TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel
“Aure yana da wata irin daraja,yana garawa namiji kwarjini a idanun macen daya aura din albarkacin wanann igiyoyin guda uku, kibi a sannu bestie, toufeeq ba irin kalar mazan kike kalla bane ba irin adam bane,yadda banbaci da tazara yake a bayyane muraran tsakanin sama da qasa,haka yake tsakanin adamu da toufeed” a lokacin tsaki taja,akwai abinda take son saurara amma gaba daya afifa ta hanata sakat,motsi kadan ta fara mata wa’azin aure
“Kina tsammanin don kawai ya biya sadakina sai yayimin kwarjini afifa?”
“Bestie” bata barta ta gama magana ta dakatar da ita
“Bestie, idan akwai mutumin da ya cancani a duniva nayi masa kara na aureshi ma to mahmud ne,amma saboda har yanzun zucivata bataii akwai wani amintaccen namiji a duniya ba na gwammace na kawoshi,izzarsa dagawa da tsantsar jin kansa ba zasu taba razanani ba,zai kuma ci gaba da tabbata ne a mijin AUREN MANUFA, yayi rayuwarsa nima nayi irin rayuwar da nakeso” a lokacin murmushi afifa tayi ta miqe tana cewa
“Ba zaki gane ba”
“Ke kai ba zaki taba ganewa ba”.
[16/09, 7:18 pm] +234 703 451 7171: *HUGUMA*
* TABARMAR KASHI_*
Book 02 Page 16
Ko a fuska ba zaka taba zaton karantar tata yake ba,har zuwa lokacin da maji ta magantu
“‘Ki saki ilkinki dani khadijatu,ina jinki ne tamkar moha da nadeeya,ke yanzun diyata ce halak malak,zan iya raba kowacce damuwa tawa da sirrina dake” garamin murmushi ta saki tana jinjina kai. Tabe baki yayi kadan yana matsawa gefe daga gaban kwanukan alamar ya qoshi,duk wadan nan abubuwan gani yakeyi kawai salo ne irin na mata wanda kaidinsu ba qarami bane,sai yanzu ya karanci dalilin da ya sanya dukkansu ta tafi da hankalinsu,cikin ransa yake gulmarta,ta wani sadda kai qasa,tamkar ba itace wannan mara kunyar ba me shegen tsiwa dake iya yarfa masa maganar da duk duniya ba macen data isa ta gaya masa bayan maji
“Ban baku kowacce gudunmawa ba ko?” Maji ta fada tana murmushi,a nutse toufeeq ya waiwaya ya dubeta
“Wacce iri maji?”
“Ta aurenku mana” kasa cewa komai yayi,don baisan wacce gudunmawa kuma maji keson bayarwa ba bayan dukka abinda tayi da uwar kudaden data kashe,tamkar zaiyi auren fari ne ko kuma auren autarta nadeeya takeyi. Wani envelope ta ciro ta ajjiye a tsakaninsu
“Maldives, turkey Malaysia,su sajjad ya zaba muku as Honey moon destination” bashi
daya ba,hatta da sãahar sai da taji gabanta
ya fadi,yayin da toufeeq din yaji abun gazo
masa a mugun ba zata,yayi imanin akwai
gudunmawar sajjad a zancan,tunda yafi
kowa sanin abinda ke gabansu,duka duka
da niyyar yij sati hudu kacal wato wata guda
yazo,amma gaddarar da baisan da faruwarta
ba ta rigeshi har yayi watanni biyu. Bayajin zai
iyayin wannan tafiyar da yarinyar,ya dauketa
duk inda suka shiga suna tare idanuwa a
kansu,dauriyarsa ta qare don haka a tausashe
.ya hada envelope din da hannun maji ya riqe
cikin nasa hannun
“Indai bakiyi booking ba sannan baki biya
kudaden ba ki zaremu a ciki please maji,na
tara ayyuka da yawa da suke jirana,inason na
idasu cikin watan nan” idanu ta sanya masa
sosai tana kallonsa tare da gasgata zarginta
“Moha,sabon aure fa kayi,akwai Cabinda
yakai iyalinka muhimmanci?” Kai ya girgiza a
tausashe
“Ba haka nake nufi ba maji,koma inane kikeso taje din zata je,amma a yimin uzuri na kammala ayyukan gaba na,zan biya da kudina na kaita ko ina ne ma indai yawo ne,amma kinga tun yanzun bai kamata nabar ayyukana na tafi ba” ran sãahar ya dan sosu,indai yawo ne wato gata shanshani wadda bata taba hawa jirgi ba.
“Shikenan,amma wannan tafiyar bata soku ba,koma wanne aiki ne ka kammalashi nan da watanni biyu kacal zaku tafin, daga nan inason ku sauka a Algeria”
“In sha Allah” ya fada yana lumshe idanu yana jin nutsuwa na saukar masa ta yadda yayi nasarar soke tafiyar ba tare da wani dogon turanci ba,yasan ya taki sa’a ne kawai,amma maji har yau tana nan a yadda ya santa tun yana da gananun shekaru.
A nutse ya bude fararen idanun nasa,baisan yadda akayi ba suka sauka saman fuskarta.
Tsaf ta gama fahimtar manufarsa ta soke tafiyar,koda baiyi hakan ba ita sai tasan yadda ta bulowa maganar ta rushe,don ko dogon zama ba zata iya yi dashi ba bare doguwar tafiya ta satittika,idan kowa baisan me ya dawo da ita gidan ba,ita da shi duka sai sun sani. Cikin jikinta tai idanun nasa saman fuskarta,wani abu ne da ita kanta batasan ta yadda yake faruwa ba,a duk sanda yake kallonta sai taji a jikinta,tun haduwarsu ta farko. Nata kewayayyun idanun masu cikar eye lashes ta daga,sai suka hadu guri daya da nasa,sai ya basar yana shirin kau da kallonsa,saidai kuma hararar data watsa masa ya sanyashi kasa aiwatar da hakan. Take ransa ya sosu,mamaki kuma ya cikashi. Ita ba abinda ta iya daga tsaki sai harara?,me yasa ta maidashi kamar sa’anta,da gaske dai ya fuskanci sai yayi maganinta ya saita zamanta.
Tarko ya sanya mata da idanun nasa,saidai tunda ta harareshin bata sake waiwayowa sashensa ba,hasalima ta maida hankalinta kan maji dake magana da ita qasa qasa.
Migewa yayi cikin nutsuwar nan tasa yana ware hannun rigarsa da nufin fita yabar musu dakin,saboda yadda maji din ke magana da ita kamae bataso yaji ne. knocking qofar akayi,maji dake gab da säahar wadda kanta ke a sunkuye tace
“A shigo” A hankali aka murda handle din gofar aka turo aka shigo tare da sallama.
Ba maji kawai ba,hatta toufeeq yayi mamaki qwarai da ganin mahaifinsa dr mahmud kai tsaye cikin dakin. Tsakanin toufeeq da sãahar ne kadai aka amsa sallamar banda maji da ta dauke kanta gefe kamar bata ga shigowarsa ba,ta kuma tsuke fuskarta,wannan kyakkyawan murmushin dake saman fuskarta ya bace bat. Sanye yake da wani irin yadin cashmere da aka yiwa dinkin manya,riga da wando ‘yar ciki me dogon hannu,sai wata a sama kamar gown ta maza me gajeran hannu
Tun daga rigar cikin wandon da kuma gown din aikin hannu na sarauta aka zauna aka zuba masa me matugar daukan hankali da masifar tsada,saman kansa hular dara ce maroon color. Ya sake fitowa sak mahmud din data sani shekarun baya da suka shude,matashin saurayin da ya zuba tashen kyau da farinjinin
‘yammata wanda take da imanin a yanzu shi toufeeq ya debo,abu daya ya dakushe wannan a wancan lokacin,akwai wadatar kunya me tarin yawa ga ‘yammatan wancan qarnin ba kamar yanzu ba.
Gurin zama toufeeq ke gyara masa,amma dukka idanunsa da hankalinsa suna kan majin,wadda ita dinma babu abinda ya sauya daga gareta tsahon shekaru ashirin da bakwai da suka shude sai shekaru kawai da suka dan nuna kansu kadan.
* HAJIVA OARAMA_*
Tunda gari ya waye bata zauna ba,sai data tabbatar an kammala shirya breakfast na alfarma a babban dining din dake sassanta,bayan an kimtsa ko ina ta tabbatar komai yayi yadda ya kamata sannan ta shiga wanka ta shirya kanta cikin wani Swarovski lace dake ta fidda walwalin Swarovski crystal dake manne a kowanne pattern na lace din.
Ta riga ta sani ma,koda bata fadi ba kamar wancan auren nasa,a nan zasuyi breakfast shida matarsa kafin ya shiga kowanne sashe na gidan,don haka ta shirya ta koma falo ta dauki wayarta tare da saka me aikinta ta canza mata channel tanata dakon shigowarsu. Tun tana chart a wayarta don rage lokaci har ta gama lissafe lissafenta ta maida hankalinta ga tv tana dan bibiyar program din da akeyi din.
Sannu sannu ta fahimci lokaci yana tafiya,ta duba wayarta ko zata ga kiran toufeeq amma babu komai,mamaki yadan kamata,to me yake faruwa? aure dai ba na soyayya bane bare tace itace ta hanasu fitowa. Zuciyarta nata yi mata kokwanto ko yana wajen uwarshi?to amma batajin hakan zata faru,saboda sam babu wannan sabon a tsakaninsu,hasalima yaushe rabonsa da ita da har zai iya wuceta ita ya tafi gurinta? har ta dauki wayar zata kira taji alamun bude gate din gidan,dai dai shigowar ‘yar aikinta,sai ta maida dubanta kanta