HAUWA KULU Book 1 Complete Hausa Novel

HAUWA KULU Book 1 Complete Hausa Novel

HAUWA-KULU
Kusan shakuwar tafi yawa tsakanin Inna da Sarham maimakon Sarham da Hauwa, kasancewar Hauwa bata da magana kuma taki sabawa da Sarham har gobe, duk kuwa da yadda yake kyautata musu, kuma yake jan ta da wasa lokaci-lokaci, iyakaci in ta ji ya zo ta gaida shi, ta shige daki ta bar su, in ya mata tambaya akan karatu ta bashi amsa a gajarce, kuma in an bata sakamakon ta bata kasa a guiwa wajen nuna masa da zarar ya zo gidan.
Don ta yarda Dr. Sarham shine ginshikin karatun nata. Kuma ta kwana da sanin taimakon da yake yi musu mai dimbin yawa ne, da yafi karfin a gode masa, don duk da Inna ta cigaba da sana’ar ta ta sayar da wake da shinkafa duk wata hidima ta karatun Hauwa shi yake yin ta kamar biyan Salele albashin kaita makaranta da daukota, da basu kudin hawa hayis zuwa da dawowa, sayen littatafai da kananan abubuwan da makaranta ke bukata kasancewar special school makaranta ce ta gwamnati domin yara masu bukata ta musamman yasa babu bukatar biyan kudin makaranta.
Daga baya kuma Sarham baya zuwa gidan Inna sosai saboda ayyuka da suka tarar masa amma duk weekend baya fasa lekowa. Ya zama dan Inna, Inna ta zama uwar sa, ya zama dan gidan Bilyaminu kofar Na’isa, don ganin sa take ya maye mata gurbin Zulkifilu.
A yanzu hatta a weekend dinma Dr. Sarham baya samun zuwa hira wajen Inna kamar da, domin yana shirye-shiryen komawar sa Jiddah, bayan kwashe shekaru biyu yana aikin gwamnati, tun akan abinda ya faru da Hauwa yasa a ran sa zai koma zurfafa karatun sa, domin ya ki yardarwa kansa har zuwa yanzu cewa ba rashin kwarewar sa bane ya janyo wa Hauwa’u cataract blindness, yasa a ran sa yana bukatar kara zurfafa ilmin sa zuwa mataki na gaba. Sai ya ga abinda ya turewa buzu nadi daga ilmin likitancin ido, akan dai specialization din sa na ophthalmology a shirye yake har ya tsufa in dai da rai, bazai gushe ba kuma bazai gaji ba yana karawa kansa kwasa-kwasai na fadada ilmin sa da zurfafa shi, don zama kwararren ophthalmic surgeon din da zai zamowa kasar sa abin alfahari watarana da fiddawa kansa ‘inferiority complex’ din da yake fama da shi tun akan aikin da yayiwa Hauwa-Kulu. Duk da cdewa bayan nan yayi wasu ayyukan fidar da yawa kuma an yi nasara. Abba Prof. kuma ya lamunce masa ya koma din, don a cewar sa gara ya gama karatun duk da zai yi cikin kuruciyar sa, kamar yadda shima ya samu yayi nasa yake cin moriyar sat un da jimawa.
**** **** ****
Jikin kafatanin mutanen gidan yau a matukar sanyaye yake, wannan ya faru ne kasancewar gobe da asubah ake saka ran in sha Allah, Bhaiya (Dr. Sarham Shanono), zai tashi zuwa kasar da ya baro a can baya a karo na biyu wato kasar Saudi-Arabia don zurfafa karatun sa.
Sabo, wani abu ne mai matukar muhimmanci ga rayuwar iyali, musamman irin wannan wadanda suka gina tubalin rayuwar su akan tsari na (nuclear family) wanda akasari ‘yan boko ke yi, wato rayuwa ta daga su sai ‘ya’yan su, kamar yadda yake a gidan Prof. Abbas Shanono.
Don haka ficewar daya daga cikin su rana daya zai haifar da wawakeken gibi ne a gidan, musamman shi Sarham da yake jigon gidansu, sannan ‘personality’ din shi ya banbanta dana kowa cikin gidan, shi mutum ne na kowa!
Likita mai farin jini da sakewa da mutane wanda kowa nasa ne, mai faram-faram da hidima da kowa nasa, shi kadai ne Da namiji a cikin su, in ka cire mahaifin nasu.
Don haka shi din, tamkar wani bango ne a gidan su abin jingina. Gabakidayan su jama’ar gidan, in ka dubesu yau zaka fahimci tsantsar damuwar da suke ciki, kowa fuska ba annuri, banda Abba Prof. da ke shi babba ne, ya boye tasa damuwar, maimakon hakan, sai ya raja’a wajen lallashin su da karfafa musu gwiwa kan tafiyar Sarham din da cewa,
“menene abun damuwa don Sarhamu ya tafi? Tunda ga waya yanzu, ta fara zama abu mai sauki, kuma dukkan ku zaku so ganin ranar da Sarhamu zai zamowa kasar sa abin alfahari inace, wanda zai zo a dama da shi a harkar kiwon lafiya a Arewacin Najeriya”.
Amma fa shima Abban a ran sa ya fi kowa damuwa, ya fi su shiga kewar Sarhamu, tun ma kafin ya tafi, saboda yadda Sarham yake tsaye kullum kan hidimar sa data gidan sa, wani abun ko labari baya ji sai zance ya shigo da zance, Mama zata ce ai Sarham yayi kaza, kamar misali cefanen gidan sa, yana dadewa bai yi ba. Haka maganin da kowa yake sha idan rashin lafiya ta samu dayan su, Sarham da bai da iyali ya daukewa Abban su kananan abubuwa irin wadannan, su petrol din tada janerato, har ila yau, yana matukar taimakawa shi kansa Abban da nasa ayyukan ofis din kasancewar Allah yayiwa Sarham baiwar ilmi da sanin hikimar koyarwa, kuma da yake a fanni guda suke shi da Abban. Don haka shima yana cikin kewar Lelen Abba!
Shima Sarham din karfin hali yake yi, musamman in ya dubi Sumayyah, da kukan da take yi. Sai Abba Prof. yace tayi hakuri yayi mata alkawarin bin bayan Sarham da zarar ta kammala sakandire itama zata je ta yi MBBS a can inda yake.
Kasancewar Abba Prof. yana da hanyar tagomashin karatu a kasar Saudiyyah (scholarship) na Jami’ar ‘KING ABDULAZEEZ UNIVERSITY’ domin akwai abokan karatun sa da yawa da suke aiki a jami’ar, tun bayan bude tsangayar likitanci a jami’ar. Da an samu rarar gurbin karatu su kan bashi.
Mama bayan Sarham ya shiga dakin sa yana hada kayan tafiyarsa, sai ta zare jiki ta bishi a baya, kujerar karatunsa dake dakin guda daya ta samu ta zauna, Mama ta ce,
“Sarham haka muka yi da kai?” Ya bar abinda yake yi ya bata hankalin sa ya ce “akan me Mama?” Tace “maganar diyar Barr. Hannatu da na gaya maka muna so muyi muku ‘yar gida don kara karfafa zumuncin dake tsakanin mu ni da mahaifiyar ta, mun yi da kai kafin ka tafi ko sau daya ne za kaje ku gaisa da ita Sadiya din, amma har yau ban ji ka kara tada zancen ba, gashi har zaka tafi.
Kasan dai yadda nake da Barr. Hannatu, babu wasa ko rainin hankali tsakanina da ita, bana so ka je ka shantake a Jeddah babu aure, so nake da ka samu good two or three years ka dawo gida kayi auren ka in ya so in ma komawar zaka yi ka koma da matar sai hankali na yafi kwanciya da zaman ka a ko’ina ne, tunda na fahimci kafi son rayuwar Jeddah banda haka da ka zauna ka cigaba da aikin ka kawai.
Duk da nasan baka da matsala Sarham, tarbiyyah ta Allah bazan ce ni na baka ita ba, amma Allah ya yi maka tarbiyyar da kowacce uwa zata yi alfahari da ita, saidai kwanciyar hankalin iyaye a kullum shine ace yaran su sun yi aure a lokacin da ya dace”.
Sarham ya nisa, ya ajiye rigar da zai saka a cikin trolley a gefe, kafin yace cikin lallashi “Mama bana so kisa ran ki a irin wannan hade-haden auren na favouritism domin ki dadadawa wasu, wanda a karshe maimakon ku gyara zumunci sai dai ku kai ga lalata shi, saboda ni gaskiya Mama bana ra’ayin macen da iyayen ta ke nemo mata miji daga ‘ya’yan kawaye.
Yau da a ce ke da kan ki kika yi wannan ra’ayin, zan iya bi, koda kuwa bana so, amma daga sanda kika gaya min Barr. Hannatu ce ta nemi alfarmar nace a raina ‘yar ta ta rasa miji ne take nema mata, gashi ni ba rasa mata nayi ba, na tabbata lokaci ne.
Mama kin san da labarin “Madinah” ba tun yau ba, to wallahi Mama har gobe tana raina, don nina gan ta naji ina so saboda wasu dalilai, amma na gwammace in hakura da ita tunda ubanta baya kaunata, kuma daga kanta bana jin zan kara son wata ‘ya mace, daga kanta kuma na tsani soyayyar bakidayanta.
Mama we’ve had a wonderful time together nida Madinah, for as long as four years muna tare cikin kauna da fahitar juna, mun yi wa juna alkawura masu yawa amma Madinah ta saka kafa ta take su tayi fatali dasu rana daya, don haka daga kanta na daina bata lokaci na a kan ‘yammata wallahi. Duk marasa amana ne.
Madinah ta dusar da hasken sauran mata daga idanuna Mama, ba wadda nake ganin farin ta. In fact, Mama bani da niyyar aure nan kusa.
Ban san me kaddara ta tanadar min gobe ba!”.
Mama ta ce “in uban Madina baya son ka sabida ya raina ajin uban ka, su wadannan uwa da uban duka sun zo da kan su sun ce ka yi musu, suna son hada jini da ni, saboda sun san darajar mu da martabar mu, ni kuwa bana tulawa masoyi na kasa a ido. Amma ban isa in maka dole ba.
Duk abinda uban Madina ke takama da shi na tarin arziki da ilmi da har yake ganin baka isa auren diyar sa ba, uban Sadiya ya mallaki goman sa,”
Da sauri Sarham yace “ko ita Madinah ba dalilin da yasa na so ta ba kenan Mama, na rantse ban taba sanin waye ubanta ba har sai bayan ya yanke alaqar mu.
Na so Madinah ne akan wani dalili Mama…. dalilin kuma shine…. kokarin ta a karatu….” zai fara bata labarin irin kokarin Madinah da yadda take ‘excelling with high grades’ a kowacce jarrabawa Mama ta katse shi da karfi, inda tace “bana bukatar ji, na gaji da zancen Madinah Attahiru Sarham tunda ba itace autar mata ba.
Ka karbi masu son ka, ka rabu da tsammanin warabbuka.
In dai labarin nan ne ka bani shi yafi sau shurin masaki, yafi cikin carbi, har na riga na haddace shi, kana son Madina saboda kokarin ta akan karatu, na gaji da jin wannan, abinda baka sani ba, Madina ba itace karshen masu kokari ba, Sadiya ma tana da irin nata domin kuwa Quantity Surveyor ce. Kuma uwarta ta tabbatar min tana son ka sosai, ba wai ita ta ga dacewar abin ba Sadiyar ce da kanta tace tana son ka”.
“Ahap! Anzo wurin”. Mama ta bare ta gabadaya. Sarham ya fada kasa kasa “su Mama an kara bare ta, to ai ni Mama bazan taba auren macen da ta ganni wai ta ce na yi mata ba, komai lalacewar zamani akwai mata masu aji, wadda ba ni na ce ina son ta ba in the first place hankalina bazai taba kwanciya da ita ba”.
Duk ta inda Mama ta bullo don Sarham ya karbi tayin ‘yar aminiyar ta Sadiya Sarham sai ya zuqe, amma fa cikin lallami da dabara yake bin Mama don su yi rabuwar salama. Ya san kan Maman sa sarai, yana yi yana dariya da hilatar ta yadda bazai bata mata rai ba.
A karshe Mama ta gaji da ja’injar, ta sakar masa inda ta ce “Sarham! Na baka shekara daya ka kawo min matar da kake so ka aura, mai kokari irin Madinah wadda hankalin ka zai kwanta da ita din, tunda kai dai a kan Madina kowa dakiki ne, to ka nemo mai kokari irin nata, kafin shekara daya, amma ni wannan Madinar ko zancenta bana son ji.
Sarham idan shekara ta zagayo baka kawomin mata ba na rantse Sadiya zan aura maka, kana so ko baka so, in kuma dauketa in bika da ita har inda kake”.
Sarham ya ce “to Mama addu’a zaki yi min Allah ya kawo mai kama da Madinah, fara kamar balarabiya, doguwa siririya mai gashi yala-yala har gadon baya, sannan mai asalin kwanya a karatu irin ta Madinah Sorondinki”. Tsaki Mama tayi ta tashi ta bar masa dakin don haushi. Ta sani daga Madina har iyayen ta babu wanda ya damu da shi shi, kadai yake kidan sa yake rawar sa a kan ta.
Ita kuma bazata taba maraba da inda ba’a son nata ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected