun dade suna aiki anan.
Dayar tace ai hatta sauran likitocin duka asibitocin da ke cikin kwaryar birnin Kano a yanzu, bata jin akwai karamin yaro kamar wannan da kwalin likitanci, bama na MBBS kadai ba, wai har consultancy ya gama, wanda bai wuce ace masa saurayi dan tashen balaga ba, watakila dai zuqen karatu aka yi tayi masa, saboda yana da uwa a gindin murhu, tunda Baban sa wato mahaifin sa Farfesa ne (Prof.) na tsangayar likitancin ido, a jami’ar koyarwa ta Abdullahi Bayero.
Gulma tayi dadi sosai a tsakanin su. Daya daga cikin su kuma ta ce,
“a’ah fah, ku daina Magana akan abinda baku da tabbas, ai an ce ba’a jami’ar Bayero yayi karatun likitancin nasa ba, a can Jeddah ne, ta kasar Saudi-Arabia.
Wato alumnae ne na Jami’ar Sarki Abdulaziz. Can kuma kun san ba’a dadewa ana karatun likitanci kamar yadda ake dadewa a nan Kano da sauran garuruwan Arewacin Najeriya, idan muka auna a hankali, a bisa ma’auni na adalci, zamu ga cewa in har ya bar sakandire a shekaru goma sha shidda, ya shiga jami’a a shekarar da ya bar sakandire zai iya yin MBBS na tsahon shekaru biyar acan, ya kuma dora da consultancy shima na shekaru biyar zuwa shidda, zaku ga cewa babu zuke cikin ilmin sa har kuwa da hidimar kasa”, inji mai dan hankalin cikin su.
Ta kare zancen ta da cewa.
“Don haka ba abun mamaki bane don ya zama likitan fidar ido a shekaru ashirin da bakwai zuwa da takwas da haihuwa, in dai har da gaske ya fara karatun da wuri, ya kuma gama karatun sakandire a shekaru akalla 16-17, kuma dai yana da gatan sa a fannin karatun nan kowa ya sani”.
“Sai shegen iyayi da uban tsayi kamar karan raken takanda, dan sirit da shi kamar ka bushe shi ya fadi amma sai iyayi, ga dan banzan manyance kamar gyambo a kafa.
Karambanin irin su ya wuce shekarun su, don ko ni nan na tabbata na girme mishi wallahi”.
In ji wadda ta fi sauran rashin ta ido wai ita Nos Saratu. Duk suka sa dariyar maganar tata, Nos Maria har da kyalkyalawa da sukuyawa da rike ciki, irin ta wadanda dariyar gulma tayiwa dadi.