HAUWA KULU Book 1 Complete Hausa Novel
Wadannan kalaman nasa su suka zamewa Hauwa-Kulu “a food for thought”, har bayan tafiyar Dr. Sarham daga rayuwar su, bata bar mayar dasu madubin ta na rayuwa ba, fitilar dake haska mata duhun ko’ina dake cikin nakasar ta, sannan jagoran ta a duk lokacin da ta rasa dan jagora, wato kalaman sa ta saka a gaba suke saita mata hanya a duk inda ta nufa, don cimma rayuwa mai amfani a cikin halin data ke ciki na nakasar idanu.
Watanni masu dama suka biyo baya suna cikin kewar sa mai yawa itada Inna. Cikin tuno ‘precious moments’ din su tare dashi. Ko na rana guda sun kasa mantawa da shi.
Sun kasa mantawa da tarin gudunmuwarsa ga rayuwar su, da lokutan da suka kasance tare da shi cikin yanayi na zumunci da ‘yan uwantaka. Zaman sa na dan lokaci cikin rayuwar su ya dauke musu kewar Baban ta watau Malam Bilyaminu kaso 50% data dan uwanta mai rasuwa wato Zulkifl, duk da a sanda yake zuwa wajen su din bata wani damu da shi ba, sai ma kullata data biyo baya, duk da ‘repentance’ dinsa gare su akan laifin da ba lallai a kira shi nashi ba, amma bayan tafiyar sa, da irin emotional sallamar da suka yi mai zaunawa a rai, hakan yasa ta yin kewar sa bad an kadan ba.
Guzurin kudi da ya bar musu har naira dubu daya sun dade suna cin moriyar su, kafin bayan wasu watanni masu yawa su kare, duk da haka Inna bata bar sana’ar ta ba ta sayar da wake da shinkafa da juyen dabbobi a kasuwa duk shekarar sallahr layya.
A lokacin Hauwa ta shiga babbar sakandire aji biyu, watarana ta dawo daga makaranta tare da Salele kafin su hawo motar bus da zata kawo su kofar Na’isa Salele ya hango ana hawan kilisa a kan dawakai a tsallaken titi. Saleleh mayen dokuna ne na gani kashe ni, yana matukar son wasan Polo da hawan angonci ko hawan sallah na sallah da sarki ke yi a Kano, tuni suka kwashe hankalin sa daga kan Hauwa, ya bata jakar makarantar ta ya ja sandar da suke kamawa shida ita a matsayin jagora tsakanin su, don ba hannun ta yake rikewa ba duk da ta girme shi, yace.
“Hauwa, zauna kan bencin can ki dan jira ni in ga wucewar masu kilisar can akan dokuna” Hauwa tace “toh, amma don Allah kayi sauri Salele, ka san yanzu Inna tana duban hanyar mu, kada ta ga mun dade ta damu”.
Salele tunda ya nausa cikin ‘yan kallo ya bace mata bat! Shiru shiru Hauwa na jiran Salele bai dawo ba, karambani irin nata yasa taga cewa bari dai kawai tarabu da shi yau tayi kokarin kai kanta gida kada hankalin Inna ya tashi. “Dr. Sarham” yace ba ido ke gani ba hankali ne ido gululu ne kawai.
Sai ta tashi da zummar ta tsallaka titi ta tari motar kofar Na’isa, don daga yadda take jin karar motoci ta san a bakin titi suke, tana tafiya a hankali abunta kanta a kasa ba tare da ta san ina take saka kafa ba ai dai mutum ya gane da kansa bata gani shi ya kauce mata.
Ai kuwa bata jima tana tafiyar ba taji ‘horn’ din mota a tsakar kanta, wanda ya kidimata ta diririce ta kwasa da gudu, motar kuwa bata yi kasa a gwiwa ba wajen kwasheta, ta yi sama da ita sannan ta nana ta da kasa.
Salele dake tsallakowa titi akan idon sa mota ta kwashe Hauwa. Ya dora hannu a ka ya rafsa ihu yayi kanta a tsakiyar titin yana fadin “na shiga uku, Hauwa ban ce ki jira ni ba? Hauwa!!!”
Mai motar ya gangara gefen titi ya tsaya, ko kafin ya fito daga motar jama’a sun taru a kan Hauwa ana salati. Da yake na kirki ne sai bai gudu ba, ya taimaka aka saka Hauwa a motarsa, tareda wani dattijo da Salele da ya ce ai Yayar sa ce, suka nufi asibiti da ita jini nata disa a motar, amma mai motar nan bai damu ba ta ran Hauwa yake, yana rokon Allah yasa abun ya zo da sauki kada diyya ta hau kansa.
Hauwa bata san inda kanta yake ba har suka shiga babban asibiti.
Asibitin Malam suka kai Hauwa, a ka karbe ta a imajensi likitoci uku suka rufu akan ta suna kokarin ceto ranta. Sai bayan an samu an yi treating raunukan da ta ji, an kuma daure karayar da ta samu a hannu sannan aka basu daki kwanciya. Wanda ya kade ta duk shi ya biya komai, kuma ya tsaya har aka kai su dakin kwanciya din na mata inda aka basu gado.
A lokacin ne ma ya samu damar da ya kalli Hauwa tana barci, duk da ta kara girma sosai, ta zama budurwa sai yaga kamar ya santa. Ya tambayi Salele gidan su, don aje azo da iyayen ta, Salele ya ce zai je shi kadai ya zo da Innar ta.
Don haka saurayin ya ja kujera gaban gadon Hauwa ya zauna bayan fitar Salele, ya dau wata jarida a kan lokar gadon ta asibitin yana dubawa yana satar kallon Hauwa yana fadi a ransa yau tsautsayi ne ya fito da shi daga wajen aikinsa ba tare da lokacin tashin sa yayi ba, tsautsayi da baya wuce ranar sa, banda haka shi baya wani fita cin abinci har cikin bankin a ke kai musu su biya, daga yaje ya ci abincin rana a restaurant ya koma office zuwa lokacin tashi tsautsayin nan ya ritsa da shi?
Ya sake kai duban sa ga Hauwa a karo na sau ba adadi, sosai take masa kama da wata fuska da ya jima da sani, amma ya kasa tuna inda ya san fuskar ba.
Har saida Inna tayi sallama a gigice ta fado dakin asibitin kamar an turo ta, Salele ya biyo ta a baya da buta da bokiti da tabarma da bargo, nan ne mutumin ya gane ta sarai. A tsorace ya mike tsaye, ita kuwa Inna bata ma lura da shi ba kan Hauwa tayi tana salati tana godewa Ubangiji.
Bayan ta dan nutsu ne Jamilu ya matsa gaban ta ya tsugunna, ya sadda kan sa kasa cikin kaduwa da mamaki da tsoron kada Inna tace da gayya ya kade Hauwa, yace “Inna Safiya kiyi hakuri, ni na kade ta ban sani ba, ashe Hauwa-Kulu ce ma, kanwata.
Wallahi ina cikin tafiya kawai na ganta a gabana a tsakiyar titi, nayi kokari in kauce ta sake dawowa daya barin da ba yadda zan iya kauce mata”.
Inna ta kai duban ta ga saurayin, nan da nan ta gane shi duk da girma da cika idon da yayi, Jamilu ne dan wajen Zakari, Inna ta ce.
“Jamilu dan wajen Rumanatu?” Yace “ni ne Inna” Inna tayi kwafa ta ce “to babu komai, kana iya tafiya, mun gode”.
Jamilu ya ji babu dadi a ransa, yace “Inna Safiya wallahi tsautsayi ne, ba inda zani sai taji sauki, zan kasance tare da ku har Allah ya bata lafiya”.
Inna bata sake komawa ta kansa ba, ta maida hankali kan gyarawa Hauwa kwanciya, har ya karaci durkuson sa ya tashi, ya tafi cikin damuwa.
Bayan fitarsa Inna ta tambayi Salele yadda aka yi ma ya rabu da Hauwa har ta hau titi bisa ita kadai, cikin kokarin boye bacin ran ta, Salele duk rashin gaskiya ya bayyana a fuskar sa ya ce “Inna daga nace ta tsaya in je ni tsallake in dawo” Inna tace “ka dai fadi gaskiya, kai dai wallahi a kan kalle-kalle ko bakauye nan ya ganka ya barka. Allah ya kiyaye gaba”. Can kuma tace. “Oh ni Safiya, Hauwa-Kulu harda karaya?” Idon ta ya kawo ruwa, tasa habar zaninta ta share tana sake gyarawa Hauwa kwanciya, an sakale hannun da aka gyara a jikin karfen gadon.
Ba jimawa da fitarsa Jamilu ya sake dawowa niki-niki da ledoji a hannayensa, yayi sallama akan su, dakin irin dogon dakin nan ne na kwantar da marasa lafiya mata zallah, suna daga gadon tsakiya da wasu a gefeda gefen su, Inna ta juya ta dube shi ta amsa sallamar sa, fuska kadaran-kadahan ta ce “wani abu ka manta ne kuma?” Ya ce “a’ah Inna, ai na dinga zuwa kenan har sai an sallame ku, in sha Allah”. Ya ajiye mata ledojin da ya shigo dasu a gaban ta cikin matsanancin ladabi, sai Inna ta rasa me zata ce, yaushe ‘ya’yan Zakari suke da hankali balle su yi halin da yake yi a gabanta yanzu?
Koda yake ko dama can shi daban yake a cikin su ta san wannan, saboda uwarsa ta masa tarbiyya daidai gwargwado, bayan Zakari ya saketa da shi ta tafi tayi aure a wani gidan, ba laifi yana gaida mutane duk inda ya gan su ba kamar kannen sa ba da sau dubu zasu wuce ta ko kallo bata ishe su ba. In zata iya tunawa rabon ta da Zakari da wani da ya shafe shi tun batan Malam Bilyaminu, shekaru hudu baya da ta je neman sa yayi mata korar kare. Wani cikin su shi ko ‘ya’yan sa bai kara neman su ba, yau kuma sai ga Jamilu ya kade Hauwa.
Inna ta nisa, ta kasa ce masa ya kwashe tsiyar sa, don sosai taga damuwa a tare da shi na irin karbar da take masa. Haka suka zauna shi da ita zugum-zugum, ba mai iya ce da kowa uffan, daga baya yayi mata sallama ya tafi. Yace sai gobe in sha Allah kafin ya tafi wajen aiki zai leko ya ga jikin Kulun.
Inna tayi masa godiya, amma sai ta ce “don Allah ba sai ka dawo ba Jamilu, taimakon da kayi mata ma an gode sosai, madallah. Allah yayi albarka”.
Jamilu bai ce komai ba ya juya ya fita don ya san tabbas Inna ta kullace su duka ahalin gidansu daga su har mahaifin su, don ma dai tana da kai zuciya nesa.
To bayan fitar sa kuma ta samu kanta da bude ledojin da ya aje musu, ta farko kayan shayi ne a ciki, da katon biredi (Laziz) sabon gashi, sai kayan marmari shake a daya ledar harda Tuffa da Inabi, daya ledar kuma gasashshen naman rago ne mai zafi sosai a ciki.
A lokacin Hauwa ta farka tun bayan kawo ta asibitin da kyar ta iya ta dan motsa, sai ta ji ta kamar a daddaure, ko’ina na jikin ta ciwo, bata san me ya faru da ita ba, ta kai hannun ta da ba’a daure ba kan goshin ta tace “wash!” “Inna tace “sannu Kulu kin ji, tsautsayi ne da baya wuce ranar sa, mota ta buge ki, Allah dai ya dada kiyaye gaba”.
Nosis suka zo suka bata magungunan ta, suka ce a bata shayi mai zafi ta sha, kuma zata iya cin wani abu, Inna tace basu zo da ruwan zafi ba, sai suka bata aron karamar heater ta jona ta hada mata shayi mai kauri da kayan shayin da Jamilu ya kawo.
Ta taimaka mata ta zauna a jikin filo tana bata shayin a baki har ta koshi, ta debo naman da zafin sa a faranti irin gasashshen naman nan ne na babbar tukuba mai ruwa-ruwa wanda da kasa a bakin ka ka tauna zaka ji ya baje tsabar laushin sa, wanda yaji yajin citta, Hauwa duk da jikin ta na ciwo taji dadin cin naman nan, don baza ta iya tuna yaushe rabon ta da cin nama ba, tun zamanin Likita Sarham na zuwa gidan su! Balle mai dadi da laushi irin wannnan ai sai zamanin Dr. Sarham.
Daga nan ta koma barci har dare bata tashi ba, Inna ta sallami Salele ya tafi gida bayan ta masa sautun abubuwan bukata da zai zo musu da su washegari har da filas din ruwan zafin su da hita.
Washegari ‘yan dubiya fululu daga kofar Na’isa, Salele ya barabada musu mota ta kade Hauwar Inna. Hauwar Inna mai jama’a kowa na son ta, koda makanta ta same ta jama’ar unguwar su kowa kokari yake ya kyautata musu, musamman da aka san mahaifin ta ya bata, kuma Innar ta bata da matallafi sai Allah.
Makwabta na ta tururuwar zuwa duba Hauwa kullum, koda Inna ta aika Salele don ya fada a makarantar su Hauwa kada aga bata zuwa, sai ga Malaman su Hauwa sun yo kungiya a motar makarantar su a washegari daga ‘special school Kano’, suka zo suka duba ta da kayan dubiya niki-niki, kasan yaro mai kokari da shiga ran malamai. Don haka a wannan jinya su Hauwa sun samu alheri sosai, don Jamilu ma kullum yana tafe, abin arzikin da zai kawo na yau daban na gobe daban.
Tun Inna na daure masa fuska tana korar sa a wayance, har ta fara gane Jamilu neman shiri yake yi sosai dasu, rannan ya kawo dafaffen abinci yace mata inji Hajiyar sa, da yake bata gidan mahaifin sa ita kuma tare suka yi ‘yanmatanci da Inna, kusan lokaci daya Bilyaminu da Zakari suka aure su.
Ta manta rabon ta da Rumanatu don tun Jamilu na yaro Zakari ya aunata gaba.
Daga baya ma ya dauko Innar tasa ya kawo dubiya, nan suka baje ita da Inna a kan tabarma ana labarin yaushe gamo da tuna baya. A bakin Hajiya Rumanatu Inna ta ji cewa Jamilu yayi karatun shi mai zurfi har digiri a hannun ita mahaifiyar shi a boye, ba tareda Baabnsa ya san yana yi ba, tace yanzu haka Jamilu aikin Banki yake da bankin Afrika (United Bank of Africa) da akafi sani da UBA. Kuma da wannan aikin har yana taimakawa kannensa sosai da suke garari da gararramba a gari, matan yawanci an sako su suna gidan uban suna zawarci, tace ‘ya’yan Zakari mata basa jimawa a gidan miji zaki ji an sako su, uban duk kudin da ya tara baya iya saya musu ko gasarar koko, sai dai ya je tukubar mai shayi a lafta masa kwai da shayi mai kauri, ta ce ai ita kam Allah ya cece ta da ya raba ta da gidan su Jamilu.
Ta shiga lissafo wa Inna yawan matan da Zakari ya aura bayan ita yana shika musamman bayan yayi kudi abun babu ko dadin ji.
Tace bayan rabuwar ta da Zakari ta yi aure ta haifi wasu ya’yan mata guda biyu Hansatu da Lami, duk ta aurar dasu. Shekarar baya Allah ya yiwa mijin ta rasuwa wanda ya rike mata Jamilu kaamr shi ya haife shi.
Har yamma kafin Jamilu ya zo daukar Hajiyar sa, suna tafe a hanya Hajiyarsa na bashi labarin irin mutuncin Inna Safiya tun suna ‘yammata. Jamilu ya sosa kai, da damuwa yace.
“Hajiyata ina da magana, tuntuni, amma ina shakka, kin ga ba don halin Baban mu ba da illar da ya yiwa mutuncin mu gun Inna Safiya ba, me zai hana na auri Hauwa? Da ba sai kawai a yi ‘yar gida ba ni da Hauwa’u? Rai kwance hankali kwance?”
Hajiya Rumana ta ce cikin mamaki “wai kana nufin kana son Hauwa din ne?” Jamilu ya koma sosa keya da hannun sa daya yace “gaskiyar maganar kenan, Hajiyarmu tun ranar da na buge ta, nake fama da zuciyata a kanta, zuciyata bata kara zama lafiya ba a kan tunanin yadda zan yi na mallake ta, kullum tunani na shine yadda al’amarin zai yiwu cikin sauki, amma na hanga na duba ta bangaren Babanmu na tabbatar zan samu matsala sosai da shi.
Jiya na je gaishe shi, na same shi na gaya masa tsautsayin da ya gifta na kade Hauwa, cewa yayi tun da na kaita asibiti na biya magani kada ya kara jin na koma inda suke”.
Haj. Rumanatu ta ce “umh, ni na rasa irin wannnan ‘yan ubanci da yake yi wa dan uwan sa, shikadai ya rage masa amma ya kasa kaunarsa, wallahi shi bai dauke shi haka ba Bilyaminun, baka ga irin cin kashin da yake masa ba, haka yake masa tun suna yara saboda bakin cikin ya fi shi samu a sana’ar sa ta gwanjo.
Kaima dai Yayan Hansatu banda kana son taro aradu da ka, ba zaka kaiwa mahaifin ka wannan maganar ba”.
Jamilu ya ce (with boldness) “idan har Hauwa ta amince min in sha Allahu zan yi nasara a kansa. Hakan ne kadai zai gyara wannangurbataccen zumuncin ya rage kiyayyar idan mun haihu nida Hauwa”. Ta ce “to idon ta fa? Zaka iya zama da makauniya Jamilu?
Ba wai ina kin Hauwa bane saboda lalurar ta, tunda kuwa ‘yar uwar kace jininka ce, amma akwai abun dubawa.
Tarbiyyar ‘ya’ya, dawainiyar cikin gida, abubuwa ne da sai mai ido zai iya yin su. Da aikin banki zaka ji, ko da kula da nakasassar mata a cikin gida musamman in ta fara haihuwa? Kaida in ka fita tun sassafe wani zubin sai dare kake tasowa?
Don kuwa Hauwa, kasa a ranka in ka aure ta duk kai zaka yi mata wadannan abubuwan dana fada a can baya tana daga zaune tana fama da kanta”.
Jamilu ya nisa cikin jin karin kauna da soyayya da tausayin Hauwa, sannan ya ce “Hajiyata, a irin son da na samu raina yana yi mata, sam ban hango wadannan kalubalen ba, amma ni Jamil Zakari naji na gani, na yarda in har zan samu auren Hauwa, zan hadasu duka ita da ‘ya’yanta in raine su in kula dasu har aikin bankin duka bazan kasa ko daya ba”. Hajiya Rumanatu tausayi ya cika ta, ta dade da sanin dan ta Jamilu mutum ne har mutum, mai kyakkyawar zuciya akasin ta mahaifinsa, ta dade tana dakacen dama ace Bilyaminu ne ya haife shi, saboda halinsa na yawan kirki da nagarta shiyasa ma mahaifin sa sam bai cika shiri da shi ba don komai nasu Allah daya ne gari banban.
Sai ta ce “Allah ya tabbatar da alkhari a tsakanin ku idan akwai, ya huwwace maka lamunin mahaifin ka cikin sauki. Auren Hauwa hakika Jihadi ne babba zaka yi, na gyaran zumunci da kuma na taimakon miskinin da baida maraba da maraya”.
**** **** ****