TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel
******Bai taba kawowa zata dauki wadan nan kwanakin ba tare data nemeshi ba,cikin kwanakin gaba daya karsashi da komai nasa ya ragu,yana jin kamar yayi missing wani part na jikinsa, komai yana yinsa ne kawai cikin qarfin hali da juriya,bai taba kawowa cewa ta kama zuciya da rayuwarsa har haka ba sai a wannan lokacin
“Wanann wanne irin abu ne?” Ya tambayi kansa da kansa a wani dare da bacci ya qauracewa idanunsa. A nutse ya miqe ya sauka daga saman gadon nasa,yana sanye da wasu silk pyjama bagaqe da suka fitar da zallar kyansa cikin hasken dakin da bashi da yawa,yana bugatar wani abu da zai debe masa kewarta,yana jinsa kamar mara lafiya, kowanne sashe na jikinsa yana bugatarta. Slippers dinsa ya zura,ya miqa hannu zai dauki wayarsa dake kan bedside drawer sai wanilabu yaja hankalinsa. A nutse ya miqa hannu cikin wani glass bowl dan garami ya dauko wani abu. Dan kunnenta ne,dan kunnen da ya fadi a wancan ranar cikin elevator,a wancan lokacin da yake matuqar jin zafi da haushinta, zafin da ya tabbatar yana jinsa ne a sannan saboda yadda zuciyarsa ta kasa jin qinta a ransa kamar vadda yakejin na sauran mata,yana tsoron faruwar wani abu tunda har zuciyarsa ta kasa jin wannan emotion din a kanta sai wani feeling na daban. Wannan abun dai da yake gudun faruwarsa sai gashi a yanzu ya tsinci kansa dumu dumu a cikinsa, dumu dumu din da ko gefenta bai taba isa ba sai a wannan lokaci, mummunan kamu na soyayya me wahalar cirewa a rai, soyayyar da ya fuskanci tamkar tanason jefashi zuwa ga son maso wani. Yana shaugi da burin ganin martani me zafi daga kan fuskarta,duk da ya sanya zuciyarta tayi laushi yadda ya kamata, amma mizanin soyayyarsa a zuciyarta yana hasashen kamar bai kai ba,yana tsoro da fargabar sake, afkawa wani ramin da baisan iyakacin zarfinsa ba a kanta. A kullum ya tuna kulawa da tattalin da ya bawa ameesha da sakamakon da ya samu daga baya sai gwiwarsa ta karye akan lamarin soyayya. Kissing na earring din yayi, sannan yasa hannu ya jawo drawer din ya zura,baikai ga rufewa ba dairy dinta daya dauko yaja hankalinsa.
Qasan ransa ya gayawa kansa ya samu abun debe kewa,sai ya fiddoshi yana budewa,ya sake bude page din farko ya maimaita rubutub rannan, sai ya zare slipper din da ya sanya ya maida jikinsa kan gadon ya zauna sosai vana sake bude next page.
Kai tsaye a kuma tsanake ya fara bin rubutun dake shinfide cikin tsari da kuma qwarewa, tun daga farkon haduwarta da ADAM,a nan ya dinga gaza jure wasu abubuwan ya dinga jin wani abu me kama da zallar kishi yana tabashi saidai zuwa sanda zai kammala karanta labarin zuciyarsa da ma gangar jikinsa sunyi tubus
_Thats me,hurt in private, heal in silence,we fall, we learn we rise_
_My dear heart,one day you will heal to such an extent that you will smile as if it was never broken in sha Allah_
“In sha Allah” din shima ya maimaita a bayyane yana rufe bangon qarshe na littafin,fararen zagayayyu idanun nan nasa sun canza launi, kwanyarsa ta cika da abubuwa masu tarin yawa,ya mots lips dinsa a hankali
“We are all hurting and healing in silence, tabbas we go through one similar condition, i have made many errors in my life,but loving you is definitely the thing i have done right!” Ya furtawa kansa da kansa yana lumshe nasa idanun,tashi madubin rayuwar na haska masa,cikin jiki da zuciyarsa wani irin gamammen aminci da kanta yana gauraye jinin jikinsa, da gaske! Allah yaso wanke musu kowanne bacin rai da suka shiga,shi yasa ya jarrabesu a mabanbantan gurare da kuma mabanbantan mutane. Hikimarsa!, Ya hadasu zaman tare na har abada a sannan shine zasu Fi fahimtar muhimmancin funansu
“Exactly!” Ya fada yana bude idanun nasa. He really missed her,yana jin kamar zai zauce da son ganinta, me yasa tun tuni bai karanta diary din ba? ‚sai yanzu da tayi nesa dashi.
Saman gadon ya zauna sosai yana duba number dinta, saidai duka kiran da zaiyi matan a kashe layin,ya sani dama ba samunta zaiyi ba,kawai idanunsa sun rufe ne da son jin muryarta.
“A ina zai samu number dinta?” Itace tambayar dake masa yawo akai. Har zai kira nadeeya ya tambayeta sai kuma ya fasa gudun raini. Maji ya tuna, don haka ya maida akalar kiran nasa gareta, KARON FARKO da wani qulli ya warware daga tsakiyar kansa ba tare da ya sani ba. A dai dai lokacin kuma hajiya qarama tayi wata mummunar firgita cikin baccinta,ta kuma miqe ta zauna sosai saman gadonta a gigice tana dube dube.
Fadeela ta gani cikin asibiti, asibitin ya cika da yan uwa da abokan arzigi wai ana tayata murna ta warke daga ciwonta,yarinyar tana ganinta ta karbi wuga daga hannun säahar dake yanka mata fruit tayo kanta da gudu, tana tsaka da gudun ta farka a mafarkin.
Jikinta sharkaf da gumi ta sauka daga gadon,ko ina na jikinta rawa yakeyi tanason ta fassarawa kanta da kanta mafarkin. Kai tsaye ta isa drawer din data killace magungunan da take sauyawa fadeelan dasu,ta fiddosu gaba daya ta fito falonta dasu.
Zaman dirshan tayi saman carfet ta zazzagesu,ta kuma hau irgasu daya bayan daya tsaf har ta gama
“Turqashi” ta fada a bayyane tana goge gumin fuskarta.
Yau kwana d’ai d’ai har kwana sittin bata samu damar bawa fadeela maganin ba
“Ko warkewar ne ma a gaske ai sai tayi, tunda na zauna yarinya qarama tana son firgitani da kawomin tsaiko akan aiki na” ta fada a fili kamar wadda ke magana da wani.
Tattara magungunan tayi ta maida cikin leda tana rayawa a ranta yanzun nan komai duhun dare sai ta isa dakin fadeela ta aiwatar da shirinta.
Daxu daxu ta dawo daga Cotonou order din wasu atamfofi,bata da masaniyar ma fadeelan basa gidan yadda ta saba ba,sai kawai ta sauka a sashenta tana huce gajiya.
Mayafi ta yafa,ta kuma taka a hankali ta fita a sashen nata. Farfajiyar gidan tsit take,babu kowa sai hasken fitilu da kuma kukan qananun qwarika dake cikin tsirran dake baibaye da gidan.
Babu tsoro ko fargaba ta sanya spare key ta bude qofar falon ta kuma saka kai cikin takatsantsan. Bata tsava a ko ina ba sai dakin fadeelan, ta tura ta shiga ta sauke ajiyar zuciya ganin babu kowa,ranta ya bata yau a sassan toufeeq din zasu kwana kenan, don tana lissafe da duk sanda basu kwana a nan din ba suna sashensa
“Bagar matsiyaciya,kin kusa fita daga rayuwata, kin kusa barin gidan nan,gidan nan gidan meenal ne, toufeeq da abinda ya mallaka dama wanda ubansa ya mallaka duka na meenal ne da abinda zata haifa” ta sake fadi a fili cikin sumbatun da batasan tana yi ba.
Zafafa biyar
[04/10, 8:52 am] Mimah Yusuf: *HUGUMA*
* TABARMAR KASHI *
Book 02Page 48
Loko da saqo na dakin ta dinga bincikawa tana neman robar maganin fadeelan,sai data gaji sannan ta samu nasarar ganota. Saman gadon fadeelan ta zazzage maganin duka,ta lissafa wasu ta kwashe,ta debo iya wannan adadin ta zuba ta cakuda su da kyau sannan ta maidata kamar yadda take ta ajjiye, ranta fes, zuciyarta na mata dadi. Har abada ba zata taba bari maji ta huta completely ba,babu wata hanya mafi sauqi da zata ci gaba da razana rayuwarta irin wannan hanya,kafin zuwan lokacin da. zata maidata marainiyar da bayan rasa uwa da uba,yaya da jikokinma suyi ma rayuwarta sallama su barta ta rayu cikin maraicinta na haqiqa,ledarta ta dauke ta juya tana fita a dakin cikin nutsuwar da sai a yanzu ta sameta.