HAUWA KULU Book 1 Complete Hausa Novel
Tun daga wannan ranar gidan su Hauwa ya zama wajen zuwan Dr. Sarham hira, wato tsakar ginan Inna ma tsafta da wadatar iska ya zama dakalin hirar sa, kusan kullum ya taso aiki sai ya je, su yi hira su yi dariya shi da Inna, hirar duniya iri-iri haka suke yini yin ta suna nishadantuwa da daukewa kai damuwar duniya. Inna tayi girkin ta mai dadi ta zubo masa, tuwo ne, dambu ne ko danwake ko dafadukan alkama da ire-iren su, ko gudun kurna da miyar taushe, sai ka ga Dr. Sarham ya mike kafa a kofar dakin Inna ya nade hannun riga ko yayi ‘loosing tie’ din suit din jikin sa yana kwasar girkin Inna na gargajiya irin wanda baya ci sam a gidan su koda sadaka za’a hadashi, musamman da ya fahimci irin tsaftar Inna, har ‘yan gidan su saida suka gane ya daina cin abincin ranar sa yanzu a dining. Ballde ya zana ya ci abinci tare dasu. In sun yi magana ya ce ya ci wajen wata Innarsa ne. Ga Inna da jin radio komai ta ji a radio sai ta kwashe ta gayawa likita Sarham, shikuma da yake ba ma’abocin sauraron radion bane sosai yake jin dadin labaran duniya daga radio mai jini wato Inna, sam Hauwa bata iya saka musu baki don ta fahimci daga Innar har Sarham maganannu ne na karshe (talkatives), ita kuma Allah bai halicce ta da yawan magana ba, ciwon kai take saka ta, don haka sau tari haushi sosai suke bata.
A wani hutun karshen mako wato ranar wata lahadi Sarham ya zo gidan, Hauwa na duke gindin famfo wai wankin kayanta take yi, ba yadda Inna bata yi da ita ba kan ta bar su zata saka Salele ya wanke mata in ya shigo, Hauwa ta ki, wai wankin Salele baya fita, Inna ta ce cikin subul da baka,
“da wanne idon zaki ga wankin har ki san ya fita ko bai fita ba?”
Ai kuwa Hauwa ta fashe da kuka sosai, wai Inna ta yi mata gorin ido. Ta tattara kayan wankinta ta yi bakin famfo tana ta dirzar su kamar Allah ya aiko ta tana kuka wurjanjan. A haka Dr. Sarham yayi sallama a gidan.
Inna ta amsa daga dakin ta, ya shigo har dakin nata don yanzu ba bakon sa bane, dardumar Sallahr ta ta shimfida masa tace “Lale Maraba da Da na Sarhamu” yayi dariya yana kokarin zama ya ce “Inna kema sunan bakin Abban mu zaki koyi lika min, don a ce ni din wani tsoho ne ko? Bayan ko talatin ban rufa ba, ina cikin twentieth dina?” Inna ta ce kai da Kuluwa ban san waya fi wani son yarinta da gudun tsufa ba, ita ta hana a kira ta Kulu, kai ma kace Sarhamu tsoho ne, bayan ainahin sunayen kenan kuke bata ma’anar su da zamananci”. Sarham yace “by calling Hauwa’u da Maijiddah, ai ba’a bata ma’anar sunan ba Inna, tunda inkiyarta ce ta hakika”. Inna ta ce “hakane kuma, duk inda Hauwa take, Jidda ce”.
Sai ya dubi inda Hauwa ke wanki bata kula shi ba yau, duk da dama ba wai kula shi ta ke sosai idan ya zo ba, amma akalla ta kan ce masa sannu da zuwa, tacigaba da sabgar gabanta ta manta dasu, ta hanyar kame bakin ta, amma yau kam ko uffan bata ce masa ba, bata kuma kai hankalin ta kan su ba, sai wanki take dirka lokaci zuwa lokaci ta na tsane ido da habar zanin ta.
“Inna me ya samu autar ki haka? Wa ya taba miki Maijiddah? Kamar kuka haikan naga tana yi?” Inna tace “ai tana jin ka, tambaye ta mana. Waka a bakin mai ita tafi dadi.
Wai daga cewa ta bar wakinnan Salele yayi mata, shikenan ta maida abun tashin hankali”.
Sarham ya ji wani iri, ganin kukan Hauwa’u ya karu da maganar da Inna tayi, kamar ta kara kunna ta, amma duk da haka bata fasa wankin da take faman yi ba kamar na dole, har da kara karfin sheshshekar kukan ta, Sarham ya mike daga kan dardumar da yake zaune ya matsa har inda Hauwa take wankin a gindin famfo ya russunna a gaban ta yace.
“Maijidda yaya haka zaki tadawa Inna hankali? Kinsan bata son kukan ki”.
Hauwa tayi sharbe, hannu a bayan ido, ta ce “bayan gorin ido tayi min?!”
“Gorin ido kamar yaya?”
Ta fashe da kuka ta ce “cewa fa tayi wai da wanne ido zan san kaya na sun fita ko basu fita ba, menene wannan in ba gorin ido ba?”
Sarham yayi kokarin danne dariyar sa ya ce “easy Maijidda, ko kowa zai miki gorin ido, ai banda Inna. Ke dai kin fassara maganar ta ba daidai ba sabida dama akan tsini kike, amma ba haka Inna take nufi ba, kin ji?”
Ta gyada kai tana share hawaye. Ya ce “to tashi ki bar wankin haka, in ya zo sai ya karasa” “ai har na gama dauraya nake yi, sai shanya”. Yace “to dinga daurayewa kina bani ina shanya miki” Hauwa ta zaro ido ta ce. “Lah! Likita da kai, zan saka ka shanya ka jika jikin ka?” Sarham ya ce likita bazai taimaki kanwar sa ba? Shi dama ai mai taimakon al’umma ne tun asalin sa” da haka ta yarda, ta ke dauraye su daya bayan daya tana miko masa, yana karba yana shanyawa akan igiyar shanyar su, nan da nan suka gama.
Dr. Sarham ya ce da Inna zai tafi gida, ba zai jima ba yau, dama ya leko ne kawai ya gansu ya wuce saboda Mama ta aike shi Dakata. Suka yi sallama shi da Inna.
Har ya kai bakin kofa ya tuna abinda ya kawo shi yau, kukan Hauwa yasa ya manta, sai ya dawo ya ce “Inna kiyi wa Maijidda shirin tafiya makaranta gobe, amma ba tata ta da zata koma ba.
Na nema mata makaranta wadda tayi daidai da masu irin lalurar ta (special school), yadda za’a yi ta dinga zuwa tana dawowa kullum shine ban sani ba, inata tunani a kai har yanzu”.
Inna taji idon ta har kwalla ta taru, wato shi Da nagari wanda ya samu tarbiyyar iyayen kwarai daban yake, ba sai wanda ka haifa ne kawai zai iya zame maka Da ba, da gaske akwai ‘ya’yan mutane ‘yan albarka fal a duniya wadanda baku hada kowacce irin alaqa ta jini ba, don dama damuwar ta kenan tun bayan makancewar Hauwa cewa itada karatun sakandire yaya zasu karke?
Gashi tun ba’aje koina ba likita Sarhamu yayi musu maganin wannnan damuwar. Ya share musu wannan hawayen. Me zata yiwa wannan bawan Allah banda duk sallahr farillar ta ta roka masa rahmar Ubangiji da gafara ga iyayen sa ba don sun mutu ba? da gamawa dasu lafiya.
Godiya sosai Inna tayi masa, ta shi masa albarka iyaka, sannan tace “kai ta da daukota wannan ba damuwa bane Salele zata yiwa magana ya dinga kaita kullum yana zuwa ya dawo da ita in sun tashi”. Sarham ya ce shi kuma ya saka masa albashin hakan, don kada yau da gobe ya gaji.
A yammacin ranar Sarham ya kawowa Hauwa uniform na Special School ta Kano, littafai, jakar makaranta da takalmi sau ciki da socks. Ita da kanta Hauwa saida ta rasa ta inda zata godewa Dr. Sarham.
Mafarin fara karatun Hauwa Bilyaminu a special school kenan, tare da sauran yaran Kano da zagayen ta masu ‘visual impairment’ (lalurar gani.) Dr. Sarham yayiwa Hauwa photochromic glass baki saboda ta dinga sakaya kwayar idanunta cikin hasken rana kada (sun exposure) yayi ma kwayar idon ta lahani wadanda kyawun su mai matukar ban mamaki ne, kamar bayan makancewar tasu an kara musu wani (added beauty) a cikin su, da haske mai daukar idon duk mai kallon ta.
Washegari litinin tun kafin ya tafi asibiti ya zo gidan don kai Hauwa makaranta da kansa, ya kuma ce da Inna da Salele duk su tafi tare don su ga makarantar ya kuma gabatar da su ga malaman makarantar. Hakan kuwa a ka yi.
**** **** ****
Hauwa-Kulu ta soma zuwa makaranta kullum tare da Saleleh da yake yi mata jagora, in lokacin tashi yayi ya je ya taho da ita. Hauwa ta soma karatu tare da sauran yara irin ta ta hanyar ‘Braille reading and writing’. Wanda ake koya musu tun a mataki na farko a matsayin hanyar rubutu da karatun su.
Hauwa’u an zama daliba, karatun data ke yi kullum ya dauke mata damuwar rashin idon ta manta da komai, kafin shekara ta zagayo a yi canjin aji na gaba Hauwa tayi na daya har sau uku a kowane zango, ta iya rubutu da braille sosai ta kuma iya karatu da braille din tiryan-tiryan. Sabida har a gida karatun take yi bata hutawa yasa Inna ta dauke mata tayata da ayyukan gida, ko tayi kokarin karba don ta taya ta Inna cewa take koma daki kiyi karatu kin ji Kulu na yafe miki, ba nakasashshe sai kasahshe, nakasa ba kasawa ba, kiyi ta karatu da nakasa domin kubuta daga bara da tozarta, aikin gida ba naki bane. Nawa ne, nida Allah ya baiwa lafiya”.
Sarham ba sosai yake zuwa gidan su Inna yanzu ba, saboda yanayin ayyukan nasa sun koma safe da yamma. Don haka sai karshen mako yake samun leko su Inna ya ji lafiyar su, ya kawo musu sayayyar da yakan yi musu ta kayan masarufi idan ya dauki albashin sa, yana matukar farin ciki da cigaban Hauwa ta fuskar karatu, da kokarin da take yi a ajin su kullum. Don yakan je wajen malamanta ba tare da su Inna sun sani bama, don bincikar progress din ta, ana kuma tabbatar masa da irin kokarin Hauwa bana wasa bane, gifted ce.
Don hatta lissafi (mathematics) da yake baiwa makafi wahala a braille ita Hauwa tsaf take ganewa abinta.