HAUWA KULU Book 1 Complete Hausa Novel
KANAWAN DABO
A
l’ummar Kano su akewa kirari da laqabi da KANAWAN DABO. Ni Hauwa-Kulu ina alfahari da kasancewata (‘yar asalin cikin BADALAr Kano), don haka ne na dauko muku labari na tun daga tushe, wato na fara da baku shimfidar labarina daga inda na taso, kuma inda aka haifeni, wato cikin kwaryar BADALA.
Garin Kano gari ne da ake ma kirari da “Ta-Dabo Tumbin Giwa (Yaro ko da me ka zo an fi ka)”.
Mun samo wannan lakabin ne daga masarautar Kano (Dabon Kano) ta Sarki Abdullahi Bayero, Kano garin Sarki Ado, Kano mai Mata mai Mota, mai Ganuwoyi da Badaloli da wasu irin kofofi wuri-wuri lungu-lungu na tarihi, suna nan birjik bila adadin zagaye damu.
A takaice tarihin birnin Kano tarihi ne mai dogon zango kuma mai zaman kansa, wanda in aka ce za’a bada shi saidai a dauko shi tun daga tushe, wato tun daga lokacin zuwan Habe, har zuwa shigowar Turawan mulkin mallaka, da rayuwar Mai-Tatsine a Kano, data sarakunan Kano da suka gabata.
Don haka ba zai takaitu a shafi guda na gabatarwar/shimfidar littafi ba, sai dai ‘I can boldly say; Kano ta zarta kowacce jiha a arewa kyakkyawan tarihi na sarauta, da ilmin addini dana boko da rike kasuwanci da muhimmanci.
Abinda kowa ya sani ne Ba-kanon mutum bai yarda da zaman banza ko zaman kashe wando ba. Haka kuma bai yarda da zama cikin jahilci ba komai yawan shekarunsa; wato dai Gemu baya hana Ba-Kano neman ilmi.
Saboda zaka ga daga yara har manya a Kano kowa dalibi ne, matan aure ma a wancan zamanin duka da suna dakin miji dalibai ne a gidan auren su, da zarar an yi sallahr isha, zaka ga suna firfitowa daga gidajen su cikin lullubi da shigar mutunci don tafiya makarantar dare ta matan aure, haka da safe akwai masu halartar makarantun manya (adult education schools) irin su Gidan Galadima, ko makarantar Gidan Makama, don haka akasari a Kano maza da mata bakidaya kusan kowa yana da abin yinsa daga neman ilmi zuwa sana’ar da ta karbe shi, ko kuma wadda ya gada daga iyayensa.
Zauna gari banza ga Bakanon mutum mace ko namiji sai mu ce sai dai abinda baza’a rasa ba, don hatta ma’aikatan gwamnati baka raba su da kodago a kasuwar kantin Kwari, ko Bata (Sabon gari), ko kofar Wambai, kasuwar Singa, ko kasuwar Kurmi, manyan kasuwannin birnin Kano kenan.
Mafi yawan jama’ar Kanon kuma da kasuwancin kacokam suka dogara, basu damu da aikin gwamnati ba, koda sun dan yi karatun zamani kuwa, balle wadanda basu samu yin mai zurfi ba, kamar mahaifina, wanda akafi sani da suna “Malam Bilyaminu dan Kofar Na’isa”.
Sana’ar Babana Malam Bilyaminu itace sayar da kayan yara na gwanjo a kasuwar kofar Wambai. Da wannan sana’a muke rayuwa kuma da ita ya dogara, sannan kuma ta rufa masa asiri ya rike iyalin sa daidai gwargwado da kulawa irin ta Bakanon mutum, mai zucciyar kula da iyali, wato Mallam mutum ne har mutum wanda ya san ciwon iyalinsa.
Malam Bilyamin ya taba yin sakandire ya kuma yi aikin masinja a wata ma’aikata daga baya ya bari ya kama kasuwar gwanjo sadidan.
Duk wanda ya san Malam Bilyaminu, (kafin a neme shi a rasa rana daya), ya san cewa mutum ne da ya dogara da sana’ar sa ta gwanjo, ya kuma bata muhimmanci sosai, sannan kuma shi din mai kula da iyali ne fiyeda kima da duk abinda Allah ya hore masa a lokacin da yake tare damu, bai yarda ya tara komai ba, in dai iyalin sa bazasu nemi komai su rasa ba.
Kafin ni Hauwa, Innarmu Safiya da Babanmu Malam Bilyaminu sun haifi Yayana Zulkifilu, wanda ya jima da rasuwa tun yana saurayi dan shekaru sha biyar da haihuwa, ya rasu ne a sanadin wankan cikin rafi (wankan kogi) na samari irinsa marassa ji da fitina, sai ni kanwar sa Hauwa’u, Hauwa – Kulu, ko kuma ace “Kuluwa” duk babu wanda bana amsawa sai Kuluwa.
Mahaifiyar mu wato Inna ita kadai take kirana “Hauwa” ko ta ce “Kulu”. In kuma ta bushi iska ko in ta so ganin zumburo bakina, sai ta ce “Kuluwa” din.
Malam Bilyaminu Ya kasance mutum mai kyakkyawar mu’amala da makwabta da abokan sana’arsa a kasuwa, kai dama duk wadanda suka zauna tare da shi a unguwar Kofar Na’isa da Wambai sun yi masa kyakkyawar shaida.
Shiyasa al’amarin bacewarsa rana daya ya girgiza duk wanda ya san shi.
Ni kadai ce ‘yar sa a raye a duniya yanzu, a ‘ya’yan da ya Haifa wajen guda biyar, wasu sun mutu a ciki, wato wasu an haifesu stillbirth, daga kaina kuma ni Hauwa-Kulu, ko batan wata Innata bata sake yi ba, ni nasan Inna tana matukar so na, watakila don ni kenan guda da Allah ya bar mata.
Tun daga wata fitar Babana kasuwa bai dawo gida ba, babu inda Inna bata je neman sa ba, haka ba inda bata turani ba data san yana zuwa. Har gidan kanin sa Zakari ta je neman sa, duk da ta san ba wajen zuwan sa bane, masu iya magana suka ce “in abinka ya bata, duba har inda baka tsammanin shigar sa”.
Wannan ne dalilin ta na zuwa Dan agundi gidan Baba Zakari cigiyar mijin ta Malam Bilyaminu.
Baba Zakari da ya fito sai ya gyara tsayuwar sa a kofar gidan sa yana gyatsa, sannan ya dubi Innar Hauwa da wani kallo a tsiyace, irin na kashi wannan ya fi ku daraja a ido na, yace cikin gatse,
“Halan kin yi batan kai ne? To yana inda kika bani ajiyar sa a kuryar daki na ko, in banda neman jidali yaushe rabo na da matsiyacin mijin ki da bai san hakkin zumunci ba, yo banda neman magana irin naku na mata me zai zo yayi min? Ko ya gaya miki akwai wata sauran kadara tsakanina da shi ne bayan ta ‘yan ubancin da ke tsakaninmu?”
Don haka sawun ta a likkafa ta bar kofar gidan Zakari. Bayan ya caccaba mata bakaken maganganun da gobe koda sadaka aka hadata bazata yarda ta sake tako kafafun ta kofar gidan sa ba.
Tun ana maganar batan nasa kadan-kadan, har Innar Hauwa ta tabbatar mijin ta wani abu mara dadi da bazata ce ko meye ba watakila ya same shi, ko daga irin muggan mafarkan data ke yi a kan sa, ko dai ya bata, ko ya mutu a wani wuri inda ba’a san shi ba, don bai taba kwana a wani waje tun sanin ta da shi da ba a gidan sa cikin iyalin sa ba.
Batan mahaifina ya faru ne tun ina ‘yar shekaru goma, wannan al’amari ya sanya mu cikin wani hali na damuwa da dimuwa mai tsanani, wanda ya kusa haukata Innar Hauwa, kasancewar mahaifiyata wato Innar Hauwa, irin matan nan ne da miji ya gatanta ta hanyar dauke musu nauyin komai na rayuwar yau da gobe, don haka bata sana’ar komai sai kiwon dabbobin ta, duk abinda zasu ci shi yake kawowa, hatta omon wanki da sabulun wanka Malam Bilyaminu ya daukewa iyalin sa.
Don haka batan sa ran daya ya daga hankalin ta dana duk wani mai kaunar mu kamar Malam Isa, kada tilon ‘yar sa wato ni Hauwa in ji labari, domin na saba da shi kusan har fiye da yadda na saba da Inna don shi kam Baba ba kwaba ne ba hantara ba kamar Innata ba.
Daga baya da watanni suka mika ba’a gan shi ba, kuma babu labarin sa, sai aka tattaro duka kayan sayarwarsa na gwanjo da ke rumfar da yake ajiyewa a kasuwa aka kawo mana gida.
Daga wannan lokacin rayuwa ta sauya mana nida Innata, takalihun rayuwata ni Hauwa ya koma kan Innata kacokam, kasancewar bamu da tabbacin Malam na raye ko mutuwa yayi ya fi komai daga mana hankula, sannan a wancan lokacin ba’a satar mutane balle a yi tunanin ko an yi garkuwa da shi ne mu jira kira.
Daga baya daga ni har Innar Hauwa muka ga babu mafita banda addu’a agare shi, sai Inna ta maida komai ga Allah ta kuma saka nima na koma yi masa addu’a kan Allah yasa a ko’ina yake ya fada a hannu nagari, hannun da ba zai taba cutar dashi ba.
A duk sallahr farillar Inna tana rokon Allah idan Baban Hauwa yana raye, Allah ya bayyana mana shi cikin koshin lafiya, idan mutuwa ya yi, Allah ya bayyanar da hakan a gare mu hankalin mu ya kwanta, ta maida hankalin ta kacokam! Kan kula da rayuwar tilon ‘yar ta wato ni (Hauwa-Kulu).
Ganin cewa yanzu bamu da mai taimaka mana ta fuskar ciyarwa sai Allah sai makwabta da muka saba ciyar da junan mu, musamman gidan malam Isa, komai na gidan da Malam ya ajiye mana a rumbun abinci a hankali ya kare tas, sai hakan ya sa Innar Hauwa ta fara tunanin sana’ar yi, daga karshe ta tsayar da sana’ar da ta fi yawa ga matan cikin Badala wato sana’ar dafa abincin sayarwa a cikin gida don nemar mana na batarwa dana cefane da bukatun yau da kullum.
A kullu yaumin Inna ta kan dafa shinkafa da wake tiya daya, dahuwa mai kyau, ta soya mankulin ta da albasa, ta daka yajin maggi, bata dora min talla a dalilin tana cikin masu adawa da tallan yara mata, ta fi yarda da in je makaranta fiye da in nemar mata kudi, don haka tun Baba yana nan ina zuwa makarantar boko da safe, da ta allo da yamma. A rashinsa kuma ban fasa zuwa ba.
Da aka gane tsaftar abincin ta a hankali har gida ake zuwa a saya, kuma akwai wani yaro anan makwabtanmu wai shi Saleleh, yaron ya saba da Inna ya shiga jikinta don shi yake zamarwa Babana a shago in zashi wani wuri, bayan batan sa ya cigaba da shigowa gun Inna tana bashi abinci da haka har suka saba don haka shi ta roka yake zuwa ya fitar mata da abincin makarantar bokon da nake zuwa, wato makarantar firamare ta gwamnati ta Kofar Na’isa, wadda bata da nisa da gidanmu. Ita kuma tana bashi abincin data dafa da naira goma daga cikin cinikin kullum ya dawo.
Kafin sha biyun rana Saleleh zai dawo da kudin ta a kulle a leda cif. An sayar da wake da shinkafan, har ana neman kari, sabida dadi da tsaftar abincin Innar Hauwa.
Sai mu yi cefanen abincin gobe kuma, mu kuma yi amfani da ribar da muka samu. Idan shekara ta zagayo Innar Hauwa na fitar da ragunan data kiwata ta sayar a kasuwar Raguna duk sallar layya, sai ta sayi wasu kanana ta kara kiwatawa zuwa shekara ta gaba.
Da wadannan sana’o’in guda biyu ni Hauwa da Inna ta muke rayuwa har tsayin shekaru biyu da batan Malam, muna cikin alhinin rashinsa.
Duk da cewa ni Hauwa ba wata kyakkyawa bace acan-acan, gani nan dai kalar Kanawan usli, wankan tarwada kuma makimanciya ga kyau, banda idanuna farare manya dasu masu kama da zagayen kwan zabo, ba abinda zaka ce mai bayyannnen kyau ne a halitta ta.
Na farko bani da tsayi, kuma bani da rama, amma bazaka kira ni mai kiba ba, gani nan dai ‘yar duma-duma haka, lubu-lubu mai jiki (luscious) tubus-tubus kamar na kulba, na kasance yarinya mai zafin nama tun ina karama da kwazon taya Inna aiki, sannan da tsananin son Uwa-mahaifiya da tausaya mata, musamman dana wayi gari babu Baba tare da ita, na fahimci ita kadai take buga-buga da kulle-kulle don ganin ban rasa komai ba.
Hakika na saka son Inna ta da yawa a raina, da tausayinta tun ina kankanuwa mai cikar lafiya, ga Inna da kujuba-kujuba a cikin gida tayi wannna ta koma ta yi wancan, shiyasa nima bana kyuya wajen taya Innata aikin abinci da ayyukan cikin gida tunda na soma kawo karfi, ni dai bar ni da shiru-shiruna na rashin son magana da rashin son hayaniya, sai manyan idanuwa tubarkallah masu yiwa wanda duk na harara barazana, farare kal dasu, masu haske da sheki da wani kwantaccen ruwa a kasan su, inna juya ido sai ka ga kamar hawaye ya kwanta.
A kaina akwai tarin sumar hausawa baka mai karfi irin cunkus dinnan, wadda bata taba ganin man shamfo ba (relaxer) ko na Danjangabo da ake amfani da shi a lokacin domin motsa gashi. Ni Hauwa tun ina kwailata akwai son wanka da yawan shafa turaren ‘Binta-Sudan’ ko ‘Dan Duala’ wanda na Inna ta ne da take yawan siya don amfaninta, kullum tayi wanka su take shafawa, sai nima na ara na yafa.
Lokaci-lokaci Inna kan sai min maina na shafawa na musamman (Dela-Maigurguwa), can gaba da zamani ya kara sabuntawa wato ‘cream’ ya shigo, sai ta koma saya min ‘TonyMontana’ don nima in jera da ‘yammata, a lokacin a shekaru goma sha biyun da nake dasu sune matakin farko na fara zama budurci, duk da ko kirgen dangi ban fara ba. Komai nawa dai-dai misali ne na asalin hausawa gaba da baya, kuma na halitta wanda babu kirkirarre. Zaku iya kiran ni Hauwa – Kulu da (natural black African beauty) ta zamanin da na taso.
A wannan shekarar da aka shiga na samu kammala makarantar firamare, na zana jarrabawar kwamen intarans, watakila don na fara karatun da wuri ne na gama firamare da wuri, inda ba da jimawa ba sakamako ya fito, Hauwa sarkin himma (ta bakin Inna), na ci makarantar ‘yammata ta gwamnati ta jeka ka dawo wai ita Shekara (GGSS Shekara).
Asalin iyayena kanawa ne na usul, wadanda ake kira Kanawan cikin Badala.
Wane tudu wande gangare duk aka bi za a fahimci daga Inna har Malam ‘yan asalin cikin kofofin Kano ne, basu da wani kauye da za’a ce daga can suka fito ban da kwaryar cikin birnin Kanon.
Inna iyayen ta sun jima da kwantawa dama ‘yan cikin Kofar Kansakali ne, kusan yanzu ita kadai ta rage a raye cikin jama’ar gidan su babu wanda zata kira nata da ya saura, ta haifeni a shekaru na girma tana da kusan shekaru arba’in sanda ta haife ni, shi yasa wasu ke dauka Kaka ta ce, babu wanda Inna zata kira nata a halin yanzu duk sun gushe, banda makwabta da abokan arziki da suke rayuwa a lungu guda.
Shi kuwa Malam Bilyaminu yana da dan uwan sa na jini Zakari mai wankin hula, yana nan a raye da nasa iyalin a unguwar kofar Dan agundi wadda ke daura da kofar Na’isa.
Sabanin Malam Bilyaminu shi Zakari Allah ya bashi haihuwa da yawa maza da mata sun kai goma, sabida yana da yawan aure-aure, mata biyar ya aura, uku ne a gidan yanzu, don haka ‘ya’yan iyaye daban daban suka haife su, sai dai ka samu biyu a daki daya ko uku a daki daya, amma kowa ya san babu jituwa ko kankani tsakanin Malam Bilyaminu da kanin sa malam Zakari sai ‘yan ubanci na gani kashe ni, wanda a kan sa suka rayu tun suna kanana har gashi sun cimma furfurar su basu daina ba.
Bayan batan Malam, Inna na yawan korafi gareni, “tun batan dan uwan sa bai taba zuwa ya ga halin da muke ciki ba, bai kuma taba tuna wai dan uwan nasa ya bar diya mace guda daya, yayi tunanin kula da lafiyarmu ko da bai taimaka mana da komai ba”.
Sai in ce “Inna kenan. Ai bai ma kamata ki damu ba Inna, don dama kin kwana da sanin ba batan sa ba damuwar sa bane, da kin yi shawara da ni ma bazaki je cigiyar Baba gidan sa ba Inna”.
Amma a cewar Innar Hauwa, lalurar batan mutum ta wuce komai, don gara a ce mutuwa yayi a kan ta, a ganin ta sun cancanci kulawar sa ko yaya ne a bayan ido dan uwan nasa. Wannan shine cikar zumunci.
Wani abun mamaki shine bai fi shekaru biyu da batan Malam Bilyaminu ba, aka wayi gari aka ga Baba Zakari ya kudance, ya rushe gidan sa ya zabga ginin katon gida mai dakali biyu irin na masu kudin da, anan kofar dan agundi, ya sayi motar yayi ta zamani da ake kira Marsandi, ya kuma bude katon shagon sayar da atamfofi a Singa. Sunansa ma ya koma Zakari mai atamfa.
Ba irin maganganun da mutane basa yi akan arzikin Zakari na rana daya, wanda babu wanda ya san inda ya samo shi. Shikuwa ya kame bakin sa daga tambayoyin jama’a da an yi magana Baba Zakari zai ce “DARE DAYA Allah kan yi Bature.
Wannan ba shi ne a gaban Innar Hauwa da ni kaina Hauwan ba, sai shirin fara karatuna a makarantar ‘yammata ta Shekara, abinda Zakari bai yarda yaran sa maza da mata ko daya cikin su ya yi ba hana rantsuwa in ka dauke babban cikin su da ya saki uwarsa ta fita dashi shikadai yake yi a boye, wato Jamil Zakari, da kannen sa ke kira “Yaya Jamilu”.
**** **** ****