TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel

TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel

“Relax meenal,calm down” ya fada ta sigar lallashi,saboda gaba daya abun nata yana daukarsa ne kamar wani wasan kwaikwayo

“Ta yaya zan iya kwantar da hankalina yaa toufeeq,kasan yadda kake a zuciyata?”

“Are you okay?” Ya samu kansa da tambayarta kai tsaye wannan karon,saboda gaba daya mamaki ya gama cikashi

“I lost what i love most,i can’t keep calm”

“Kisha magani ki kwanta,Allah ya sawwaqe” ya fadi yana sauke wayar a nutse daga kunnensa. Kafin ya kashe yana iya jin yadda take kiran sunansa,ya sake kallon wayar yana sake tabbatarwa kansa kodai akwai abinda tasha,ko kuma lallai dole ya dauki tsattsauran mataki a kanta,muddin dai meenal zata ce tana sonsa,to ba shakka raini ya fara shiga tsakaninsu kenan saboda yadda yake treating nata like nadeeya.

Qarar shigowar tex ya sake sanyashi
waiwayawa ga wayar. Dukka saqon ya gama bayyana saman screen din, kasancewarsa gajeran sago bame tsayi ba
BARKA DA WARHAKA ANGON NANA
KHADIJA,KA MOREWA WANNAN DAREN
TARE D AMARYARKA,AMMA KA SANI
AMEESHA NA NAN DAWOWA CIKIN
RAYUWARKA,SABODA BA ZATA IYA BARWA WATA KAI BA HAVE A NICE NIGHT_ Samun kansa yayi da maimaita karanta saqon,a hankali a hankali wani abu me zafi yana taba zuciyarsa, emotions dinsa marasa dadi sunason motsawa,how and when ameesha ta samu wannan courage din da zata masa saqo haka kai tsaye?,saboda ya daga mata qafa? ya bata damar taje ta rayu ta tuba?. Har ya dauki wayarsa da zummar nusar da ita kuskurenta,sai kalmar

“La haula wala quwwata illa billahil aliyyul azeem” ta subuce daga harshensa. A hankali yaji yana komawa daidai dinsa,sai ya maida akalarsa zuwa blocking number tata,sannan ya goge saqon,ya jefa wayar a aljihunsa yana migewa daga gurin,yana ji a zuciyarsa bashi da lokacinta Sam,bama yanzu ba,har abada baya jin zata sake samun lokacinsa,bawai ita kadai ba,dukka wata diya mace ma idan ka debe jininsa dinnan daya zama lazim ya rayu dasu,yake kuma da yaqinin babu cutarwa a tsakaninsu har abada.

Cikin wani yanayi yake fita dag balcony din har ya riski lafiyayyen bedroom din nasa,cikin qanqanin lokaci ya gama shirin kwanciya,ya maida hasken dakin zuwa dim light,idanunsa na lumshe yana jin kewar rashi ganin fadeela saboda cinkoson gidan,yau din tun sassafe da ya fita yabar musu gidan,duk da sashen nasa baisan me cikin gidan ke ciki ba,amma sai yakejin kamar hayaniyar gidan a tsakiyar kansa take. Bacci yake da bugatar yi sosai,to amma yanayin da yake ciki ya tabbatar idan baiyi wasa ba zaici wuya ko ya dade a haka,wannan ya sanya yana daga kwancen ya miqa hannunsa ya jawo wata mp4 me siffar qwallo fara qal ya kunnata,take sautin karatun alqur ani me girma ya karade dakin da muryar sheik mahir almu’aiqaly,karatun ya fara saukar masa da nutsuwa sosai a zuciya ruhi dama gangar jikinsa,sannu a hankali baccin da bai taba zata ba yayi awon gaba dashi.

_sai muce asuba ta gari angon nana kadija_

**********A nutse ta ajiye wayarta data gama karatun qur’ani ta ciki saboda rashin hado mata da qur’aninta da ba’a yiba ta mige tana kallon agogon dake manne a bangon dakin daidai algiblar sallarta. Qarfe shida da mintuna talatin,tana da buqatar ruwan dumin da ta saba sha a kowacce safiya,bata qaunar fita sam sam saboda batason koda tsautsayi yasa su hadu dashi,duk da bata tunanin a dai dai wannan lokacin akwai wanda ya farka cikin gidan. A nutse ta ninke abun sallar tayi masa guri,sannan ta zura lausasan slippers din da suke set da kayan jikinta,wanda couple prayer set ne,ta zari nata ta saka. Blur black ne masu taushi,kala ce ta farare, don haka ta fidda hasken fatarta da kyau wani irin haske dake cakude da amarci da kuma zallar gyaran da tasha daga hannun me gyaran jikin da maii ta ajjiye mata.

Duk yadda taso dauke idanunta daga kallon yadda aka tsara hallway din hakan ya gagareta. Wani irin kyakkyawan tsari aka yiwa gurin wanda hatta weather da qamshin da yanayin iskar dake kai kawo a gurin na musamman ne. Fitilunsa na musamman, kamar yadda kome da akayi amfani dashi wajen qawata gurin ya zama favourite colour dinta ne,zaka rantse da Allah ita ta zauna ta rubuta yadda takeson a shirya komai din. Qafafunta na nutsewa sosai cikin
Tallausan carfet din da aka malale gun dashi har zuwa sanda ta sada kanta da falon.
Hallway din yafi burgeta, amma kuma yadda falon ya tsaru da wasu irin kujeru curtains da carfet carfet sai ta rasa wanne guri ne yafi wani?,nan dinma komai dake dake cikinsa zabin kalolinta ne,kamar tana gurin aka shirya komai. Duk qoqarinta da son ganin abun sam bai burgeta ba hakan ya faskara,ta dinga ratsa falon tana laluben inda kitchen yake,lallausan qamshi me kwantar da zukata yana yawo a hancinta har zuwa zuciyarta. Bata jima ba ta hangi hanyar da zata sadata da falon wanda ke daura da waje na musamman da aka tanada aka kuma qawatashi da dining na alfarma.

Bata fahimci da mutum a ciki ba saboda girman kitchen din har sai data kammala shiga

“Good morning madam” jacob daketa aikin
kintsa kitchen din don shirya abinci na
musamman da zai burge matar ogansa ya fadi
a ladabce.

Turus ta danyi tana dubansa, ya afron
da zungureriyar hular kansa kadai ta isa yi
mata bayanin waye shi,saidai duk da hakan
baiyi qasa a gwiwa ba wajen gabatar mata da
kansa

“‘Sunana Jacob,nine cook din sir,akwai wani
abu da kike bugata ne yanzu?” Mamaki ya
saukar mata,shi komai nasa ya banbanta dana
kowa?,ya kawo qatoton gardi kuma arne ya
ajjiye cikin gidansa yana dafa masa abinci
yana ci?, iyakacin zamanta a gidan ma bata
taba ganinsa ba,ko don ita din bata fiya zurfafa
kanta a lamuran da basu shafeta bane?. Ta
yaya zata zauna itakam wannan qaton yana
mata girki tana ci?.

“Bana buqatar komai, just warm water zan diba,and i can handle it” ta furta tana matsawa sashen da aka jere glass mug cikin tsafta da burgewa ta cire guda daya,ta taka a hankali ta isa ga dispenser ta debi ruwan. Saidai yayi mata zafi da yawa,batason kuma sirkashi, wannan ya sanya ta jingina bayanta da kitchen cabinet tana motsa ruwan a hankali,tana so ya rage zafi tasha tabar masa cup din a wajen.

Cikin kamewa tare da tarin nutsuwar
da sallar asuba ke haifarwa ga zuciya da ruhin kowanne musulmi yayi sallama a kitchen din. Wannan al’adarsa ce,yakan manta da cewa jacob ba musulmi bane,shima Jacob din tsabar sabo da hakan ya sanyashi ya koyi cikakkiyar amsa sallama.

Lallausar muryarsa da bacci yasa ta qara zama husky and deep voice ta ratsa kunnuwanta,idanunsa ya fara sauka a kanta,zagayayyar fuskarta dake tsakiyar hijabi tayi fayau da wani irin haske. Zare idanun nasa yayi daga kanta yaci gaba da takowa ciki a hankali, daura da ita ya tsaya shima yana daukar glass mug din ba tare daya sake duban sashen da take ba

“Good morning sir” jacob ya gaidashi cikin tsantsar girmama

“Morning Jacob”

“Kana bugatar wani abune sir?”

“Warm water” shima ya fadi a taqaice yana sake cirar spoon bayan mug din. Wani mugun kusa taji sunyi ita dashi, duk da kuwa akwai tazara a tsakaninsu,yadda ya ganta a jiya ke dawo mata fes cikin kanta,a hankali haushinsa ya soma sauka saman zuciyarta,tanason ta matsa daga gurin amma ta gaza,wani irin kwarjininsa da bata taba ji ba ya mamayeta. Ta lumshe ido tana kai cup din bakinta duk cikin son nuna bata ganshi a kitchen din ba gaba daya,gefe guda na zuciyarta yana mata bitar abinda afifa ta taba gaya mata

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected