TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel
Flip flops slippers masu taushi ya saka,wadanda suka bayyana sirrin fara tas din doguwar qafarsa,ya jefa wayarsa a aljihu yana fitowa. A falon suka hade da Jacob wanda yake sanye da afron
“Welcome sir,the food is ready” a ga’ida ya zauna din yaci,to amma haka kawai yakejin bashi da nutsuwar hakan
“Not now i will be back” daga haka ya Sanya kansa yana fita daga sashen nasa cikin takun nan nasa na nutsuwa da kamewa.
Lokacin da muryarsa ta bada sautin sallama maji na zaune fadeela na saman gafafunta kamar zata koma cikinta,fadeela na tare dasu nawwara,houria hessa,minafah ,maysam,banaan,amjad,taraneem,tayma da saneem,kusan su sha biyar ‘yan mata kamar nadeeva akazo dasu,sai manya masu dan shekaru kusan saannin maji,wasu kuma basu qarasa shekarunta ba suma sun kusa su takwas. Dukansu suna taya nadeeya shirya gifts da kayayyakin bikukuwan al’adar al’ummar gasar Algeria da maji ta shirya gabatarwa. Sarqoqi ne na wuya hannu da gafa na alfarma,dukkansu na gold,coins na gold da kuma wasu irin velvet gown tare,pakistani bride gown masu azabar kyau da tsada,wanda aka samar daga zare mafi tsada da kuma daraja,tare da wasu duwatsu masu tsada.
Ga trousseau package dake dauke da dukka nau’in jewellery na gold da zatayi amfani dasu throughout bikin gaba daya. Kudi sosai marasa misali maii ta kashe, kamar yadda tayi gayya sosai ba tare da jin kudin jirgi ba,duk da kusan kowa shi ya yiwa kansa kudin jirgi,banda
‘yammatan da tace suna wuyanta,family ne da sukayi suna a qasar,saboda sun hada komai malanta da kuma dukiya. Dakuna manya manya guda biyu masu girman gaske a wadace ya ishesu,aka zuba musu kuma dukka nau’in abinda zasu bugata bisa jagorancin baaba ramatu data kasa zaune ta kasa tsaye,takaicinta ya cika zuciyar hajiya garama,saidai babu damar yin magana ko wani motsi kada abinda ke lullube a zukata ya bayyana.
Kusan babu wadda idanunta bai sauka a kansa ba cikin ‘yammatan,zukatansu suka fara raurawa.wasu suka samu nasarar kau da kawunansu,wasu suka kasa,tamkar babu tsala tsalan mazan larabawa a Algeria.
Kallon kallon suka yiwa juna shi da maji din,kowa a cikinsu zuciya na motsawa da wani irin yanayi,kewa da soyayyar d’a da mahaifi ta fara aikinta. Duk yadda maji taso daurewa saida qwalla ta cika idanunta,amma tayi namijin goqarin hanasu zubowa duk da basu koma ba. Ta tafi tabar moha din nata dan qanqani a gabanta da qananun shekaru,sai gashi yau ya bayyana a gabanta a matsayin magidanci harda d’iya. Nadeeya ce ta janye ‘yanmatan suka fice bayan sun gama gaidashi,sunata daburtawa su sa nadeeya,ita bata qware a larabci ba,su kuma hausar tasu duka kame kame,kai tsaye ma idan kace basu iya ba bakayi kuskure ba.
[14/09, 7:42 pm] Mimah Yusuf: *HUGUMA*
* TABARMAR KASHI_*
Book 02 Page 11
Wani irin mugun sanyi dukka qafatunsa sukayi,cikin nutsuwa yake takowa gabanta bayan ya sake jaddada sallamarsa kansa a qas,yana jinsa a matsayin wani gagarumin me laifi. Qoqarin zubewa yake a gabanta amma sai ta miga masa dukka hannayenta,baiyi jinkiri ba ya sanya nasa hannuwan a ciki,tayi masa mazauni a gefanta fuskarta dauke da murmushi me hade da hawaye
“Kar kace komai,basai ka nemi gafarata ba,na riga nayi maka dukkan uzuri har a gaban
Allah,na yafe maka kai da dukkan zuri’arka”
majin ta fada tana dauke hawayen fuskarta lokacin da yake zaune a gabanta kansa a qasa har yanzu ya gaza cirashi,yana jin kan nashi yayi masa wani irin nauyi,kunya da nauyinta suna cikashi. Dai dai lokacin hajiya qarama ta hadiyi yawu da gyartaja da baya a hankali ta koma inda ta fito, zuciyarta na wani irin gonewa
“Bani labarin yadda rayuwa ta kasance” ta fada tana sakin murmushi,abinda ya sanyashi daga kansa,ya sauke idanunsa cikin na mahaifiyarsa,wani siririn murmushi ya sauka saman miskilar fuskarsa.
**********K’arfe biyu da rabi na ranar juma’a,babban masallacin juma ar dake iya daukar dubban jama’ar musulmai a wannan ranar a cushe yake da garin baqi daga qasashe daban daban da kuma garuruwan dake QASATA Nigeria domin halartar shaida daurin auren MUHAMMAD TAUFEEQ JARMA da amaryarsa KHADIJA MUHAMMAD
GIREMA,bayan gama daura auren AFIFA
AHMAD da MUHAMMAD SAJJAD a asalin garin mahaifinta da dr mamman yace lallai aje tushenta ayi don karramasu.
Duk yadda takeso taii cikin ranta da jikinta cewa yau din ba wata rana bace ta daban da dukka sauran ranakunta na rayuwa ba,yau din sunanta amarya a karo na biyu dukka taron al’ummar dake gidan da masallacin sunzo ne don su shaida ta zama matar MT JARMA hakan ya faskara,tana gayawa kanta akasin hakan zuciyarta na jaddada mata qarya take fadi,a haka ta dinga jin rauni,raunin da yakai ga zubar hawaye a idanunta masu yawa da zafi.
* MUHAMMAD TOUFEEO RESIDENT *
Kai kawo takeyi cikin dakinta,wanda a qalla ta kusa awanni biyu cur tana yinsa ba tare data zauna ko kuma ta huta ba.
Tashin hankalin da take ciki ya zarta duk yadda hankali zai iya dauka,ya kuma shafe tunanin me tunani. Asara mafi muni tare da faduwa muraran take gani a gabanta,a dai dai lokacin da tafi bugatarsa a dai dai lokacin da mummunar labarin shudewarsa ta sameta?,batasan haka zata faru da ita,batasan haka zata kasance ba,da babu shakka ba zata bashi baya har na tsahon shekarun nan ba.
A nata ganin da hangen bugatarta ta biya,ya kuma tabbatar mata da cewa qulli me dan karen garfi da warwarewarsa ba’a nan kusa ba,nasara biyan bugata da cikar muradi suna ta zuwar mata fiye da yadda tayi zata,hakan ya sake bata qaimin bazama cikin duniya,taci gaba da rayuwarta ta kuma karbeta a yadda tazo mata tana moreta yadda ya kamata.
Knocking qofarta a kayi,a mugun fusace take,don haka har ta buda baki zata tambaya cikin zafi,sai kuma ta tuna,a yanzu gidan yana cikin yanayin da bai kamata ta bari aga alamun matsala ko wata damuwa a tattare da ita ba,wanann yasa ta furzar da iska sannan tayo tattaki ta bude qofar.
Hajiya mansura ce,ita da hajiya qaraman sukayiwa juna kallon kallo,duk mutumin da ya sansu a shekarun baya,a yanzu idan yaga kallon da sukewa juna zai garyata hakan,duba daya kacal zaka yi musu ka tabbatar da abubuwa masu yawa dake qunshe a zukatansu. Abubuwa biyu itama ke neman zame mata barazana,labiba dake neman zauce mata saboda auren toufeeq,ga kuma saukar shifa a nigeria,labari mafi muni ga kunnuwanta. Abune da bata taba kawoshi ga ranta ba,saboda tana da tabbaci daga gurin masu bata tabbaci.
..ita da Nigerian
har abada,tamkar yadda jinjiri yake barin cikin mahaifiyarsa. Ita kadai tasan abinda take gani take kuma karanta daga gurin Dr jarma,bai cancanci shifa ta shigo Nigeria ba ma sam a irin wannan lokacin
“Amarya na dab da shigowa cikin gidan nan,ya kamata a ajiye zafin rashi ko ayi abinda ya dace” sarai ta fahimci mansurar magana take danqara mata,amma sai ta sake mata wani murmushi,saboda ta tabbatar tana wasa ne kawai da wuta me tsananin ruruwa da azabar turiri cikin rashin sani,tayi imani bata gama sanin ita din wacece ba,da tabbas! batayi wasa da ita har haka ba,saidai kuma zata dandana kalarta ta ainihi, wala’alla a nan gaba kome irin sunanta ta gani da gudu zata gusa daga wajen
“Karki wani damu,dama ni nafi cancanta da karbar matar toufeeg” hajiya qarama ta amsawa mansura. Ciki ta juya tana duban suturar jikinta. Girman kanta ne ya motsa,taji tafi gaban fita haka,don haka ta bude makekiyar closet dinta ta fara laluben suturar alfarma.