TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel
* BAYAN SHEKARA BIYU_*
Ana murna bago ya tafi ashe bago yana bayan gari,shekarar fauziyya biyu da aurenta da diyarta daya
HASEENA MEENAL arziqin Mahmud ya fara dawowa yadda ya kamata. A take shaidan yayi mata kururuwa,taji sam zaman gidan YA’AQOUB bai dace da ita ba, hakan kamar ta tauyi rayuwarta ne,ta kuma barwa wata dan uwanta tana cin arziqin da daga ita har mahaifiyarta basu cishi ba,duk da babu abinda Mahmud ya rageta. dashi,komai ya samu tana ciki kuma taba da kaso a ciki.
Dare daya ta shiga ta fita da yawan gidan malamanta ta tilastawa ya’aqoub ya rubuta mata takardar saki uku a jare,don bata tunanin har abada zata dawo,don yanzu ba wannan ravuwar bane a gabanta. Manya manyan zawaran dake tashe a media ake damawa dasu ta fannin kasuwanci su suke rudarta, rayuwar ‘yanci da business,fita qasashen qetare a duk sanda suka so,gidan kansu da manyan motocin hawa da sutturu na alfarma vanzu sune babban burinta, sai kuma diyarta meenal wadda Allah ya jarabta da mugun sonta,irin soyayyar da bata taba yiwa wata halitta irinta ba.
Tanason ta tara mata dukiyar da ba zata taba sanin meye talauci ba har garshen tata rayuwar.
Ranar data isa gidan Mahmud da takardar shaidar saki a ranar baiwar Allah shifa na cikin farinciki,karon farko tun bayan karayar arziqinsa ya sake siyan mota,a lokacin yace ta dinga hawa tana hidimar gida,kai yara makaranta da daukosu,da sauran abinda ba’a rasa ba,idan ta kama kuma shima zai karba ya hau ya fita sabgoginsa,kafin ya samu damar siya mata tata.
Sallamar fauziyya kadai a gidan janye da meenal da faggon kaya ya sanya maji cikin matsanancin faduwar gaba,tana fadin cewa sakinta yayi maji ta samu ta daddafa kuiera ta zauna a kai cikin zucivarta tana ian
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” yadda takeji cikin ranta da jikinta a sannan tamkar ita aka saka ba fauziyya ba.
Zaman dai bai sauya zani ba,saima canza salo da fauziyyan tayi, cikin salon wata hikima da iya taku take tatsar kudi daga hannun Mahmud, adadin kudin da ko ita maji wadda ita tasha wahalar kusan komai kawo yanzu bata samesu ba daga jikinsa. Tunda majin ta qyalla idanu ta fuskanci mugun shiru fauziyya ta yi, wanda ya ninka na baya,saboda ayanzun ta samu makiran qawaye gwanaye iya bin malaman tsubbu, sai ta hana kanta sakat da addu’a ba dare ba rana,wanann ya sakawa majin qarfin zuciya da ruhi,duk wani kalar iskanci da fauziyya tayi mata awancan zaman wanna karon ko daya bata dauka ba,wanann ya kawo gagarumin sabani tsakaninta da mahmud, saboda muddin kanason kaga tashin hankalinsa ka taba fauziyya da ‘yar lelenta meenal.
Yarinyar Allah ya zuba mata rashin ji na tsiya,zuwansu ba dadewa amma ta fashe duk wani kayan ado da alatu na falon gidan.
Lokaci galilan kuma ta fiddo dabi’ ar tara mata qawaye a gidan,sabbin qawaye irinta,wadanda suka bawa duniya amana da dukkan qauna,suka kuma riqeta da kyau,wasu ‘yammata ne wasu kuma zawarawa ne kamarta,cikinsu kuma akwai MANSURA wadda tafi kowa zagewa tare da rawar kai.
Da farko falonta ake zuwa a baje,fauziyya ta shiga kitchen cikin taqamarta da jin izza harda yin gayyata ta bare duk abinda takeso tayi musu abincin wadata da alfarma,su bata ko ina a kuma fice abata guri a barta da aiki. Idanunta maji ta rufe, cikin tsayayyar nan tata da dakewa randa suka cika sati guda suna mata tayi musu tasss daga fauziyyan har qawayen,kai fauziyya ta jinjina
“Zakiyi nadama” kamar yadda ta furta kuwa daren ranar majin bata samu cikakken bacci ba,saboda mugun tashin hankalin data haddasa tsakaninta da mahmud,ya gaggaya mata maganganu masu zafi da gori wanda tunda sukayi aure bai taba gaya mata irinsu ba. Ta kwana tana kuka tana kuma gayawa Allah,da safe kuma tayi qoqarin ta tashi kamar komai bai faru ba, abu daya ta sani, ko zasu dawwama suna rikici da Mahmud, ba zata. dauki wasu bagin halayen cin fuska na fauziyya ba,ba ita kadai bama,ace har gawayenta suna da power din shiga mata kitchen suyi yadda sukeso?, bazai yiwu ba, inda ita daya ce zata iya kau da kai, saboda kau da kai da haquri ta sani su kadai ne suka kawota warhaka gidan.
Ba’a jima da gama wannan ba tana zaune da wani yammaci tana gyarawa su toufeeq farce fauziyya ta shigo,tanata baza qamshi hade da taunar chewing gum, tunda taji hayaniyar tarkacen qawayenta na banza marasa da’a ta hada kan yaranta cikin falonta suka zauna a nan
“Key zaki bani” a nutse ta daga kai ta kalleta
“Key na me fa?”
“Na motar yaya na,zan fita unguwa,wani ma yayi rawa bare dan makadi, a bani na mori arziqin dan uwana ko kuma rai ya baci” bacin rai ne ya tasowa maji,yadda take mata magana a tsaitsaye saman kanta,sai ya maida dubanta ga aikin da takeyi
“Bazan bayar ba,rai kuma ya dade bai baci ba,idan kuma kina da qarfin qwata saiki danne ni ki karba”
“Abu me sauqi, kamar qofar dakin naki baqona ne” ta furta tana takawa zuwa hanyar bedroom dinta. Tsam maji ta mige ta kuma daka mata tsawa
“Ke fauziyya!, dakata,kikayi kuskuren shigamin daki wallahi saikin gane sakarya ce ke,ina da kaidi da kuma tuggun da yafi naki ninkin baninkin,saidai kawai banbanci na dake ni din ba jahila bace,nasan sakamakon dake iya biyo bayan aiwatar da sharri tuggu da kuma makirci” tsaiwa tai tana duban idanun maji,ta rasa meye a tattare da matar da har yanzu ta kasa juyuwa a gareta kamar yadda take juya yayanta? ita kadai ce yanzu matsalarta
[02/10, 2:56 pm] Mimah Yusuf: *HUGUMA*
*_TABARMAR KASHI *
Book 02 Page 43
“Zaki bayar ko sai nasa an karbarmin?” Murmushin takaici maii ta sauke
“Har abada ba zaki taba cin galaba a kaina ba fauziyya,yadda baki taba karbar abu a hannuna gaba gadi ba saidai kisa a karbarmiki, har abada a haka zaki qare, ni maji bazan taba sallamamiki komai nawa hannu da hannu ba,saidai kisa na gaba dake din ya karbar miki,zoki wuce ki fitamin a daki” maji ta fada cikin zafinta,abubuwan da fauziyya ke mata tana kau da kai tana tarasu cikin haquri irin nata yau suna taso mata. Ganin ta tsaya zata bata mata lokaci sai kawai tasa hannu ta fincikota baya ta watsata waje ta maida gofar falonta ta rufe.
A sanyaye ta koma gasan carfet ta
zauna,gabanta na tsananta faduwa,batayi dana sanin abinda ta yiwa fauziyya ba,amma yau tabbas ba shakka tasan abinda zai biyo baya a gidan bame dadi bane, wannan ya sanya ta tattara ta gama yanke musu farcen da wuri,ta hadasu sukayi sallar magariba duk da nadeeya dama shi kansa toufeeq din basukai wannan munzalin ba amma ta soma horas da su,saboda haka kawai cikin jikinta takejin ba zatayi dogon zama dasu ba,ta basu abincin dare sukaci ta kaisu dakinsu ta kunna musu cartoon a tv din dake dakinsu tace idan sun gama kalla suyi bacci,sannan ta dawo ta zauna a falo.
Ko minti talatin ba’a cika ba taji shigowarsa gidan,ta runtse idanunta saboda yadda gabanta ke duka tana kiran sunayen Allah tare da jan addu’o’in
“Allahummakhfinihim bima shi’ ita,inna kafainakal mustahzi’een,ya rabbi innalqaumas tad’afuni, wa khadu yaqtulunany fala tushmit biyal’a’ada’a wala taj’alni ma’al gaumizzalimin” a hankali ta dinga maimaitasu qasan ranta idanunta a runtse har zuwa sanda taji ya bankado gofar.
Tana bude idanunta ya fada cikin nasa,a hankali yaji wani abu ya dakeshi, kaifin bala’i da masifar da yakeji suna tafasa cikin ransa sai yaji suna raguwa. Ci gaba tayi da kafeshi da idanu,yayin da fauziyya da idanunta sukayi luhu luhu na kuka wadda ke tsaye a bayansa tace