TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel

TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel

“Germany ne maji,bonn, amma don Allah mai, inason nayi wannan aikin da kudina ne, ko da duk abinda nake dashi zai qare, ina kwadayin ladan” kai ta gyada

“Bansan wanne lokaci zaya daukeni kafin na samu visa
din can ba,tunda ban taba shiga ba,amma zanyi iyakar
bakin goqari na,ina matuqar alfahari da wanzuwarki cikin ahalina khadijatu,banzan kuma da kalar bakin da zan miki godiya ba”.

Hirarsu da maji a ranar ta maqale mata a wuya,ta yini
tana juya abinda suka tattauna da ita. Yau gaba daya sai ta kasa fita a sashen,saidai duk wani motsi idan akayi cikin gidan yana kan kunnenta,sai ta dinga jin taron data baiwa fadeela a baya ma kamar yayi kadan, kamar hajiya qarama zata iya yin wani motsi don ta cutar da fadeela,don haka a idanunta da kunnuwanta motarsu ta shigo gidan,cikin motar toufeeq jarma wanda a yanzun ya zamana vadda suke fita tare tare suke dawowa.

Labulen ta sauke tana sakin ajiyar zuciya sanda ta tabbatar sune tanason taje ta tari fadeelan amman kuma tasan suna tare ne da toufeeq. Har yanzu wani matsanancin kunya ce take lullubeta idan ta tuna abubuwan da suka faru a dazun,wuni tayi abin yana dawo mata tana mamakin kanta na vadda ya sanyata ta saki layi haka lokaci daya, sai ta juya a nutse ta koma kitchen din,ranar farko da zata girka wani cikakken abinci a ciki.

Yadda jilkinta vake a sanyaye yau tasan ba lallai ta gama abinci da wuri don haka tun bata dora ba ta fara yiwa fadeela pancakes da smoothie ta ajiye mata,sai fura data dama daban Incase ko batason smoothie din.

Tana aikin yayyanka vegetables amma hankalinta yana cikin gidan. Tana jin lokacin da suka bude gofar suka shigo,fadeela ta rada mata kira da kyau. Tanason ta amsa amma idan ta tuna da toufeeq na gurin sai ta kasa. Har zuwa sanda fadeela ta kalleshi

“Abby,ko anty N na wajen baaba ramatu?” Kafada ya maqale yana murmushi tare da dan tabe baki

“Muje na rakaki ki gani” ya fadi can qasan ransa yana jin zumudin ganinta.

Sallamar yarinyar cikin kitchen din ya sanyata sakin abinda takeyi tana amsawa ba tare data juyo ba

“Anty,yau bakiyi welcoming dina ba” fadeelan ta fada tana togewa daga bakin qofar gami da qin qarasowa ciki.

Qaramin murmushi ya saki yana jin farinciki na saukar masa a zuciyar ,kamar fadeela tasan muradinsa a yanzun na kallon qwayar idanun säahar din,wanda ya tabbatar ko zai narke a banza ba zata bari ya gani ba.
Gyara tsaiwarsa yayi sosai yana sake zube idanunsa a kanta,tana sanye da high tummy skirt na yadin chiffon wanda aka yiwa qananun tattara ainun,hakan ya santa qugunta fita das a jikina,ya kuma fitar da shape dinta.
Rigar jikinta ta plain chiffon din ce wadda ta dace da skirt din jikinta, gashinta na nannade a boye cikin dankwalin kayan. Idanunsa ya lumshe yana fitar da iska tun daga hunhunsa,hancinsa na dawo masa da sassanyan qamshin gashinta wanda yake jinsa kamar yanzun yake nutsa kansa cikin sumar sa. Tana takowa idanunsa nakan lips dinta,baya gajiya dasu sam, akwai sirri me yawa da wani irin softness samansu

“‘Faddee rigima” ta furta a hankali, abinda ya bawa lips din nata damar motsawa da juyawa a hankali, wannan ya sanyashi sake fidda wata iska me nauyi ta hancinsa.

Duqawa tayi tana karbar lunch bag da school bag din
fadeelan

“Sannu da zuwa” ta fadi ba tare data dubi sashen da
yake ba. Banza yayi da ita kamar baiji ba

“Sannu da zuwa” ta sake fada still da yanayin dazu,sai a sannan ya saki hannayensa yana dan waiwayawa,kamar me neman da wanda take magana

“Da wa kike?” Yayi mata tambayar da ta sanyata daga
kanta zuwa gareshi cikin mamaki, don dai ita bataga
kowa a kitchen din ba saishi da ita sai kuma fadeela

“My angel, karba kayanki ki qarasa dasu daki,oya” ya fadi yana duban fadeelan. Bata musa ba ta miga hannu ta karba komai nata da sãahar din ta cire, ta kuma fella da gudu ta fice ta barsu a tsaye.

Da kallo säahar tab fadeela duk data qule, gabanta na
faduwa kadan kadan,tana tsoron kada ya zamana wata muguntar ya sake hada mata,har yanzu bata warke daga mikin jiya ba. Bata gama tunanin ba kuwa tattausan gamshinsa ya ya soma ratsata qofofin hancinsa,ta daga idanunta ta kalleshi, karon farko da yaga karaya da tsoro a cikinsu. Taku ta fara yi da baya yana biye da ita,cikin zafin nama ya sanya hannu ya rigo qugunta ya tsaidasu cak shi da ita tsakiyar kitchen din yana jifanta da wani shu’umin kallo da narkakkun idanunsa
*HUGUMA*

*_TABARMAR KASHI*

Book 02Page 45

“Na dawo daga office a gajiye, ina jin yunwa,inaso nayi wanka,amma duk baki lura ba, sai kawai ki bini da wata sannu da zuwanki me kama da bada umarni umarni?” Ya qarashe maganar yana lashe lips dinsa,hankalinsa na fusga akan nata lips din zuwa qirjinta da yaketa son rudar masa da tunani, rigar jikinta din doguwace sakakkiya,amma duk da haka akwai wata tattara a qirjinta data sake yiwa halittunta mazauni da kyau. Sake fincikota yayi sosai zuwa cikin jikinsa yana ci gaba da ifanta da wani narkakken kallo cikin qwayar idonsa

“You know what?” Ya fada yana hadiye yawu,ba tare da ya jira amsarta ba ya bata amsa yana sake jawota cikin jikinsa da kyau

“I swear i straight up forget my name for a second duk
sanda na kalli wadannan qwayar idanun” ya qarasa fada yana sanya yatsarsa tare da yi mata yawo dasu softly saman idanun nata, abinda ya tilasta mata lumshesu, tana jin tsigar jikinta na neman fara tashi

“Hold me so close for some minutes your breath already become my oxygen” ya fada yana kama hannuwanta ya kuma sanyata ta zagaye bayansa da su,sannan ya kama fuskarta a tausashe ya rige suna musayar numfashi me dumi dake fita daga hancin kowannensu.

Qafafunta ne suka fara rawa, ta fara gogarin zamewa,bai hanata ba ya barta ta janye,saidai bai barta ta matsa duka daga jikinsa ba ya rige hannunta

“Wannan shine kalan gaisuwar da nakeso bayan na dawo a office,zan shiga nayi wanka, kafin na fito please i want something to eat….am starving” tuntuni ta juya masa baya,a haka ta gyada masa kai tana addu’ar ya fita a kitchen din, tana tunanin zai fitanne tunda ya gama abinda ya kawoshi saita tsinci muryarsa cikin karyar da murva a shagwabe

“Please,my lips are so lonely one kiss please” har cikin bargonta taji tasirin muryar tasa. Qarasa rudata yayi,har spoon din hannunta na faduwa qasa,ya tsugunna ya dauka yana miga mata

“Matsiyaciya” ya fadi yana sakin wani tattausan murmushi hadi da soma takawa a nutse yana fita a kitchen din.

Bayan ta tabbatar ya fita din sai data samu guri ta zauna saboda ta daidaita bugun zuciyarta,idonta ta lumshe tana mamakin yadda yake yawan sanyata faduwar gaba da rudewa, abinda a baya Sam ba dabi’arta bane?.

Komai ta zubawa fadeelan har furar ma tace tanaso, sanann ta dawo ta shirya masa nasa saman wani kyakkyawan tray bisa tsari,sai taji kaman ta aikata fadeelan takai masa,amma kuma tunda ya fuskanci ya zama dan garari me neman dalili galilan ya moreta son ranshi,sai ta haqura ta zura hijabinta ta dauki tray din ta wuce dakin nasa tabar fadeela na kallo a parlor.

A nutse ta bude bedroom din ta shiga gamshin da yake fitarwa da sanyi suka buso mata,first night dinta da tayi da ranar Allah shi ya fara dawo mata fes a kai,ta dauke kai daga kan bed din ta soma takawa da gaggawa,tanason ajiye masa ta fice kafin yakai ga fitowa daga toilet din da take jiyo qarar ruwa. Har ta kusa isa qofar fita ya bude qofar bandakin ya fito

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected