TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel

TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel

“Fushi nake dake saboda haka bazan zauna ba,rakiya kawai na yowa abba” idanu sãahar ta fiddo waie cikin mamaki

“Wai Dr?” Sai ta jiniina kai

“Suna waje shida abban gidan nan” sosai mamaki ya kama sãahar,sai ta sauke fadeela ta kama hannunta sukayi kitchen don samarwa dr jarma din wani abun shan.

Falon sai ya zamana babu sai su biyu ita da afifa,afifan ta qaraso tana murmushi

“Yaudai naga sister nadeeya,ki zauna mana” tana murmushin itama ta zauna,sannan tace

“Don Allah bestie kiyi haquri, kaina ya kulle,tambayoyi ne dani fal bakina,kuma nasan aunty N ba zata taba tsaiwa tayimin dogon sharhin da nakeso ba,and na tabbata kedin kina da amsar kowacce tambaya tawa” hannu afifa ta miga tana murmushi

“Kaina ya kawomin wasu tambayoyin da kike dasu,nasan kuma dole ki bugaci amsarsu,zo muie ciki” tsam ta mige tabi bayanta,suka wuce kai tsave zuwa dakinsu säahar din.

Ko afifa bata fada ba nadeeya tasan dakin na saahar ne,don kusan yadda ta tsara dakinta na gidansu haka wannan,har yafi wancan nesa ba kusa ba,komai a kammale cike da tsafta da qamshi da wani irin tattausan yanayi.

Tana dauke da babban tray din fadeela na biye da ita tana zuba mata labari a nutse daya bayan daya,riqe take da gefan doguwar rigarta tana biye da ita kamar jela,kai kace guduwa zatayi ta barta. Tun kafin su qarasa sai kunya ta kamata ganin yadda Dr da abbanta suka bisu da idanu kamar dai irin kana zancan mutum sai kuma kukaga tahowarsa daga nesa. Ta qarasa gabansu cikin girmamawar nan da kuma mutuntawa takai qasa tana gaida dr jarma,tare ta bude murafun abubuwan shan da tazo dasu tana zuba masa fadeela na matso mata da cups din. Cikin matugar kulawa ya amsa

“Amma daa saura kadan nima nayi fushi dake,kin biyewa wancan tsatstsauran kuna shirin yin sakarci?” Sai ya maida dubansa ga dr girema

“Ban taba sanin ita ke kulamin da jikata ba sai da muka iso gidan nan na fahimci hakan,bana fatar wannan alaqar ta yanke ta tsaya iya haka” dr mahmud ya fada yana jin wani karsashi yana shigarsa. Tun farkon saninsa da sãahar ta kwanta masa,yanayin kamun kanta,sanin kima da martabar dan adam, da tsantsar tarbiyyar daya gani daga gareta,duk kuwa da zurfin karatun bokon da take dashi…hakan ba qaramin burgeshi yayi ba, dabi’ unta sun banbanta dana sa’o’i da takwarorinta masu matakin karatu da gata irin nata.

“Ga ‘yarki nan na kawo miki,zata zauna tayi jinya a gurinki” kalaman da dr mahmud ya fada kenan lokacin da sukayo masa rakiya zasu koma shida nadeeya,maganar da tadan daurewa sãahar kai,anya da sanin wancan dan wulaqancin Dr jarma ya kawo mata fadeela?.

“In sha Allah zaka jini,na gode qwarai da ziyara,duk da ba takanas akazomi ba,sahun diyarka ka biyo” muryar dr mamman girema kenan yake fadiwa dr jarma

“Diyata ta cancanci a biyota,idan ban jika bama mamman ni zaka iini,ni zan fara nemanka ma”
“Karka damu” ya fada yana murmushi,sannan ya maida masa murfin motar,suka tayar da motocin suna ficewa a gidan.

Zuzzurfan tunani nadeeya ta shiga,daya bayan daya qwaqwalwarta ke mata bitar maganganun da sukayi da afifa,akwai abubuwa da suka bata mamaki tausayi da kuma daure kai,ashe already yaa toufeeq da anty N din sunsan juna?,but itafa laifin yayanta take gani to be frankly,a nan bataga laifin sãahar ba,cikar diya macen kenan ko ita ba zata dauki izzar d’a namiji ba. Amma abinda yafi gigitata rayuwar da säahar din ta fuskanta,wadda ta tilastata sauyawa daga ainihin dabi’unta. Abu mafi ban mamakin shine daya zamana wai ta taba aure,babu abinda zai nuna maka alamun hakan tattare da ita tafi miliyoyin ‘yammata cikar haiba da komai na halitta. Sake juya kanta tayi wata shawara me girma na tsargawa cikin ranta,sai ta kira sunan
Dr da

“Abbana”

“‘Ya akayi?” Ya tambayi nadeeyan yana qoqarin ajiye wayarsa bayan ya gama duba wani abu.
Idanunta suka dan kai kan wayar,sai taga kamar hoton MAJI dinta

“Abba dama kana da hoton maji ne?” Bakinta ya subuce ta jefa masa tambayar,don basu taba magana makamanciyar irin wannan baidanunta a kansa tana kallonsa. Harara ya watsa mata

“Yau nine na koma abokin wasanki?” Janye dubanta tayi zuciyarta da gwiwarta tana karyewa

“Kayi haquri” ta fada a sanyaye,sai yaji tausayinta ya kamashi

“Me ya faru kika kira sunana?” Gara zamanta tayi

“Ka taba sanin wani abu akan anty säahar?”
Shuru ya danyi sannan ya girgiza kai

“A’ah,akwai wani abunne?,mahaifinta Dr mamman munyi karatu dashi tsahon shekara biyar,sanann musan juna sosai a wancan lokacin,yanayi da lokaci ya jefa kowa inda yaso sai kuma aka rabu,sai bayan dogon lokaci bayan mun hadu da muhyiddeen na
fahimci dansa ne,shekaru masu yawa kuma
sai yau Allah ya gaddara ganawarmu” kai ta
jinjina,sannan ta warwarewa dr jarma din
kome data ji daga afifa.

Tsahon lokaci yana jinjina kai ba tare da
yace komai ba

“Amma abba ni ina da shawara” juyawa yayi ya
dubeta
“Wacce irin shawara ce?”

******Tun daren ranar da aka kawota take
magale da sãahar,duk inda ta motsa sai ta
bita gafarta qafartaji takeyi kamar zata gudu
ta barta. Ko da sukazo kwanciya sai data
rungumeta sosai,a haka bacci yayi awon gaba da ita.
Afifa na gefe tana kallonsu,dariya tayi lokacin da take zare jikinta daga na nadeeyan a hankali

“Ah kin hadu fa da chewing gum” murmushi sãahar tayi,tana shafa kan fadeela gami da maida mata gashinta da ya ya mutse baya

“Ta saba aiko a gida sai tayi bacci kafin na koma dakina” kai afifa ta gyada tana kallon fuskar fadeelan cikin tausayawa,farat daya taji yarinyar ta shiga ranta.

Kwana uku cakal amma sai ka dauka fadeelan ta shekara a gidan,ta sake sosai tana ta walwalarta da harkokinta,zuwanta sau ya sake raya gidan,baya rabo da motsinsu da kai kawonsu ita da saahar,maama dai ‘yar kallo ce,amma ita kanta yarinyar ta shiga zuciyarta,idan ka gansu zaka dauka itama daya ce daga cikin jikokinta,hadda da dr girema fadeelan ta shiga zuciyarsa,yana kallonta kamar su Aleena,idan ka shigo gidan zakayi tunanin itama jikar gidan ce kamar su khalifa.

Fadeelan bata taba jin rayuwa tayi mata dadi ba kamar wannan lokacin,saahar ce komai nata,yadda take kula da ita a gida haka a nan,harna sama da gidan,saboda a nan din a sake take fiye da can da take ganin bata da wani hurumi da can din. Batun ciwo kuwa tun randa aka kawota babushi ya tafi,gefa guda kuma kullum sai sunyi waya da nadeeya da kuma dr Jarma,wanda ya dauke nadeeyan ya maidata gidansa,yace itama ta zauna a can na wani lokaci.

*****Duk yadda yakai ga son ya dauke kai ya bar musu fadeelan yaga iya gudun ruwansu amma ya gaza. A yau yana tsaka da aiki ya kashe system din ya mige gafafunsa saman table din hadi da relaxing bayansa jikin couch din da yake kai yana lumshe idanunsa,jiya ya kira nadeeya yayi mata titsiye,ta kuma tabbatar masa fadeelan tana can. Yaso qwarai ya tattara ya zuba musu idanu,to amma zuciyarsa ta kasa dauka,gidan gaba daya shuru,babu kowa,dr din ya dauke nadeeya kamar yadda ya dauke fadeela.

Miqewa ya sakeyi yana kaiwa bakin corridor din dab da wasu flowers dake fidda sanyi me qamshi,ransa yana zafi sosai game da yarinyar. A baya yana lallaba rayuwarsa,yana yinta hankali kwance ba tare da wata baquwar fuska ta kutso musu ba.
Amma daga bayyanarta cikin watanni kacal tana neman ta zame musu qarfen gafa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected