TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel

TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel

“Idan kabar mata fadeela tayi winning a kanka” daga can tsakiyar zuciyarsa ake gaya masa,kamar an zaburar dashi ya dawo da baya ya dauki wayarsa yayi kiran number dr jarma.

Bugu biyu ya daga ya koma ya zauna sosai yana gaidashi cikin girmamawa. Kadaran kadaham ya amsa masa,cikin kamewar nan tasa yace

“Abba idan babu damuwa zan qarasa na dauki fadeela, kusan hutunsu nex week zai qare,ya kamata ta dawo ta shirya a nutsr kafin lokacin” gyara zamansa dr jarma yayi

“Eh to ai babu laifi.
..ummm… babu laifi,amma
idan kaje ka tano harda yarinyar khadijatu me kula da ita din kenan” hannunsa ya dunqule guri daya yana shigar da tafin hannunsa ciki

“Okay abba” ya fadi yana jin kamar dr jarma din yayi masa wata mummunar bushara

“Ka dauki saiiad kuma ku tafi tare” dr jarma ya gara fada,saboda yanason ya samu me masa monitoring abubuwa “In sha Allah” ya fada sanann ya gimtse wayar.

Iska me zafi ya furzar daga bakinsa zuciyarsa na sake soyewa da bacin rai da kuma damuwa,dr yana girmamawa al’amuranta da yawa,ya bata wani matsayi me girma,ya bata kuma yarda dari bisa dari

“Ya Allah, ya rabb,kada ka sanya yarinyar nan ta zame mana sharri cikii rayuwarmu,dukka abinda ya qulla ya Allah ga wargazashi” ya samu kansa da furtawa.

Lokaci ya duba yaga akwai sauran lokaci da zai isheshi yaje ya dawo,sai ya fada toilet ba tare da ya kira sajjad ba,nufinsa idan ya gama shiryawa sai ya kirashi,idan yace baya cikin gidan shikenan sai yayi tafiyarsa,ya tabbatar aikin Sanya Ido zaije yayi,shi kuwa sam sam bazai iya wani tsaiwa lallabata ko neman alfarma daga gareta ba.

Tsaf ya shirya cikin kamala da wani ajiyayyen kyau da kwarininsa cikin wani lallausan vadin boyel me garancin kauri,fari ne qal kamar yadda kake iya hango fara tas din singlet dinsa daga ciki,rufaffen takalmi ya saka charcoal color na kamfanin Stuart Weizmann me asalin kvau da tsada. Kansa sai dake dauke sassalkar sumar daya gada daga bangare biyu,dr girema asalin shuwa dan qasar borno,da kuma maji balarabiyar
Algeria ta kwanta luf saman kansa tana sheqi da fidda tattausan qamshi. Lafiyayyar fatarsa yake daurawa agogo,dai dai lokacin sajjad ya tura gofar ya shigo sanye da wata abaya ta maza,da alama yana cikin gidan yana hutawa,idanunsa akan TOUFEEQ da yayi wani mugun kyau

“Yanzu nake shirin kiranka ka fito zaka yimin
rakiya”

“Amma dai my man…..
.Wannan kwalliyar
zance zakaje?” Ya jefa masa tambayar cikin shakku. Kyawawan fararen idanunsa ya dago ya watsa masa,bayan ya dakata daga sanya agogon,wani abu yayi masa tsaye a wuya,kamar zaiyi magana sai ya maida bakinsa ya rufe yaci gaba da daura agogonsa,don yiwa sajjad magana ma bata bakine,kome zai fada bazai fasa jansa da magana ba,kuma gobe sai ya qara. Shi kuma a yadda yanzun yakejin zuciyarsa ko doguwar magana bayason yi. Gaban dressing table dinsa ya qarasa,ya dauki turarukansa ya fara feshe jikinsa daga wuyansa zuwa qirji,sannan ya sauya wani ya feshe sauran sassan jikinsa dashi,ya ciri key din mota guda daya daga inda yake ajiyesu yayi gaba yana fadin

“Kada ka wuce minti uku,ina parking lot” ya garasa fita ba tare daya waiwayoshi ba.
Qaramar dariya sajjad ya saki yana dan buga qafansa, already yasan da fitar,tuni Dr ya sanar masa,amma baisan da wurwuri haka zasuje ba

“Ko second daya ka bani sai fa na rakaka” yayi zancan shi daya,sai ya juya ya fita daga dakin.bava iin zai canza komai a jikinsa,don dakin,baya jin zai canza komal a jikinsa,don haka takalmi kawai ya sanya ya biyo bayanshi.
[11/09, 3:42 pm] Mimah Yusuf: *HUGUMA*

* TABARMAR KASHI_*

Book 02 Page 04

Sosai take zaune gaban dr girema gafafunta a tanqwashe kamar zata maidasu cikinta,ko cikakken motso batayi tun zamanta a wajen

“Sati guda suka rage miki,har yanzu bazan hanaki damarki ba,ki bawa Mahmud dama,ko kuma ki gabatar da wanda kikeso ban hanaki ba,bance lallai sai mahmud ba,shikenan maganar,kina iya tafiya” kamar qafafunta ba zasu iya daukar gangar jikinta ba haka ta miqe tana hada hanya,tun jiya kanta yake mata ciwo kadan kadan tunda taji abban nata yana nemanta,ta sani dama tatsuniyar gizo ba zata wuce ta qoqi ba. Sannu sannu takai kanta daki,Allah yasa yau din afifa ta dauki fadeela sun fita yawonsu,itama meson fita guraren shan iska ne kaman afifa,sai biyu ta hadu sukayi tafiyarsu suka barta.

Ba irin saqe saqen da zuciyarta
batayi mata ba a sanda take kwance saman gadon,tana hasaso yadda yau za’a daura mata igiyar wani,wanda dukka wani nauyi nasa da haqgin aure zai rataya a wuyanta,duk wata kebantacciyar mu alama ta maaurata zata hadasu?, Saita runtse idanunta gabanta na tsananta faduwa. Bata shiryawa wannan al’amarin ba sam cikin rayuwarta,ta sake mallakawa wani namiji zuciyarta da gangar jikinta?,wani abu ne me wahala da ko cikin mafarki batason ganinsa bare a zahiri. Kuka takeson yi amma a yau din zuciyarta gaba daya ta ida qeqashewa,sai faman zafi da radadi da zuciyar keyi.

Baaba rabi ce ta shigo dauke da wayarta data wuce ta bari a falo

“Alhaji yana kiranki” tana daga kwancen ba tare data cire kanta daga cikin duvet ba ta miga hannu ta karba wayar ta kara a kunnenta

“Kina ina?” Dr girema ya tambayeta

“Ina dakina”

“To yayi,ki duba nan veranda dake baya kina da bago” wayar ta saki ta sulale cikin duvet din. Wai me yasa mahmud bazai haqura ya sakar mata mara tayi fitsari ba? yafison suvi zama mara alfanu?,zaman da ba zai qaru da ita da komai ba?,tabbas yau zata sake jaddada masa da babbar murya,don bata shirya wani rayuwar aure da kowa ba,dole idan abba yaga ya janye kuma bata kawo kowa ba ya haqura ya ayaleta. Da wannan qudurin ta sauko daga saman gadon cikin bacin rai,Adire boubou ce a jikinta,saita yafa mayafinta zalla saman kanta ba tare data nema babban mayafi ba ta zura takalmanta ta fice.

Tun bata qarasa ba jikinta taji yana bata ba mahmud bane,to amma idan ba mahmud bane waye zaizo har cikin gidansu nemanta?,tanason ganin fuskarsa amma babu dama saboda ya bada baya,sai lallausan gamshinsa daya karade ilahirin gurin har ya bazu zuwa wasu sass na gidan,da kuma cikakkiyar baqar sumarsa dake kashe ido, kasancewar bai sanya hula ba.

Tsaye tayi daga bayansa nesa kadan dashi,yaji alamun takun tafiyarta,tsaiwarta ta sanyashi waiwayowa,lokaci guda idanunsu suka gauraya cikin na juna. Baya ta dania da sauri saboda juyowar da yayi sai taga kamar ya cika wajen,kamar kuma ya sake rage tazarar dake tsakaninsu ne. Ta lumshe idanunta tana jin faduwar da gabanta yayi wanda har yanzu bugun zuciyarta bai koma dai dai ba,yayin da tasa zuciyar yaji ta danyi shacking saboda yadda lallausar sumar kanta ta fito sosai saboda janyewar da siririn mayafin kanta yayi ya koma rabin kanta,sajen dake kwance gefen kunnuwanta shima ya fito sosai,sai bagin gashin ya zama ado ga kyakkyawar farar fuskarta. Kwashe idanunsa daga kanta ya maida gefe yana jan qaramin tsaki wani bacin rai vana sake taso masa. Tayi nufin juyawa ta barshi a nan,sai taga idan tayi hakan zaiyi tsammanin tsoronsa ko shakkarsa takeyi don haka ta gyara tsaiwarta tana harde hannuwanta a girjinta,abinda ya baiwa tudun girjinta damar fita sosai ba tare da tasan hakan zata faru ba

“Lafiya kake nema na?” Tayi masa tambayar kanta tsaye da siriryar muryartan nan dake cike da tsiwa. Lokacin daya waiwayo ya kalleta sai da taji dukka wani qarfi da qafafunta ke dauke dashi yana raguwa,tsakiyar idanunta yake kalla sannan yace

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected