TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel

TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel

Tsaye tayi a gaban madubi bayan fitowarta daga toilet din tana kallon fuskarta data fito sosai saboda qananun kitson da aka zauna aka yarfawa gashinta me santsi,abinda zata iva cewa tsahon rayuwarta ba zatace ga lokacin da irin hakan ta faru ba,hasalima kwata kwata kitsonta baya wuce manyan kalba guda hudu,saboda tsaho da santsin gashinta, amma a yanzun an samu wata gwana jarababbiyar iya kama gashi ta kitse mata kan tsaf,kuma hakan ba qaramin qarawa fuskarta kyau yayi ba,jelolin kitson gaba daya sun kwanta sosai a gadon bayanta har tsakiyar bayan nata. Hannu ta sanya tana qogarin zuge zip din rigarta wanda afifa ce dama ta zuge matan,da qyar hannun nata yakai,ta fara jan zip din ya fara saukowa,har yakai rabi taji an taba qofar,saita tsaya cak tana kallon madubi dake haska mata bakin gofa,tanason tantance qofar dakin nata aka taba ko kuma sauran qofofin dake wajen.

A hankali qofar ta bude,ya bayyana daga bakin qofar da daurarriyar fuskar nan tasa,tashin farko qamshin da dakin ke fiddawa ya marabci hancinsa kafin a sannu idanunsa su suka a bayanta da fara qal don brassiere dinta ta bayyana. Sosai ta razana don batayi tunanin ganinsa ba wannan lokacin,tunawa tayi da zugaggen zip dinta data tabbatar a vadda ya sauka har brassiere dinta za’a iya gani,wanann tunanin ya sanyata juyawa da sauri kamar numfashinta zai dauke ba tare data tuna yadda rigar ta fidda tudun qirjinta ba da kyau.

Kamar daukewar majigin tv,gushewar baya zuwa bayyanar qirjinta ga idanunsa duka sun faru cikin abinda baiyi damanda second uku ba,bazaice ga yadda akay ba ya samu idanunsa dumu dumu suna kallon qirjin nata ba da suke a cike,farar fatar dake lullube ko ta ina ta jikinta ta bayyana daga samansu tana nuna mizanin cika da suke da ita. Wani mugun fusga ya yiwa numfashinsa da idanun nasa ma gaba daya yana sanya qarfin zuciya dana ruhi gurin janye kallonsa daga kanta. Yayin da sãahar din gaba daya ta qarasa rudewa,ta fisgi dankwalinta dake ajjiye saman madubin ta yafa ranta a bace.

Tamkar baiga komai ba ya sanya kansa cikin dakin yana furta sallama can qasa,kanshi tsaye yake takowa dakin tamkar dai mallakinsa bawai nata ba,bai tsaya ba har sai da ya isa kusa da bedside drawer ya zube dukka ledojin a kai ba tare da ya dauki ko daya ba,sannan ya juya abinsa zai fice daga dakin. Kasa jurewa tayi,tadan daga muryarta kadan

“Ba kowanne daki bane mallakinka a yanzu,kafin shiga kowanne daki a gidan nan ya zama dole ka nema izini” tsaiwar mashi maganar tayi masa bisa kansa,har ya rage saurin tafiyar tasa,sai kuma yaci gaba da ficewar,saboda wata kasala dake sauka a kowanne sashe na jikinsa,muddin kuma yace zai tsaya cewa wani abu,a matsayinta na me aure na biyu dole zata fuskanci wani sauyi tattare dashi, wanda hakan mugun abun kunya kasawa da kuma gazawace a tattare dashi but yayi alqawarin zai saita mata bakinta da wasu dabi’u nata,bazai yarda da rashin girmamawa ba,she can live duk yadda taso,amma dole tasan girmansa.

Tsuka tayi ta murguda bakinta saboda baqincikin da ya cikata,batasan tsautsayin da ya sanyata barin qofarta a bude ba,bata taba kawowa wai zai shigo ba wannan shine dalili,amma dole daga wannan karon ta tabbatar bai sake shiga mata daki ba. Har tayi banza da ledojin daya shigo dasu,sai kuma taga duk abinda ta bari ya lalace zai shiga sahu ne na almubazzaranci.

Short note din data gani jikin wata
leda ya bata tabbacin babu abinda ya siya da kansa ko daya,dukka sagon maji ne.
Murmushi ya subuce mata,tana qaunar mata sosai har cikin ranta,sonta majin take da gaske har hakan baya iya boyuwa,ta miqe ta adana komai ta dawo ta rage kayan jikinta ta kwanta.
[15/09, 5:29 pm] Laila Abdulqadir: “HUGUMA*

•_TABARMAR KASHI_*

Book 02Page 13

Cikin nutsuwarsa ya gama komai na shirin bacci,saidai gaba days baccin ya gagara zuwa a idanunsa,ganin dazun yayi affecting tunaninsa sosai,abinda bai taba kawowa cikin ransa zai zama wani abu har haka ba. Da kansa ya buda qofar dakinsa ya wuce kitchen ya hada coffee ba tare daya bi takan abincin dake jere a dining ba,aikin jacob kenan, baya wasa da aikinsa,duk wata hidima da ake muddin yana qasar yana kuma gari baya fashin dafa masa abinci,ko a yanzun duk hidimar da akeyi cikin gidan part dinsa baisan anayi ba,shi yasa yakeji da jacob din shi da wanda yake tsaftace masa sashensa.basu da wasa sam a aikinsu

Dakinsa ya dawo,ya buda balcony
din dake manne dashi,duk da cewar dare ne amma bai damu da hakan ba,bacci kawai yake nemawa idanunsa tare da hutu da nutsuwar
ruhi da gangar jiki.

Kurba daya yayi masa kamar lokutan
baya ya ajjiye saman dan qaramin table din dake a gefansa,tun daga waccan ranar daya dandani taste din coffe dinta kowanne ya daina masa dadi a harshensa,saidai yasha Black tea Kawaltunda bava snan madara kwata kwata,ko ya gwada shan madaran da nufin ko zai yi masa irin taste din milk tea dinta
sai yaji gaba daya basu hada hanya ba.

Tafin hannayensa ya hada yana murzawa
guri guda da sauri da sauri,lokaci guda ya dakata yana furzar da iska daga bakinsa,dai dai lokacin da wayarsa tayi qara. Mamakin wanda zai kirashi a dai dai wannan lokacin da sha daya na dare tayi ya kamashi,ya qarasa inda ya aje wayar a hankali ya dauka yana duba me kiran,sai kuma kiran ya katse,sagon da ya gani da number sajjad yaja hankalinsa,yayi sliding ya bude wayar ya shiga saqon

_Duk wani nutsuwa farinciki walwala da kwanciyar hankali yana tattare da diya mace muddin ka dace,ka raya darenka na yau da kyau da soyayya da kawo jituwa da fahimtar juna tsakaninka da iyalinka,zaka fahimci inda maganata ta dosa_ tsaki yaja,sajjad yana bashi ciwon kai,baisan mata bane,amma yana da tabbacin zai dawo daga mararin gardin da yake ganin ya samu. Muddin diya macace tabbas wataran sai ta bashi madacin da zai maye gurbin zaqin zumar data lasa masa a harshensa,duk kuwa da cewa baya taba yiwa wani wannan fatan bare sajjad din da dadi wuya ko tsananin yana tsaye tare dashi.

Kira ne ya shigo wayar tasa lokacin da kwanyarsa ke shirin nutsawa duniyar tunani.
A nutse ya dauki wayar ba tare da tantama shakka ko mamakin kiran da akayi masan a dai dai wannan lokacin ba,saboda waya ce da dukka kiran da zai biyo ta cikinta ya tabbatar kira ne me muhimmanci da ya shafi duk wani makusanci a gareshi.

Cikin lallausar muryarsa da ta gara yin wani irin sanyi saboda yanayin da yakeji yana bibiyar kowace gaba ta jikinsa. Saidai a maimakon amsar sallamar,sai sautin kukanta cikin siriryar muryartan me matugar siranta qwaral ta maye gurbi. Wayar yadan cira yana duba number din ya tabbatar babu wanda zai kirashi da number wannan qasar sai mutum daya wato HASEENA

“Yaa toufeeq wai da gaske ne?,da gaske ne don Allah?, kayi aure?” Tambayar tata ta daure masa kai,meye manufar wannan tambayar? duk da ya jima zuciyarsa da hasashensa suna son kaishi gurin,amma sai ya jaddadawa kansa ba hakan bane,saboda sam baya fatan yarinyar ta jefa kanta shingen da bazata iya samun aminci ba a cikinsa

“Yaa toufeeq,wallahi bazan iya jurewa ba,yaa toufeeq kai na yiwa zuciya tanadi,dukka tsahon shekarun nan,mommy ce takeyimin burki” sai ta sake sakin kukan da yake nuna ciwone daga zuciyarta na gasken gaske yake motsawa. Mamaki gaba daya ya sanyashi kasa cewa komai, yarinyar da yake kallonta bata da maraba da nadeeya a gurinsa saboda rainonsu da hajiya qaraman tayi? ‚bugu da qari sam babu hira da tayi kamanceceniya da wannan a tsakaninsa da ita

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected