TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel

TABARMAR KASHI 2 Book 2 Complete Hausa Novel

hajiya qarama ta saki
“Yaro baisan wuta ba sai ya taka,sanin ni wacece bazai miki dadi ba sam,abu daya zan zaya miki,ki samawa kanki lafiya da salama,ki watsar da dukka wata huduba da uwar mijinki tayi miki muddin kinason ki qarasa kwanakinki da suka rage miki a gidan nan lafiya lau” murmushi sãahar ta sakar mata ta juya tana ci gaba da aikinta,zatonta da zarginta akan matar yana sake qarfafa,dukka wani haushi nata dake tattare da adam tana jin a yanzu ta samu damar saukeshi akan hajiya qaraman ne,tayi imanin idan akwai banbanci tsakanin hajiya garama da adam to na jinsi ne kawai ,komai nata ya gama bayyana a idanunta,a yanzun tana jin zargi me garfi da rashin yarda da matar yana shigarta

“Duk wannan ba matsalata bace, matsalata daya kibar rayuwar fadeela ta samu salama,ki daina ci gaba da birkita kwanyar da take neman ta rayu da cikakken hankali da bawa gangar jikin data mallaketa kariya da ingatacciyar rayuwa” Wani mugun shock hajya qarama taji

“What!” Ta furta a rude tana duban fuskar säahar. Kallon tsakiyar idanu sãahar din tayi mata tana gyada mata kai

“Basai kince min eh kinayi ko a’ah ba haka bane, umarni

dava ne zan bayar, a matsayina na matar ubanta…wadda a yanzu take a mazaunin uwa a gareta,daga yau kula da lafiyarta da alhakin shan magungunanta yana wuyana,ban yarda ba ban lamunce kowa va sake baiwa fadeela magani ba, koda uban da ya haifeta ne!” Ta fada da kakkausar murya. Kamar ba zatayi respond ba saita saki murmushi tana duban saahar
“Kada ki qirqiri game din da bazaki iya kai qarshenta ba”

“Ba game nakeyi ba,ba kuma maganarta nakeyi ba, saboda ni din ba ‘yar wasa bace, ina gaya miki magana ne ta zahiri” ta sake jaddadawa hajiya qaraman ba tare data dubeta ba bata kuma fasa aikin da takeyi ba

“Idan kina ganin abune me sauqi yin hakan ki gwada aikatawa” hajiya qarama ta fada tana juyawa ta fita a dakin,don dukka kalaman bakinta sun gama qarewa,abu daya ta sani ya zame mata dole ta fara gamawa da saahar. Sai a yanzu ta fuskanci ba qaramar barazana bace a gareta, ita din wata babbar barazana ce da zata iya wargaza shirinta na shekara da shekaru. Abinda ta yita gudu kenan,ta sake tsanantawa wajen gain toufeeq bai rabi kowacce mace ba sai d’iyarta MEENAL AJI.

Dogon tsaki säahar ta sauke bayan fitar hajiya qaraman, gefan kanta ya saara tadan dafeshi kadan,a duk sanda zata tuna abinda ya shafu rayuwarta a baya saita shiga yanayi,ashe har yanzu akwai ragowar

azzaluman mutane irin adam a duniya? bama cikin jinsin maza ba kawai harda wai mace?,macen da aka santa da rauni? waishin meye dalilin hajiya qarama ne?, me take shiryawa?.

_tambayoyin dani kaina bansan amsarsu ba,saidai lokaci zai bayyana mana komai
[18/09, 7:21 pm] Mimah Yusuf: “HUGUMA*

_TABARMAR KASHI_*

Book 02 page 19

Da gyar ta garasa gyaran dakin, zuwa lokacin kanta ya fara ciwo sosai saboda damuwoyin da take ta tunawa ta kowanne sashe wanne rayuwa fadeela zata fuskanta daga gurin hajiya garama lokacin da zata rayu babu wani a gefanta da zai zame mata garkuwa?, meye shirin hajiya garama ne? me dame ta sarqa a rayuwar wadan nan bayin Allah wanda basu da babanci da marayu?, tsananin tunanin da ya tsananta mata ciwon kenan. A nan dakin fadeela ta duqunqune ta kwanta tana fatan bayan wasu mintuna kan zai sauka. Bata wuce awa guda kwata kwata da dawowar ba taji muryarsu da alama sun dawo, ba jimawa kuwa sai gata ta iso tana kiran sunanta.
Daurewa tayi ta bude idanunta ta zauna sosai, garasowa tavi ta kama hannunta ta riqe

“Anty N gidan uncle sajjad zamuje ni da sister nadeeya,tace na gaya miki, tana cikin mota tana jirana abby ne yace kada mu batawa driver lokaci” murmushin garfin hali ta saki, tana tunawa yau kwanaki shida kenan amma sau daya tak sukayi waya da afifa, abinda bata taba kawowa ba akwai randa zasu dauki kwanaki basuyi waya da bestie dinta ba,saidai bawai hakan yana nufin ta qullaceta ko taji haushinta ba, ko kadan, uzuri kawai ta bata.

“Ki cewa bestie na ina godiya da kulawa,a gaidarmin da uncle sajjad” maimakon taga yarinyar ta mige ta tafi sai ta kama hannunta sosai tana kallonta

“Anty N. kaman baki da lafiya” kai ta girgiza

“Gajiya nayi sai kaina dake dan ciwo kadan” säahar din ta fada tana kallon tsakiyar idanun yarinya zuciyarta na karyewa,tare da mamakin meye tayi da za’a cutar da ita ne? ita ba kudi ko dukiya ba kaman dai ita,ita ba wata babba ba bare ace ta aikata wani abu,bata mallaki komai ba sai rayuwarta da numfashinta da soyayyar makusantanta, a ciki me ake nema?.

“Bari na gayawa sister nadeeya‚mu zauna dake” yarinyar ta fada a karye. Kai ta jinjina mata

“A’ah, karki gayawa kowa,inajin sauqi,kafin ku dawo na warke in sha Allah” saita sakar mata murmushi don bata qwarin gwiwa. Duk da haka yarinyar tana tafe tana waiwayenta har ta fice a dakin, abinda ya sake karya zuciyar säahar din kenan, ta koma ta kwanta tana lumshe idanunta zuciyarta a cunkushe.

Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi yana duban hajiya qarama dake sharar hawaye hadi da fyace majina bayan kukan data sharba, fuskarta na nuna zallar alhini da bacin rai. Har cikin ransa baiji dadin vadda take kuka tana gaya masa sãahar ta zageta ba tare da gaya mata bat iva kula da fadeela ba, daga yau kuma kada ta sake kusanto inda take, magungunanta da komai nata ta haramta mata tabawa saboda wai bata yarda da ita ba.
Iska ya furzar me dumi daga bakinsa

“I will talk to her,stop crying mommy” ya fada calmly. Kai ta girgiza

“Kada kaie ka tareta da zancan toufeeq taga kamar na hadaku rigima kuna zamanku lafiya ” baice mata komai ba,ya dai fara takawa yana barin wajen.

Bayason kuka gaba daya,bare kukanma na babba,babban ma macen data rainesu har suka kawo haka. Amma kuma ta wani gefen zuciyarsa ta kasa nutsuwa da statement na abinda ya farun,haka kawai kuma yakejin zuciyar tasa ta gaza karba. Ba kasafai yake yanke hukunci kai tsaye ba ba tare daya ji ta bakin mutum ba,wannan ya sanya ya wuce sassansa kai tsaye.

A parlor ya samu Joseph yana sake tsaftace falon,duk da bawai yayi datti bane, a’ah wannan tsarinsa ne, ko yana nan ko baya nan,sharar safe data yammaci irin haka. Rusunawa yayi ya gaidashi, ya amsa sama sama ya wuce yana jiyo motsin jacob daga kitchen,shi kuma yaci gaba da aikinsa yana maida earpiece din kunnensa.

A nutse yake takawa cikin hallway din har ya isa bakin gofar dakin, hannu vasa ya murza handle din sannan ya tura qofar baya ya shiga a nutse. A kintse dakin yake,komai fes fes cikin wadatacciyar tsafta da kulawa,ba abinda ke tashi a dakin sai wani nau’in qamshi me sanyi d kwantar da zuciya. Tsaiwa yayi yana qarewa dakin kallo karon farko tunda aka shirya dakin cikin gidan, komai cikin favourite colours dinsa yake ya sauke hannunsa yana takawa zuwa ciki, duk kuwa da ya fuskanci ba kowa cikin dakin. Gefan gadonta ya qarasa ya zauna,haka kawai yaji weather din dakin tayi masa qwarai, ta kuma saukar masa da kasala,ya cire hannuwansa daga aljihun wandonsa da zummar dorawa saman gadon,sai yaji ya dora saman wani abu ne taushi da santsi. Waiwayawa yayi yana duban gurin. Panties dinta ne da braziers dukkansu farare gal gal kamar hannu bai taba tabasu ba. Janye hannun nasa yayi da sauri tsigar jikinsa tana zubawa,sai ya kauda kansa,idanun nasa suka sauka saman bedside drawer dinta. Hannunsa ya miqa ya dauki litattafan da suke kai na farko al-qur’ani ne ya maidashi ya ajjiye, na biyun littafin azkar dinta ne,ya buda ya karanta wasu daga cikin addu’o’in da suke ciki na wasu mintuna sannan suma ya mayar ya ajiyeshi,na ukun kuma MY DIARY shine abinda ke rubuce a fuskar littafin da manyan harufa da aka yiwa aloo da ruman azurta. Har ye maida ya ajiye ya mige sa ya koma ye sake dauka, ya bude shafin farko. Rubutu ne ekin tsari da daukan hankali kamar haka

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected